Complete Hausa Novels

Auren iyayya Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Auren_iyayya_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 22 of 33

Washe gari Nanah tunda ta tashi jikin ta bbu ƙwari da kyar take komai take komai,cikin wata doguwar riga shadda milk colour ta musu anko ita da Noor yaji zubi banda na Noor dayake iya guiwa,da ƙaramin hannu sai sucks da cover shoe brown tasa mata ta kwatar da gashin kanta tayi kyau sosai,itama tayi kyau sosai koda yau har red lips tayi sosai tayi kyau hotuna tashiga watsa musu,sun yi kyau sosai wanda yafi kyau tasa a profile dinta,Kiran Jamal ne yashigo sanda tabari ya ɗanyi ringing kafin tayi picking,cikin farin ciki yake sanar mata after asr prayer zaizo insha Allah, "Allah ya kawo lfy abinda tace knan sun ɗan jima suna hira kafin sukayi sallama.

Wajen 4:30 ya iso yakirata yasa nar da ita,fitowa tayi a jiye Noor a ɗakin Ammih zata fita saide,tsala ihu Noor tayi tana kuka tana kiran sunanta har takai stairs kuma sai tsaya jin bazata iya tafiya tabarta ba yasata,koma wa ta ɗakko kota suka fito tunda ya hangu su yasake baki yana kallon su har suka isoh, murmushi ne ɗauke a face dinsa yana faɗin, "Masha Allah ashe ƴar tamu tafi Maman ta kyau gsky za'a bani kyautar ta Masha Allah balarabiya knan, murmushi Nanah tayi batare da tace komai ba hanu yamika ma Noor har Nanah zatace tana ƙiyuwa kuma sai tayi shiru,ga mmki kuwa yana miƙa mata hanu taje sama ya cillata yana faɗin i love children most especially daughters banida mace duka ukun are boys,murmushi tayi suka isa zuwa Parlour tamasa iso kiran Hajara me aiki tayi tasa ta kawo masa ruwa juice da snacks ta haura sama kiran Ammih.

Shigowan Salkhan knan ya hango motar sa ji yayi wani abu ya tsaya masa a zuciya, Parlour yanufo dan bai zaci yana Parlour ba yana shiga suka haɗa ido,wani abu ya haɗiye me ɗaci cikin ƙarfin hali ya ƙaraso suka gaisa cikin fara'a Noor ce tafara miƙa masa hanu yasa ya karɓe ta suka fice zuwa side dinsa,dai² da sakkowan Nanah tana murmushi tace masa Ammih nazuwa,kasa hkri tayi tana tambayan sa Noor kallonta yayi yace mata, "yayanki ya karɓe ta murmushi kawai tayi ta buɗe juice zuba masa ta koma gefe ta zauna.

Bbu jimawa Ammih ta sakko cikin shigarta ta manyan mata a mutunce,yana ganin Ammih ya sauka ƙasa ya zauna tana isowa yafara gaida ta Nanah kam gudu sama tayi tabarsu agun,nan yayi mata bayanin kansa family dinsu sanannu ne sbd zamanin mahaifin sa attajiri ne sosai yana da Mata biyu mahaifiyar Jamal itace amarya kuma Jamal shine danta nafari sunyi zama zaman da mahaifiyar Jamal ta wahala a hanun uwar gidanta da makirci wanda idan ba kasani ba kuma baza kace hkanba,sbd makirci irin na hajiya Rabi,sosai hajiya Dije ta wahala ahanunta.

Kuma yanemi izini kan cewa yana so yaturo mutanen sa ayi tambaya,idan ansa masa rana sbd shi ba yaudara yazo yiba tsaka ni da Allah yazo auren Nanah,sosai Ammih taji daɗi kuma tace bbu damuwa ai sanannu ne su insha Allah zaiji rana gun Nanah, 50k ya ajiye mata yafice yana fita yakira Nanah yace mata yana dayan Parlour din cikin sauri tafito karo sukayi da Salkhan da Noor a hanunsa dake wasanta,ganin Nanah kuwa yasata tafara miƙa mata hannu harta sa hanu zata ƙarbe ta amma ga mamaki saita ga Salkhan ya rungume Noor sun shige ciki ji tayi idonta sun cicciko amma saita matse ta shige.

Tana shiga tanemi guri can gefen sa ta zauna,kallonta yayi yana faÉ—in, "sannu sarauniyar kunya wato shine kika gudu kika barni nida mamah ko zan rama bari Allah ya kawo ranar da zan kaiki gun ummih na nima hkan zan miki, "murmushi tayi tace kaima kace naji kunya tom shikenan naji dama haka akeson mace ai.
"Dama kinada brother ne shiru tayi kafin da kyar tace, "masa aa cousin dina ne kuma shine daddyn Noor har ransa yaji kishi saide ya daure cikin tsoka na yace "ashe anan Noor tasamo kyau murmushi tayi batare da tace komai ba,hira suka ɗan taɓa kafin sukayi sallama yatafi,ta ɗan ji daɗin hira dashi sosai da fara'arta tashiga ta tarar da Ammih da Salkhan suna hira.
"Ammih ce takirata take sanar da ita yadda sukayi saide tace zata sa yayanta yayi bincike akan sa,kaman daga sama sukaji Salkhan na faɗin, "Soja ne kuma lieutenant colonel ne one star kuma one eagle shine fari gun mahaifiyarsa hajiya Dije yanada ƙanne huɗu uku maza ɗaya mace cikinsu akwai,Auwal,sadeeq,Abdul maleek da lst born dinsu Rahma kuma duk sunyi aure suna gari daban² macen kuma tana Spain da mijinta da ƴarsu ɗaya dukan su ma'aikatan government ne,ta ɗayar kishiyar kuma yaranta takwas biyar Mata uku maza matan duk suna aure ne suma gari daban² saide duk cikin Nigeria,mazan sauran suma ma'aikata government ne duk sunada Mata biyu na gari nan ɗayane yake kudu da matarsa da yaransa,iyayen su har yanzu suna gida ɗaya duk hidima tare yaran ke musu bbu banbanci barina tsaya anan na dawo kan Jamal,yana da Mata da yara uku duka maza sunan matarsa Hajiya Nabila kuma bata fiye zama a Nigeria ba shidai bayida da damuwa a iya bin cike na danayi,mutum ne shi me temakon talaka kuma bayida damuwa sam kowa faɗan kirkin sa yakeyi iya bincike na dai knan saide Ammih kisa aƙara bin cikawa zaman aure ba wasa ba,amma shikan mutum ne meyi nayi bin cike tun ranar daya fara zuwa gidannan,yana gama faɗin hka ya miƙe ya miƙama Ammih Noor yafice duk da mamaki sukabi sa da kallo.

Bbu wanda yasake mgna Nanah ta hau sama Ammih tafara kiran Brother dinta ta sanar masa da halin da ake ciki nan yasar mata da insha Allah gobe zai fara bin cike insha Allah.

3days ltr Brother din Ammih ne yazo har gida still yasake mai² ta mata cewa duk inda yayi sheda tagari ake basa,sosai Ammih taji daɗi saide basuyi saurin sanar dashi akan ya turoba sai da kusan bayan kwana 8, ranar da Nanah tasar dashi yayi murna sosai kuma yace Mata insha Allah jibi za'azo, Ammih na lura da Salkhan sosai ya rage shigowa sometimes ko Noor yake son gani zuwa yake ya ɗauke ta ba kaman da da suke hira ba duk ya canza sosai,Ammih ce takira sa tayi masa nasiha sosai tare da faɗa yaji daɗi sosai ranar har yaɗan sake.

Washe gari Jamal yakira wayan Nanah yake sanar mata cewa gobe zasu zo nan gidan su zasu ko akwai wasu dangin babanta da zasu kaiwa gaisuwar,ce masa tayi bari ta tambayi Ammih nan tasanar da Ammih tace nan zasu zo,saide ga mamakin ta yace shi gun dangin mahaifinta yakeso akai gausu wa ai mahaifin ta suna da main house,Nanah jin zancen sa sanda zuciyarta ta buga dan tasan komai dake ƙasa ce masa tayi tom bari tasa sake sanar da Ammih,jiki bbu ƙwari ta mayar ma da Ammih ita kanta ji tayi zuciyarta ta buga ta ina zata soma ita rabon ta dasu ai tamanta kuma yanzu meye abunyi daga dukan alamu wannan mutum yasan su sosai, "shikenan yau karya ta taƙare yanzu ya zanyi shiyasa akace dan gin uba sune akan gaba Ammih ranar har hawaye sanda tayi dan batasan ta ina zata fara ba lalle tana cikin wani hali.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.