Abnur Complete Hausa Novel
Reading file: Abnur_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 24 of 24
*Page 24*
Kwanan su Papi uku, suka tattara suka koma Kaduna, cike da kewar Noor, bayan Papi ya zaunar da su gabaÉ—aya ya musu nasiha sosai.
Duk da yadda Abbu da Maami, suke kula da Noor, amma sai da tayi kewar Ammi da Papi, da su Farhaana, daƙyar suka rabu a Airport, tana kuka kaman zata shiɗe.
Rungumeta Zannur yayi, yana aikin rarrashi, amma sam Noor taƙi yin shiru, har suka shiga Mota Noor kuka take, ya rasa yanda zai yi da ita tayi shiru, ya yi rarrashin, yayi daɗin bakin amma duk a banza.
Har suka iso Noor taƙi yin shiru, yana yin parking tayi saurin ficewa daga motan, da gudu ta ƙarasa cikin gidan ta haura sama tare da shigewa ɗakinta har da murza key.
Murmushi yayi kawai, tare da shafa sumarsa, a ransa yana faÉ—in
"Zakiyi bayani yarinya."
Bai bi takanta ba yayi wucewarsa É—akinsa, shiryawa yayi ya fice a gidan tare da TaufeeÆ™.
Sai da ta gaji dan kanta tayi shiru, har bacci ya É—auke ta.
Ƙarfe 12 dai-dai ta farka, a hankali ta miƙe daga kan gadon, tare da yin miƙa.
"Hmm" Zannur ya faÉ—a yana gyara zaman laptop É—in dake kan cinyarsa.
Miƙewa tayi daga kan gadon, ta wuce toilet, Yana kallonta har ta fito, ta gama shiryawa cikin riga da wando band ta saka a kanta, kafin ta ɗauki hijab ɗinta ta zura, sai da tayi sallah, tayi addu'o'inta kafin ta miƙe ta naɗe sallayan, ta zame hijab ɗin ta naɗe ta ajiye.
Gadon ta sake haurawa, ta ja bargo tayi kwanciyarta.
Murmushi yayi, a zuciyarsa yana faÉ—in
"kin gaji da kukan kenan?"
A hankali ya rufe laptop É—in, kafin ya É—au wayarsa ya kira kitchen.
Asabe yasa ta kai mata abinci kafin ya kashe wayarsa.
Har yamma kafin ya dawo, a falo ya sami Maami, da Abbu, wanda suma zuwa jibi suke shirin komawa Dubai.
Kasancewar Maami ta gama zaga danginta, dama abinda ya jinkirta tafiyan nasu kenan.
Zama yayi a falon yana É—an hira sama sama da su Maami, amma gabaki É—aya hankalinsa na ga Noor.
Daga ƙarshe miƙewa yayi kawai ya nufi sama.
Ƙofan ta da yaji a kulle ya sa shi yin murmushin da bai shirya ba,
kenan fushi takeyi da shi.
Juyawa yayi ya nufi É—akinsa, laptop É—insa ya bude yana kallonta, ganin tana cin abinci da aka kai mata ya sashi shafa kansa, a fili ya furta
"Silly girl."
Bai sake ganinta ba, sai ranan da su Maami zasu tafi, kasancewar tare zasu kaisu Airport ya sa ta shiryawa cikin abaya kalar ja da fari, da yayi mata matuƙar kyau.
Har suka isa Airport, taƙi kallonsa, ita a dole fushi take dashi, ai yana ganin tana kuka amma ya shareta.
Shidai satan kallonta kawai yakeyi ta mirror, idan suka haÉ—a ido sai dai yayi murmushi, ita kuma ta galla masa harara.
Nan ma dai bata fasa kukan ba, ganin su Maami zasu tafi, dan ta saba da Maami sosai.
Kallonta kawai yakeyi, a ransa yana tunanin ina zata kai saurin kukanta.
Sai da jirginsu Maami ya ɗaga kafin suka bar Airport ɗin, amma sam Noor taƙi kulasa.
Shima bai kulata ba har suka iso gida, buɗe motar tayi a fusace ganin ya ƙi tankanta ta bugo murfin da ƙarfi, ta nufi cikin gida.
Girgiza kansa kawai yayi, shima ya fito daga motan, sannan yayi mata key ya nufi cikin gidan.
Har dare babu wanda ya kula wani, Noor kam ta cika tayi fam.
*********
Ƙarfe 12:00pm Zannur ya rufe laptop ɗin, kasancewar ya gama aikin da yakeyi.
Miƙewa yayi ya nufi ɗakin Noor, jinsa a rufe ya sashi komawa ya ɗauko spare key, a ransa yana addu'ar Allah yasa ta cire makullin jiki.
Cikin Sa'a kuwa Kofar ta buɗe, wani ajiyar zuciya ya sauƙe, kafin ya ƙarasa cikin ɗakin a hankali, ya maida ƙofar ya rufe.
Kallonta ya tsaya yi, yadda ta duƙunƙune a bargo, ta ɓata fuska, sai kawai yayi murmushi tare da ƙarasawa, botiran rigan baccin sa ya buɗe gabaki ɗaya, kafin a hankali ya haura kan gadon, tare da jawota gaba ɗaya jikinsa.
Wani ajiyar zuciya suka sauƙe a tare, cikin bacci Noor ta jita a jikin mutum, hakan yasa ta sake gyara kwanciyar ta a kan bare chest ɗinsa, tana turo baki.
Hannunsa yasa ya zare band É—in kanta, gashin ta ya barbaje, kafin ya sa hanunsa a cikin sumar, yana shafawa, a hankali.
Buɗe idanunta dake cike da bacci ta shigayi, kafin ta miƙe da sauri, fahimtar da tayi ba mafarki takeyi ba, a jikin mutum take da gaske.
Da sauri ya maida ita ya matse a jikinsa yana hura mata, iska a fuska.
Æata fuska tayi, tana faÉ—in
"Miye hakan ka shigo min ɗaki?, ta ina ma tukunna ka shigo bayan na rufe ƙofar?"
Murmushi yayi a hankali ya raÉ—a mata
"Dama baki san cewa mijinnaki aljani bane, ɓullo wa kawai nayi"
"Hmm" kawai tace tana sake yunƙurin tashi daga jikinsa.
Ƙin saketa yayi, a hankali yace
"Baby, meye na?" ya faÉ—a yana marairaicewa
Dukansa ta shiga yi a ƙirjinsa, kafin ta fashe da kuka,
"Ni bansani ba, baka damu da Ni ba, ka mayar da ni wajen Papi, baka so na!"
Da sauri ya birkito da ita, ya koma Samanta, yana kallon cikin ƙwayar idanunta.
"Don't ever say that again, wallahi ina sonki kaÉ—ai yayi kaÉ—an, akan abinda nake ji tattare dani akanki, ina sonki, irin son da babu wani namiji da kema matar sa irinsa,
Ina sonki fiye da duk yanda wani mai kwatance zai kwatanta, i never knew you were the reason I live, sai da kika barni Noor."
Ajiyar zuciya kawai Noor take sauƙe wa, tana kallonsa, yadda yake confessing soyayyarsa a gareta, da sauri ta sa yatsanta a bakinsa tana faɗin
" Shhhh, Its enough, ya isa haka, na yarda mijina, nasan kana sona, ko da ace baka furta komai ba."
Ta faɗa hawaye na sauƙa a gefen idanunta. Sai da ta yi shiru kafin ta cigaba
"Wallahi nima ina sonka, fiye da yadda zaka iya misaltawa, bansan sanda na fara sonka ba, amma abinda na sani a yanzu shine, bazan iya rayuwa ba tare da kai ba..."
Kasa ƙarasawa tayi jin bakinsa a cikin nata, wani hot kisses ya ke bata, da ƙwaƙwalwarta ta gagara ɗauka, jikin sa har rawa yakeyi, gabaɗaya ya gigata mata lissafi."
Sun shafe tsawon lokaci a haka, kafin a hankali,ya mirgina ya koma gefe yana sauƙe numfashi, idanunsa sun kaɗa sunyi jajir, batare da ya ce mata komai ba ya sauƙa a kan gadon, zagayowa yayi, a hankali ya riƙe hannuta yana kallon ta,
"Zo muje"
Zuciyar ta ce ta tsinke da sauri cikin in Ina tace
"Ina..za..mu je..?
Bai bata amsa ba, ya sunkuyo tare da É—aga ta cak,
Nutsuwa ta samu kanta da yi a kan faffaɗar ƙirjinsa, a hankali ya juya da ita, ya bar ɗakin.
Har suka shiga nasa ɗakin bata daina jin bugun zuciya ba, a hankali ya sauƙe ta a tsakiyar daƙin yana kallonta kafin ya juya ya nufi toilet.
Gefen gado ta samu ta zauna, tana ƙare ma ɗakin nasa kallo, ba ƙaramin kyau ɗakin yayi mata ba,kasancewar bata taɓa shiga ba, mayen turarensa na *_SHUMUKH_* ya gama kama ɗakin.
Fitowa yayi daga toilet É—in, yana daure da towel da alama, wanka yayi, a hankali ya dubeta kafin yace, ki shiga nan kiyi wanka, ki haÉ—o da alwala.
Da sauri ta girgiza masa kai tana faÉ—in,
Ah ah, zanje inyi a É—akina.
Bai kulata ba ya ƙarasa jikin Kofar ya rufe da key, sannan ya zare key ɗin ya ƙarasa jikin mirror, yana gyara sumar kansa.
Babu yadda ta iya haka ta ƙarasa toilet ɗin.
Mamaki ta tsaya yi, yadda toilet É—in sa yake abin sha'awa, kamar ba bayi ba.
A haka ta ƙarasa, sai da ta zare kayan jikinta, tayi wanka, sannan ta ɗauro alwala, bathrub ta sanya a jikinta, kalar skyblue kafin ta fito a hankali, tana leƙawa cikin ɗakin.
A zaune ta gansa a bakin gado yana operating system É—insa.
A hankali ta fito, cikin sanɗa, har ta iso tsakiyar daƙin, kafin ya ɗaga kansa yana kallonta.
Tura baki tayi, cikin shagwaɓa ta ce
"to Ni ai babu kayan da zan saka a É—akinnan"
Shafa kansa yayi kafin ya juya ya fice a É—akin, can sai gashi ya dawo, da kayan bacci, har da hijab.
Miƙa mata yayi, ta karɓa, sai da ta gama shiryawa tsab, kafin ya gabatar musu da sallah raka'a biyu.
Addu'o'i yayi musu sosai, kafin a hankali ya zare hijab É—in jikinta, linkewa yayi da kansa ya ajiye yana mata murmushi.
A hankali ta miƙe, dan bacci take ji, ta nufi gadon, kwanciya tayi tare da shigewa bargonsa mai tsananin laushi.
Sai da ya gama abinda yake yi duka, kafin ya hauro gadon shima, a hankali ya janyota jikinsa, tareda yi Mata raÉ—a a kunne.
Zaro ido tayi waje tana kallonsa, ta buÉ—e baki da niyyar magana, bai bata daman maganan ba ya haÉ—e bakinsu waje É—aya yana jin wani shaukin sonta na É—ibarsa.
Tun Noor na ganin kamar wasa, har abin ya fara wuce tunani da lissafinta, sai lokacin kuka ya zo mata, ta shiga magiya amma ina, Zannur ya riga yayi nisa, ya sha alwashin mayar da ita cikakkiyar mace, sannan Mrs Zannur Shuraim.
Ba ƙaramin wahala Noor ta sha ba a wannan daren, har sai da kukan ma ya daina fita.
sai bayan komai ya lafa kafin ya janyota jikinsa wasu hawaye Masu É—umi na bin fuskarsa, albarka kam ta shasu kwando kwando. Ita kam Noor banda kuka babu abinda takeyi, sai sake birkita masa lissafi takeyi.
A ranar ya tabbatar yana ma Noor son so, irin sonda baya tunanin wani ya taɓa hasashensa.
***_10 years Later_*
Mrs Zannur Shuraim ce a zaune, a babban falon da ya ji komai na rayuwa, a hankali ta miƙe tare da yaron da ke kan Cinyarta wanda bazai wuce shekara ɗaya da watanni ba.
Daƙin yara ta kaisa, tare da kwantar da shi a kan gadonsa, tana lallaɓa shi, dan ta tabbata idan har ya farka, rikici zai saka mata, a hankali ta zare hannunta, tare da fita daga ɗakin.
Ƙasa ta sauƙo, ganin babu kowa a falon ya sata ƙarasa wa ɗakin hoto dan ta tabbatar duk suna can.
Daga bakin ƙofa ta tsaya tana kallonsu, yadda Zannur ya sa ƴaƴansu guda biyu a gaba, Fatima, da Shuraim, yana koya musu ɗaukan hoto
Fatima wacce suke kira da, Nihal tace
"daddy na É—auka, wallahi i clicked it right! Adnan ka gani!"
ta faÉ—a tana tsalle tare da nuna ma Shuraim da ya kasa É—aukan ko É—aya.
Murmushi Zannur yayi yana faÉ—in
"shima yanzu zai É—auka ki bar yi mishi dariya"
Ƙarasowa tayi cikin ɗakin a hankali tana murmushi,
"Daddy saura Ni"
Ta faɗa cikin shagwaɓa da sigar zolaya.
Juyowa sukayi Dukansu suna kallonta, kafin Shuraim yace
"daddy ni Ummi zan É—auka, bazan É—auki mimi ba, tunda ta min dariya"
"To shikenan, but is daddy allowed to join Ummi? Ya tambaya yana murmushi
"Eh kai kaÉ—ai amma"
Matsawa kusa da ita yayi yace
"to my boy"
Ai Yana shirin É—auka Mimi tayi saurin shiga ya É—auka da ita, nan fa suka shiga rikici.
Noor ce ta ƙarasa tare da karɓan mini câmeras ɗin hannunsu, to ya isa haka, kuje lesson teacher ɗinku na hanya, don't keep her waiting.
"Toh Ummi" suka faÉ—a a tare, Da sauri suka juya suka fice a É—akin dan É—auko littafan makarantarsu.
Janyota Zannur yayi yana faÉ—in,
"me kikace É—azu?, kikace saura ke? To muje in koya miki naki"
Turo baki tayi tana faÉ—in Nikam
"ah ah yanzu fa na samu sadeeq yayi bacci"
bai jira mai zatace ba, ya ja hannunta suka fice a É—akin.
Yasira kam zuwa yanzu, ƴaƴanta huɗu, dan kuwa tun komawarta, Baba yayi mata aure da wani dattijo, mutumin yana da hankali sosai, kuma yana son Yasira sosai, a yanzu ta kwantar da hankalinta, ta riƙe mijinnata da ƴaƴan sa tana zaune lafiya da su.
TaufeeÆ™ da Amina duniya sabuwa, dan kuwa yanzu Æ´aÆ´ansu biyu, suna zaune cikin kwanciyar hankali da soyayyah.
Asabe tayi aure Ita ma, har tana da ya'ya biyu.
Papi da Ammi, suna zuwa Nigeria, duk sanda suka ji kewan su Noor, haka Abbu da Maami, kamar yadda suma suke zuwa musu duk sanda suka samu hutu daga wajajen aikinsu.
A yanzu ana shirin auren Farhaana, da saurayinta ashraf acan Dubai kenan, Noor ana ta shirye shiryen zuwa, dan kuwa itace ƙirjin biki.
Tammat bi hamdillah, anan na kawo ƙarshen littafin ABNUR, kuskuren da nayi ina roƙon Allah ya yafemin, da Ni da ku baki ɗaya,na taƙaita labarin saboda wasu dalilai nawa.
Alhamdulillah, Alhamdulillah Alhamdulillah.
Maimoon#
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.