Abnur Complete Hausa Novel
Reading file: Abnur_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 2 of 24
*page* 2
Tunda ya fito gidan yake yawo a cikin gari yama rasa ta ina zai fara neman NOOR ,ina zata je ,wata sani bayan shi, ya tabbata bata da inda zata je da ya wuce gidansa ,har yamma yana gararamba.
Gefen titi ya samu yayi parking ya jingina kansa da steeryn motan, ya rasa ina zai nufa don neman ta, É—ago kanshi yayi da idanuwansa da suka gama rinewa sukayi jajir ya jingina kansa da seat É—in motar .
Why Noor? ,am I really that bad to you da kika zaɓi ki barni? ,do you have any idea halin da nake ciki yanxu ?please Noor ki dawo gareni i promise I will mend my ways ,na miki alƙawari zan gyara please Noor.
Da ƙyar ya samu ya kai kanshi gida, har jiri yake ji dan rabonsa da abinci tunda ya fahimci Noor bata gidan .
Baibi takan kowa ba har bodyguards É—in da suke gaishesa, ko takalmansa bai cire ba ya faÉ—a kan gadon katafaren É—akinnasa yana kallon saman É—akin, yana sake zurfi a tunanin ina zata shiga a garin Abuja .
Kamal ne ya fito daga ɗakin ,mahaifiyarsa na biye dashi ,zama tayi a tsakar gidan shima yaja ƙaramar kujera ya zauna yana fuskantar ta yace ,"umma da muka fita dama bata ce miki komai bane? ".
ÄŽan shiru umma tayi kamar baxatayi magana ba sai kuma tace," wlhy kamal nayi iya tambaya amma batace min komai ba, banda kuka babu abinda takeyi, yarinyar tana da babbar damuwa sosai ,amma rashin sanin daga ina ta fito shine babbar damuwar ".
Kamal yace ,"hakane amma gaskiya tana buƙatar taimako sosai ,kawai mu bari muga kwana biyu ko xata ji sauƙin abinda yake damunta, sai tayi mana bayani" .
Shiru umma tayi sai kuma tace "toh Allah dai ya kyauta gata kyakkyawa wlhy kuma daga dukkan alamu yar gidan masu kuɗi ce ,"kamal ya miƙe yana faɗin," wlhy nima haka na gani".
Fita yayi daga gidan dan yanaso ya je gidansu Abdul, dan yanaso ya amso kuɗin sa dake wajensa dan komai na gidannasu ya ƙare kuma gashi amfanin gona bai nuna ba bare ,
har ƙofar gidan yaje ya aika yaro ya kira masa shi, a ƙasan wani bishiya suka zauna Abdul ya kallesa yace "kuɗinka ko kamal" .
Kamal yayi murmushi yace "saboda bana zuwa wajen ka sai idan inason kuɗi koh ",Abdul yayi dariya yace "wlhy ba haka bane kawai dai nasan halin garin ne yadda babu kuɗi", shiru kamal yayi sai kuma yace "wlhy Abdul banso na tambayeka ba amma wlhy ina matuƙar buƙatarsu ".
Duk sukayi shiru kafin Abdul ya nisa yace" wlhy kamal bandashi nima ",shiru yayi sai kuma yace, "babu damuwa karka damu wlhy", daga haka ya miƙe yana faɗin "to sai mun haɗu anjima da daddare", Abdul ma ya miƙe yace "ba damuwa nagode kamal ".
Daga haka ya juya yana ta tunane tunane har ya iso a tsakar gidan ya samu umma tana ƙoƙarin shiga kitchen kusa da ita yaje yace," umma dama naje wajen Abdul ne ko zan samu kuɗin wajensa amma bansamu ba ",umma ta nisa tace ," to Allah ya kyauta amma dai yau yaza ayi kenan, yanzu babanka ma ya dawo bai samuba ,wlhy gashi muna da baƙuwa " .
D'an murmushi yayi yace "yanzu dai akwai wani É—an canji a jikina idan na fita zan nemo mana abinda zamuci yau, amma dai gobe sai yadda Allah yayi da mu", duk juyawa sukayin jin motsin mutum a tsaye suka ganta tana kallonsu umma tace "ah ah Noor Kin fito ".
Girgiza mata kai tayi tace ,"umma inaso zan shiga bayi ne," da sauri umma tace "ayya gashi can bari na saka miki ruwa a buta ",da sauri ta karɓi butan hannun umma tana faɗin "laa umma karki damu dan Allah".
Ta wuce wajen randar ta É—ebi ruwan umma tace ."ga ruwan zafi idan zaki surka ,tace "toh" cup ta É—auka ta É—ebi ruwan ta wuce bayi ,
Umma da kamal na nan zaune ta fito ta ajiye butan sannan ta nufi wajen tabarmar da taga sun shimfiÉ—a sun zauna.
Itama zama tayi sai kuma tace "umma dan Allah kuyi haƙuri da shiga rayuwarku da nayi, amma ina neman alfarma a wajenku dan Allah ina so in zauna da ku na wasu kwanaki, nasan ya dace na faɗamuku abinda ya raboni da gida , amma na muku alƙwari zan fada muku insha Allahu ".
Aai da ta ɗan yi shiru sai kuma ta sanya hannuta ta ciro ɗan kunnen gold ɗin dake kunnenta ta miƙama kamal tace "yaya kamal gashi ina so dan Allah ka siyarmin da wannan ɗan kunnen ".
Sai da ya kalleta ya kalli ɗan kunnen sai kuma yasa hannu ya karɓa yana kallo yace," tabb Gwal ne fa".
Tayi shiru tana kallonsa yace," sai dai bazan iya sayarwa a garinnan ba , sai dai gobe insha Allahu , tunda ranar kasuwan cikin garin kusa damu ne , su suna siya sai inje can na sayar miki ," ahankali tace "nagode sosai Allah ya saka muku da alkhairinsa ", duk suka amsa da ameen .
Washe gari kamar yadda sukayi haka ya shiga cikin gari ya sayar , duk da dai an masa an siya ba yadda kuɗin sa ya keba ganin cewa ɗan ƙauye ne, haka ya ɗaure kuɗin a mayafi ya dawo gida, a tsakar gida ya samesu suna hira da umma ya zauna shima yana warware wa ya miƙa mata.
"Yace gashi Noor ",ta karɓa tana murmushi ta ƙirga kuɗin sai kawai ta girgiza kai sannan ta kama hannun umma ta danƙa mata kuɗin.
Dubu biyar kaɗai ta ɗauka a kuɗin umma ta zare ido tana kallonta girgiza kai tayi tana kallon umma tace "umma dan Allah karkice komai kiyi haƙuri jiya naji hirarku da kamal dan Allah ku karɓi kuɗinnan ,na baku ne a matsayin yan uwana saboda kunyi min taimakon da bazan taɓa mancewa daku ba, kunyi min taimako alokacin da nake tsananin buƙatarsa".
Umma rungumeta kawai tayi tana sake jin son yarinyar har ranta, tana sake kwaÉ—aituwa da son jin dalilin ta na barin gida , a hankali ta share hawayen ta tace.
" Ni ban san me ya raboki da gida ba Noor, amma ke É—in alkhairi ce a wajenmu, kuma mungode Allah ya saka miki da alkhairi kuma ya fitar da ke a cikin duk matsalolin da rayuwarki ke ciki".
Shidai Kamal kallonta kawai yakeyi sai kuma yace "Noor kuÉ—innan", shhhh tace masa "yaya kamal pleaaaaase karkace komai".
Nurmushi kawai yayi yace "to shikenan nayi shiru Allah ya saka", daga haka suka ci gaba da hirarsu tana samusu baki jefi jefi, but hankalinta da tunaninta gabaÉ—aya suna wani wajen daban.
Wasu sabbin hawayene suka cika idanunta, she is sure baida buƙatarta a rayuwarsa, kuma bayida asara idan har bata tare dashi , he never loved her but tayima kanta alƙawari koda mai kama da ita bazai sake gani ba.
zatayi nisa dashi irin nisan da bazai taɓa cinmata ba, a hankali ta sanya hannu ta share hawayen tana ƙaƙalo murmushi, ganin umma tana kallonta sai kuma ta miƙe ta nufi ɗaki duk suka bita da kallo .
🥱🥱🥱🥱🥱🥱
#maimoon
💖 **ABNUR**💖
*By* *maimoon* 🤓
*Elegant* *online* *writers*
**Freebook**
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.