Complete Hausa Novels

Abnur Complete Hausa Novel

Reading file: Abnur_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 9 of 24

*Page* *10*

Ita dai kallon su kawai takeyi,ba tare da tace uffan ba,
kallon juna suka yi sannan suka maida kallonsu gareta, Amina tace "Ni sunana Amina,wannan kuma......"

"Asabe". Asabe ta faÉ—a tana tarar numfashin Amina.

Murmushi kawai tayi musu ba tace komai ba.

Taufeeƙ da ke sauƙowa ya kallesu yace

"wai kun san waye ce ita kuwa kuka ajiyeta a tsaye, nace ku kaita É—akin sama, baku Kaita ba kun tsaya kuna cika ta da surutu koh"

ya faɗa yana ƙarasa sauƙowa

"Sir Taufeeƙ dan Allah a ina kuka samu wannan kyakkyawar yarinyar son kowa ƙin wanda ya rasa,wallahi har ta shiga raina"

cewar Amina tana murmushi.

"Matar Sir Zannur ce"

ya faɗa a taƙaice yana nufan ƙofan falon dan dai baya son tambayoyi,
dan ya riga ya san halin su Asabe.

a ranshi yana ayyana irin zaman da za'a yi a cikin gidan tsakanin Sir da kuma Madam É—in sa.

"Matar Sir ce", maganar daya doki ƙwaƙwalwar Yasira kenan wacce ke fitowa daga kitchen,dan yiwa su Amina magana suje su cigaba da aikinsu,

kasa ƙarasowa falon tayi daga bakin kitchen ɗin ta ƙura ma Noor idanu, wacce ke tsaye duk tsayuwar ma ta isheta.

Bata gama tantance
abinda kunnuwanta suka jiyo mata ba taji Muryar su Asabe dake ta murna kamar waÉ—anda aka ma bushara da aikin hajji

Asabe na faÉ—in "Sannu da zuwa Madam, wai da gaske ke matar Sir ce,ya ilahi,ina zansa kaina"

ta faÉ—a tana sake
kwashewa da dariya kamar taɓaɓɓiya,

Duk yadda take jin zuciyarta sai da ta É—an murmusa ba tare da ta shirya Ba.

Amina tace"mun shiga uku, matar gida muka bari a tsaye, Asabe bazaki nuna mata É—akin ba" ta faÉ—a cikin rashin sanin abinyi itama murnar ta kasa barinta.

A hankali tace"Sunana Noor, kuma ina so in yi sallah, a ina zanyi"

ta faÉ—a tana murmushi

Da sauri Dukansu suka fara rige rigen yi mata jagora zuwa É—akinta,

tsaf ɗakin yake, hakan yasa suka barta tayi sallah,suka sauƙo suna cigaba da hirar abin,

Asabe tace"anya Sir TaufeeÆ™ ba wasa yake mana ba kuwa, ya za'a yi Sir yayi aure babu sanarwa babu komai"

Amina tace wallahi kamar kin shiga zuciyata,ko Maami ma bazata yarda da wannan auren ba".

"Nima haka nake gani" cewar Asabe suna ƙara sa sauƙo wa daga matakalan.

Hango Yasira da sukayi yasa suka canza hirar

Asabe ta É—aga murya tana faÉ—in"wallahi Fah matar Sir kyakkyawa, daga gani zatayi hankali"

Amina ta karɓe "kuma wallahi ba ƙaramin dacewa sukayi ba, Allah dai ya barsu tare ya tsole idon maƙiya"

ta faÉ—a tana kallon gefe.

Har suka wuce ta bata ce musu komai ba, zuciyarta banda tafasa babu abinda takeyi.

"ya za'a kayi min haka?, ya za'a yi ka auri wata ba Ni ba?, kai kaÉ—ai na tanadawa kaina, kai nawa ne Ni kaÉ—ai,
dan Ni kaɗai aka halicceka Sir Zannur, bazan taɓa yarda ka zauna da kowace mace idan ba Ni ba,sai dai bayan raina" ta ƙara sa faɗa kamar mai shirin zarewa.

Juyawa tayi a fusace ta wuce su Amina a kitchen ta bi ta ƙofar baya ta tafi ɓangaren su, tana tunanin yadda zata ɓullo ma lamarin idan har ya kasance gaskiya ne.

Asabe da Amina suka bita da kallo sannan suka ƙyalƙyale da dariya ƙasa ƙasa suna faɗin "a sauƙa lafiya".

Tunda suka fita suka barta, ta tsaya tana ƙarema ɗakin kallo,
nan É—in É—akin ta ne kenan?, ita ce yau zatayi rayuwa a nan ba tare da Nennen ta ba, tabbas mutuwa bata barin wani dan wani yaji daÉ—i,idan ba haka ba da Nenne bazata mutu ta barta ba,

hawayen idonta ta share sannan ta juya ta nufi ƙofan da ta gani wanda tafi tunanin shine banɗaki, shiga tayi ta tsaya tana kallon toilet ɗin.
yafi na hotel ɗin da suka sauƙa a Kaduna kyau da girma da tsaruwa nesa ba kusa ba,
bata wani sha wahalan yin amfani da toilet É—inba kasancewar ta gane tun na hotel É—in hotel É—in, sai da ta yi wanka ta wanke tsefeffen gashin kanta da shampoos É—in da ta gani a toilet É—in,sannan ta É—auro alwala, sai kuma ta tsaya tana tunanin kayan da zata saka,

bathtub ta gani kala kala a banÉ—akin,haka kawai taji a jikinta shi ake sakawa idan anyi wanka, murmushi tayi ta jawo guda É—aya mai kalar sky blue tana kallo,

sai da ta saka sannan ta sake jiƙaƙƙen gashin kanta a bayanta, ya sauƙa har kusan ƙugunta duk da a jiƙe yake.

A hankali ta buɗe ƙofan banɗakin ta fito tana rarraba idanu,
da sauri ta ƙara sa wajen ƙofa ta murza key tana sauƙe ajiyar zuciya,a fili ta furta

"hmm kawai sai wani ya shigo ya ganni a haka ai da kunya ta kasheni"

sake kallon jikinta tayi sai ta rufe fuskarta da hannunta tana É—an dariya,

Duk abinda takeyi yana zaune yana kallonta, a cikin laptop É—in sa, da yayi connecting da duka cctv cameras na gidan,murmushi kawai yayi ganin yadda ta rufe fuskarta a fili ya furta

"silly girl"

Amma a cikin ransa yana mamakin kyaun yarinyar ga ta da gashi abinda yake matuƙar so a wajen mace,
sai dai shi baya ganin har gaban abada zai taɓa iya zaman aure da ita.

rufe laptop ɗin yayi ya miƙe yana kai komo a ɗakin, babban damuwar sa a yanzu bai wuce yadda zai sanar da Maami da Abbu zancennan ba,

waya ya É—auka yayi dialling Numbern TaufeeÆ™ Yana É—agawa yace

" ina so zuwa gobe ka kai yarinyar can ka yi mata siyayyan kayan anfaninta and banaso ta nemi komai ta rasa i hope you understand"

daga ɗayan ɓangaren Taufeeƙ ya amsa da

"Yes Sir"

katse wayan yayi sannan yayi cilli dashi a kan gado yana kai hannunsa ya ya mutsa lallausan yalwataccen sumarsa, a hankali ya furta

"everything will be alright soon".

juyawa yayi ya fice a É—akin gaba É—aya ba tare da ya É—au wayan ba.

Knocking ɗin da taji a ƙofar ɗakin ya sata saurin mayar da kayan da ta cire, ta ƙara sa bakin ƙofan tana faɗin

"waye ne?"

jin shiru ya sa ta ƙara sawa, ta murda ƙofan ta buɗe tana kallon wanda ke bakin ƙofar,

kallon kallo suka shigayi kafin tayi murmushi tana faÉ—in

"bismilla"

daga haka ta koma ciki

Sai da Yasira ta haɗiye wani mugun yawu kafin ta yi ƙarfin halin ƙarasawa ciki tana ƙoƙarin yin abin da ya kawota ba tare da ta kwafsa ba.

Da murmushi ta dube ta tana faÉ—in

"sannunki da zuwa, Sunana Yasira ni ce in charge na kitchen É—in gidan nan gaba É—aya"

ta ƙarasa tana ƙura ma Noor ɗin ido

A hankali tace

"nagode".

É—an shiru Yasira tayi sai kuma tace ko zan iya sanin ke kuma wacece ta faÉ—a tana sake kallonta.

"Bakida hurumin sannin wace ce ita!"

da sauri dukkansu suka juya suna kallon mai magana,
da mamakin Noor ke kallonsa yayinda Yasira cikin sauri ta shiga faÉ—in

"Sorry Sir i just came to welcome her,am sorry Sir"

ta faÉ—a tana raba idanu
Bai ce mata komai ba yaƙarasa cikin ɗakin,

zuwa lokacin ƙamshin turarensa na SHUMUKH ya gama cika ɗakin,

fuskarsa babu yabo babu fallasa yace

"ina so ki haÉ—a min duka staff É—in da ke cikin gidannan by 6 o'clock",

"Okay Sir" ta faÉ—a da sauri.

"You may leave" ya faÉ—a ba tare ta ya sake kallon inda take ba.

Da sauri ta fice a É—akin tana waiwayensa.

Sunkuyar da kanta Noor tayi tana wasa da yatsunta, zuciyar ta na wani irin bugu,
dan gaba É—aya ya canza mata daga wanda ta sani a da.

Taku biyu ya ƙara yana kallonta yace

" ƙarfe 6 yayi miki a falon ƙasa, i hope you understand!?.

Girgiza kai kawai tayi batare da tace komai ba.

Buɗe ƙofar da akayi ya sa duk suka juya suna kallon Asabe da ke ƙoƙarin shigowa, tana turo ƙaramin table ɗin da aka jera abubuwa daban daban akai,
wani burki taci tana riƙe handle ɗin, tayan jikin table ɗin suka tsaya cak akan tiles ɗin da sauri ta juya tana dariya ƙasa ƙasa tare da faɗin
"Sorry Sir",ai bansan kana tare da Madam ba".

daga haka ta juya da sauri ta bar ɗakin, kallo yabi ƙofar da shi sai kuma yayi ƙwafa yana juya wa shima ya fice a ɗakin, ya barta a tsaye tana binsu duka da kallo

Da gudu Asabe ta nufi kitchen tana dariya,Amina dake goge plates tace

"kee Asabe lafiyarki "

"Bari kawai Amina Nikam ai yau naga yadda ake love"

ta faÉ—a tana satan kallon Yasira da ke duba time table É—in girkin satin.

Amina ta ajiye plate É—in hannunta tana faÉ—in

"fisabilillahi fah, a Ina kika gani"

"Hmm ke dai bari wallahi, dana je kaima Madam abinci bansaniba ashe Sir yana É—akin kekam dai abin ba'a magana "

Ta faɗa tana ƙoƙarin ƙular da Yasira ai kuwa haƙar ta, ta cimma ruwa, dan kuwa dangwarar da schedules ɗin girkin tayi, ta bar kicin ɗin tana danne kukan da ke shirin zuwa mata.

Amina tace tana ƙoƙarin kwaikwayon Muryar Yasira
"Wallahi Sir bazai yi aure yanzu ba"

duk suka tuntsire da dariya.

Ƙarfe 5:00 dai dai ya shigo ɗakin nata,
ganin bai ganta a ciki ba yayi tunanin tana banÉ—aki,

a jiye ledar hannunsa yayi sannan ya zaro takadda a aljihunsa ya É—aura akan ledan ya juya ya fice a É—akin.

Tunda ta fito take kallon babbar ledan dake kan gadon,

ƙarasowa tayi ta na kallon farar takaddar da aka linke ta tsaf, a hankali ta ɗau takaddar tana warwarewa,

"Don't make the mistake Of making me wait,make sure 6 ta miki a ƙasa"

Ƙara maimaita karantawa tayi sai kuma ta jawo babban ledan tana kallo kayan dake ciki.

Dress ɗin take kallo babu ko ƙiftawa, a hankali ta kalli agogon ɗakin ƙarfe 5:31

Da sauri ta warware kayan tana ƙoƙarin sanya su,doguwar rigace irin ta princesses ɗin nan blue colour,
sai da ta saka kayan sannan ta warware gashinta da ya riga ya bushe, ta sake naÉ—eshi kamar yadda ta saba, sannan ta É—au gyalen kayan mai É—an girma amma ba sosai ba ta sanya,

kallon kanta ta tsaya yi ganin bata da maraba da princess ɗin da take gani a littafan makarantar ta murmushi tayi, nan take hawaye ya kawo idanunta, tayi iya ƙoƙarin ta na ganin ta mayar da su,

a hankali ta zura flat shoes É—inta tana fitowa É—akin da sauri, ganin six É—in ya kusa,

a hankali take sauƙowa daga kan steps ɗin idanunta nakan inda take sanya ƙafafuwan ta, dress ɗin ta ne ya harɗe ta da sauri tayi baya tana rutse idanunta,

jinta a jikin mutum yasa tayi saurin buɗe idanunta tana kallonsa, yayinda ƙamshin turarensa na _SHUMUKH_ ya ke mata maraba a duk ƙofofin hancinta.

Da sauri ta miƙe daga jikinsa tana kallon dukkan ma'aikatan gidan da suka zubo musu idanu suna kallonsu,

wani kunya taji ya rufe ta, shikam ƙara tsumewa yayi, ba tare da ya sake kallonta ba ya ƙara sa sauƙa a matakalan, itama binsa tayi a baya tana tattare dress ɗinta,

Ma'aikatan ne suka shiga gaishesa cikin matuƙar girmamawa,

Asabe da Amina da gulma ya kusa kashe su kasa jurewa sukayi sai da suka yi ƙus ƙus ɗinsu,suna dariya ƙasa ƙasa.

Yasira kam fashe wa ne kaɗai batayi ba amma ta kumbura tayi suntum, sai ƙwafa takeyi.

A hankali ta ƙara so ta tsaya a gefensa tana kallonsa,

"have a seat"

ya faÉ—a ba tare da ya kalleta ba, a hankali ta zauna a kujeran dake kusa da nashi tana wasa da hannunta,

da sauri duk ma'aikatan suka shiga gaisheta, murmushi kawai takeyi amma ta kasa amsawa,

Sai da yayi gyaran murya kafin ya soma magana.............

Maimoon🤓#

Maimoon🤓#

*💖ABNUR💖*

*By* *maimoon* 🤓

*Elegant* *online* *writers* 📚📖

*Free* *book*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.