Abnur Complete Hausa Novel
Reading file: Abnur_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 23 of 24
*Page 23*
Kallon kallo suka shiga yi ma juna, babu ko ƙiftawa, kallonta kawai yake yi, kamar ya samu tv, yama rasa me za iyi.
Juyar da kansa yayi, kafin yayi wani Murmushi yana shafa kansa,
da sauri ya shiga sauƙowa daga steps ɗin, bai damu da Papi, Abbu, Maami, Ammi, da kowa dake falon ba.
Wani irin kyakkyawar
runguma ya bata, da har sai da Dukansu suka sauƙe ajiyar zuciya, gaba ki ɗaya ya manta da wani fushi da yake da ita, ita kanta ta manta wai tana jin haushinsa, dan dama ita kanta tasan ƙarya take ma kanta, amma tasan tana matsanancin son Zannur, kuma tayi kewansa fiye da misali.
ÆŠaga ta yayi yana juyi da ita a tsakar falon, gabaki É—aya ya rasa ma me zai mata ya tabbatar mata da irin farincikin da yake ciki.
Dariya ta shiga yi, tana wuntsula ƙafafunta, shima kansa dariyar kawai yakeyi, yana jin kamar kar wannan moment ɗin ya taɓa wucewa har abada.
Direta yayi a hankali, yana faÉ—in
"Noor, Ina kika je?, inata nemanki, meyasa Kika yanke min the worst hukunci da za'a taɓa yankewa wani ɗan Adam?, Noor me yasa baki jira na gane gaskiya ba?, wallahi yanzu na gane komai, I will never misunderstand you ever again, please ki yafe min"
Ya faÉ—a yana kamo dukkanin hannuwanta.
Kowa a É—akin kallonsu kawai yakeyi kamar suna cinema, Abbu da ya buÉ—e baki da niyyan magana da sauri Maami ta girgiza masa kai tana murmushi,
Shima murmushin yayi kawai, suka tsaya ganin ikon Allah
Shi kansa Papi murmushi yakeyi haka Ammi da su Amina.
Shiru Noor tayi ba tace komai ba, sai hawaye daya ciko idanunta,
"Noor!"
Ya Kira sunanta,
Kawar da kai tayi taƙi kallonsa.
Da sauri ya juyo da fuskarta,
"Don't do that Noor it hurts, Please kimin magana, what do you want me to do, me kike so inyi miki, so kike inyi kneeling in baki haƙuri"
Ƙin magana tayi amma a zuciyar ta dariya take yi tana faɗin "bazan kulaka yanzu ba ko me zakace."
ÆŠurkushewa yayi akan gwuiwowinsa, yana faÉ—in
"Noor please ki yafemin I won't repeat my mistake."
Da mamaki take kallonsa, bata taɓa tunanin zai iya hakan ba, da sauri itama ta ɗurkushe a ƙasan tana faɗin
"Miye haka kake yi?"
hannuwansa ta lalubo duka ta riƙe tana kallon cikin idanunsa
"Na yafe maka, na jima da yafe maka, kuma har abada baka min komai ba, nima ka yafe min Please"
Tana kaiwa nan ta fashe da kuka, rungumeta yayi tsam tsam a jikinsa, ya lumshe idanunsa, yana jin wani relieve na sauƙa masa tun daga kansa har ƙafafunsa.
"Awnnnnn🤗"
Amina da Asabe suka faɗa a tare suna ƙyalƙyalewa da dariya.
Sai lokacin yayi saurin sakinta, Dukansu suka miƙe tsaye, Noor kaman zata mutu dan kunya, shikam shafa kansa kawai yayi, kafin yayi magana Maami ta riga sa tana faɗin
"To idan kun gama, sai kabar ta tazo ta zauna, daga tafiya take, ai ka barta ta zauna ta huta ko?"
Murmushi yayi kawai bai ce komai ba, saima ƙarasowa falon yayi ganin baƙin fuska, wanda ɗaya yayi matuƙar kama da Noor ɗinsa
Maami ma kama hannun Noor tayi, suka ƙarasa cikin falon, itakam sai sunkuyar da kanta takeyi.
Yasira dake tsaye a gefe, idanunta sun kaɗa sunyi jajir, ta share hawayen idanunta tana jin ƙuna a zuciyarta.
TaufeeÆ™ ne ya shigo falon, ganin mutanen da ke ciki ya sashi faÉ—in
"sorry I will come back later."
Da sauri Abbu yace
"ah ah Taufeeƙ a ƙaraso Noor ne ta dawo tare da mahaifinta."
Sai lokacin ya lura da Noor, Itama ido ta zuba masa, ganin ya warke rass kamar ba shi ba, sai kuma ta sunkuyar da kanta ƙasa.
Da sauri ya ƙaraso cikin falon da fara'a sosai akan fuskarsa
"Alhamdulillah, mun godema Allah da ya dawo da Madam Noor cikin ƙoshin lafiya, congratulations Sir ya faɗa yana dariya."
Zannur dai kasa amsawa yayi, sai murmushi da yake yi kawai, wanda ya daÉ—e rabonsa da fuskarsu gabaki É—aya.
Asabe da Amina ne suka ƙaraso da sauri suna faɗin,
"Our Madam, Sannu da dawowa, wallahi bakiji yadda gidan ya zama ba da bakya nan"
Murmushi tayi musu, dan dai kamar an sace Mata kalaman bakinta ta kasa furta komai.
Kowa ka kalli fuskarsa cikin farinciki yake a falon, banda Yasira da ta rakuɓe can gefe tana tsiyayar da hawaye.
Juyawa tayi zata bar falon, da sauri ta dakata jin Muryar TaufeeÆ™ da tayi yana faÉ—in
"Yasira bazaki ma Madam Barka da dawowa gidanta ba, her rightful place, gurin da babu wani mahaluki da yake da iko sai ita kaÉ—ai."
Turus tayi, sai kuma ta share hawayen da ya zubo mata, ta juyo a hankali.
Gani tayi gabaki ɗaya mutanen falon idanunsu na kanta, jiki a saluɓe ta ƙaraso cikin falon.
A gaban su ta tsaya kafin cikin ƙarfin hali tace
"Sannu da dawowa Madam"
Ta faɗa tana ƙoƙarin danne shahararren kukan dake zuwa mata.
Ko kallonta Noor batayi ba, bare ta sa ran zata amsa mata, hakan yasa Papi faÉ—in
"Daughter sannu da zuwa take miki"
"Na ji ta, Papi"
"To meyasa baki amsa ba?" ya tambaya yana kallonta da kulawa
Turo baki tayi tana shirin magana suka ji ance
"Saboda bata cancanci Zama a gidannan ba, talkless of amsa gaisuwarta"
Duk juyawa sukayi suna kallon TaufeeÆ™
Cikin tsananin takaici ya soma faÉ—in
"Sir ka tambayeni several times, wanene yayi yunƙurin kasheni to ba kowa bace face ƙanwata Yasira."
Duk miƙewa suka yi tsaye, har shi kanshi Zannur ɗin.
"What Are You saying Taufeeƙ?, me yasa Yasira zata yi yunƙurin kasheka, bayan bata da kowa a duniya da ya wuce kai."
Zannur ya faÉ—a with disbelief yana kallon TaufeeÆ™
Murmushi TaufeeÆ™ yayi kafin yace
"tabbass Yasira ita ce tayi yunƙurin kashe ni kuma ba komai ya sata aikata hakan ba face soyayya, soyayyarma naka Sir Zannur."
Gaba É—aya É—akin salati suka sanya, da Sallallami.
TaufeeÆ™ ya cigaba,
"saboda nayi yunƙurin hanata, hakan yasa ta gwammace in bar duniyan, har asibiti ta bini dan ta ƙarasa ni, Amma Allah bai bata iko ba"
Ya ƙarashe zancen yana jin wasu hawaye Masu ɗumi.
Cikin kuka sosai Yasira ta nufi Sir Zannur, akan gwuiwowinta ta zube tana kama ƙafafunsa
"Dan girman Allah Sir ka tausayamin, wallahi na aikata duka hakane saboda tsananin son da zuciyata ke maka, bazan iya rayuwa idan babu kai ba, wallahi kaine rayuwata" ta ƙarashe da wani irin kuka har shiɗewa takeyi.
Noor da idanunta suka gama rufewa, sai yanzu ta fahimci komai, tabbas tayi wauta da ta tafi ta bar Zannur, wato wannan duk sharrin Yasira ne,
Ƙarasowa tayi, ta sa hannu ta ɗago Yasira sai ji kake tassss ka wanke ta da mari, kafin ta farfaɗo ta sake wanke ta da wani marin,
Marinta ta rinƙa yi har sai da Zannur ya riƙe ta, nan take fuskar Yasira tayi fulu fulu yatsun Noor ne akwance a fuskarta ta ko ina.
"Allah ya isa tsakani na da ke, kuma wallahi sai dai ki mutu, amma mijina yafi ƙarfin ki"
Ta faɗa tana ƙoƙarin kwacewa daga riƙon da Zannur ya mata gabaki ɗaya idanunta sun gama rufewa.
Asabe da Amina al'ajabi ya kashe su a tsaye.
Papi ne yayi gyaran murya kafin yace
"kowa ya samu waje ya zauna."
Duk zama sukayi, sai Yasira dake tsugunne tana cigaba da kuka
Papi yace
"to bansan me zance akan wannan al'amari ba, abu dai ya riga ya faru, saboda haka dan Allah kukai zuciya nesa,
Ke kuma Yasira kike ko waye?, kije, duniya ta isheki riga da wando, bazan bari su miki Allah ya isa ba saboda ko a yanzu zuciyarki baƙace ina ga kuma kina ɗauke da Allah ya isan jama'a."
Abbu dake jin zafin abinda Yasira tayi shima ya É—aura da faÉ—in
"Yasira i didn't expect that from you, É—an uwanki, TaufeeÆ™ ya ma fi uba a wajenki, babu abinda ya nuna miki sai tsantsar soyayya, amma abinda kika saka masa da shi kenan, saboda haka na baki 20 minutes ki tattaro duk abinda yake naki a gidan nan ki fice ki bamu guri, kinci Sa'a bamu haÉ—a ki da yan sanda ba saboda kinci darajar TaufeeÆ™ amma ina mai tabbatar miki idan har kika wuce wannan lokacin, nan ne zakisan cewa bawai tsoronki mukeji ba zamu iya yanke hukunci akanki."
Kuka ta sake rushewa da shi, kafin ta rarrafa ta je wajen Maami
"Maami ki taimakeni, bani da wajen zuwa please ki roke su?"
Juyawa Maami tayi ta dubi Abbu kafin tace
"Abbu idan har na buÉ—e idona, naga yarinyar nan a gabana, wallahi duk abinda na aikata mata kar kowa ya sake ya min magana."
Yasira na jin haka ta miƙe da sauri ta nufi su Asabe tana faɗin
"please ku taimaka min"
Matsawa Amina tayi da sauri, tana jawo Asabe
"Ke Asabe matsa a kusa da wajen kar ta shafa miki zuciyar kafirai"
Asabe kam kallonta takeyi cikin ido kafin tace
"Wallahi Yasira, ba tun yau nasan cewa zuciyar ki baƙa bace, amma ban taɓa tunanin ya kai haka ba, Yasira Taufeeƙ Fah, Yasira ko kin manta waye Taufeeƙ a wajenki ne?, sannan kuma ki rasa wa zaki so sai Sir, ki ruguza masa rayuwarsa da matar da yake so, wallahi Yasira ko a hanya bana fatan na sake haɗuwa da ke."
Da gudu Yasira ta nufi ɗakinsu jin Abbu na ƙirga lokaci, ko abu ɗaya bata dauka ba, taji Abbu na faɗin
'ku shiga ku fito min da ita, idan taƙi fitowa ku ɗauko ta aka ku yasar min da ita a wajen gidannan."
Bodyguards ne har guda huÉ—u suka shigo, ganin da gaske suke yasa ba tareda ta musu gardama ba, ta biyosu suka fito, da kallo tabi Zannur, wanda ke rarrashin Noor da banda kuka babu abinda takeyi, har suka fice a falon, sai raba ido takeyi ganin bataga yayanta ba.
Sai da suka rakata har bakin gate,kafin suka rufe ƙofan, suka yi shigewarsu, a gurin ta ɗurkushe tana wani irin kuka.
Handkerchief ɗin da taga an miƙo mata ya sata ɗaga kai ta kallesa
Da sauri ta miƙe tana faɗin
"yaya!"
Ba tareda ya kalleta ba yace
"tashi ki shiga Mota muje."
Miƙewa tayi ta shiga motan, shima Taufeeƙ ya zagaya ya shiga ya tada motar ya bar unguwan.
Kuka kawai takeyi da ƙyar ta buɗe baki tana faɗin
"Yaya dan Allah ka yafemin, Ni kaina bansan meyasa na aikata hakan ba, wallahi soyayya ce ta rufe min ido dan Allah yayana ka yafe min."
Ta ƙarasa da kuka
Bai ce komai ba, sai da ya yanki kwana kafin yace
"Yasira Ni ɗan uwanki ne, ko me kika aikata a duniya bazan so inga kin tagayyara ba, amma Ni kaina bazan iya zama da ke ba, saboda ke guba ce a cikin mutane, saboda haka yanzu zan saka ki a mota, ki koma ƙauye wajen Baba, Allah ya sadamu da alkhairinsa."
A daidai lokacin yayi parking a bakin tasha, fita yayi, itama ta sauƙo tana jin wani irin kuka na taso mata kamar zata haɗiye ranta.
Babu yadda ta iya, haka Taufeeƙ ya sata a mota, sannan ya bata dubu ashirin ta riƙe a hanunta, daga haka bai sake kallon ta ba ya juya ya bar wajen.
Tana kallonsa har ya tada motarsa ya fice a tashan gabaki É—aya kafin ta sake rushewa da wani matsanancin kukan.
Maimoon#
*💖ABNUR*💖
*By Maimoon*
*Elegant online writers* 📚📖
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.