Abnur Complete Hausa Novel
Reading file: Abnur_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 13 of 24
*Page* *14*
ÆŠagowa yayi karaf suka haÉ—a ido da ita, da sauri ta sunkuyar da kanta, sakamakon hararar da ya watsa mata,
miƙewa yayi yana faɗin,
"Maami, You really scared me"ya faɗa yana ɓata fuska, dariya Maami tayi tana faɗin,
"You know Bai kamata na sauƙo yanzu bama, but I have no choise, tunda kun haɗani da Abbu"
Dariya yayi sosai yana faɗin, "i trust Abbu shiyasa right away na faɗa masa, gashi komai ya wuce cikin sauƙi"
Ita dai Noor ta kasa ɗauke idanunta akansa, yadda ya ke dariyan sai ya sa ta shagala sosai da kallon sa, dan bata taɓa ganin ya na farinciki haka ba.
Sake haÉ—a ido sukayi dashi, ganin ta na kallonsa ya sa shi jan kumatun ta ya na faÉ—in,
"kallon Fah baby!"
Sai da ta kusa ƙwarewa, saboda yadda abin ya zo mata a bazata, Maami tayi murmushi tana faɗin,
"Wayene É—azu ya ke cewa 'bana sonta kuma bazan sota ba nikam"
sosa kai ya yi yana murmushi,
"so you take me as a fool, ta ya ma za'ayi ba zaka so wannan kyakkyawar yarinyar ba, she is more like Arab don't you see?
Itadai ta kasa cewa komai, sai kallon sa take da zallar mamaki.
Miƙewa ya yi ya na faɗin,
"Maami, seriously am starving"
ya faÉ—a ya marairaicewa, Maami ta kalli Noor da ke jikinta har sannan,tace
"daughter your husband is starving" a hankali ta É—ago ta kalleshi, sai ya kashe mata ido, ya shafa cikinsa.
Miƙewa kawai ta yi ta ce"Maami i will arrange the table sai mu ci abinci, kema bakici komai ba"
tana faÉ—in haka ta juya ta fice a É—akin, da ido ya bita sai kuma ya shafa kansa ya yi murmushi.
Maami ta ce, "zauna Ina son magana da kai"
Zama ya yi a ƙasa dai dai ƙafafuwan ta, ya kwantar da kansa akan cinyar ta, a hankali ya furta
"ina jinki Maami na"
Hannunta ta sa a kansa ta na masa head massage a hankali,lumshe idonsa ya yi saboda yadda yakejin É—aÉ—in yadda takeyi É—in
A hankali ta ce
"what about her family Habibi,ya zamuyi kenan"
Shiru ya yi sai kuma yace
"Maami i don't know much, but ita zata faÉ—a mana ai koh?,
Ki bari idan kin huta sai muyi maganan da ita"
Jinjina kai tayi ta na faÉ—in "Ok I think it will be better"
Sallama tayi ta shigo É—akin, Maami tace
"daughter sannu fah"
Girgiza kai kawai ta yi tana faÉ—in "the table is ready Maami."
Bai so ya kalleta ba, but Sam zuciyarsa ta kasa bashi haÉ—in kai, É—agowa yayi ya na kallonta suna haÉ—a ido ya sake galla mata harara da yasa tayi saurin juyawa zata bar É—akin
Maami ma miƙewa tayi tabi bayanta kafin shima yabi bayansu zuwa dining hall ɗin.
Sai da ta yi serving Maami, sannan ta saka nata ta ja kujera ta zauna, dan tana tsoron ta saka masa, ya gwaleta a gaban Maami
Har ta saka spoon, zata fara ci, ta ji ya ce
"Baby kin manta da Ni ne,I told you am starving"
Da sauri ta ajiye spoon É—in tana kallonsa,
Maami dai abincinta kawai take ci, bata kula su ba,
Plate ta ɗauka zatayi serving ɗin sa ya yi saurin riƙe hannuwan ta, ya ce "barshi kawai I will eat with you"
Ya faɗa ya na matso da kujerar sa kusa da nata, baki a sake take kallonsa ita iya saninta ko a guri ɗaya basu taɓa cin abinci ba bare plate ɗaya.
Ba tace komai ba ta koma ta zauna, tana tsakuran abincin, shima kaɗan yaci ya ajiye spoon ɗin, itama ajiye nata spoon ɗin tayi, ta tsiyaya masa ruwa, ƙarba yayi ba tare da yace komai ba, sai da yasha kaɗan ya ajiye cup ɗin sannan ya miƙe
"Habibi har ka gama kenan"
Maami ta tambaya itama ta na zarar tissue
"Yeap Ina so zan É—an fita but I won't be long"
"Okay take care"
Bai ce komai ba ya juya ya fice, ita dai Noor da ido take binsa, ta gagara gane shi wani irin mutum ne, sai ta yi ƙoƙarin gane halinsa sai ya sake canzawa completely.
Landline É—in kitchen ta Kira akan suzo suyi clearing É—in table É—in kafin tabi bayan Maami da ta wuce sama.
É—akinta ta wuce dan yin sallah, sannan ta bar Maami ta huta, a hankali ta zauna a gefen gado bayan ta idar da sallah, tana tunanin abubuwan da yayi ta yi É—azu, sai kawai tayi murmushi,
miƙewa tayi taje gaban madubi ta na kallon kanta, wasu hawaye taji sun cicciko idanunta, cikin kukan ta shiga furta
"Abba ina ka tafi ka barmu Ni da Nenne, gashi Nenne ta rasu ta barni Ni kaÉ—ai, Nenne ta rasu ba tare da ka nemi gafarar ta ba, me ya hanaka dawowa garemu Abbana."
Sai kuma ta share hawayenta ta na sake faÉ—in,
"bana buƙatarka har abada, dan dama bansan soyayyarka ba ban taso naji ɗumin kaba, sannan bansan koda kamannin ka ba,"
Kuka ne ya sarƙe ta ta zube a wajen tana cigaba da kukan gwanin tausayi.
Yasira jin shiru shiru, bata sake jin wani hayaniya ba ya sata fitowa falo, a lokacin taga Sir Zannur yana fita a gidan, da sauri ta ƙara sa ƙofar dining hall ɗin tana leƙawa, ganin Noor da Maami suna cin abinci tare, ba tare da wani alama na tashin hankali ba, ya sata ja da baya, a hankali take ja da baya kafin ta ruga da gudu ta koma ɗakinsu, durƙushewa tayi a wajen tana sakin kuka mai sauti, sai kuma ta shiga sumbatu cikin kukan tana faɗin,
" wallahi tallahi ina sonka, kuma bazan taɓa yarda na rasa ka ba, kai ne rayuwata, Allah ne ya ɗaura min sonka, kuma bazan taɓa haƙura da kai ba, kamar yadda bazan zauna da kai tare da ko wace mace ba, zan iya aikata koma miye ne dan na mallake ka, koda kuwa ta kama da wani ya bar duniyan nan ne"
sai kuma ta share hawayenta tana murmushi ta cigaba da sumbatu kamar zautacciya
"ai nayi zaton zai zo min da sauƙi ne shiyasa na kira Maami na faɗa mata, amma yanzu naga alama babban shiri kake buƙata Sir Zannur wallahi, wallahi, wallahi, duk wanda ya shiga tsakanina da farin cikina kwanan shine ya ƙare ta faɗa tana miƙewa a zabure kamar mahaukaciya.
Su dai su Asabe basu san me ake ciki ba, suna can baya suna wanki, suna hirar su, gabaÉ—aya basu ma san da zuwan Maami ba bare haukar Yasira.
*******
*_*_
AL RAJWA VILLA'S, AJMAN, DUBAI_*_*
Zaune yake a katafaren falon, ya jingina da kujera, da alama yayi matuƙar zurfi a tunani.
dafa shi da yaji anyi yasa ya É—ago idanunsa da har sun kaÉ—a sunyi jaa, farin Balarabe ne kyakkyawan gaske mai cikar kamala sosai.
Ammi, cikin harshen larabci, ta soma faÉ—in,
"me yasa bazaka daina uzura ma kanka ba mijina." kallon farar balarabiyar yayi ba tare da ya ce komai ba ya miƙe tsam ya bar mata falon, wani ɗaki ya shiga inda kana gani kasan na zane zane ne,
ƙara sawa yayi gaban board ɗin zanen, ya ɗau brush ɗaya ya saka a paint, a hankali ya lumshe idanunsa sai kuma ya buɗe ya shiga zane, wasu siraran hawaye na sauƙa a kan fuskarsa,
Ammi ce ta sake shigowa ta tsaya ranta a ɓace ta ke faɗin
"yanzu a tunaninka wannan shine abinda ya dace ka dinga yi koh?, ka zana hoto ɗaya a iya lissafina yafi ɗari, kullum sai ka zana, meyasa bazaka sauwaƙema kanka, nima ka dube Ni ba?"
ÆŠagowa yayi, ya kalleta sai kuma yace
"Please nadiya, I need a break"
Daga haka ya fice ya koma É—akinsa yana rufewa da makulli
Ƙwafa tayi,tana jin zuciyarta na suya, a fusace ta ƙarasa gaban allon ta yi wurgi dashi, tana faɗin,
"na tsaneki, ya zan yi da ke?, kin zame min annoba, kin kasa barina in ji daÉ—in rayuwata."
sai kuma ta juya a fusace ta bar É—akin tana huci.
Falonta ta wuce, inda Æ´an mata biyu da namiji É—aya ke zaune suna video game, babbar cikinsu bazata fi 15 ba sai mai bi mata wacce ita ma bazata fi 10 ba namijin kuwa bazai fi 7 ba,
A fusace tace, "farhaana, ku wuce falonku, ku barmin falona bana son hayaniya yanzu"
Da sauri farhaana tace, "Ammi Are You ok, ke da papi ko?"
Bata kulata ba, sai zama da tayi ta riƙe kanta da duka hannuwanta, da sauri farhaana ta kora ƙannen nata suka wuce part ɗin su, tana tunanin sai yaushe papi zai koma kamar kowa?, sai yaushe zai zauna tare da su kamar yadda ko wani uba yake zama da ƴaƴansu?
************
Tunda Maami ta zo, Zannur ya canza mata,
gabaÉ—aya Noor ta rasa gane ina ya dosa, a gaban Maami kulawa yake bata da har take jin dama har zuciyansa yake mata hakan, amma inaa, bayan idon Maami banda harara babu abinda ke haÉ—ashi da ita, a rashin sanin ta kuwa duk wani shiga da fitanta akan idanunsa takeyi, dan kuwa yana iya yini yana kallon ta a laptop É—in sa, TaufeeÆ™ ya tafi Bangaladash saboda wakiltar Zannur akan wasu ayyukansa,hakan yasa bata ganinsa, Asabe da Amina kuwa, kullum cikin É—ebe mata kewa da sakata dariya suke, Yasira ta sake kamar babu komai a zuciyarta, but ita kaÉ—ai ta san gagarumin abinda take shiryawa wanda zai ruguza farin cikin duka Æ´an gidan.
Satin Maami biyu ta koma Dubai, da kewan Habibi da kuma Noor, dan kuwa shaƙuwa sosai ya shiga tsakaninsu, ta sake wayar mata da kai akan abubuwa da dama, sannan kafin ta tafi ta sa an nemo mata malamai har biyu na islamiyya da boko tana cigaba da karatunta, a halin yanzu Noor Bata da wata damuwa da ya shige ta Zannur, amma shiɗinma sam bata saka shi a rai ba bare ya hanata walwala.
12 ga watan August dai dai da cikar Noor shekara ɗaya da wata huɗu a gidan, shine ranar da abubuwa suka fara canzawa, ƙaddarar da bazata taɓa mantawa ba, da duk wani wanda yake gidan ya faru wanda yayi sanadiyar ruguza duk wani hasashen farincikin Noor.................
Kuyi haƙuri page ɗin yau yayi kaɗan, bana ɗan jin daɗi ne shiyasa, Amin uzuri
Maimoon#
*💖ABNUR💖*
*By* *maimoon*
*Elegant* *online* *writers* 📚📖
*Free* *book*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.