Complete Hausa Novels

Abnur Complete Hausa Novel

Reading file: Abnur_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 12 of 24

Page 13

Har ya isa Airport É—in, bai dai na tunanin mai ya ka wo Maami Nigeria all of a sudden ba.

A hankali ya ƙaraso in da ta ke tsaye,ta na sanye da abaya, fuskar ta da glass mai kyau,ta fito a Mrs shuraim ɗinta.

Rungume ta ya yi ba tare da yace komai ba, sai lokacin ta lura da shi,da sauri ta É—ago kansa ta na kallon sa

"Habibi are you Ok?" murmushi ya yi ya ce

"babu kawai am happy saboda zuwanki ne"
ya faÉ—a ya na murmushi.

Cikin matuƙar farinciki,ta manna masa kiss a both chicks ɗinsa da forehead ta na faɗin

"I missed you so much Habibi,mu je gida".

Bai ce komai ba ya É—ago daga jikinta,ya na Jan trolley É—inta,kasancewar bai fito da bodyguards ba.

Sai da ya sa a mota, kafin ya zagayo ya buɗe mata ƙofan motan,

"my Queen,shall we?"

ya faÉ—a yana nuna mata motar

Dariya tayi sosai tana kallon shi, kafin ta shiga ta zauna, shima ya zagaya ya shiga motar, amma gabaÉ—aya tunaninsa na ga abinda zai faru idan Maami ta haÉ—u da Noor.

Ganin he is carried away ya sa Maami shafa furkarsa ta na faÉ—in

"Habibi are you hiding anything?"

Da sauri ya girgiza mata kai,yana faÉ—in

"Maami kin san na ce miki ina son muyi magana idan nazo Dubai!, so tunda kinzo, I will explain everything to you Amma sai kin huta"

Ƙura masa ido tayi tana kallonsa,sai kuma ta ce,

"nima kai na akwai abinda nake so in tambayeka that is very important, Dan kusan ma shi ya kawo Ni Nigeria, duk da nasan ba zaka taɓa yin hakan ba da amincewa ta ba".

shiru yayi yana sauraranta, dan bai kawo ko a ransa ta san da aurenshi ba, to wa ma zai faÉ—a mata idan ba shi É—in ba.

Motar ce ta kusa kufce masa saboda tambayar da ya jita a bazata

"Habibi wai kayi aure ba mu sani ba?"

Da sauri ya ja burki da ƙarfi yana duban ta

"Who told you this Maami?"

"Kar ka damu nasan ba gaskiya bane, wata ce kawai ta kira ni wai ka yi aure but I didn't believe her" ta faÉ—a tana murmushi

"Maami zan faÉ—a miki komai idan mun je gida"

Shine kaɗai abin da ya iya furtawa, zuciyarsa na tafasa, tabbass da ya san waye ya faɗa ma Maami zancennan, sai ya sashi yayi regretting, but yasan yanda zai ɓullo wa Maami,

fatan shi kawai Allah ya sa kar Maami ta ɗauka da zafi, dan ya san ta, tana sonshi sosai, amma tana da matuƙar kafiya akan abinda ba ta so.

Har suka iso gidan ba wanda ya sake cewa komai,

da sauri bodyguards suka buɗe musu ƙofa suna yi ma Maami sannu da zuwa cikin matuƙar girmamawa,

hannu kawai ta É—aga musu, ta wuce, shima ya bi bayanta jiki a sanyaye,

A falo ya sameta tana tsaye ta na ƙarema ko ina kallo,

"Ƙarasowa yayi yace Maami ki huta sai muyi maganan kinji!"

Bata ce masa komai ba ta nufi bene,
tsayawa tayi cak,ganin wata kyakkyawar matashiyar budurwa tana sauƙowa,ja baya tayi tana kallon Noor,sai kuma ta juya da sauri tana kallon Zannur

Har ta ƙarasa sauƙowa kafin ta lura da waɗanda ke falon, kasa wucewa tayi,sai ta tsaya kawai tana kallonsu,

"Ina wuni"ta faÉ—a cikin in-ina dan dai daga ganin matar kasan itace mahaifiyar Zannur duk da ba wani kama yake da ita sosai ba.

Kallonta kawai Maami keyi,tama kasa amsawa,sai kuma ta juya da sauri ta na kallon Zannur

"and who is she?"ta faɗa a ƙausashe

"Maami pleaaaaase na ce miki za muyi magana idan kin huta please"

Cikin tsawa ta katse shi tana faÉ—in

"Habibi who is she?,don't you dare lie to me, wayece wannan?,kuma daga ina take?,me takeyi a sama?"

Sunkuyar da kansa yayi dan ya san irin ɓacin ran Maami, idan har bai faɗa mata ba to tabbass ranta ƙara ɓaci zaiyi wanda zai sake ɓata komai.

Cikin inda inda yace
"my w..i..f.e"

"You Are Mad Habibi, ka haukace, how could you?
ta faÉ—a tana zare ido, da sauri kuma ta juya ga Noor da duk a tsorace take da ita.

Cikin faÉ—a tace

"me kika yi ma yarona, tell me before I deal with you personally"

Ta faÉ—a tana tunkaro Noor,

Da sauri Zannur ya sha gabanta yana faÉ—in

"Maami listen to me,zan faÉ—a miki komai, pleaaaaase muje É—akin ki"

"Out of my way Zannur"
ta faÉ—a tana kallon cikin idonsa.

With suprise Shima yake kallonta, rabonta da ta kira sunansa har ya manta, ya tabbata yau ranta ya kai matuƙa wajen ɓaci.

Cikin sauri yace

"Maami ki saurareni, she is my wife, but I promise bana sonta, ban taɓa sonta ba, kuma bazan taɓa sonta ba, I only helped her, kuma ke kika ce in dinga taimako Maami!"

Wani kallon ka raina min wayo Maami ta ke masa, kafin ta sa hannu ta matsar da shi daga gabanta ta na nufan Noor

Ai da gudu Noor ta juya ta koma sama ta shige ɗakinta ta rufe ƙofar da key, dan wallahi ta tsorata ainun da matar,

amma maganganun sa sun fi mata ciwo fiye da fushin mahaifiyarsa saboda ta san fushin Maami is justified, dole ranta ya ɓaci.

A hankali ta ƙarasa gefen gadonta tana toshe bakinta da tafin hannunta saboda kukan da ke ƙoƙarin cin ƙarfinta

Juyowa Maami ta yi ta kallesa sai kuma ta haura sama, ba tare da ta sake cewa komai ba

Shafa kansa yayi,dan abin ya wuce yanda ya yi tunani, a hankali shima ya haura ya nufi É—akin Noor, jinsa a rufe yasa ya wuce É—akin Maami shima a kulle, bai san sanda yayi murmushi ba ya juya ya wuce É—akinsa ya na kiran layin Abbu

Yasira da ke jin komai, ta yi saurin wucewa É—akin su ta na jin wani farin ciki,
burinta ya kusa cika, Zannur ya kusa zama nata, ta kusa tashi daga in-charge na kitchen, itama ta zama Mrs Zannur Shuraim,

da sauri ta rufe ƙofar dan tasan su Asabe suna can baya suna wanke kayansu yau,

rawa tayi ta tiƙa tana juyi a ɗakin sai kuma ta faɗa gadon ta na ƙyalƙyalewa da dariya.

*****

"Son, meyasa kayi haka, kaima kasan Hilwa batada wanda take so fiye da kai, da baka ɓoye mata ba tun farko zata fahimceka, but zan mata magana,make sure You apologise"

Cikin sauri yace "i will Abbu,Wallahi i will,but please talk to her she shouldn't be angry,it hurts"

Okay I will talk to her insha Allah, kaje ka samu matarka kuje tare ku bata haƙuri, kasan tayi burin aurenka but ka ɓata mata komai dole tayi fushi"

A hankali yace

"toh Abbu"
duk wannan maganan cikin harshen larabci suke yin sa,

Sai da Abbu ya ƙara yi masa nasiha, da nuna masa kuskurensa kafin sukayi sallama,kasa zuwa ya yi sai kawai ya kwanta a dakin ya na jin a little bit of relieve.

****

"Hilwa!!" Shiru tayi daga masifan da take ta yi tana mayar masa abinda ya faru,

"Hilwa!" ya sake maimaitawa

"Abbu bazaka gane ba..."
bai barta ta ƙarasa ba yace

"na gane i understand you wifey, kawai ina so ne kiji other side of the story, ki tsaya kiji dalilin sa please for me"
ya faÉ—a yana marairaicewa

"Why are you blackmailing me emotionally" ta faÉ—a tana murmushi

Shima murmushin yayi dan da alama ta ɗan sauƙo, a hankali yace

"cause I know exactly the type of wife I am married to"

dariya tayi tana zama akan gadon ba tare da tace komai ba

A hankali yace

"i missed you hilwa!"

"Tun yanzu ai kuwa bazan dawo ba sai nan da 2 month"

"You are joking" ya faɗa da ƙoƙarin sata ta manta da duk ɓacin ran ta.

"Am serious...." shiru tayi jin ana knocking sai kuma taja tsaki tana faÉ—in

"ÆŠan ka da ka turo gashi nan har ya iso"

Cikin harshen larabci shima ya mayar mata,

"É—anki dai, Habibi ne Fah kin manta"

Batace komai ba ta miƙe ta buɗe ƙofan ta dawo bakin gado ta zauna tana ɓata fuska ,

A hankali kamar wani Maraya ya ƙaraso ɗakin yana kallonta da fuskar tausayi, har abin ya kusa bata dariya,
amma ta gimtse ta ƙi kulawa.

Zama ya yi kusa da ita ya kwantar da kansa a kan Cinyarta, har ta ƙarasa wayan ta kashe ta ajiye ba tare da ta kula shi ba, a hankali ya soma magana

"Maamiii" bata kula ba

Ya cigaba da magana

"Maami pleaaaaase an so sorry, please Maami listen to Habibi"

Juyar da kanta tayi tace ina sauraron ka

Da sauri ya miƙe ya zauna daman he trust Abbu shi kaɗai yasan yanda ya ke sauƙo da Maami duk tsananin fushin da tayi kuwa.

A hankali ya soma bata labarin abinda ya faru tun zuwansa Baulawa har kawo yanzu.

With shock ta juyo tana kallonsa, sai kuma ta sake haÉ—e rai tana faÉ—in "none of my business,
Yanzu abinda nake so da kai, kaje ka kira min waccar da kake ikirarin matar kace, kuzo nan yanzunnan"

A sanyaye ya buɗe baki zai yi magana ta ɗaga masa hannu tana nuna masa ƙofa,

Miƙewa yayi ya fice a ɗakin yana jin kamar ya kurma ihu, ya zaiyi ya mata bayani ne wai.

A ƙofar ɗakin ya tsaya, sai da ya ɗan yi jim sai kuma ya soma knocking a hankali,
sai da yayi sau huɗu kafin ta buɗe ƙofan

Kallonta yayi tayi ganin Yadda idanunta suka yi jajir suka kumbura,

Tana haɗa ido dashi tayi saurin juyawa ta koma ɗakin shima shigowa yayi ya jingina da ƙofa ya harɗe hannuwansa yana kallonta, sai kuma yace

"kukan me kike yi?"

Bata kula shi ba, ta share hawayen da ya zubo mata,

ƙwafa yayi a hankali yace
"taso ki biyoni"

Da sauri ta kallesa,

Bai sake kallonta ba ya juya har yakai bakin ƙofa ya juyo yace

"zo ki wuce"

A hankali ta miƙe ta biyo bayansa, har ɗakin Maami.

Maami na ganinsu ta haɗe girar sama da ƙasa tana karkaɗa ƙafanta,

Noor kam ta gama tsurewa, ƙirjinta sai dukan uku uku yake.

Da sauri ta ƙaraso ta durƙusa, tana faɗin

"Maami dan Allah kiyi haƙuri wallahi bazan sake ba"

Dariya ce ta kusa kufce wa Maami sai ta
miƙe kawai tana faɗin

"keee tashi ki tsaya"

A hankali ta miƙe ta tsaya tana share hawayenta,

Sai da Maami ta ƙara taku biyu zuwa gabanta kafin ta jawota ta rungume gabaki ɗaya tana murmushi,

BuÉ—e idonsa yayi a hankali dan yayi zaton marinta Maami zatayi, da kuwa bazai iya jure gani ba.

Da mamaki yake kallon Maami, sai kuma ya sauke wani wawan ajiyar zuciya a ransa yana faÉ—in

"You Are the best Maami na"

"Me ya saka ki kuka daughter,is this how to welcome your mother in law?"

Ta faÉ—a tana É—ago ta daga jikinta, kasa cewa komai Noor tayi

A hankali Maami ta miƙa masa hannu tana faɗin "come my boy"

Ƙara sawa ya yi ya shige jikinta, ta haɗa su duka ta rungume ta na shafa sumar kansa

Da ƙyar ya buɗe bakinsa da yayi masa nauyi yace

"thank you Maami naa"

ÆŠago kansa tayi tana kallonsa tace

"You know I love you Habibi,so dole ne naso duk abinda ka ke so!,
but gaskiya You both have to apologise to me Dan kun rage min burina akan aurennan"

Da sauri suka haÉ—a baki wajen faÉ—in

"We are so sorry Maami"

Dariya Maami tayi tana faÉ—in
"You Are pardoned "

Sake rungumeta yayi yana ƙara jin tsantsan ƙaunar ta .

Ita dai Noor Satan kallonsa kawai takeyi

Maimoon🤓#
*💖ABNUR💖*

*By* *maimoon*

*Elegant* *online* *writers* 📚📖

*Free* *book*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.