Complete Hausa Novels

Abnur Complete Hausa Novel

Reading file: Abnur_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 19 of 24

cigaba tayi da shafa kansa, har taji sauƙar numfashinsa alamun bacci ya ɗauke sa, a hankali ta gyara masa kwanciyarsa a kan gadon.

Hannunta ta sa a cikin na Abbu dake miƙa mata hannunsa.

A hankali ya miƙar da ita suka fice a ɗakin, suka nufi ɗakin Maami, sai da suka isa ɗakin kafin Maami ta fashe da kuka

"Abbu ka ga Habibina kuwa?, meyasa Noor ta tafi tanar min yarona a haka?, kashe min shi takeso tayi ne?.

Ta faÉ—a tana sake fashewa da kuka.

rungumeta Abbu yayi yana shafa kanta, karki damu Hilwa, Zannur will be alright, kuma za'a sami yarinyar, ki kwantar da hankalinki Please."

Haka Abbu yayi ta rarrashin Maami, har sai da yaga ta samu nutsuwa kafin shima nashi hankalin ya kwanta.

************

Khamal ne ya shigo gidan yauma da saurinsa, da jarida a hannunsa, tun daga tsakar gida yake ƙwala kiran

"Noor! Noor! Ina kike?

A tare suka fito da umma, jin kiran yaƙi ƙarewa

"Khamal lafiyanka?"

Umma ta tambaya tana kallonsa.

"Umma bayan mijin Noor da ke nemanta, yau kuma wani ne yake nemanta, wanda yake ikirarin shi mahaifinta ne, gashinan dai hotonta ne ɓaro ɓaro akan jaridar, sannan yasa kuɗi mai tsoka ga duk wanda ya san koda labarinta ne."

Ya karashe zancen yana mikawa umma hoton.

A hankali Noor ta jawo ƙafar ta ta ƙara so gaban Umma, hannu ta saka ta amshi jaridan tana kallo sai kuma tayi wani murmushi tana tafa hannunta

"Kai a tunaninka kana da wayo ko?, umma ba fa mahaifina bane, Zannur ne zai raina min wayo, shine kaÉ—ai yake da wannan hoton, shine ya É—aukeni, ta yaya za'a yi mahaifina da koni kaina bansansaba zai samu wannan hoton, a tunaninsa idan yace mahaifina zan dawo ne hmmm."

sai kuma ta ajiye jaridar ta yi wucewarta É—aki

Daga khamal har umma da kallo kawai suka bita, kafin khamal yace,

"Ummah kina ganin a barta kawai?, a gaskiya Nikam zan kira numbar da aka saka dan nemanta, in sanar dasu inda take, idan ma mijinnata ne gwara yazo a sasanta komai ta koma gidanta ko ya kuka ce."

"To khamal me zance maka, ka dai jira Malam ya dawo muji ta bakinsa koh?"

Bai sake cewa komai ba ya juya ya bar gidan.

Maimoon#

*💖ABNUR💖*

*By Maimoon*

*Elegant online writers* 📚📖

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.