Abnur Complete Hausa Novel
Reading file: Abnur_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 11 of 24
*Page* *12*
_Washegari_
Tun safe Zannur yake jinsa wani iri,ya kasa fita,ko nan da can.
ganin ya kasa nutsuwa
ya sa ya jawo laptop É—insa,yana kallon ta,
yadda ta shige cikin bargo ta rufe har kanta.
sai kuma ya ja tsaki yana faÉ—in,
"mutum yayi ta bacci tun safe".
Yana ƙoƙarin rufe laptop ɗin yaga tayi miƙa tana yaye bargon daga jikinta,
sai ya fasa rufewa, ya cigaba da kallon ta,
miƙewa tayi zaune a kan gadon tana mutsuka idanunta,sai kuma ta zuro ƙafafuwan ta ƙasa, slippers ɗinta ta sanya kafin ta miƙe,
har ta shige banɗaki,kafin ya sauƙe ajiyar zuciya yana shafa sumar kansa a fili ya furta
"Ke amana tace, saboda haka dole ne in sa ido akanki"
sai kuma yayi murmushi yana rufe laptop É—in, dan har yaji mood É—insa ya canja, yana jin sa cikin nishaÉ—i,
duk da wani sashi na zuciyar sa na fargaba wanda bai san fargabar miye ba.
Agogo ya kalla, ganin ƙarfe goma saura minti goma, ya sashi miƙewa shima ya wuce toilet.
sai da yayi daɗe a banɗakin kafin ya fito ɗaure da towel a ƙugunsa,
cikin abinda bai fi 30 minutes ya shirya tsaf cikin riga da wando na *_Louis Vuitton_* Agogo ya sanya da pcap a kansa duka na *_Louis Vuitton_* sannan ya feshe jikinsa da mayen turarensa na *_shumukh_* slippers ya sa a ƙafan sa shima na *_Louis Vuitton_* sannan ya koma gefen gadon ya zauna,ya jawo laptop ɗinsa Yana dubawa, dan baya tunanin zai fita ko ina.
Iska da fara sauƙan yayyafi ya shashi miƙewa yana leƙa waje,
ai kuwa sai ruwa ya tsuge kamar da bakin ƙwarya, saurin matsawa yayi daga jikin window,aransa yana tunani yadda za'a yi wasu da basu san ciwon kansu ba har su bari ruwa ya jiƙasu idan ba tsautsayi ba.
Komawa yayi ya zauna ya sake jawo laptop ɗin,kai tsaye ɗakinta ya duba ganin bata ciki yasa yayi ƙwafa yana kashe laptop din gabaki ɗaya, ya miƙe ya fice a daƙin,
Ɗakin hoto ya shiga yana ƙarasawa ya ɗauki Camera,saboda yana son yin capturing ruwan yanda yake sauƙa,
a hankali ya yaye labulen balcony É—in yana saka Camera É—in a idanunsa,iskan ruwan na kaÉ—awa yana sa rigar jikinsa haÉ—ewa da jikinsa .
Abinda ya gani ta cikin Cameran ya sashi saurin janyewa daga idanunsa yana ƙura mata idanu,
tabbass ba gizo idanunsa ke masa ba, ita É—ince a cikin ruwan sama, baki a sake yake kallonta, yanda take juyi tana nishadi a cikin ruwan,
shagala yayi da kallonta, tundaga sama har ƙasa yake yake kallonta,
riga da wando ne a jikinta masu laushi na *_Dior_* kanta ta saka band Wanda ya Bama gashinta daman sauƙa ta bayanta, *_Stuart weitzman Cinderella slippers_* ne a fararen ƙafafuwan ta,
yanda take dariya ya sa shi mayarda Cameran idanunsa ba tare da ya sani ba.
hotuna yayi ta mata ba tare da tasan ma yana gun ba,Dan kuwa babu wanda yake zuwa ta bayan balcony ɗin,shiyasa ma ta je can dan bazata iya ƙin shiga ruwa ba.
Ajiye Camera É—in yayi a hankali ya fice a É—akin.
Hannuwanta ta tara a ruwan ya cika ta watsa a fuskarta,ta sake tara hannun tana shirin watsawa taji an riƙe hannuwan nata,
a tsorace ta ɗago, idanunta suka shige cikin nasa,fuskarsa babu alamar wasa,gaba ɗaya ya gama jiƙe jikinsa,ƙirarsa na ƙarfafa ta sake bayyana saboda yadda ruwan yasa kayan ya manne da ƙirjinsa,
Kallonta kawai yakeyi ba tare da ya ce komai ba, da sauri ta ƙwace hannunta tana shirin barin wajen dan batasan sam zaizo wajenba,
ita bata mayi zaton yana gidan ba,dan rabon ta da shi tun ranan da ya kawota,
da sauri ya sake riƙe hannunta, yana jawota gabaki ɗayanta zuwa jikinsa,kasa koda ƙwaƙƙwaran motsi tayi,cikin Muryar da shi kansa bai san yana da ita ba ya soma faɗin
"me yasa kike shiga ruwa,bakya tsoron mura ya kamaki?"
ÆŠagowa tayi ta kalleshi,sai kuma ta sunkuyar da kanta,ta kasa cewa komai,
"Tambayar ki nake"ya faÉ—a a hankali yana dubanta.
"To ai Ni ina so,kuma ko a Baulawa ma ina shiga"
ta faÉ—a tana turo baki.
"To nan ba Baulawa bane, nan ba'a shiga ruwan sama, idan dai baso kike ki ƙarar min da kuɗina a asibiti ba".
"Ni ruwa baya sani rashin lafiya" ta faɗa a shagwaɓe,
"I see"ya faÉ—a ya na sake ta
Ai kaman jira takeyi da gudu ta bar wajen,ya bita da kallo yana shafa jiƙaƙƙen sumarsa,
su Amina da Asabe da ke leƙe ta kitchen sai tafawa sukeyi duk da basa jin me suke faɗa,
Asabe ta É—aga hannu sama tana faÉ—in"Allah ka aurar da mu"Amina ta amsa da
"Ameen ya Allah muma dai muji me ake ji"
suka sake ƙyalƙyalewa da dariya,
Yasira da ke tsaye itama ta ɗayan ɓangaren ta ja tsaki, sai kuma tayi murmushi a zuciyarta tana faɗin
"komai ya kusa zuwa ƙarshe".
kallon jikinsa yayi, yaga yadda yayi sharkaf da ruwa,a hankali ya furta
"Yuk"
Yana ɓata fuska,sai kuma ya ja tsaki, sam ba abinda yake son ce mata ba kenan,
so yayi ya mata faÉ—a, amma bai san ya akayi harshen sa ya kasa bashi haÉ—in kai ba,shima juyawa yayi ya bar wajen yana sakin attishawa.
Ƙarfe 3:00 ya fito daga ɗakinsa ya sake shiryawa cikin wasu ƙananan kayan,but ya ƙara rigar sanyi akai,
sauƙowa yayi falon ƙasa ya zauna yana danna wayarsa.
a hankali itama take sauƙowa ta canza kayanta zuwa doguwar rigar abaya ƙafafuwan ta san ye cikin flat shoes na *_Miu Miu_* kitchen ta nufa batare da ta lura da shi ba, a hankali yace
"tea"
Cak ta tsaya,sai kuma ta juya ta kallesa,ganin idanunsa a lumshe yasa kawai ta juya ta nufi kitchen É—in,
Amina da Asabe na ganinta suka soma gulma ƙasa ƙasa suna dariya,
"Ku kuma fa"
ta faÉ—a tana murmushi itama,
"Ina kwana Madam"
suka haÉ—a baki wajen faÉ—a,murmushi kawai tayi.
"Ina kwana"
Yasira ta gaisheta a daƙile, itama ƙasa ƙasa ta amsa, tana faɗin
"Yasira ki haɗa tea, ki saka kayan ƙamshin a ciki, da citta, yanzu ina jiranki ki kawomin parlour".
Yasira ji tayi kamar ta fashe ƙasa ƙasa tace"ok ma"
Daga haka ta juya ta bar kitchen É—in.
Asabe da Amina suka tafa suna faÉ—in
"wannan irin shiga ruwa na masoya ai dole su sha shayi saboda sanyi"
Amina tace "haka abin yake"
suka sake kwashe wa da dariya.
Ita dai Yasira ko takan su bata bi ba,ta haɗa shayin,ta jera a kan tray mai matuƙar kyau sannan tace
"Amina kikai mata"
"In kai mata ina?,Ni rufa min asiri, matar gida tace ki kai mata kice in kai mata, ah ah wallhi"
Yasira tayi ƙwafa ta suri tray ɗin ta fito,
ganin Sir Zannur a falon ya sa ta saita kanta da fuskarta ta gyara tafiyarta, a yangance ta ajiye a kan Centre table É—in tana kallon sashin da Noor take zaune,
itama kallonta takeyi,kawar da kanta tayi tana kallon Zannur tace
" Sir should I serve you tea"
Itadai Noor kallonta kawai takeyi
"don't worry,ki barshi, ki je ki cigaba da aikin ki"
ya faÉ—a ba tare da ya dube ta ba,
"ok sir"
ta faɗa badan ran ta ya so ba, ta miƙe ta bar wajen, da ido Noor ta bita kawai,
ÆŠago wa yayi daga danna wayar yace
"Are You waiting for me to ask you to serve the tea"
Da sauri ta sauƙo daga kujeran tana ɗaukan cup ɗin ta shiga tsiyaya masa shayin.
Satan kallonta kawai yake yi yadda take yin komai a nitse,har ta gama ta miƙa masa, yana shirin karɓa wayarsa tayi ƙara,
Ganin Maami haka kawai yaji gabansa ya faÉ—i, É—agawa yayi tare da yin sallama,
"Habibi come and pick me up at the airport"
Da sauri ya ajiye cup ɗin daya karɓa yana faɗin
"what!!, Maami, wani airport É—in"
"Nnamdi Azikwe International Airport"
ta faɗa a taƙaice tana katse wayar ta.
Wayar hannun sa ya bi da kallo, sai kuma ya juya ya kalli Noor, ba tare da yace komai ba kawai ya juya ya nufi ƙofa,
kallo ta bishi da shi,a ranta tana tunanin anya lafiya kuwa, shayin da ya bari ta É—auka,sannan ta kira landline na kitchen, tace suzo su maida tea É—in.
daga haka ta haura da nashin a hannunta tana tunanin abinda ya É—aga masa hankali haka.
Maimoon#
💖ABNUR💖
By maimoon🤓
Elegant online writers📚📖
Free book📚
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.