Abnur Complete Hausa Novel
Reading file: Abnur_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 16 of 24
*Page 17*
Da safe ma kiran doctor ne ya tashe sa, akan yana nemansa da gaggawa, a gaggauce ya shirya ya bar gidan, ba tare da ya ma Noor sallama ba.
Noor kam, tunda tayi sallah, ta gagara koma wa bacci, tunani takeyi meyasa bai zo ba?, bayan ya mata alƙawarin zai zo komin dare.
"to ko bai dawo bane jiya" abinda zuciyarta ta raya mata kenan, Definitely bai dawo ba, tasan da zai shigo, to ko jikin TaufeeÆ™ É—in ne, ya hanashi dawowa,
wani zuciyar ta sake raya mata, haka tayi ta tunane tunane, kafin daga bisani ta miƙe ta wuce toilet.
Wanka tayi, ta fito ɗaure da pink towel mai kyau, fararen ƙafafuwanta, sanye cikin room slippers pink,
jiki a sanyaye ta ƙarasa ta buɗe sif tana kallo, riga da skirt ta zaro na atampa, ɗinkin riga da skirt, ta ajiye akan gadon, kafin ta ƙara sa gaban mirror ɗinta, dake shaƙe da abubuwan anfaninta.
Mai ta É—auka tana shafawa akan lallausa fatar ta mai santsi, amma duk tunaninta na wani wajen daban,
a haka har ta ƙara sa, kayan da ta ajiye ta ɗauka ta sanya, yadda suka zauna ajikinta tubarakallah masha Allah, kallon kanta ta tsaya yi a madubi, sai kuma ta ɗan yi murmushi, dan ko ba'a faɗa mata ba tasan ita ɗin mai kyau ce, akan laɓɓanta wanda suke pink shar, sannan kamar ta shafa musu lip gloss, saboda yadda suke koda yaushe da santsi da yalƙi ta furta
"Alhamdulillah"
Gefen gado ta koma ta zauna, tana kallon agogon hannunta, ƙarfe takwas saura, da sauri ta miƙe tsaye a ranta tana faɗin "bari kawai na dubo shi, anya ma ya kwana a gidannan."
Daga haka ta fice a ɗakin, tana tafiya a hankali, turus tayi a bakin ƙofan tana kallon Yasira, da ta fito daga ɗakin, daga ita sai kayan bacci wanda ko Cinyarta basu gama rufewa ba, idanunta da alamun, tana ganinta itama tayi saurin yin baya, tana kallon ta, sai kuma ta zo zata gilma ta,
Hannu Noor tasa ta dawo da ita, tana kallonta cikin ido tace
"Yasira me kike yi a É—akin Zannur"
Ta faɗa tana zare mata ido, kamar zasu faɗo ƙasa
Cikin nuna tsoro da kuma kuka Yasira ta soma magana
"Madam dan Allah kiyi haƙuri, ba komai bane, kawai Sir yaga halin da nake ciki jiya saboda rashin lafiyan Yayana, shine yace nazo, to shine bacci ya ɗauke Ni a nan, ba komai bane"
Noor kallonta ta tsaya yi kafin cikin tsawa tace
"ƙarya kikeyi, aka gaya miki shi jahili ne da zai gayyaceki ki kwana a ɗakinsa, alhalin ke ba muharramarsa bace"
Cikin kuka wiwi, Yasira ta soma faÉ—in,
"wlhy da gaske nakeyi Ma"
"Ok to da ya kiraki ke kuma sai kikazo, saboda ke munafuka ce harda sako kaya irin waÉ—annan"
Ta faɗa tana nuna jikin Yasira, rai a ɓace idanunta sun gama canza kala
"Ma kiyi haƙuri Sir ne ya bani yace in saka, nima bansan dalilinsa ba, kuma Ni bazan iya yi masa musu ba shiyasa nasaka"
Girgiza kai kawai Noor takeyi, kafin ta sake Yasira ta juya a fusace ta nufi É—akin ta, wato abinda ya hanashi zuwa gareta jiya kenan!
me yasa zuciya ta yaudareta da har take ganin kodai Zannur ya fara sonta ne, gadonta ta faÉ—a tana cigaba da rusa kuka wiwi.
Da sauri Yasira ta zaro dogon hijab ɗinta, a inda ta ɓoye ta zura, sannan ta koma ɗakin Zannur cikin sassarfa, inda tasan yana ajiye laptop ɗinsa ta nufa, kasancewar babu security yasa ta buɗe da sauri, sai da ta tabbatar ta goge wannan footage ɗin kamar yadda ta goge na Garden, kafin ta shiga tafa hannunta tana murmushin mugunta,
"Yaya Taufeeƙ, kayi kuskure, da har kake ƙoƙarin rabani da rayuwata, dan kuwa Zannur rayuwa ta ne, zan iya komai dan na mallakesa, amma bazan ƙi gode maka ba, saboda makarantar computer da ka sakani, har na zama computer guru, idan ba haka ba, da tuni asirina ya tonu, sannan ina mai tabbatar maka bazan taɓa bari ka farfaɗo ba,bare har ka tona min asiri, har sai Zannur ya Zama nawa."
Daga haka ta fice a É—akin tana murmushi, da jinjina ma kanta.
******
"Congratulations, gaskiya dan uwanka, yana da matuƙar Sa'a, ba kowa bane ya ke shiga coma ya dawo da wuri, but da izinin Allah jiya ya motsa, kuma daga nan zuwa ko wani lokaci, zai iya farkawa."
Da sauri Zannur ya É—ago yana kallon likitan, jinjina masa kai doctor yayi alamar tabbatarwa,
"But saboda lafiyarsa, yasa bazamu bari ya gana da kowa ba, har sai bayan kwana uku"
Likitan ya ƙara sa faɗa yana gyara glass ɗin idanunsa, da murmushi a kan fuskarsa.
"Alhamdulillah, Alhamdulillah, alhamdulillah"
shine kaÉ—ai abinda Zannur ke iya faÉ—a, ko babu komai, TaufeeÆ™ zai faÉ—i wanda ya aikata masa hakan da kansa.
Miƙewa yayi yana miƙa ma doctor ɗin hannu, suka yi musabaha, kafin ya fice a office ɗin yana jin matuƙar farin ciki, bai zarce ko ina ba sai gida.
ÆŠakin Noor ya nufa, dan yana so ta amsa masa tambayoyin da ya kwana dasu,
Tunda ya shigo ɗakin taji shigowar sa, amma sai tayi kamar tana bacci, ƙarasowa yayi ya zauna a gefen gado yana kallonta, kafin a hankali ya sa hannuwansa duka biyu ya ɗago ta gabaɗaya,
yatsine fuska tayi kafin tace "miye hakan?"
Bai kulata ba ya zaunar da ita a tsakiyar gadon yana kallonta da fuskar da babu wasa yace " " " Noor! "
Tone ɗin da yayi maganar dashi, ya sata nutsuwa ta tsura masa ido tana saurarensa, duk da matuƙar haushinsa da takeji.
A hankali ya cigaba da magana
"Noor ina so ki faÉ—a min, me ya haÉ—a ki da TaufeeÆ™, da har kika aikata masa haka"
Zaro idanunta tayi duka tana kallonsa kafin tace
"Me kake nufi na aikata masa haka, meyasa zan masa haka?, me ya min?"
Cikin ɓacin rai yace
"Noor na riga nasan komai, ina so ne ki faÉ—a da bakinki, miye TaufeeÆ™ ya aikata miki daya cancanci haka?"
Idanunta da suka ciki da hawaye, ta rintse ,kafin tace
"Wallahi tallahi, a haka na gansa, nima..."
"Ƙarya kikeyi", ya faɗa a tsawace yana miƙewa tsaye, gabaɗaya fuskarsa ta gama canzawa, hannunsa yasa a gashin kansa ya birkita kafin yayi ƙwafa yana faɗin
"nayi zaton zan iya amincewa dake, saboda kamilalliyar fuskarki, ashe zuciyar ki baƙa ce, Ni ina da shaidan cewa lokacin da kika shiga kika samesa da ransa, sannan babu wanda ya ƙara shiga bayan ke, wace irin zuciya ce dake, azzaluma mara imani"
Kasa haƙura tayi, idanunta ya rufe, a fusace ta sauƙo daga kan gadon tana kallonsa, hawaye wasu nabin wasu
Cikin Muryar kuka ta shiga faÉ—in
"abinda yasa ka kawo Ni gidanka kenan?, meyasa baka bar Ni a can na mutu ba, meyasa ka ɗauka ma Nenne alkawarin da bazaka iya cikawa ba?, nagode wa Allah, kuma bana buƙatar kowa ya yarda dani saboda Ni nasan kaina, Ni ba azzaluma bace, kuma Ni ba mai kisan kai bace, sannan Ni ba fasiƙa mai zina bace"
ta faɗa da ƙarfi tana rushewa da kuka.
Da sauri ya É—ago fuskarsa ya kalleta, a hankali ya tako dai dai inda take, fuskarsa tayi jajazir
"Waye fasiƙi mazinaci?"
ya tambaya yana kallonta.
Ƙin dagowa tayi da ƙarfi ya ɗagota yana kallonta
"nace miki waye fasiƙi mazinaci?"
Da zafin rai take kallonsa kafin tace
"ka ɗauka zan ji tsoronka ne in kasa maimaitawa, kai fasiƙi ne kuma mazinaci, kuma Allah bazai Barka ba"
ÆŠif ta É—auke wuta sakamakon wani shahararren marin da taji a fuskarta har sai da jinta da ganinta ya É—auke na wasu sakonni
"Ni ne mazinaci?, Ni?"
sai kuma ya furzar da iska mai zafi, yana faÉ—in
"nayi dana sanin baki dama, nayi dana sanin tunanin kin cancanta na so ki, nayi da na sanin saninki, kuma ina mai tabbatar miki da kaina zan hukunta ki,bana buƙatar kowa, zanmiki mafi munin hukunci wanda bazaki taɓa mantawa da Ni a tarihin rayuwarki ba, yanzu zakisan waye Abubakar shuraim a baya Zannur kika sani "
daga haka ya juya ya fice a ɗakin, kai tsaye gidan ya bari, dan gidan ya masa baƙiƙirin ba zai iya zama a cikinsa ba, so kawai yakeyi Taufeeƙ ya tabbatar masa da bakinsa cewa Noor itace ta caka masa wuƙa, daga nan kuma zai yanke mata duk hukuncin da ya dace da ita.
Ɗurkushewa tayi tana wani irin kuka, ta shiga uku, shin dama fuska biyu yake dashi, sai da ya nuna mata ɓangarensa mai kyau, kafin ya nuna mata mafi munin ɓangarensa,
"Bazai yiwuba"
ta faɗa tana miƙewa tsaye,
Sai kuma ta nufi sif É—inta kamar zararriya,
birkito kayan tayi, amma ta kasa É—aukan ko É—aya, jakanta ta nufa ta buÉ—e ta ciro atm dinta, ta zura hijab É—inta tana rusa kuka kamar ranta zai fita.
Fitowa tayi daga ɗakin bata ko ganin gaban ta, da sauri Asabe da Amina da ke tsaye cirko cirko suka nufo ta, dan suna jiyo hayaniyansu daga sama, amma basa jin me suke faɗa, sai kuma sukaga Sir ya fita ranshi a ɓace,
"Madam lafiya, ko jikin Sir TaufeeÆ™ ne ya tashi?"
Ko kallonsu batayi ba ta nufi ƙofa,
Da sauri Asabe ta sha gabanta "ina zakije please madam, ki faÉ—a mana Please"
"Out of my way" tafaÉ—a tana zare dukkanin idanuwanta,
Da sauri Asabe ta matsa tana matsar kwalla, dan dai ta tabbatar ba fitan lafiya Noor zatayi ba yanzu
Ko dai jikin Taufeeƙ ne ya tashi, to ko Taufeeƙ ɗin ya mutu ne, da sauri ta juyo da nufin ta tambayeta, amma inaa har ta fice a falon, da ƙafa ta taka har gate, ba tare duk ma'aikatan gidan sunyi yunkurin hanata ba, dan babu wanda bai san Madam bace, dan Taufeeƙ da kansa ya sake tara su kamar yadda ya tara su a baya, ya shaida musu, matarsa ce, kuma subi dukkan umarnin ta.
Mai gadi dake tsaye jikin gate da sauri yace
"Hajiya meke faruwa?, ko jikin TaufeeÆ™ É—inne? naga yallabai ma ya fita a fusace"
Ba ta basa amsan sa ba sai cewa da tayi
"baba buɗe min ƙofa"
Yadda yaga babu alamun wasa a tare da ita yasa shi saurin buɗe ƙofan yana faɗin
"Hajiya a dawo lafiya, Allah ya ƙara bashi lafiya bawan Allah."
Bata kulasa ba, tayi ficewarta, tafiya kawai takeyi, da kafa burinta kawai ta bar Area din gidan gabaki É—aya,
Sai da ta iso main junction kafin ta samu abin hawa, yana tsayawa,
Shiga kawai tayi ba tare da ta ce masa komai ba.
Sai da ya fara tafiya kafin yace
"Hajiya ina zan kaiki?"
Rasa inda zatace tayi, dan babu inda ta sani a faÉ—in Abuja, ahankali tace
"ka kaini guri mai nisa daga nan ko nawa ne zan baka"
ta faÉ—a tana kifa kanta, shiru mai adaidaita yayi har suka iso inda yake ganin tayi nisa sosai da inda ya É—auko ta.
Juyowa yayi yace
"Hajiya mun iso"
idanunta ta É—ago ta kallesa kafin tace
"bari in cire kuÉ—i sai na baka."
Dayake indaya kawota kusa da kasuwane, bata sha wahala ba ta cire a P.O.S ta bashi, godiya yayi ganin ta bashi fiye da kuÉ—in sa, yaja mashin É—in sa yayi gaba.
Guri ta samu can gefe ta zauna, tana kallon área din, sai kuma ta miƙe, gurin wani mai sai da kati ta nufa a hankali tace masa, malam dan Allah akwai tashan mota anan, nuna mata yayi yace gashi can a gaba kaɗan
A hankali ta masa godiya kafin ta juya ta nufi tashan, dan gani takeyi har yanzu batayi nisan da ya kamata ba tunda suna gari É—aya.
Tana shiga tasha, yaran tasha suka soma tambayanta inda zataje,
"inda yafi nisa"
kawai ta iya furtawa tana share hawayen da yaƙi tsayuwa a fuskarta
Yaron motan da ke son motan kano ya cika, yayi saurin faÉ—in,
"aikuwa Kano ne inda zakije, dan dai kam akwai nisa daga nan"
ya faɗa yana ƙoƙarin janta dan karta fasa tafiyan, miƙa masa ATM dinta tayi tace
"sai na cire kuÉ—in mota"
da sauri yace
"babu damuwa Madam, ga p.o.s nan ma"
sai da ta sake cirewa ta biya kuɗin motan, kafin ta soke sauran canjin, har mota ya cika tana jingine da window hawaye na sauƙa a fuskarta, sai da suka hau hanya sosai kafin ta lumshe idanunta a hankali ta furta
"Dama yaudarar kaina nakeyi, U never loved me,kuma zanyi nisa da kai, nisa na har abada."
(wannan shine dalilin Noor na barin gida har ta haÉ—u da su khamal)
Zannur kam tunda ya fito a gidan, direct hotel yayi booking, yana shiga ɗakinsa ya rufe kofar yana faɗawa kan gadon ɗakin, yana jin zuciyarsa na suya, shi zatace ma mazinaci, sai kuma ya yi ƙwafa, yana jaddada ma kansa,
bazai koma gidan ba har sai Taufeeƙ ya amsa masa tambayoyinsa nan da kwana uku, a lokacin zai kamata da hujja, daga haka ya miƙe ya wuce toilet.
Ranar da Taufeeƙ ya cika kwana uku, a ranar Zannur ya samesa a asibiti, da ƙyar Doctor ɗin ya bashi daman ganinsa.
Yana shiga, ya zuba ma TaufeeÆ™ idanu, yanda ya rame, oxygen ne a hancinsa, dan baya iya numfashi yadda ya kamata,
Kujera ya ja ya zauna kusa da shi ya riƙe hannuwansa, ga mamakin sa, sai yaga hawaye na gangarowa a fuskar Taufeeƙ.
Shafa hawayen yayi, kafin yace
"ka kwantar da hankalinka, ka sanar da Ni waya maka haka, duk da na riga na sani amma inaso inji daga bakinka, shin Noor ce ta caka maka wuƙa?"
Ya tambaya a ƙagauce
Zaro ido Taufeeƙ yayi sai kuma ya shiga girgiza kansa da sauri, sauƙe masa oxygen din yayi dan ganin kaman Yana son cewa wani abu
"Ba ita bace.. batasan komai akai ba.. watace daban..." kasa ƙarasawa yayi, jin an murɗa ƙofan ɗakin an shigo,
Yasira ce ta shigo, da basket a hannunta tana kallon yayannata, wanda shima ya ke kallonta, hawayen idanunsa na ƙara zuba,
juyowa yayi da niyyar cema Zannur ita ce, amma sai yaga Zannur ɗin ya miƙe, a hankali ya ƙara so ya maida masa oxygen ɗin, dan bayason suyi maganan a gaban kowa, shafa kansa yayi yace
"we will talk later ok"
Sai kuma ya juya ya kalli Yasira
"waya kawoki nan"
Da sauri tace "Sir dan Allah kayi haƙuri, na kasa jurewa, ina so inga yayana, shiyasa nazo"
"Babu komai" ya faÉ—a yana juyawa yabar É—akin, dan hankalinsa gabaÉ—aya yana ga Noor a halin yanzu, dan kuwa ya tabbata ya mata laifin da zaiyi wuyan kankaruwa,
duk da Taufeeƙ bai faɗa masa wacece ta caka masa wuƙa ba, amma ya tabbatar masa ba Noor bace, hakan yana nufin zargin da yake mata ba daidai bane, fitowa yayi a gaggauce ya nufi motarsa, dan yana buƙatan magana da Noor ya wanke kansa.
Wlhy na gaji, naso mu dawo kan labari yau,amma dai saura ƙiris, mudawo.
Maimoon#
*💖ABNUR💖**
*By Maimoon*
*Elegant online writers* 📚📖
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.