Abnur Complete Hausa Novel
Reading file: Abnur_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 20 of 24
*Page 20*
Kamar yadda Umma tace kuwa, Baba na dawowa, khamal ya zo ya samesa da maganan
"Khamal gaskiya kayi tunani mai kyau, amma kaÉ—an jira kaÉ—an,yarinyar tana cikin damuwa, kuma nima ina tunanin mijin nata ne yace mahaifinta, dan yasan zata so haÉ—uwa da mahaifinta."
"Shikenan Baba, babu damuwa, duk sanda kuka ga ya dace a sanar da su, sai a sanar dasu."
"Yauwa khamal Allah yayi maka albarka."
"Ameen Baba" daga haka yayi ma Baba sallama ya bar É—akin.
**********
"Abdul kaji yadda mukayi da Baba, Amma gaskiya ya kamata ta koma ga mijin ta, bana tunanin zamanta anan shi yafi"
khamal ya faÉ—a yana kallon Abdul da ke zaune a gefensa ya zuba masa ido.
Gyara zama Abdul yayi kafin yace
"to kai miye damuwarka ne, tunda ba akanka take ba, ka barta mana ai zasu maidata koh?"
"Bazaka gane ba, ni nafiso ta koma kawai, nima kaina bansan meyasa ba, ina mata kallon ƙanwata na jini, kuma ai kaga zanso ta zauna a gidan mijinta, kuma idan ka duba yarintace kawai yasa ta baro gida, idan ba haka ba ai alkhairinsa yafi cutarwarsa yawa a gareta."
"Hakane kam to mai zai hana kawai idan mun shiga cikin gari anjima, mu nemi waya mu kira kawai mu sanar da shi mahaifinnata, idan ma mijinnata ne ke ƙaryar mahaifinta, duk dai mu sanar musu, kaga da kansu zasu zo har nan su dauke ta, sai kace ba ka san ta yaya suka sani ba, ko ya ka gani."
Shiru khamal yayi kamar mai tunani, sai kuma yace
"kana ganin babu wata matsala?"
"Kaji ka da wani zance, ai taimakonta kake son yi ba cutar da ita ba."
"Shikenan to, Allah ya kaimu, sai muje mu kira É—in."
"Yauwa abokina, Allah ai yaga nufinka"
Daga haka suka miƙe suka jera suna cigaba da tattauna maganan.
*_Kaduna Nigeria___*_
Papi ne a zaune a falonsa, ya ƙura ma hoton Noor idanu, yayi zaton abin zai zo masa da sauƙi wajen neman Noor, Amma yanzu ya gane aiki ne babba a gabansa idan har yana so ya gana da ƴarsa.
Miƙewa yayi da hoton, ya nufi ɗakin zane zanensa, a hankali ya zauna a kan kujerar zanen, ya shiga zana Noor, idanunsa na kawo ruwa, Fatima kaɗai yake tunawa, ta rasu ba tare da taji uzurinsa ta yafe masa ba.
Wayar sa dake gefensa ce tayi ƙara, a hankali ya juya ya kalli screen ɗin ganin babu suna ya sashi cigaba da zannen,
wani kiranne ya sake shigowa, a hankali ya kai hannu ya É—aga yana faÉ—in
"Assalamu alaikum"
Mai shagon kiran jin an amsa ya mikawa khamal wayan yana faÉ—in
"gashi kayi magana"
Karɓa khamal yayi a nutse yana kallon Abdul dake gefensa yana gyaɗa masa kai alamun ya faɗa kar yaji komai.
Cikin sanyin murya ya amsa sallaman sannan ya É—aura da faÉ—in
"Ina wuni?", ba tare da ya jira amsa ba ya cigaba
"sunana khamal, kai ne kake neman ƴarka data ɓata?"
A zabure papi ya miƙe yana faɗin
"Ni ne!, eh Ni ne, ka ganta ne?, ka san inda take?, faÉ—a min a ina take please zanzo yanzu"
"Uhm..eh Noor tana wajenmu, kuma yanzu haka mu muna Kano ne, a wani ƙauye mai suna Marke, Noor tana tare da mu a can"
"Alhamdulillah, Alhamdulillah ya Allah, pleaaaaase ka min wannan taimakon, kar ka bari ta bar inda kake, zan nemi Flight zuwa Kano yanzu, Please ku jirani."
Shiru khamal yayi kafin yace
"ranka ya daÉ—e ka bari zuwa gobe mana, idan ya so sai mu zo mu jiraka, ta yanda zamu iya yin waya da kai, dan wayar ba namu bane, na wani ne muka ara."
"Kar ku damu, dan Allah ku jira Ni zanzo bazan iya kai gobe banga Noor ba", ya faÉ—a yana fitowa da sauri daga É—akinsa cikin sassarfa.
"To yallaɓai zamu gwada jiranka sai kazo."
Abdul da ke kallonsa bayan ya kashe wayar, yace
"wai jiransa zamuyi?"
"Haka dai yace"
"Tabb, ko da yake ba zai fi awa ɗaya ba zuwa da rabi, sai mu nemi waje mu zauna, sai kace wani abin yaƙi ya bari gobe mana."
"Nima haka nace amma yace kawai mu jira sa."
Papi na kashe wayan ya fito da sassarfa, Farhaana da Ammi dake falon ƙasa, suka miƙe suna kallonsa.
ganin yana shirin fita a falon yasa Ammi faÉ—in
"Ina zakaje haka?, ina fatan lafiya!"
Batare da ya juyo ba yaje,
"na samu Æ´ata, zanje in zo da ita."
Bai jira amsar su ba ya fice a gidan, ko driver bai nema ba yayi driving kansa zuwa airport, bai wani ɓata lokaci ba ya gama duk abinda zai buƙata, jirgi ya tashi da shi zuwa Kano.
A cikin awa daya jirgi ya sauƙa a Kano.
Layin da suka kirasa da shi yayi ta kira amma ba'a É—auka, rasa yanda zaiyi yayi, idanunsa har sun kaÉ—a,
Sake dialling yayi a karo na bakwai, kafin mutumin wanda dama su khamal sun sanar dashi ko da an kira basa nan, ya kirasu dan babu wajen zama a wajen, ya É—aga yana faÉ—in
"ranka ya daÉ—e sunje suci abinci"
da sauri papi ya ce,
"dan Allah a ina kuke, zanzo yanzu na samesu a nan"
"To babu damuwa bari na maka kwatance."
Da ƙyar papi ya samu ya isa inda suke masa bayani, dan ma mai motan da yayi shata ba inda bai sani ba a garin Kano.
Motan na parking yayi saurin fitowa, da sauri mai shagon yace
"ranka ya daÉ—e kai ne muke waya da kai?"
"Eh nine Ina khamal din yake? wanda ya kira Ni É—azu"
"Eh suna zuwa ai, ina ganin bayan sunci abincin sun tsaya Sallah ne."
Bai rufe bakinsa ba sai ga khamal da Abdul suna tahowa.
"Yauwa gasu can ma, sune suka kiraka."
Ya faÉ—a yana nuna su khamal.
Suma tun daga nesa suka kallonsa,
"Tabbass wannan shine mahaifin Noor, ko kokonto banayi"
khamal ya faÉ—a yana dafa Abdul
"To mu ƙarasa mana"
Sai da sukayi musabaha, kafin yace
"wayene khamal wanda ya kirani yace min yasan inda Noor É—ina take a cikinku?"
Da sauri Abdul ya nuna khamal yana faÉ—in
"ai a gidan su noor É—in take."
Rungume sa papi yayi, ba tare da tunanin komai ba,
"Nagode khamal, dan Allah ka kaini wajen Æ´ata yanzu ina so in ganta."
"Babu damuwa yanzu zan kaika, zakaga Æ´arka insha Allahu" kamal ya faÉ—a yana É—agowa daga jikin papi.
Sai da suka ma mai shago godiya kafin papi ya basa kuÉ—i masu yawa, ai kuwa ya zube yana ta godiya.
A motar da papi ya zo da ita suka nufi cikin ƙauyen, kasancewar mota kan shiga yasa har ƙofar gidan su khamal suka zo.
Sai lokacin khamal yayi tunanin, me su Umma zasuce masa?, amma sai ya share ko ma me zasu ce, shi ya haÉ—a Æ´a da mahaifine.
Noor da ke tsakar gida tana kwasan shanya, taji zuciyarta ta buga da ƙarfi,
da sauri ta dafe ƙirjinta tana faɗin
"inna lillahi wa inna ilaihi raji'un"
"Lafiya Noor"
Umma ta faÉ—a daga zaunen da take a tsakar gida tana kallonta.
"Zuciyata ce ta tsinke Umma, babu komai"
daga nan ta cigaba da
Abinda takeyi.
Baba da ya fito daga É—akin Umma yana shirin fita, sai ga khamal ya shigo jiki a sanyaye.
Sunkuyar da kansa yayi kafin yace
"Baba mun yi baƙo yana neman izinin shigowa"
Da mamakin duk suke kallon sa kafin, Baba yace
"wayene?"
Khamal bai amsa ba hakan yasa Baba faÉ—in
"kace masa ya ƙaraso, tunda kai ka kasa faɗan wayene."
Sai kuma ya juya ga Noor Yana faÉ—in
"Noor É—auko wani tabarmar a shinfiÉ—a masa."
"To Baba" ta faÉ—a tana sake jin yadda zuciyarta ke bugawa.
Sallamar da taji ya sata saurin É—agowa dan taji ta kwaÉ—aitu da ganin mai sallaman.
Cikin idon mahaifinta idanunta suka faɗa, da sauri ta dafe ƙirjinta tana kallonsa babu ko ƙiftawa.
Shikam hawayen idanunsa ne suka kasa tsayuwa, suka shiga sauƙa akan fuskarsa.
Da sauri ya ƙara so ya na faɗin
"Noor!"
Da kokonto, wai gashi ga Æ´ar Fatima kuma Æ´arsa, ko dai mafarki yakeyi ne?
Itama tuni hawaye ya jiƙa fuskarta, dan tabbass bata buƙatar ace mata wannan mahaifinta ne, kamar da takeyi da shi ma kaɗai ya wadatar.
Da sauri ya nufe ta, yana faÉ—in
" yarinya ta ashe kina nan?, ina ta nemank...."
Hannu ta É—aga masa da sauri idanunta na kwararar da hawaye,
"Kar ka ƙaraso kusa dani, Ni ba ƴarka bace, kuma bazan taɓa zama ƴarka ba, da ace Ni ƴarka ce bazaka taɓa wofintar da rayuwata da ta mahaifiyata ba, bana son ganinka Dan Allah ka tafi ka barni, in cigaba da rayuwa kamar yanda na faro."
With shock yake kallonta, amma ya gagara ƙara ɗaga ƙafan kamar yadda ta faɗa
"Noor ki saurareni, ban wofintar da ku dan son raina ba, hasalima bansan da akwai cikinki ba Noor, kuma wallahi duk duniya babu wanda ya kaini sonku ke da Fatima."
"ƙarya kakeyi kai ba mahaifina bane, kuma bazan taɓa ɗaukan ka a matsayin mahaifina b........"
Tass!, sauƙar Marin da taji a fuskarta, ya sata haɗiye sauran maganan da ke bakinta, tana kallon Umma da shock,
Jawota Umma tayi ta rungume, tana kuka itama tana faÉ—in,
"Noor mahaifinki ne shi, ko me yayi miki bai cancanci ko wani irin magana daga bakin ki ba, ki sauraresa kiji dalilinsa, daga nan sai ki yanke duk hukunci da kika ga ya dace dashi."
Fashewa tayi da kuka tana sake rungume Umma,
"Ummah baya so na, bayason Nenne, shiyasa ya tafi ya barmu, kowa baya sona, Zannur baya sona, wani irin rayuwace irin tawa."
Ta faɗa tana ɗurkushewa a wajen, tana cigaba da wani irin kuka mai taɓa zuciya.
Da sauri papi da ya gama daskarewa a tsaye, shima ya kai ƙasa ya riƙo ta gabaɗaya, fuskarsa ta gama yin jajazir.
'Wayace miki banasonki Noor" ya faÉ—a jikinsa har rawa yakeyi,
"wallahi Noor nafi kowa sonki, pleaaaaase ki yafe ma papi kinji daughter."
Rungumesa tayi tana sake fashewa da sabon kuka, shi kanshi ya kasa daurewa, hawaye kawai ke fita daga idanunsa, ya rungumeta sosai a jikinsa yana jin kamar ya maida ita cikinsa ya sake haifo ta, saboda tsananin son da yake ji yana mata.
Sun É—auki tsawon lokaci, kafin kowa ya dawo nutsuwarsa.
Baba da ke tsaye har lokacin yayi gyaran murya yana faÉ—in,
"To masha Allah, Allah mai hikima"
Umma da ta ƙarasa shinfiɗa tabarmar da Noor ta yasar tace,
"Alhaji bismilla."
Khamal kam da Abdul kallon ikon Allah kawai sukeyi.
Kafin kowa ya sami waje ya zauna, Noor kam tana jikin papi, Dan shi kanshi ya ƙi bari ta matsa daga kusa da shi.
Sai da kowa ya nutsu kafin Baba ya faÉ—a ma papi komai da ya faru, daga haÉ—uwarsu da Noor zuwa yanzu.
Jinjina kai kawai papi yakeyi kafin yace
"nagode, nagode, bansan da wani kalma zan yi anfani in gode muku ba, dan kun riƙe min yata mafi soyuwa a gareni, bani da abinda zan biyaku da shi, sai dai ina muku addu'ar Allah ya saka muku da mafificin alkhairinsa."
Ameen duk suka amsa dashi kafin papi ya É—ora da fadin,
"kuma ina neman alfarmarku, ku barni in tafi da Noor yau, dan Allah."
Da sauri Umma tace
"Alhaji da dai an bari zuwa gobe, yanzu yamma tayi", ta faÉ—a hawaye na ciko idanunta dan sam batason rabuwa da Noor.
"Ah ah Aisha ki barshi ya tafi da Æ´arsa, ai da nan da can duk É—aya ne, kuma ai zumunci ba yanke wa zai yi ba, Noor Æ´arkice har abada."
Da sauri papi yave
"wannan haka yake, har abada zumuncin ku da Noor ba zai taɓa yankewa ba na muku alƙawarin hakan."
"Shikenan Alhaji mun gode sosai",
Umma ta faÉ—a tana matsar hawaye.
Babu abinda Noor ta É—auka, daga ita sai kayan jikinta, sai gyalen abayar a kanta suka fito daga gidan, su Umma suka musu rakiya har bakin mota,
Zare hannunta Noor tayi daga na papi, da sauri taje ta rungume Umma tana kuka,
A hankali Umma tace
"Noor ki kwantar da hankalinki, insha Allahu zamuzo muga inda kike bada jimawa ba kinji."
GyaÉ—a kai tayi kafin taje gurin Baba dake tsaye shi kansa daurewa kawai yakeyi
"Baba zan tafi'
ta faɗa tana rufe fuskarta saboda kukan da ya ci ƙarfin ta,
"Allah ya miki albarka Noor, sai munzo."
Ya faÉ—a yana shafa kanta, juyawa tayi zata shiga motar, khamal yace
"Wato Ni kadai ne baza'a ma sallama ba koh Noor?"
Da sauri ta juyo tana kallonsa
Murmushi yayi yana faÉ—in ba
"laifinki bane wato anga Baba, an manta da yaya ko?"
Kuka ta fashe da shi, da sauri Baba yace
"khamal ka kiyayeni fah."
Dariyar ƙarfin hali khamal yayi ya matso kusa da ita yana faɗin
"wasa nake miki ƙanwata, Allah ya kiyaye hanya ya kai mana ke lafiya Noor, sai munzo."
ÆŠago idanunta tayi kafin a hankali tace
"nagode"
Bai ce mata komai ba ya buɗe mata baya ta shiga, papi ma sallama yayi musu ya shiga motar, driver ya tada motar suka bar ƙauyen suna ɗaga ma juna hannu.
Maimoon#
*💖ABNUR💖*
*By Maimoon*
*Elegant online writers* 📚📖
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.