Complete Hausa Novels

Abnur Complete Hausa Novel

Reading file: Abnur_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 18 of 24

*Page 19*

*Two days later*

Noor ne ta fito daga kitchen, hannunta ɗauke da kofin roba, tana sanye da abaya kalar baƙi, wanda khamal da kansa ya shiga cikin gari ya siyo mata da ATM ɗin ta, dan dama ta manta da shi ne ya sa har ta siyar da ɗan kunnenta.

Waje ta fito, ta samu waje ta zauna, a kusa da umma dake tsintar shinkafa, ajiye cup É—in tayi ta shiga taya umma tsintan suna hira sama-sama.

Khamal ne ya shigo, da sallama, ya ja kujera ya zauna yana faÉ—in

"Sannu da aiki Umma"

"Yauwa sannu khamal ya gonan dai?"

"Alhamdulillah wallahi, ya gida?"

"Lafiya ƙalau"

A hankali Noor tace

"ina wuni yaya khamal"

"Lafiya"

ya amsa a taƙaice kafin ya miƙe yana faɗin

"Umma bari naje wajen Abdul"

"To sai ka dawo"

Sai da ya fice a gidan, kafin umma da maida dubanta ga Noor dake cigaba da tsintan shinkafan.

"Noor!"

"Na'am Umma" ta faÉ—a with full concentration.

Bakya kewan mijinki?, bakya tunanin kina so ki gansa?, Noor zaman aure da kika gani, wani abune mai matuƙar buƙatar haƙuri, da soyayyah, Noor ke mace ce, bakida inda yafi gidan mijinki daraja a wajenki.

Kuka Noor ta fashe da shi ba tare da ta bari Umma ta ƙarasa magananta ba.

Umma Ni bana sonsa, Umma ko ina sonsa zan hakura da shi, saboda idan har babu yarda to babu soyayya, me yasa bazai yarda da Ni ba?, meyasa zai yi tunanin zan iya aikata hakan ga Taufeeƙ?, laifin me yamin da har zan aikata masa haka?, umma na riga na yanke hukunci, banason komawa garesa har abada, idan kuma har kun gaji da zama da Ni ne please kuyi haƙuri."

ta faÉ—a tana cigaba da kuka

"Batun mun gaji da ke bai taso ba Noor, kawai ina faÉ—a miki ne a matsayinki na Æ´ata, dan ko da ace Ni na haife ki haka zan faÉ—a miki."

Cikin kuka Noor tace

"nagode Umma, amma dan Allah banaso na koma ga Zannur, please ki barni a nan."

Daga haka ta miƙe ta wuce ɗaki, Umma ta bita da kallo tana jinjina kai.

Baba da shigowar sa kenan ya tarar suna maganan, bai ce komai ba ya wuce É—aki.

Miƙewa umma tayi tabi bayansa, a zaune ta samesa akan ɗan gadonsu yana matsa ƙafarsa da take ɗan masa ciwo.

Da sauri ta ƙaraso ta tsuguna ta sa hannu tana matsa masa ƙafafun,

"sannu Malam, ƙafar ce take ciwo har yanzu?"

"Eh wallahi Aisha, Amma ba sosai ba, Allah ya miki albarka."

"Ameen." ta faɗa tana cigaba da matsa masa duka ƙafafuwan.

"Yauwa Aisha naji kuna magana da Noor!"

"Wallahi Malam taƙi saurarata, kuma kasan halin yaran yanzu, tsoro na kar taga kaman zamu takurata mu neme ta mu rasa yanda mijinnata ya rasa ta."

Numfashi Baba yaja kafin yace

"hakane, amma duk da haka ai bazamu biye mata ba, yarintace kawai ke damunta, amma shima yaron dole na zauna dashi, kafin na bashi Noor, dole ne a aure ya zama akwai cikakken yarda da aminci, ai ba'a haka, yanzu so nake mu cire anfanin gona, idan mun siyar, kuÉ—in sai muyi anfani dashi mu maidata gidan mijinta, dan shine mutuncinta."

"Hakane kam Malam, Allah dai ya saka maka da alkhairi."

"Ya saka mana gaba É—aya uwar Æ´aÆ´ana"

ya faÉ—a yana kallonta da murmushi.

Itama Murmushin tayi tana miƙewa tace bari

"naje na ƙarasa girki."

Daga haka ta fice a É—akin.

***********

*_Kaduna Nigeria*_

What? Papi ya faɗa yana miƙewa tsaye,

"banganeba, me kake nufi?, papi ya faÉ—a yana ja da baya,

"Abinda kunnuwanka suka jiye maka nake faÉ—a."

Mai gari ya faɗa yana miƙewa shima.

"Yarinyar nan da ka gudu ka bari, ta rasu shekara biyu kenan sannan Æ´arta tayi aure, ta auri wani É—an Balarabe É—an birni da ya zo garinnan, ya tafi da ita mu kan mu bamu san ina ya tafi da ita ba."

Girgiza kai papi ya shiga yi idanunsa sun kaÉ—a sunyi jajir

"Kana nufin Fatima tana É—auke da cikina sanda na tafi na barta?, kana nufin ina da wata Æ´ar bayan su farhaana?, pleaaaaase ku faÉ—a min ina Æ´ata take É—an Allah, ita É—in jinin Fatima ce, matar da nafi so fiye da kowa a duniya."

A fusace Ammi ta miƙe tana faɗin,

" ba sai ka cigaba da maimaita cewa baka sona a gaban kowa ba razaÆ™ Abdulkarim, laifina ne dana so ka, sannan na biyoka Nigeria."

Daga haka ta miƙe daga kan tabarmar da take, tana riƙe hannun sudais,ta bar wajen.

Kasa cewa komai papi yayi, sai wasu zafafan hawaye dake sauƙa akan fuskarsa.

Farhaana ce ta ƙaraso inda yake, a hankali tace

"Papi zamu sameta insha Allahu, zamu nemo ƴar uwata a duk inda take a duniya, kuma Ammi zata sauƙo, but Please papi Kar kayi kuka."

Rungume ta kawai yayi, baice komai ba, shi kaɗai yasan me yake ji a cikin ƙirjinsa.

A hankali ya É—ago jajayen idanunsa, yana kallon mai gari,

"Dan Allah ko kuna da koda hoton Æ´a ta ne, zan nemo ta duk inda ta shiga a duniya."

ya faɗa yana share hawayen da ya sauƙo masa.

Shiru mai gari yayi kafin yace,

"ai kuwa kayi matuƙar Sa'a, dan kuwa yaron da ya aure tan yana ɗaukan hoto, kuma bikin shekaran da akayi,
a shekaran da yazo garinnan ya musu hotunan, ina tunanin Noor É—in na ciki, kuma ya kawo min wasu daga cikin hotunan, bari dai na duba, dan kuwa na adanasu dan tarihi ne."

"Noor!" papi ya maimaita sunan,

*kenan sunan Æ´ata da Fatima ta haifamin Noor"
sai kuma ya lumshe ido, sabbin hawaye na zirya akan farar kyakkyawar fuskarsa.

Miƙewa mai gari yayi, ya nufi cikin gida, can kuma sai gashi ya dawo da hotuna a hannunsa, sai da ya kalli hoton yaga da Noor kafin yayi wani Murmushi,

"aikuwa harda ita a ciki amma dai kam sai ka siya, dan bazan baka kyauta ba."

Da sauri papi yace

"zan siya ko da ace da dukkan kuÉ—in dana mallaka ne, pleaaaaase ka bani inga Æ´a ta."

"Ah ah sai na fara ganin kuÉ—in"

da sauri ya miƙe yana zaro dukkanin kuɗin aljihunsa yana zube su gaban mai gari

"Idan basu isa ba, zan ƙara maka, akwai wasu a mota, a can mukayi parking sai naje na ƙaro maka."

papi ya faɗa yana miƙewa tsaye da alama baya cikin hayyacinsa.

Zaro ido mai gari yayi ganin bandir É—in kuÉ—i har huÉ—u, ai baisan sanda ya watsar da hoton ba ya rungumi kuÉ—aÉ—e,

tsugunnawa papi yayi ya É—au hoton yana kallo.

"Subhanallah, laa haula wala ƙuwwata illa Billah."

Babu inda Noor ta barsa, sai dai yanayi na Fatima data É—auko.

Wasu hawaye Masu ɗumi ne suka wanke masa fuska, kafin ya miƙe, ba tareda yabi ta kan mai gari ba ya juya ya bar wajen Farhaana na biye dashi.

A jikin mota suka tarar da Ammi, ta cika tayi pam.

Bai bi takanta ba ya shiga Mota, suma shiga sukayi kafin ya tada motar ya bar garin gabaki É—aya, a zuciyarsa yana tunanin ta inda zai fara neman Noor!.

************

Idan akwai abinda yafi tashi hankali, Zannur ya shigesa, gaba É—aya ya rasa sukuni, ya rame, kamar ba Zannur ba, sai suma da ya tara har ya masa yawa.

Aƙalla yau watan Noor uku kenan babu ita babu labarin ta, yayi Neman har ya fara cire rai.

An sallami TaufeeÆ™ a asibiti, bayan jinya da yayi, a yanzu ya warke rass, sai dai baya cewa komai, sai an daÉ—e yake buÉ—e baki ya ce wani abu,

gaba ɗaya Zannur ya fita hayyacinsa, a yanzu ya ma daina neman wanda ya yi yunƙurin kashe Taufeeƙ, gabaki ɗaya hankalinsa naga inda zai ga Noor.

Yasira kam, komai ya jagule mata, dan kuwa Zannur ya koreta a aiki a matsayin chief staff na kitchen, hakan yana nufin, batada hurumin zuwa inda yake, sai dai zata zauna a gidan albarkacin TaufeeÆ™, sai dai batada hurumi da mai gidan, dama da hakan take fakewa tana kallonsa tana jin sanyi a ranta, gashi yanzu TaufeeÆ™ ya toshe duk wata hanya da zata gansa, kwata kwata,

gabaɗaya tá rasa mai zatayi, tsoronta kaɗai kar ya faɗama Zannur, duk da a halin da Zannur yake a yanzu, bazai saurari kowa ba, dole ne tayi gaggawan ɗaukan mataki, kafin lokaci ya ƙure mata.

Yauma, a zaune Zannur yake a dakin Noor, Wanda ya jima da tarewa anan, Camera ne a gabansa, ya zuba ma hotunan ta ido yana kallo ko ƙiftawa bayayi.

Gashin kansa ya sauƙa gefe da gefen fuskar sa, he look pale, but duk da haka ya ƙara haske da wani irin kyau kamar wanda yake cikin kwanciyar hankali, ramar dayayi ne kaɗai zai tabbatar maka da halin da yake ciki.

"Habibi!" yaji an faɗa da ƙarfi

ÆŠagowa yayi yana kallon Maami with suprise Dan baisan zatazo ba, Abbu da ya gani a kusa da Maami sai ya sake basa mamaki, amma sai baice komai ba, ya mayar da kansa wasu hawaye na taruwa a idanunsa.

Da sauri Maami ta yasar da jakanta, tana ƙarasowa gabansa, ɗago fuskarsa tayi

"Habibi talk to me, miye duka hakan?, TaufeeÆ™ ya kira mu yace muzo bakada lafiya me ya sameka, kaga yanda ka rame kuwa rabin raina?, meyasa bazaka faÉ—a wa Maami ba?."

Kasa cewa komai yayi, kawai dai ya rungume ta sosai yana sauƙe ajiyar zuciya.

A hankali ya buɗe bakinsa daya ƙafe yana faɗin

"Maami Noor ta tafi ta barni, Maami bansan ta ina zan fara nemanta ba, Maami where can I find Noor?, I need to apologise, idan wani abu ya sameta bazan yafewa kaina ba.

Shafa kansa tayi tana faÉ—in

"Habibi calm down, TaufeeÆ™ ya faÉ—a min komai, zamu sameta da izinin Ubangiji, ka kwantar da hankalinka."

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.