Complete Hausa Novels

Abnur Complete Hausa Novel

Reading file: Abnur_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 22 of 24

*Page 22*

Zannur kam, gaba É—aya ya rasa me ke masa daÉ—i, ya canza kamar ba shine Zannur the master of All ba, tun Maami na É—auka da wasa, har hankalinta ya soma tashi, kwata kwata ya daina walwala, ko magana ba yayi sai dole.

sometimes Maami har kuka takeyi, sai dai Abbu ya rarrasheta, zuwa yanzu shima abin ya fara damunsa.

Yasira ta rasa yanda zatayi, gabaÉ—aya komai ya kufce mata, ita sam ba haka ta so ba, to yaushe ma Zannur ya soma son Noor har haka?, lallai tayi mugun sake.

Amina da Asabe kansu sun rage walwala, da yake yanzu Amina ce chief of kitchen staffs, kullum ta gansa, cikin damuwa take ganinsa, duk da cewa a da ma ba wani shiga harkarsu yakeyi ba, sai dai TaufeeÆ™, amma yanzu daga shi har TaufeeÆ™ sun zama wasu iri, hakan yasa gidan kowa baya cikin farinciki.

*******

"Habibi wai meyasa yanzu baka jin maganata ne?, rabonka da abinci tun yaushe?, Please Habibi kaci abinci kaji?" ta faÉ—a da alamun damuwa a tattare da ita

Bai ɗago ba, bare tasa ran zai tanka, hakan yasa ta ajiye tray ɗin akan center table na ɗakin ta juya ta bar ɗakin tare da ja masa ƙofa.

Tray ɗin abincin ya ƙura ma ido, yana jin zuciyarsa na bugawa da sauri, bai taɓa sanin yana ma Noor irin Wannan matsanancin son ba, har sai da tayi nisa dashi.

ÆŠaga idanunsa yayi yana kallon saman É—akin, kafin ya shafa kansa, yana gyara kwanciyarsa a kan gadon Noor.

***********

"Abbu ya zanyi?, yarinyar nan ta cutar min da yarona, me yasa in the first place zata tafi ta barsa?"
Maami ta faÉ—a tana fashewa da kuka.

Jawota Abbu yayi ya rungume, shi kansa daurewa yakeyi, a hankali yace

"Hilwa, listen to me, ki kwantar da hankalinki, idan har tana raye za'a sameta."

Ya faÉ—a yana shafa sumar kanta, É—ayan hannun kuma yana share mata hawaye

Shiru tayi tana kallonsa, kafin tace

"Abbu ya zamuyi mu taimaka ma Habibi ya sami yarinyar nan?, don itace kwanciyar hankalin mu duka."

Shiru Abbu yayi kafin yace,

"ga shawara"

Da sauri ta miƙe daga jikinsa tana faɗin

"Dan Allah Abbu faÉ—a min, zan yi ko miye ne"

Murmushi yayi yace

"Me zai hana mu siyi gaban mujallar gobe, mu da kanmu on behalf of Zannur, mu roƙi Noor ta dawo."

Shiru tayi sai kuma tace

"Shikansa Zannur É—in ya sa an buga mujalla ana nemanta, but ba'a sameta ba."

"Nasani Hilwa, but still zai iya yiwuwa, shi tana jin haushinsa, amma ai mu zata ji kunyar mu ta dawo, mu dai kawai ba burinmu Noor ta dawo ba?"

Shiru Maami tayi, kafin tace

"Allah ya sa mu dace, wannan yarinya dai ta taimake Ni ta dawo."

Kamar yadda Abbu yace, haka mujallar washegari ta fita da jawabin Abbu da Maami, da hoton Noor ba tareda ko shi Zannur É—in ya sani ba.

Papi dake karatun jaridar safiyar ne ya ci karo da hoton Noor da kuma bayanin su Abbu, wanda duk banbaki ne, da kuma sanar da ita haalin da Zannur ke ciki akan rashin ta.

Murmushi yayi a hankali ya furta akan laɓɓansa

"Daughter kinyi punishing É—insu enough, it's time ke ma kiyi rayuwa kamar kowa da mijinki"

Daga haka ya juya ya fito a ɗakin, Ammi ya samu a ɗakinta tana shirya siff ɗin ta, a hankali ya ƙaraso da sallama, kafin ya samu guri a gefen gadonta ya zauna yana kallonta

Ƙarasawa tayi, itama tazo kusa dashi ta zauna tana faɗin

"Is anything wrong?"

Murmushi yayi mata yana jan kumatunta,

"Babu komai Fah, look how you are worried for reason"

Murmushi tayi itama tana faÉ—in
"dole na damu na ganta kamar abu na damunka."

Shiru yayi sai kuma yace

"Ina Noor?"

"Tana É—akinta, I think bacci ma takeyi."

"Ok", ya faɗa yana ɗaura mata jaridan akan ƙafarta

Sai da ta gama karantawa kafin tace

"to yanzu kai me ka yanke akan hakan?"

"Zata koma gidan mijinta mana, babu abinda yafi mata daraja kamar wannan, sannan ai sun gane kuskurensu, and am sure they won't repeat"

"Ok but da munji ta bakinta"

"Nope ki ce mata ta shirya zamuyi tafiya, i will return her myself, sannan in yi magana da mijinnata"

"Ah ah sai dai mu tafi tare Please Papi, Ina so in kai Æ´ata da kaina gidanta."

"Ok babu damuwa, zan kira su a waya tunda sun bada Number É—in da za'a yi contacting É—insu, in yaso zuwa Next week sai mu tafi."

"Allah ya kaimu"

Daga haka ya miƙe ya fice a ɗakin

Waya Ammi ta ɗauka ta kira wata balarabiyar ƙawarta, kayan gyaran jiki irin na amaren larabawa take só ta haɗa mata, and tana so ta turo mata zuwa gobe please it's urgent.

Sai da ta tabbatar mata babu damuwa, kafin ta kashe wayan, ta sake kiran wata ƙawarta wacce suka haɗu a Nigeria, watannanin da suka wuce, matar shuwa Arab ce, itama dai kayan gyaran jikin ta tambayeta, aikuwa matar tace mata zuwa gobe da safe ɗan ta zai kawo mata, a taƙaice dai Ammi sai da ta kira mutum kusan uku.

Washegari kuwa kaya suka iso, na Dubai ne kaÉ—ai sai zuwa yamma.

Noor da bata san abinda ake ciki ba, washegari sai gani tayi Ammi ta saka ta a gaba da gyara, daga a mata wannan sai a mata wancan, daga a bata wannan sai a bata wancan, da ta tambaya sai Ammi tace, so take ƴarta tafi ta kowa kyau, ita kuwa Noor ta yarda ta zage tana karɓan duk abinda aka bata.

Zuwa kwana uku, Noor ta koma wata sabuwar halitta, wani irin glow da skin É—inta keyi kaÉ—ai har abin mamaki ne.

Ita kanta har tsayawa take tana kallon kanta, Farhaana kam tasa ta take a gaba, tayi ta kallo sai dai kawai tayi murmushi.

Papi sunyi magana da Abbu, dan har ya sanar ma Maami, amma ko da wasa, basu sanar da Zannur ba, dan so suke suyi masa abinda ake kira suprise.

Da yamma Zannur na sauƙowa daga sama, dan yau yana so ya ɗan fita, kasancewar ya kwana biyu baya fita ko ina.

Maami da Abbu dake magana sukayi saurin yin shiru, suka zuba masa ido suna kallonsa, Maami na sake gode ma Allah a ranta, wai wannan kyakkyawan cikakken namijin É—an ta ne.

yana sanye da riga da wando na Louis Vuitton, Dan dai shi baya anfani da kowane kanfani idan ba wannan ba, sai dai gabaÉ—aya ya gama yin sanyi.

Ƙarasowa yayi falon yana kallonsu, sai kuma ya samu waje ya zauna yana faɗin

"Maami, Abbu me kuke cewa ne?, naga kunyi shiru da na zo, Ku cigaba da maganan mana, ina so inji"

Ya faÉ—a yana kallonsu

"Ehm dama batun komawa mukeyi, mun yanke shawara zamu tafi tare da kai
Ko ba haka ba Abbu?", ta faɗa tana ƙiftawa Abbu ido.

Murmushi kawai Abbu yayi ba tare da yace komai ba.

Cikin rashin damuwa da maganar yace

"Maami i don't wanna leave, ku tafi kawai ku barni."

Shiru Maami tayi Jin yadda yayi maganan, he sound very worried, sai taji kamar tace masa jibi iwar haka Noor tana tare da shi.

Cikin sanyi itama tace

"meyasa?, saboda Noor ne bazaka bi mu ba?"
Ta tambaya tana kallon fuskarsa

Kallonta yayi sai kuma yayi ƙwafa yana faɗin

"not at all since ita ta zaɓi ta barni, ba yanda zanyi da ita, I guess zan haƙura kawai, i won't force her into anything she don't wan't to, I will move on with my life, bana buƙatar in cigaba da tauye rayuwata a kanta, zan yi iya ƙoƙarina inga na saba da rashin ta."

Daga haka ya miƙe ya bar falon gabaɗaya.

Da ido duk suka bisa, Maami kam baki sake take kallonsa, kafin ta juya ta kalli Abbu, gyaÉ—a mata kai yayi tare da faÉ—in

"kar ki damu idan ya ganta komai zai dai-daita."

"Allah yasa" ta faÉ—a cikin sarewa.

Mutanen Kaduna sun gama shirin tafiya, wanda sam Noor bata san inda zasuje ba, dan ko da wasa babu wanda ya faÉ—a mata komai.

Tun a Airport take jin wani irin tsinkewar zuciya, a hankali ta kama hannun Papi ta riƙe tana maimaita duk addu'ar ta tazo bakinta.

Tunda aka kira passengers ɗin Abuja ta sake jin ƙirjinta ya buga, juyawa tayi ta kalli su Farhaana da Ammi da har sun wuceta.

Jan hanunta da akayi ya sata dawowa cikin hayyacinta, tana kallon Papi

"Daughter what are you thinking?, muje Mana" ya faÉ—a yana murmushi

"Papi zuciyata ce ke tsinkewa" ta faÉ—a idonta na ciko wa da hawaye

""Common not now Noor!, kiyi addu'a babu komai sai alkhairi, kinji?"

"To" tace, kafin Papi yaja hannunta suma suka bi bayan su Ammi.

Har jirginsu ya tashi, ta kasa samun nutsuwa.

In less than 30 minutes jirginsu ya sauƙa a Abuja, waya Papi yayi da Abba, akan sun iso, wanda dama tuni driver na jiransu a Airport ɗin.

Tunda suka É—auko hanya daga Airport Noor ke zare ido, ganin in da suka nufa yasa Noor fashewa da kuka, janyota Ammi tayi tana faÉ—in

"miye hakan Noor?",
Kasa cewa komai tayi, sai shesheƙa da takeyi.

A hankali ta ɗago kanta, tana ƙare ma compound ɗin parking space ɗin kallo, tabbass su Papi gidan Zannur suka dawo da ita.

Body guards Ne suka ƙaraso tareda buɗe musu ƙofan motan, gaba ɗaya zama tayi kamar doluwa, tana bin kowa da kallo, a hankali ta zuro ƙafafunta ƙasa, tana jin wani iska na kaɗa ta, ta ko ina a jikinta.

Cikin nutsuwa ta sauƙo tana kallo su Papi da su Farhaana da har sun yi gaba abinsu.

Riga da wando ne a jikinta na *PRADA,* sai kimono da ta sanya a zamansu kalar maroon, veil ɗin kanta shima kalar maroon ne, sai karamar jakar dake rataye a kafaɗanta, gashin ta ya kwanta lub lub har gaban goshinta, da gefen fuskarta, fuskarta looks natural, Dan babu komai a fuskar, lips ɗinta sun yi pink shar suna shining kamar ta saka lip gloss, Wanda sam babu abinda ta saka, haka suke naturally, ƙafafunta sanye cikin flat shoes na *GUCCI* .

Papi jin baiji alamar ta ba, ya sa shi juyowa, sai kuma yayi murmushi yana dawowa inda take, siririn hannunta dake sanye da agogo na *CHANEL* ya janyo yana faÉ—in

"Ya kika tsaya anan daughter?, mu ƙarasa Mana."

Binsa kawai takeyi kamar wata sokuwa.

A ƙofar main parlour suka ci karo da Abbu da Maami, ai kuwa Maami na ganinta, da sauri ta ƙaraso ta rungumeta tana faɗin

"Noor, marhaban Noor, you are welcome back", ta faÉ—a wasu hawaye na cika a idanunta.

Abbu ne yayi ma su Papi iso zuwa babban falon.

Zannur dake Zaune yana danna wayarsa, gaba É—aya ya gagara nutsuwa, danna wayar kawai yakeyi, shi kansa bai san me yakeyi a wayan ba.

Jin hayaniyar shigowar mutane, ya sashi miƙewa da niyyar haurawa sama, dan sam baya don hayaniya, kuma Maami batace masa zatayi baƙi ba, da bazai ma zauna a falon ba.

Cak ya tsaya da haurawa steps É—in da yakeyi, jin ihun su Asabe dake faÉ—in

"Oyoyo Noor, oyoyo Noor"

In slow motion yashiga juyowa, har ya juyo gabaki ɗayansa sa, yana sauƙe idanunsa akan Noor, wacce ke tsaye jikin Maami,

Cikin idanunta, idanunsa suka shige, kasancewar itama shi take kallo..............

Maimoon#

*💖ABNUR*💖

*By maimoon*

*Elegant online writers* 📚📖

*Free book*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.