Complete Hausa Novels

Abnur Complete Hausa Novel

Reading file: Abnur_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 3 of 24

*Page* *3*

Kwanci tashi asarar mai rai,yau kwanan Noor goma kenan a ƙauyen Marke dake jihar Kano.

duk da cewa har yau ba tayi musu cikakken bayanin abinda ya rabota da gida ba,amma sun fahimci ita ɗin mutum ce mai matuƙar daɗin zama, sannan bata da son magana sosai.

Hakan yasa suke zaune tare da ita, har zuwa sanda zata yanke shawarar sanar dasu ainihin abinda ya rabota da iyayenta ,

Umma tana matuƙar ji da ita, kuma hakan yasa basa ma ɗago maganar, saboda yadda daga an tambayeta, sai dai ta fara kuka, Sannan akoda yaushe maganar ta baya wuce"Umma kuyi haƙuri insha Allahu zan sanar daku ,har ma abinda baku tambaya ba".

A bangaren ZANNUR kam babu sauƙi, yayi iya ƙoƙarin sa ,ya haukace da neman ta har gidajen Radio,but har yau shiru ,ga baki ɗaya ya fita hayyacinsa ,bai taɓa tunanin za tayi koda tunanin hakan a zuciyar ta ba, talkless of aikata shi a aikace

Yau ma a gajiye ya dawo,bayan ya gama yawan nemanta kamar yadda ya saba ,duk da ya baza mutane sunfi a ƙirga da hotunanta ana nemanta, but shikanshi ya kasa daina wa.

kullum gani yake idan ya fita yau zai ci karo da ita ,bazai taɓa manta yadda abubuwa suka kasance ba shekaru biyu da suka wuce,ɗakinsa ya wuce ya zauna akan kujeran dake ɗakin yana jingina da kujeran "i can never give up on you, har sai na ganki sannan kin tabbatar min da bakinki zaki dawo gida na, idan ba haka ba, ban san tayaya zan yafe ma kaina ba ,I know I will never be able to
forgive my self idan har wani abu ya sameki".

Da ƙyar ya miƙe daga kan kujeran ya zare rigar jikinsa,ƙirarsa na ƙarfafa ya bayyana, duk da yanzu rabonsa da workout ɗinma tun ranar da Noor ta bar gidan, wanda a da yake cikin morning schedules ɗinsa da baya iya tsallakewa,

bayi ya wuce yayi wanka, yana fitowa kayansa kawai ya zura, yana jin yanda cikinsa ke kukan yunwa.

A hankali yake sauƙowa stairs ɗin, gaba ɗaya ya canza kamar ba Zannur ba, 'the master of all' harta masu aikin gidan sun san baya cikin kwanciyar hankali, duk wanda yake tareshi yasan yana cikin matuƙar damuwa.

Falon ya ƙaraso ya zauna yana rage ƙarfin ac, dan kamar sanyin zazzaɓi ma ya keji a jikinsa, Yasira ta ƙara so wajensa da sauri tana faɗin "Sir Should I serve your dinner?" Kallonta kawai yayi ,sai Kuma ya mayar da kansa ya jinginar, yama rasa me zai ce mata, bakinsa ya masa nauyi,sai da ta sake tambayan tukun ya ɗaga idanunsa,masu rikitarwa ya zuba mata su, sai kuma yayi gyaran murya yace "miss You Are fired!"

Zaro ido tayi tana kallonsa, nan take tafara hawaye tana faÉ—in "Sir I am very sorry Dan Allah Kar ka koreni" "why shouldn't i?" ya katse ta a tsawace , "sanda ta tafi ta barni why don't you stop her ?"

Ta buÉ—e baki zatayi magana, yayi saurin sanya yatsansa a baki , yace "shhhhh not another word, abinda nakeso dake yanzu shine,U Should get out of my sight immediately,before I lose my temper completely".

Da sauri ta miƙe daga tsugunan da tayi, takoma kitchen da sauri! ,Ƴan matan da ke cikin kitchen ɗin suka kece da dariya ,Amina tace "sai da nace miki kar kije! ,kwanakin nan Sir neman inda zai huce haushinsa yake".

Asabe da ke goge goge, tayi ƙwafa tana faɗin "sai kace sanda Madam ɗin takenan ya damu da ita" ,Ameena tace "Wallahi fah nima abin mamaki yakeban" ,Yasira dai bata bi ta kansu ba, ta wuce ta ƙofar baya dake kitchen ɗin, ta nufi shashen ma'aikatan gidan, a zuciyarta tana sake dana sanin zuwa tambayarsa da tayi.

Shi kuwa ko a jikinsa, kawai burinsa ta inda Noor zata ɓullo ,wayarsa ce tafara ringing,a hankali ya ɗaga wayan yana kallon mai kiran "Maami" da ya gani ya shashi shafa yalwataccen sumarsa, he has been avoiding her since, dan baisan me zai ce mata ba sam, shahada yayi ya ɗau wayan "sallama yayi daga ɗayan ɓangaren ammi ta amsa tana faɗin

"Habibi ina ka ajiye wayarka, I have been trying to reach you but baka picking calls ɗinka, I hope everything is fine there? " shiru yayi kafin ya samu ƙarfin halin haɗa kalmomin bakinsa "maami ya Dubai?" "lfy ƙalau habibi ina Noor" shiru yayi ya kasa cewa komai ,shirun da taji yayi yawa ya sata sake faɗin "Habibi are you there? "Umm...Maami" "are you okay my boy? mai yake faruwa me kake ɓoyemin? I hope you are not trying to hide anything!"
"maami babu komai fah don't you believe me"

"na yadda da kai mana my boy, to yanzu ina Noor? it has been long tunda mukayi magana da ita, kai mata wayan "

A É—an daburce yace "umm wai Noor ..in kai mata wayan? to ai tayi bacci,batajin daÉ—ine shine sai ta kwanta"
"ok shikenan maybe next time Allah ya sauwaƙe ka kira abbun ka, yace yakiraka baka picking " "a hankali yace "insha Allah Maami" daga haka yayi hanging Kiran yana sauƙe ajiyar zuciya.

Da sauri kamal ya shigo gidan, hannunsa riƙeda jarida wanda hotonta ke jiki ɓaro ɓaro ,ita kaɗai ya samu a tsakar gidan tana wanke kwanukan da suka ɓata da safe ,yanayin da taga ya shigo ya sata saurin ɗauraye hannunta,

tana ƙarasowa tsakar gidan dai dai umma ma ta fito daga ɗakin ta, tana faɗin "Noor Nikam Ina kikaga na ajiye goron da ke cikin ledannan ne?

tsayawa tayi tana kallonsu yadda sukayi cirko cirko a tsakar gidan. "Lafiya?" Ta tambaya tana kallon Noor "umma nima wallahi bansani ba, haka naga ya shigo kamar ba lafiya ,umma ta karkata akalar tambayan nata ga kamal da ke tsaye yana kallonsu,

miƙa mata jaridar yayi yana faɗin, Abdul ne ya shiga cikin gari ɗazu, shine nace masa ya siyomin jarida dan na karanta, shine fah kawai naga hoton Noor ajiki ,Umma ta karɓa tana dubawa, sai kuma tace to me aka rubuta ajiki? ko yan uwanta suke nemanta? ai dama dole su nemeta!! "

Kamal kallonta kawai yake ganin tana ƙoƙarin wucewa ɗaki ya sa yace"Noor!" Ta juyo Amma Bata dawo ba, a hankali yace "bakya tunanin 'yan uwanki suna cikin wani hali na rashin ganinki? kuma haryanzu baki ga buƙatar ki sanar damu komai ba!?"

shiru tayi ba tare da tace komai ba, a hankali umma ta ƙaraso inda take ta dafata tace"Noor bana miki kallon ƙasa da abinda na haifa, bakya tunanin idan ke 'ya tace kika bar gida irin haka, hankalin dole ya tashi to bare mahaifiyar ki, Yakamata ki faɗa mana abinda ya rabo ki da gida Noor, ko kina tunanin bamu kai musan damuwarki bane ?

da sauri ta girgiza mata kai tana faɗin"umma dan Allah karkice haka, wallahi kun kai kuma har kunfi haka a gurina"ta share hawayen da ya zubo mata tace "insha Allah na muku alƙawari yau zaku san komai game dani, amma ina neman alfarmarku, ku bari zuwa baba ya dawo zuwa dare, ina so na baku labarina a gaban sa "umma ta yi murmushi tana faɗin Allah ya kaimu Allah ya muku albarka "suka amsa da ameen

Maimoon#
*💖*ABNUR**💖

*By* *maimoon* 🤓

*Elegant* *online* *writers* 📚📖

*Free* *book*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.