Abnur Complete Hausa Novel
Reading file: Abnur_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 4 of 24
*Page* *4*
Kamar yadda ta faÉ—a kuwa, hakan ce ta kasance, bayan sallar isha duk suka taru a É—akin Baba ,kasancewar Umma ta sanar masa komai ,
Kamal na shigowa ,Umma ta aikasa ya kira Noor,tunda ya zo ya kirata take jin faÉ—uwar gaba,shi kuwa dama bai tsayaba, yana kiranta yayi juyawarsa ya koma É—akin,but zuciyarsa na cike da É—okin jin labarin nata.
Hijab ta sanya, tana karanto addu'a a ƙasan ranta ,tasan yanayin da take ciki yana da nasaba da tuno labarinta da zatayi.
a hankali ta ƙarasa ɗakin kanta a ƙasa ,sallama tayi duk suka amsa suna kallon ƙofar ,a hankali ta ɗaga labulen ɗakin ta shiga ,can nesa kaɗan da su ta zauna tana fuskantarsu gabaki ɗaya, a hankali ta gaishe da Baba,ya amsa da fara'a yana tambayar lafiyanta ,ta amsa da ladabi ,kana Baba ya ƙara da cewa
"Noor naji komai a bakin Aisha, tacemin yau Zaki faɗamana daga inda kika fito, da kuma dalilin fitowar taki ,naji daɗi matuƙa da kikayi wannan tunanin dan yana da kyau musan hakan ,saboda haka muna sauraranki kuma inaso ki faɗamana iya gaskiyarki".
A hankali Kamal ya gyara zamansa yana kallonta ,Umma ma kallonta kawai takeyi,sai da ta share guntun hawayen idanunta, kafin ta fara da faÉ—in......
WAIWAYE (mafarin labarin)
_Garin_ _BAULAWA_ _dake_ _ƙarƙashin_ _jihar_ __Kaduna_Nigeria_
Yarinya ce yar kimanin Shekaru 16 ,doguwa ce sosai ,fara tass kamar balarabiya, fararen ƙafafuwan ta da babu takalmi take tsalle dasu, tana caɓalasu a cikin ruwan daya kwanta a ƙasan saboda ruwan saman da ake kan yi a garin,
Gaba ɗaya ta gama jiƙa jikinta,har gashin kanta da yake tare waje guda ta cureshi ,wani irin farin ciki take wanda fuskarta ya kasa ɓoyewa ,
Yara ne sun kai su shida a zagaye da ita,suna jiƙa jikinsu suna wasa ,ta biye musu kamar wata sa'ar su ,
duk wanda yake garin ya kwana da sanin wannan hali nata,tana matuƙar son ruwan sama, hakan yasa ko a ina take idan har ana ruwa to akanta yake ƙarewa, kuma abin mamakin shine ko irin zazzaɓin nan na mura batayi idan ta shiga ruwan.
Malaman makarantarsu kuwa sunsha dukanta, akan ana aji tana shiga ruwa, amma inaaa gobe ma zata koma har sun haƙora sun ƙyaleta .
Ɗaga kanta tayi sama ganin ruwan na shirin ɗaukewa ,ta ɓata fuska sauran yayyafin da ke sauƙa yana sauƙa mata a samar kyakkyawar fuskarta ,a hankali ta kama ƙasan rigarta tana matse ruwan, sannan ta nufi ƙasan bishiyan neem ɗin dake kusa da su ta zaro takalmanta ,ta sanya su ba tare da ta kula yaran da suke cigaba da wasansu,da ruwan caɓalin da ya kwanta ba kawai tayi hanyar gida.
A daidai zauren ɗan ƙaramin gidan ta tsaya tana sake matse kayan jikinta ,sai kuma tayi sallama tana ƙarasawa tsakar gidan ,babu kowa hakan ya bata daman saurin faɗawa ɗakinta ta kwaɓe jiƙaƙƙun kayanta,ta canza wasu ,ta buɗe jakarta ta ciro littafan makarantarta ta zauna ta naɗe ƙafafu ta ajiyeshi a gefe,
Jin alamar mutum na zuwa kusa da É—akinnata ya sata saurin buÉ—ewa ta fara karantawa ,É—aga labulen Nenne tayi tana kallonta,sai kawai tayi murmushi tana faÉ—in
"Noor!"
Da sauri ta amsa "na'am Nenne" Nenne ta ƙaraso cikin ɗakin tace "ina jiƙaƙƙun kayan da kika jiƙa" shiru tayi tana kallon Nenne ta ƙasan ido ,a ranta tana addu'ar Allah yasa kar tayi mata faɗa,
Ai kuwa kamar Nenne tasan miye a ranta ta soma faÉ—in "wai Noor meyasa baki san ciwon kanki bane sam,mutum bayi da aiki sai shiga ruwan sama, bakya tsoron sanyi ya kamaki?"
Ita dai bata ce komai ba, sai ma wasa da ta shiga yi da takaddar hannunta ,idanunta na cika da hawaye ,dan Allah na gani batason faÉ—a sam ,tsorata ta yakeyi ,
Tsagaita wa Nenne tayi da faɗan,sanin halin ƴartata ta ƙarasa kusa da ida tana jawota jikinta,ai kuwa kamar jira take ta rungume ta ta soma kuka, shiru Nenne tayi sai kuma tace "Noor,bawai Ina miki faɗa bane dan bana sonki Ah ah ina miki faɗane saboda babu wanda ya kaini sonki, a yanzu ina tare dake ,watarana ba na nan Noor,banaso ki sha wahalan rayuwa ko bayan raina ,shiyasa nakeso ki san ciwon kanki tun yanzu,Noor ko babu komai watarana aure zakiyi ki tafi gidanki ,koh haka zaki je ki masa idan kunyi auren ?" ta tambaya tana murmushi jin bata amsa ba sai ajiyar zuciya da take sauƙewa ,yasa Nenne cigaba da magananta dan tasan ba amsawar zatayi ba ,
"Kina jina Noor"Nenne ta faÉ—a tana shafa kanta ,girgiza mata kai tayi ,Nenne tace"Noor ko babu aure Akwai mutuwa ,banaso na rigaki mutuwa ki shiga wani haali,da sauri ta É—ago tana rufe mata baki take wasu hawayen suka sauko mata ,ta sake rungume Nenne tana faÉ—in "Nenne bazaki barni ba, idan har kika mutu nidai binki zanyi,kuma Ni bazan yi aureba har abada".
Murmushi kawai Nenne tayi tace "to shikenan naji ,yanzu ki cigaba da karatunki bari naje wani unguwa yanzu na dawo" ,da sauri tace Nenne zan biki ,nan take Nenne ta haɗe rai tace bazaki bini ba kuma idan kika kuskura kika fita a gidannan kafin na dawo zan saɓa miki" ,a hankali ta gyaɗa kai tana faɗin "insha Allahu Nenne "
Nenne ta fice a É—akin ,ita kuma ta cigaba da karatun ta tana tunanin," ina Nenne take zuwa kwana biyunnan da bataso ta sani?"
Sai da ta tabbatar Nenne ta bar gidan sannan ta rufe littafin, ta mayar jakanta, ta ɗauko jiƙaƙƙen kayan taje ta shanya ,sannan ta dawo tayi kwanciyar ta a ɗan ƙaramin gadonta ,tana sake tunanin maganganun Nenne,
Ita bazata yi aureba har abada, saboda bazata taɓa yadda ,wani yayi mata abinda mahaifinta yayi ma Nenne ba,kowa yasan mahaifinsa amma banda ita,ko kamanninsa bata saniba, sai sunansa da take anfani dashi ,alhalin yana raye ,yana birni yana cigaba da rayuwarsa ,kamar bai san da su ba.
_ABUJA_ _NIGERIA_
Murza steery kawai yake, hankalinsa gabaki ɗaya yana kan tuƙin da yakeyi ,a hankali yayi horn a gaban wani babban Duplex house,mai gadi ya wangale masa gate ɗin yana ɗaga masa hannu,bai bi ta kanshi ba, sai ma cusa motar da yayi cikin gidan Yana driving a hankali ,fuskarsa ɗauke da wata ƙasaitacciyar murmushi,tafiya kamar na minti takwas a cikin gidan, ya kaisa parking space ɗin da aka adana dan motocinsa .
A hankali ya ƙarasa ciki yayi parking, sannan ta fito daga motar, wani remote ya danna, nan take motar ta ɗagu sama ta jeru a cikin ƴan uwanta da suke hawa hawa ,anan take wata motar daban tayi replacing ɗin waccar,
body guards ɗinsa su shida ya kalla yadda suka tsaya suna jiran umurni,bai ce musu komai ba, ya nufi main entrance ɗin gidan, yana taɓa bluetooth ɗin kunnensa ,a hankali cikin murya mai amo ya fara faɗin "then they are all fired" ɗan shiru yayi yana cigaba da tafiyarsa, alamar yana sauraron mai maganan sai kuma yayi ɗan murmushi yana faɗin,"then I will meet you in 3 hours time"
daga nan ya kashe wayarsa ,daidai ya iso ƙofar da zai sada shi da main hall na gidan ,security ɗin ƙofar ya sanya sannan ya ƙara sa cikin parlorn yana zama a kan kujera , turarensa na _SHUMUKH_ shi ya kaima su Amina da ke kitchen saƙon dawowarsa, dan tuni ya karaɗe ko ina ,
da sauri Yasira ta fice daga kitchen ɗin ,kasancewar ita ce in charge na kitchen ɗin ,ɗan nesa dashi ta tsuguna tace " Sir lunch is ready , should I serve you!?" bai ɗago daga danna wayar da yakeyi ba, ya miƙe ya nufi bedroom ɗinsa Yana faɗin "maybe later" da kallo kawai ta bisa .
wani ɗaki ya shiga ya jingina da bangon ɗakin yana bin ɗakin da kallo ,cameras ne kala kala ,da kuma hotuna iri iri na nature da na mutane iri iri ,murmushi kawai yayi ya nufi Camera ɗaya ya ɗauka, sannan ya ƙarasa balcony ɗin ya kai Camera ɗin idonsa, sannan ya ɗauki entire area ɗin a hoto ,yana jin matuƙar farinciki,
ɗaukan hoto is his passion,he is very proud to be an explorer ,tunanin inda zai je next domin ɗaukan hotunansa yakeyi ,yana buƙatar zuwa guri that is full of nature, but still local,
Yana son capturing al'adu da kuma sabbin abubuwa that's why yake neman inda zaije a cikin Nigeria ya gaji da capturing ƙasashe ,so yake ya fito da beauty na ƙasarsa ,ya kamata yayi research yaga ina zaije tourism this time a cikin Nigeria,
fita yayi a ɗakin ya nufi ɗakinsa, ya zauna gefen gado yana dialling Numbern Maami, ringing biyu taɗaga tana faɗin "Habibi" a hankali kuma a shagwaɓe yace "Maaami " yadda yayi maganar yasa ta faɗin "and now ,me kake so kuma this time!?",wani murmushi yayi dan yasan Maami ta gama ganesa ,ya shafa yalwataccen sumarsa, da bayida maraba da ta asalin larabawan Dubai, a hankali yace"not much Maami ,kawai suggestion ɗinki nake nema akan wani abu"
tace "ok am all ears Habibi, hope dai bawani abu bane ya dameka ko" murmushin ya kuma yi yana lumshe idanunsa sannan yace "not at all ,kawai dai so nake nayi exploring a ƙasata ,Ina so naje tourism somewhere very local but full of nature ,shine nace bana tambayi suggestion ɗin ki ,i know, no one will know better than you do"
wani murmushi Maami tayi da har yana iya jiwowa tace " ok then why not Kaduna state well the state is full of nature just the way you like it" shiru yayi sai kuma yace " amma kin manta nace miki local ,Kaduna ai is too polished for what I want"
dariya Maami tayi tana faÉ—in "and what about villages É—in dake under Kaduna" É—an shiru yayi sai kuma yace "kamar wanne kenan?"
"Wannan kuma you have to research to find out " "okay Maami ,Abbu fah ?" "Abbu yaje finalizing deals da wasu companies a ukraine " "okay then I guess we will talk later" "okay Habibi take care" a hankali yace "sure" sannan ya katse wayar ,ajiyeta yayi ya jawo laptop É—insa ya shiga yin research akan Kaduna state ,
_BAULAWA_ ya sake maimaita sunan ,a hankali yayi murmushi yace "i guess I already got it!"
Wayansa ya ɗauka yayi dialing Numbern personal assistant ɗinsa , Yana ɗagawa yace masa "we are going to Kaduna by Wednesday ,so prepare the needful " "yes Sir " taufeeƙ ya amsa ,kashe wayar yayi yana faɗawa kan gadon a hankali ya furta"its going to explore, Allah yasa na samu abinda nakeso a wannan ƙauyen" ,sai kuma ya ƙara murmushi yanajin kamar wani al'amari mai girma na tunkarosa
Is it really going to explore!?me zai faru a Æ™auyen BAULAWA ,zai samu abinda yake so kuwa !?🤓the story has just begunðŸ¤
*ABNUR*
*By* *maimoon* 🤓
*Elegant* *online* *writers* 📚📖
*Free* *book*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.