Complete Hausa Novels

Abnur Complete Hausa Novel

Reading file: Abnur_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 21 of 24

*Page 21*

Har suka isa Airport, babu mai cewa komai a motan, daga Noor har Papi, kowa da irin tunanin da yake a zuciyarsa.

Juyowa Papi yayi ya kalleta, yadda ta matsa can jikin window, ta jingina kanta, idanunta a lumshe, sai kayi tunanin bacci takeyi.

Amma a bangaren Noor tunani kawai takeyi,

gwara ma tayi nisa da Zannur, idan ta tafi tare da mahaifinta, bazai sake ganinta ba, bazai sake jin É—uriyarki ta ba, ta fita daga rayuwarsa na har abada.

Tsayuwar da motar yayi, shi ya dawo dasu daga tunanin da suka lula, a hankali suka sauƙo daga motar, kowannen su jikinsa a sanyaye yake.

Har papi ya gama duk abinda zasu buƙata, hannunsa na cikin Noor, haka suka shiga jirgi yana riƙe da hannunta.

Duk da Noor bata taɓa shiga jirgi ba, but ta daure sosai, har jirgin ya daidaita a sararin samaniya.

Ƙarfe 8:00 na daren ranan Papi ya shigo da Noor cikin gidansa, a matsayin ƴarsa halak malak, wacce zai iya nunawa duka duniya with proud yace

"Noor Æ´atace."

A Falon ƙasa suka sami Sudais da Namra, suna hide nd seek, suna ganinsa suka nufosa da gudu suna faɗin
"papi"

ÆŠaga sudais yayi yana dariya kafin yace

"kazama ƙatoto kaima fa"
duk suka tuntsire da dariya, Namra tace

"papi you are welcome"

ta faÉ—a tana kallon Noor.

Jawo hannunta yayi yace

"oya common, greet your elder sister"

What's her name?

Namra ta tambaya tana cigaba da kallonta, dan ganin tsananin kaman da sukeyi da papinta.

"Noor"ya faÉ—a yana murmushi.

Ƙarasowa tayi gaban Noor kafin tace

"Ina wuni anty Noor"

Wani sanyi Noor taji tundaga tsakiyar kanta har babban yatsanta,
Yanzu waɗannan ɗin ƙannen ta ne?
Wani irin sonsu taji ya shiga ranta fiye da tunaninta,
Ta tsura ma Namra ido bata ko ƙiftawa.

Ammi dake sauƙowa daga sama, Farhaana a biye da ita, suka ƙaraso Falon, fuskar Ammi babu yabo babu fallasa, tace
"sannunku da zuwa." cikin harshen larabci.

Da sauri Farhaana ta ƙaraso tana kallon Noor, sai kuma ta juya ta kalli papi da sauri.

GyaÉ—a mata kai yayi yana murmushi.

Ai da gudu ta ƙaraso ta haye jikin Noor tana faɗin

"ukhty, Finally mun sameki, muna ta nemanki up and down, Ina kika shiga kika sa Papi kuka"

Dariya kawai Noor tayi, sannan tace

"gani ai na dawo"

ta faÉ—a tana matsar da Farhaana daga jikinta ta nufi Ammi dake Zaune, tsugunnawa tayi a hankali tace,

"ina wuni Nenne"

Wani kallo Maami tayi mata, kafin tace

"point of correction, Ammi, Ni ba Nenne bace, Ni Ammi ce."

Ta faɗa tana miƙewa ta bar falon.

Da ido duk suka bita, kafin papi ya ƙaraso ya riƙe hannun ta

"don't worry daughter, that's how she is, but zata sauƙo kinji, muje in kaiki ɗakin ki kiyi wanka kiji abinci, kiyi bacci, kin gaji, gobe sai ayi introducing ɗinki ga kowa duk dama kowa ya sanki,kece dai baki san kowa ba."

Batace komai ba tabi bayansa, har ya fara hawa steps ya juyo ya dubi Farhaana, kafin yace

"kuje ku kwanta dare yayi"

"Night Papi" duk suka faÉ—a a tare

"Night Papi's Angels"

Daga haka ya ja hannun Noor suka haura sama, sai da ya kaita wani katafaren É—aki, da ya gaji da haÉ—uwa, kafin ya ce mata

"Daughter kiyi wanka akwai kaya a cikin siff É—in, kafin zuwa gobe muje muyi shopping, za'a aiko miki abinci, sai kici ki kwanta kinji rabin raina?"

Kallon sa kawai takeyi, har ya miƙe ya je bakin ƙofa ya tsinkayo muryarta tana faɗin

"Meyasa ka tafi ka bar Nenne na,sannan ka kasa dawowa har sai bayan bata raye" ta faÉ—a idanunta na ciko wa da hawaye.

Cak ya tsaya da tafiyan, kafin ya juyo a hankali, dawowa yayi ya shafa kanta shima nasa idon na cika da hawaye

"daughter kin gaji, ki samu ki huta, zamuyi maganan gobe alright?"

Ya faÉ—a yana kallonta, dan dama ko bata tambaya ba gobe dolene ya sanar da ita.

Daga haka ya juya ya fice a É—akin yana jin sanyi a ransa.

Sai da ta yi wanka, sannan ta shirya cikin kayan bacci masu laushi, riga da wando, band ta sa ma kanta, kafin ta juya ta kalli tray ɗin dishes ɗin da aka ajiye akan ɗan madaidaicin dining table dake ɗakin, ƙarasawa tayi ta zauna ta buɗe abincin.

Bata wani ci sosai ba, ta dai ɗan tsatsakura, kafin ta miƙe, taje ta ƙarayin brush, tare da alwala, sallah tai-tayi tana godiya ga Allah da ya sada ta da mahaifinta, cikin lafiya da kwanciyar hankali.

A bangaren papi ma haka ne, ya kasa bacci, shima alwalar yayi, ya hau sallaya, yana ƙara gode ma Ubangiji da ya haɗa sa da ƴarsa sannan yayi ma Nenne addu'o'i sosai yana jin he is relieved from a very big burden.

A daidai wannan lokaci kuwa a garin Abuja, Zannur ne akan sallaya, babu abinda yake roƙo da addu'a akai sai Allah ya sa dashi da Noor.

Har ƙarfe 2:00 kowannensu na kan sallayarsa, kafin dukaninsu suka miƙe kamar suna ganin juna, kowa ya kwanta tare da addu'an bacci, da tunani iri, iri acikin ransa

(Asuba ta gari 🌝).

Washegari Noor ta tashi cikin matuƙar farin ciki, tare sukayi breakfast da duka ƴan gidan, kafin papi ya faɗa mata sunayensu da shekarun su,sannan suka zaga da ita ko ina a gidan, ita dai murmushi kawai takeyi.

Ammi kam daman suna gama cin abinci tayi wucewarta É—akinta.

Kamar yadda papi ya faÉ—a kuwa haka akayi, shopping suka tafi har da su Farhaana.

Noor taga gata, wanda ake kira gata, dan daga ƙarshe fashewa tayi da kuka kawai na tsantsan farinciki.

A gajiye suka dawo da kaya niƙi niƙi, kamar masu buɗe supermarket, tare duk suka shirya kayan tsaf, kafin Papi yace

"Noor kiyi wanka sai ki sameni a É—akina."

Noor tace "toh papi"
Fita yayi ya bar su, ya koma part É—insa.

Sai da ta gama duk abinda zatayi kafin ta nufi part din papi, a can ta samu Ammi, da alama Papi ne ya kirata, waje ta samu ta zauna, kafin papi yayi gyaran murya ya fara faÉ—in

"Noor, nasan zakiso kiji, miye dalilina na barinku danayi, a yanzu zan sanar dake."
Gyaran murya yayi kafin ya cigaba.

"Ni asalina ba ɗan ƙasar nan bane, mahaifina da mahaifiyata duka ƴan Dubai ne, ƙaddara ita ta haɗani da Yusuf a makaranta, ɗan Nigeria ne da yake karatu a Dubai, sakamakon scholarship da ya samu, tunda na haɗu da Yusuf, muka shaƙu sosai, har ya zamana kamar shine best friend ɗina, sannan ina matuƙar sha'awar Yaren Yusuf wato Hausa, da Yusuf yaga ina so, sai ya fara koya min, kasancewar ina da saurin koyan abu, cikin lokaci ƙalilan na fara gane Yaren Hausa, amma sam iyayena basason abota na da Yusuf, a ganinsu shi bak'ar fata ne, ɗan Nigeria, wanda Ni sam bai dame Ni ba.
Kullum Idan Yusuf ya tashi zuwa Nigeria ganin iyayensa, sai naji kamar na biyosa, saboda yadda nakeson ƙasar a raina, amma ina tsoron iyayena.
Ana haka sai muka gama makaranta, Yusuf yace min idan ya tafi ba lallai ne ya sake zuwa ba, alokacin na masa alƙawarin zanzo Nigeria gurinsa, Yusuf ya dinga jin daɗi.
Bayan tafiyan Yusuf, sai na rasa me zan ce ma iyayena, su barni na zo Nigeria, kasancewar Ni architecture ne yasa nace musu na samu wani contract, da zai iya ɗauka na aƙalla wata shida, a wata ƙasa, amma banyi kuskuren ce musu a Nigeria ba.
A zatona, wata shida ya isheni, in San Nigeria, da komai nata, in iya yarenta, sannan in zauna da Yusuf Abokina.
Iyayena basuyi kokonto ba, suka barni na tafi, tunda nazo Nigeria na ringa mamakin irin gidan da Yusuf ke ciki, gida ne ƙarami, mai ɗakuna biyu kacal, kuma a unguwar talakawa, hakan yasa na kama mana apartment guda muka zauna, a cikin garin Kaduna.
Kullum sai mun je mun zaga gari, mun ga abubuwa iri-iri, farinciki nakeyi sosai, kasancewar wannan shine abinda nake so.
Ana haka Yusuf yace min zaije ganin iyayensa, amma bazan iya zuwa ba, saboda a ƙauye ne, ai kuwa nace bai isaba, ko a jejine sai naje.
Haka muka shirya, muka nufi Baulawa, wanda shine ƙaddarar haɗuwa ta da Fatima.
Yusuf ɗan mai gari ne,hakan yasa muka sauƙa a gidan mai gari, amma kullum sai mun fita, ganin gari, saboda yadda garin keda matuƙar kyau.
Tun ganin farko da nayi ma Fatima a wani bikin shekara da ake yi a ƙauyen, Allah ya ɗaura min matuƙar sonta, har mamaki nakeyi, tayaya za'a yi na so ɗan Nigeria, iyayena baza su taɓa amincewa ba.
Amma babu ruwan zuciya, tun ina binta bata yarda, har itama ta fara kulani, soyayya mai matuƙar tsafta ta shiga tsakani na da ita, duk da sati ɗaya mukazo yi da Yusuf,amma sai nace masa Ni bazan tafi ba, Yusuf yayi ta min dariya, yana faɗin

"ka dai ga Æ´ar fara kyakkyawa"

sai dai kawai nayi murmushi.
Babu yadda na iya bayan mun cika kwana goma, haka na tafi na bar masoyiyata Fatima, tare da alƙawarin zan dawo idan Yusuf zai sake zuwa, dan kuwa makarantar da Yusuf ke koyarwa sun nemesa.
Hankali na bai tashi ba, sai da na yi waya da mahaifiyata, kwana biyu bayan dawowan mu daga Baulawa, ita take sanar dani wai kar nakai wata shida na dawo, za'a haÉ—ani da Æ´ar uwata Nadiya aure, saboda yadda take mutuwar sona.
A take nace mata, Ni bana sonta, amma sai ta ce min, ai sun riga sun amince.
Ƙarshe sai ce mata nayi, ai bazai yiwu in dawo ba tunda contract ne, su jira six months ɗin.
Haka suka aminci badan ransu ya so ba.
Ni na uzura ma Yusuf, muka sake komawa Baulawa.
tunda naga Fatima, nasa a raina, bazan iya rayuwa babu ita ba, kasancewar a hannun matar mahaifinta take, sam bata samun kulawa.
Ai kuwa ina zuwa na zame mata cingam, ko ina zata je sai na bita, har mutane suka fara saka mana ido.
Ranar da bazan taɓa mantawa ba, a rannan ina zazzaɓi, hakan yasa banje ko ina ba, tun safe bamu haɗu da Fatima ba.
Yusuf kuma yaje gurin mai gari, ina kwance, sai naji an buga ƙyauren a hankali, miƙewa nayi da ƙarfin hali, na buɗe, ga mamakina sai naga Fatima.
Dana ce ta shigo, sai naga kaman tana tsoro, sai nace mata babu komai ta shigo, idan bata shigo ba bazan kulata a wajen ba, dan jiri nakeji bazan iya tsayuwa ba, hakan yasa ta shigo, kwanon abinci ta ajiyemin, tace wai ta kawo min inci, murmushi nayi na É—auka ina ci muna hira da ita, amma duk ta kasa sakewa.
Can kuma sai ta miƙe tace min, ita zata tafi, hakan yasa nima na rakota ƙofa.
Mutanen da muka gani a bakin ƙofa ya sani matuƙar mamaki, dan kuwa kusan rabin ƴan garin suna bakin ƙofar mu.
Haka suka ƙeƙashe suka ce wai ɓata mata tarbiyya nakeyi ai sun jima da ganin take-takena, abun ya bani mamaki, alokacin sai ga Yusuf, shima yayi iya ƙoƙarinsa ya fahimtar da su amma sam suka ƙi fahimta, a nan take suka ce sai dai muje a ɗaura mana aure, dan su ba'a ɓata musu yara a zauna lafiya,
Bayan ɗauki ba daɗi da akayi tayi, ganin Fatima na kuka, kuma nasan Ni na janyo mata, kuma ina sonta yasa na amince, ai kuwa ba'a ɗau lokaci ba aka ɗaura mana aure wanda nake jinsa yamin banbaraƙwai, su wasu irin mutane ne, babanta bai damuba, haka ma kishiyar mahaifiyarta, washe gari muka bar ƙauyen, muka taho cikin Kaduna, anan muka zauna.
Wani irin tsabtataccen soyayya muke shimfiÉ—awa, wanda har nakejin rayuwata tafi ko yaushe daÉ—i, bana son tuno cewa wata shida nayi da mahaifana.
Kwanci tashi, har wata shida, ya wuce, amma bana tunanin komawa gida, iyayena sunyi kira har sun gaji bana É—auka, a wata na takwas na samu mail daga baba na, yayi bincike ya gano ina Nigeria, kuma idan har ban koma ba a cikin sati na gaba, shikadai yasan abinda zai min.
Nasan halin mahaifina, yana da matuƙar zuciya, hakan yasa na yanke shawaran komawa, but zan je in shayo kan iyayena, in dawo in tafi da Fatima.
Na yi ma Fatima bayanin komai, ta amince, amma ta sa nayi mata alƙawarin zan dawo gareta.
Nayi iya yi na, inga na fahimtar da iyayena, amma sam suka nuna basu san da maganar ba, har ƙoƙarin tsine min sukayi idan har na cigaba da wannan maganan.
Sannan basu ɓata lokaci ba suka ɗaura min aure da Nadiya, sannan sai da mahaifina ya tabbatar ya goge duk wani abu da zai haɗa Ni da Yusuf, bare har inji lafiyan Fatima, bayan haka, mahaifina da mahaifiyata, suka ce, idan har na taka ƙafa na a Nigeria, to wallahi bazasu taɓa yafe min ba.
na shiga wani hali, har sai da na kwanta a asibiti, amma kasancewar bani da mafita ya sa na hakura na auri Nadiya, Wanda Alhamdulillah yanzu muna da ya'ya har uku da ita.
Yusuf kam ganin kuɗin gida ya ƙare, kuma bazai iya sake biyaba, yasa ya tattara Fatima ya mayar da ita Baulawa, amma acikin kuɗi mai yawan da na bashi kafin na tafi, sai ya siya mata gida, sannan yace musu nayi tafiya ne kuma zan dawo.
Sam bansan akwai cikinki ba, ita kaÉ—ai tayi renon cikinki ta haife ki.

A yanzu haka da nake faɗa miki, mahaifiyata da mahaifina, sun rasu a wani plane crash a hanyar su ta zuwa Iraq, Amma kafin tafiyarsu sun tabbatar min zan iya zuwa Nigeria. Naji matuƙar daɗi ashe sune zasu barni, dan tafiyan da basu dawo ba kenan.
Sai dai kash, ina zuwa sai mai gari ya sanar da Ni Fatima ta rasu, ke kuma kinyi Aure.
a wajensa na samu hoton ki, na bazama nemanki, amma na rasa ki, sai bawan Allah khamal ya kirani yace kina wajensa."

Ya faÉ—a ya share hawayen idanunsa.

Itakam Noor kuka take wiwi, ita kanta Nadiya kuka takeyi, dan bai taɓa bata labari ba, kenan Nenne yake zanawa duk kwanan duniya?

A hankali ta taso ta É—ago Noor tana faÉ—in

"kiyi haƙuri Noor, insha Allah zan maye miki gurbin Nenne."

Da mamaki yake kallonta, kafin yayi murmushi yace

"Nadiya na gode."

Sai da suka É—an lafa, kafin ta sake basu labarin tasowarta da rasuwar Nenne, zuwa aurenta da Zannur har kawo yau.

Duk shiru sukayi suna jinjina al'amarin, kafin Noor tace

"To papi Ammi da su Farhaana kuma a ina suka iya Hausa?"

Murmushi Ammi tayi tana faÉ—in

"ai kowa ya zauna da shi sai ya iya Hausa, sai da ya tabbatar mun iya"

ta faÉ—a tana dariya,
Shima dariyar yayi.

A ranan sun wuni cikin farinciki a gidan, jifa jifa takan tuno Zannur, amma sai ta kauda a ranta, dan bataso tana tunoshi.

Rayuwar Noor a gidan iyayenta, rayuwa ce mai cike da kulawa, gata, da soyayyah, babu abinda ta nema ta rasa, hakan yasa ta sake kyau, ta sake zama Æ´ar gayu, dan kuwa, Ammi basuga wannan shopping center É—in, basuga wannan.

Zannur kam.......

Maimoon#

*💖*ABNUR*💖*

*By Maimoon*

*Elegant online writers* 📚📖

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.