Complete Hausa Novels

Abnur Complete Hausa Novel

Reading file: Abnur_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 8 of 24

*Page* *9*

Ƙarfe 12:40 suka shigo cikin Kaduna,har lokacin babu mai magana a cikin motan.

Ɗan juyawa yayi ya kalli sashen da take, sai yaga ashe ma bacci takeyi,yadda take sauƙe ajiyar zuciyar zakasan ba daɗin baccin takeji ba .

Ƙwafa yayi,yana juyar da kansa daga kallonta,ya maida kallonsa ga faruƙ da ke ƙoƙarin packing a packing space na hotel ɗin.

Sai da duk suka sauƙa,ganin bata fito ba ya sa ya ɗan ja tsaki,a ransa yana faɗin "tun yanzu!? .

Baibi ta kanta ba yayi wucewarsa ciki.

TaufeeÆ™ ma da sauri yabi bayan sa,sai da ya gama yin all the needful ya rakashi har É—akinsa, sannan ya dawo motar da sauri,wanda dama basu rufe da key É—in ba ganin tana bacci.

Buɗe ɗayan ɓangaren yayi,a hankali ya soma buga kujerar yana faɗin "Madam "

A hankali ta buɗe gajiyayyun idanunta tana sauƙe numfashi,sai kuma ta juya a sanyaye ta kalli Taufeeƙ dake mata murmushi.

Cikin girmamawa,yace "mun iso Ma,kuma Sir yace a ƙaraso da ke"

Kallonsa kawai takeyi,yana maganan kamar wacce batasan me yake cewa ba,
a hankali kuma wasu siraran hawaye suka sauƙo akan fuskarta,dan yanzu ta tuna ashe fa aure aka mata,sannan Nennenta ta rasu .

Sauƙa Taufeeƙ yayi ya ƙara sa ya buɗe mata sashin ta,a hankali tace

"nagode"

Bai ce mata komai ba,yayi mata jagora tana biye dashi,har ƙofar ɗakin Zannur,

sai da ya É—an tsaya
yana tunani,dan bai san ya Zannur ɗin zaiyi reacting ba idan ya kai masa ita,shima da gangan yaƙi kama mata ɗaki,dan yafi so as soon as possible su koyi zama da juna.

A hankali yayi knocking a ƙofar ɗakin,sannan ya ɗan matsa ya tsaya yana jira a buɗe,dan dai ya san sau ɗaya ake masa knocking,Dan baya son hayaniya,

Har kamar baza'a buɗe ba sai kuma yaji an buɗe ƙofan, kallonsa yayi ganin ya koma ciki,yasa ya dubeta ya ce "muje".

Tana biye dashi a baya suka shiga É—akin,yana zaune a kan gado,har yayi wanka ya canza kayansa zuwa three quarters da Riga na shan iska laptop ne a kan cinyarsa yana operating, ba tare da ya É—ago ba yace

"is anything wrong?

Da sauri TaufeeÆ™ yace

"Sir, dama,ummm...Madam ce....."

dakatawa yayi da danna keyboard ɗin ya ɗago manya manyan fararen idanunsa,aikuwa basu sauƙa akan kowa ba sai a kanta,tana rakuɓe daga bakin ƙofa kamar kace arrrr ta gudu.

Maida kallonsa yayi ga TaufeeÆ™ sannan ya É—an haÉ—e rai yace

"what the hell is she doing here? me yasa baza ka Kaita room É—in ta ba?me zata min anan?"ya sake tambaya.

Da sauri Taufeeƙ yace "Sorry Sir,but am so sorry to say,all the rooms were booked,shiyasa na kawota nan,but kayi haƙuri,i can vacate my room,in yaso sai ta zauna a ciki".

"Better"
ya faɗa yana cigaba da danna laptop ɗin, jiki a sanyaye Taufeeƙ ya juya,ita dai kallon sa kawai takeyi,gabaki ɗaya ya canza mata,kamar ba abokinta na ƙauye ba.

Har sunje ƙofa zasu fita,sai kuma ya ja tsaki,ya ajiye laptop ɗin sannan ya ce "Taufeeƙ" yadda zai ji shi,da sauri ya dawo yana faɗin
"Sir"
"Let her stay here" ya faɗa a taƙaice daga haka ya miƙe ya wuce toilet.

Murmushi TaufeeÆ™ yayi,a zuciyar sa yana faÉ—in "I will try my level best,to unite you both".

Koma wa yayi ya sake kiranta, dan har ta fita ita kam, har tsakiyar daƙin ta shigo ta tsaya,sannan Taufeeƙ ya juya zai fita,da sauri ita ma ta juya tana faɗin
"umm...tafiya zakayi ka barni a nan".
dan dai ita wallahi Zannur ɗin ya fara bata tsoro,dan lokacin da suke ƙauye sam ba haka yake mata ba.

TaufeeÆ™ bai tsaya ba,bare tasa ran zai amsa mata,ganin da gaske fita zaiyi ya sata juyawa da sauri zata bisa,dan gani take gaskiya yafi Zannur É—in kirki nesa ba kusa ba

"Idan kika kuskura, kika sake ɗaga ƙafarki daga wajen, I will know how to deal with you"

Taji an faɗa daga bayanta, cak ta tsaya,sannan ta kasa juyowa, lokacin Taufeeƙ har ya fice a ɗakin ya ja musu ƙofa.

Bai sake cewa komai ba, shima yayi hanyar fita,hannunsa na É—an É—igan ruwa,sannan fuskarsa da leman ruwa,alama dai alwala yayi.

Ganin shiÉ—inma fita zaiyi ya sata saurin biyosa da sassarfa,dan dai baza'a barta a É—akin nan ita kaÉ—ai ba.

Jin alamun mutum a bayansa yasa ya tsaya da tafiyan da yakeyi ya juyo gabaki ɗayansa,fuskarsa a matuƙar ɗaure yake faɗin
"where do you think you are going? a tsawace ya sake maimaita"Nace ina zakije da kike biyoni"

Da sauri ta toshe kunnuwanta, dan babu abinda ta tsana a rayuwarta irin tsawa,jikinta har rawa yakeyi,

ganin yadda tayi ɗin sai ya tsaya kallonta kawai,bai sake cewa komai ba ya juya,ya fice a ɗakin itama bata sake gigin binsa ba, tana ji ya rufe ƙofar ta baya.

Sai lokacin ta samu daman ƙare ma ɗakin kallo,tana mamakin irin girmansa da ƙayatuwansa.

A hankali ta samu waje a ƙasa ta zauna,wasu hawayen na ture turen zubowa daga idanuwanta,

"Allah na gode maka,akan duk yadda ka so ka ga rayuwata, Allah ka jiƙan Nenne, Allah ka bani ikon cinye jarabawar da ka ɗauro min" abinda tayi ta maimaitawa kenan,tana jin zafin dake zuciyarta na raguwa.

Tana zaune a wajen har ya dawo daga masallaci,bata ma ji shigowar sa ba,saboda yanda tayi nisa a tunani,ƙarar rufe ƙofan ne ya dawo da ita daga duniyan tunanin, ta bisa da ido.

Ledan dake hannunsa ya ajiye a gabanta,sannan in a husky voice yace"kee,tashi kije kiyi wanka, ki cire waÉ—annan kayan na jikinki,kizo kiyi sallah".

"To" kawai tace ta miƙe, amma sai ta rasa me ma zatayi?,ina zata shiga?,juyawa tayi ta nufi inda taga ya shiga ɗazu,har ta kai ƙofa taji yace,
"kayan kuma fa" da sauri ta dawo ta É—auka ta wuce toilet É—in.

Da kyar ta samu ta iya gane yadda ake amfani da toilet, É—in,sai da tayi wanka da soson da ta gani a toilet É—in, sannan tayi alwala,ledan ta buÉ—e tana kallon kayan ciki,zaro su tayi,tana dubawa.

Nan ɗin ma da ƙyar ta samu ta saka shi dai dai,tanayi tana duba hoton matar da ke jikin ledan kayan.

Gashinta ta warware,sannan ta sake dunƙuleshi kamar yadda ta saba,sannan ya warware ɗankwalin kayan, ba laifi yana da girma,ɗaure gashin tayi dashi sannan da ɗau hijab ɗin da ta cire ta saka.

Tunda ta fito daga banɗakin yake kallonta ƙasa ƙasa,ganin ta maida hijab ɗin da ta cire,amma bai ce mata komai ba.

Can gefe ta ja ta tsaya tana kallon É—akin from every direction,ganin bazata iya ganewa ba yasa ta aro jarumta tace
"umm dan Allah ina ne gabar,zanyi sallah"

Ganin bai kulata ba yasa ta juya ta kalli gefe kawai,zata tada sallah.

Miƙewa yayi ba tare da yace mata komai ba,sai da yazo dai dai da ita, sannan ya sa hannunsa a kafaɗunta ya juyar da ita,ta kalli gabar ɗin sannan ya miƙa mata sallaya.

Ƙuri tayi masa da ido tana kallon sa ,har ya koma ya cigaba da danna laptop ɗinsa tukun ta shinfiɗa sallayan ta soma sallah.

Tunda ta idar da sallahn tana zaune akan sallayan , Taufeeƙ yayi knocking ya tashi ya je ya buɗe ya karɓo abinci,a gabanta ya ajiye ya koma ya cigaba da abinda dake gabansa,da alama abin nada muhimmanci sosai.

Amma gaba É—aya rabin tunaninsa naga yadda zai faÉ—a ma Maami abinda ya faru, how will she react, shikansa bai sani ba.

Har la'asar ya miƙe ya fice a ɗakin,ita ma sai da tayi sallan ganin bai dawo ba yasa ta ɗan jayo ledan abincin ta ɗan ci kaɗan,rufewa tayi ta ajiye a gefe sannan ta miƙe akan sallayan, nan da nan bacci yayi a awon gaba da ita.

Bubbuga gefen sallayar da taji anayi shi ya tada ita, a tsugunne ta ganshi gefenta,yana ganin ta buɗe idonta ya miƙe,yana faɗin "ki tashi kiyi sallah",

mutsuke idanunta ta shiga yi ta miƙe ta wuce toilet, sai da ta yi tsarki,sannan tayi alwala ta fito,karkaɗe sallayar tayi,ta sake shimfiɗawa sannan tayi sallah,duk abinda takeyi yana kallonta, sai da ta idar yace tashi
"kiyi isha",

kallonsa tayi sai kuma tace "anyi isha ne?",

"Ban sani ba" yace a taƙaice yana zaro wayarsa ya fara dannawa,

bata sake cewa komai ba ta miƙe ta yi isha sannan tayi shafa'i da wutiri, sai da tayi addu'a ta shafa sannan tayi kwanciyar ta akan sallayar,

Shima bai ce mata komai ba ya gyara kwanciyarsa a kan gadon,sannan ya kai hannu ya kashe wutar ɗakin yana shafa addu'ar bacci(asuba ta gari🥱).

Washegari da wuri suka ɗauki hanyan Abuja, duk da baiyi niyyan tafiya a mota ba amma ganin bata taɓa shiga jirgi ba ya sa yace su tafi a mota kawai,

Tunda suka iso garin Abuja take kalle kalle, yau gata a birnin da take buri kullum, amma ba tare da Nennen ta ba, a take taji wasu hawaye na shirin zubo mata,kallonta yayi ta gefe, a zuciyarsa yana faÉ—in
"wai Ni wannan yarinyar hawayenta anya bazai ƙareba kuwa".

girgiza kai kawai yayi ya juyar da kansa yana kallon window É—in shima.

Tun kafin Taufeeƙ ya gama parking motar,bodyguards ɗin suka ƙara so da sauri, su ka tsaya, da sauri suka buɗe masa ƙofa, suna gaishe shi, a taƙaice ya amsa musu yayi shigewar sa ciki,

Ganin basu lura da ita ba yasa Taufeeƙ ƙarasawa ya buɗe mata ƙofan yana murmushi dan yadda yaganta duk a tsorace.

Ƙafafuwan ta zuro a hankali,waɗanda suke cikin flat shoes Wanda ya kawo mata tare da kayan jikinta,a hankali ta ƙarasa fitowa tana kallon ƙatoton mansion ɗin da aka kawota, a hankali take bin bayan Taufeeƙ ɗin har cikin main parlour na gidan,inda bodyguards suka riga suka shigo musu da kayayyakin su.

Da gudu Asabe da Amina suka fito a kitchen ɗin suna rige rigen ƙarasowa wajen Taufeeƙ,kallonsu yayi yana murmushi yace

" kukuma Fah "

da sauri Amina tace

" Sir TaufeeÆ™ yanaga kun dawo da wuri, Ni wallahi ban ma san ran dawowan ku nan da wata uku Bama wallahi"

ta faÉ—a tana kallon Noor ta ke tsaye kawai tana kallonsu"

"Sai kuma kika ganmu koh"
TaufeeÆ™ ya faÉ—a yana hawa da kayan Sir Zannur steps É—in.

sai da ya kai ya dawo ya É—au sauran sannan ya kalli Asabe da Amina yace

"ga baƙuwa,ku gyara mata ɗaki a sama, anan zata zauna and ku kula da ita sosai fah, idan ba haka ba ku da Sir Ni dai babu ruwana"

ya faÉ—a da sigar tsokana yana haurawa saman,

Har rige rigen ƙarasowa wajenta sukeyi, Asabe tace "sannunki da zuwa baƙuwar Sir" ta faɗa tana murmushi.

*💖ABNUR💖*

*By* *maimoon* 🤓

*Elegant* *online* *writers* 📚📖

*Free* *book*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.