Complete Hausa Novels

Abnur Complete Hausa Novel

Reading file: Abnur_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 5 of 24

*Page* *5*

*Wednesday*

*Abuja Nigeria*

Ƙarfe 7:30 dai dai, ya fito daga Gym ɗin dake cikin gidan ,gaba ɗaya ya gama haɗa zufa,Gym wears ne a jikinsa na kamfanin Nike,Wanda ya karɓesa matuƙa kamar dan kwalliya ya sanyasu, a tsanake yake haura steps ɗin duk da kuwa sauri ya keyi ,dan yau zai wuce Kaduna,

Amina,Asabe,da kuma,Yasira da suka ɗan buɗe ƙofar kitchen ɗin ,suka bisa da kallon, ajiyar zuciya suka sauƙe a tare,ganin ya gama haurawa,

Amina tace"wato kuɗi yayi ne Wallahi, shidai Sir a rayuwar sa ba shida matsalar komai,na farko ga kyau,ga kuɗi, ga iya shiga mai kyau,ke Ni komai yasa gani nake kawai dan kwalliya ya sa su" Asabe ta karɓe tana faɗin "hmm! kawai mata ta rage masa Wallahi shi ke nan ya cika cif-cif" Yasira tace"taɓ Sir kam ko zaiyi aure ba yanzu ba wallahi" Amina ta amshe "to sannu Maami!, kika sani?,wataƙila ma munkusa shan biki ko ba haka ba Asabe?" ta faɗa tana tafawa da Asabe , "aikuwa wallahi idan zaiyi ma ba sani zamuyi ba sai dai muji guɗar ƴan kawo amarya" Asabe ta faɗa tana ƙarasa wanke kwanukan dake cikin sink ɗin ,

Yasira dai bata sake cewa komai ba ta fice a kitchen ɗin tana wani ɓata rai ,Asabe ta sake tuntsirewa da dariya tana faɗin"kai kaji wahalalliya,wallahi wahala ce Bata isheta ba" Amina tayi ƙwafa tana faɗin "atoh ai ita taga zata iya" suka cigaba da wanke wanke suna taɓa hira.

Wanka ya fito ,a gaggauce ya shirya cikin riga da wando na kamfanin _LOUIS_ _VUITTON_ sai da ya gyara sumarsa yanda ya keso,sannan ya gyara gemu da sajensa wanda duk wanda yasan larabawan Dubai yasan yadda Gemu da sajansu yake,sai da ya gama ɓata lokaci a gyaran sannan ya ɗau perfume ɗinsa na _SHUMUKH_ ya feshe jikinsa da shi ,wani button ya danna ,wani drawer ya buɗe wanda takalmansa suke jere ,na different companies _,WHITE ADRIAN ITALIAN SHOES_ ya zaro ya sanya a ƙafafunsa ,ya ƙara danna wani button ɗin wani mini drawer ya buɗe ,Agogo ya cire guda ɗaya ya sanya sannan ya kwashi wayoyinsa da jakan laptop ɗinsa ya fice a ɗakin,

Da sauri bodyguard ɗinsa guda ɗaya ya ƙaraso ya karɓi kayan hannunsa yana gaishesa, Taufeeƙ dake tsaye ya ƙaraso shima tare da faɗin"morning Sir". "morning "ya amsa a taƙaice ,buɗe masa mota yayi ya shiga baya ,shikuma ya shiga gaba,ɗaya daga cikin bodyguard ɗin ya shiga mazaunin driver ,sauran kuma suka shiga wata mota daban ,suka fice a gidan,

Amina,da Asabe dake leƙen window suka sauƙe Amina tana faɗin ,"to sai kuma sanda muka ganshi, Aljanun sun motsa " Asabe ta ce"kee bari a jiki babu ruwana wallahi" Amina tace "ke ma ai kinsani irin wannan fitar da yayi tunda kika ga Sir Taufeeƙ ,to zasu je yawon ɗauke ɗauke ne ,ai dama tunda naga Sir Taufeeƙ ya zo jiya ya haɗa abubuwan ɗaukan hoto da akwati da komai Na Sir ,nasan to sai kuma mun gansu"

Asabe tace "to ai hutareren mu " Amina tace "wallahi Fah " suka koma kitchen, dan dama tun sauƙowar sa sukaji shine yana fita suka fito su leƙa .

Kasancewar tsakanin Abuja da Kaduna ,ba wani nisa bane ya sa su tafiyan da mota, ƙarfe biyu saura suna cikin Kaduna, hotel suka wuce, wanda dama Taufeeƙ ya gama shirya komai ,sai da suka tsaya sukayi sallah ,sannan suka ƙarasa , a hankali ya juyo ya kalli Taufeeƙ yace"tomorrow by 8 "zamu tafi ,make sure by 7 waɗancan sun koma Abuja ,"
a ladabce TaufeeÆ™ yace "Sir your security matters, da dai anje da su for security purposes".
"just do as are told mr" ya faÉ—a ba tare da ya juyoba ,
"pardon Sir ,your wish is always my command , za'a yi kamar yadda kace"

bai sake cewa komai ba har suka iso ƙofar ɗakin nasa ,da sauri Taufeeƙ ya sa katin ,ƙofan ta buɗe ,sai da ya tabbatar ya gama masa duk wani abun da zai buƙata ,kafin ya bar ɗakin ,ya nufi nashi ɗakin dan shima yana buƙatar hutu.

Washe gari tun bakwai ya sallami bodyguards ɗin suka koma Abuja, kamar yadda Zannur ya buƙata ,

ƙarfe takwas dai-dai ya fito daga ɗakin, ya shirya tsaf cikin ƙananan kaya, kansa sanye da facing cap sai shade a idanunsa , Snickers ne a ƙafansa na kanfanin Adidas ,a hankali yake tafiya Taufeeƙ na biye dashi bayan yaje ya yi checking out daga hotel ɗin ,har packing space ɗin, "pass the key" ya faɗa a taƙaice"

Taufeeƙ ya miƙa masa key ɗin a zuciyarsa yana faɗin "shi zaiyi driving kenan" mazaunin driver ya shiga ,sai da Taufeeƙ ya gama saka jakansu da kuma jakan kayan cameras da zasu buƙata, a motan,sannan ya buɗe mazaunin mai zaman banza ya zauna ,

warming motar yayi sannan ya tada ya fice a hotel É—in, map TaufeeÆ™ ya buÉ—e ya ajiye a gaban motan ,yana ganin directions É—in daya kamata subi,

suna fara shiga garin yayi parking motar ya sauƙa , Taufeeƙ ma ya sauƙa , makullin ya wurga masa ya caɓe ,shikuma ya buɗe bayan motan Camera ya ɗauka ya haɗa komai nata sannan ya koma wajen mai zaman banza , Taufeeƙ yayi murmushi yana shiga mazaunin driver ,a zuciyarsa yana tunanin da alama za'a samu abinda a ke so a wannan garin.

Basu wani ƙara tafiya mai yawa ba sukaga hanya ta ƙare mota bazata iya bi ta shiga ba ,sauƙa Taufeeƙ yayi ya dudduba sai kuma ya dawo yana faɗin "Sir i don't think akwai hanya fah da mota zai ƙarasa, sauƙe Camera dake idonsa yayi yace "so!?"
Taufeeƙ ya sosa ƙeya ,yace "I guess da ƙafa zamu ƙara sa ,ina ganin ƙauyen is just a little bit ahead,

murmushi Zannur yayi ganin yayi capturing butterfly ɗin da yake ɗauka ,ba tare da yace komai ba ya sauƙa a motar da sauri Taufeeƙ yace "Sir zan kira faruƙ yana cikin Kaduna sai ya zo ya juya da motar ,gyaɗa masa kai kawai yayi yayi gaba yana sake kallon ɗan hanyan da zasu wuce ɗin.

A firgice ta farka daga baccin daya kwashe ta a zaune ,ta miƙe da sauri tana leƙa tsakar gida ,hasken data gani tarr ne ya sata komawa ɗakin da sauri ta ɗauki jakan makarantar ta ,da roban abincinta tasa goran ruwanta a jaka ,sauri sauri ta fito dan tasan yauma tayi latti,tun asuba ta shirya dan kartayi latti amma gashi sai da tayi latti ,ɗakin Nenne ta leƙa ,taga bata ciki,"to ina Nenne taje da sassafe nan" ganin batada amsa gashi tana sake ɓata lokaci ya saka tai saurin fita a gidan ,

sauri sauri take tafiya ,dan dai makarantar da ɗan tazara,ganin saurin bazai mata ba yasata kwasa da gudu , Allah Allah take ta isa ,saboda yau ne za'a faɗi mutum ɗaya a duk cikin makarantar da ya samu scholarship ɗin zuwa cikin Kaduna karatu , gwamnati zata ɗauki nauyinsa saboda hazaƙarsa ,

Tun da ta shigo taga kowa na aji ,aji ta wuce tana sanɗa a ƙofar ajin ta tsaya ganin akwai Malama a ciki ,sai da taga Malamar ta fara rubutu tukun tayi sauri ta shigo , ta zauna a baya ,sannan ta miƙa ma na kusa da ita jakarta ,a haka sukayi ta passing passing ɗin jakar har kujeran gaba ,wanda shine wajen zamanta ,da dabara ta dinga canza wajen zama har ta iso gaba,tana shirin zama kawai Malaman ta jiyo ,

"Noor!" Malaman ta Kira sunan ta ,da sauri ta juyo " Malaman tace "You Are late again ,right!?" da sauri acikin harshen turanci ,dan kar ta ƙara ma kanta laifi idan tayi venacular tace, "dan Allah Malama kiyi haƙuri ,wallahi makara nayi" ,juyawa Malaman tayi ta cigaba da rubutu tana faɗin "zo ki tsaya a gaban Allo har sai na gama in faɗa miki hukuncinki" tsaya wa tayi tana marairaicewa ,Malama ta sake cewa " kafin na ƙirga uku na ganki a gaban Allo Noor,ɗaya.. ,biyu.." kafin tace uku tayi saurin ƙarasawa gaban Allon ta tsaya, tana kallon duka ƴan ajin,

sai da Malama ta ƙara sa rubutun tukun tace "toh yanzu kafin a fara darasi, ina so in sanar da ku ,mutum ɗaya a cikin makarantar nan da Gwamnati ta ɗauki Nauyin karatunta ,bakowa bace face......."

Duk ɗalibai suka zuba mata ido ,sai da ta ɗan yi murmushi kafin tace " _NA'IMA_ _RAZAƘ_ _ABDULKARIM_ wacce kuka fi sani da _NOOR_ " .

Duk student ɗin suka hau murna dan dai sun san ,she deserve it ,itakam ta kasa ƙarasawa ma ,sai da Malamar tace mata "congratulations" tukun ta ƙarasa da sauri ta rungume ta kawai ta fashe da kuka,

Malamar ta shafa kanta tace "karki damu You deserve it Noor,ni dama nayi tunanin haka"

a hankali ta É—ago tace" Malama dan Allah ina so zan tafi gida" , "kije badamuwa gobe sai ki dawo congratulations once again" da sauri ta juya Æ´an aji na ta mata murna ,tana binsu da murmushi ,

sai da ta fita daga makarantar tukun tayi wani tsalle tana faÉ—in "Nenne na samo scholarship zan tafi birni ,ita kaÉ—ai take surutunta tana Allah,Allah ta isa wajen Nenne,

"Baiwar Allah" taji an mata magana da sauri ta juya tana kallon wanda yake mata maganan ,saida ta runtse idanunta ta buÉ—e ganin É—an birni ,a zuciyarta tana faÉ—in ,kar dai tun yanzu ne za'a tafi da ita karatun ,ah ah gaskiya ita fah idan ba da Nenne zasu tafi tare ba ,bazata je ba,

"Baiwar Allah" TaufeeÆ™ ya sake faÉ—a yana kallonta yadda yaga ta wani rufe idanunta da sauri ta buÉ—e idanunta ta kallesa ,ta marairaice tafara faÉ—in ,"dan Allah ba yanzu ba ,ai Ni bansan yau za'a tafi ba ,na É—auka sai na shirya dan Allah ku bari na fara É—auko Nenne sai mu tafi tare,

kallonta kawai yakeyi har ta gama tukun yace " baiwar Allah tambaya nakeyi, a garinnan ko akwai wani waje da za'a iya biya a kwana "

shiru tayi sai kuma ta watsa hannunta tace "oho" "kina nufin baki sani ba"
"Eh" ta faÉ—a tana juyawa ta cigaba da tafiya "keeeee" taji an faÉ—a da wata Muryar da ta tilasta mata juyowa tagako waye dan ta tabbata ba shi ne wanda ya tambayeta ba.

#maimoon

*ABNUR*

*By* *maimoon* 🤓

*Elegant* *online* *writers* 📚📖

*Free* *book*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.