Complete Hausa Novels

Auren iyayya Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Auren_iyayya_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 11 of 33

*Daga alƙalamin* ✍🏽📝

*Nanahkhadii* 💅🏽🛍️

*08069224458*
[8/28, 1:10 PM] Nana Khadiiii: 🕯️🕯️ *AUREN ƘIYAYYAH* 🔥🔥

*ELEGANT ONLINE WRITER'S* 📚

*A short story* 💋

*Na Nanahkhadii* 💅🏽🛍️

*Marubuciyar👇🏽*

*Cousins ne*

*Aruwan sama* *kaddara tasame*

*Almajiri ko attajiri*

*Hamdan paid book* *and now typing....* ✍🏽

*Auren kiyayya*

🅿️1️⃣8️⃣🔁 1️⃣9️⃣

*This book is dedicated to my dearies my* *Dost and my behty can't heart you less you guys mean* *a lot to me* 💝💖

*Fans dina inajin daɗin comments dinku yana sani nishaɗi saide lst page gsky banga* *comments yadda yakama ta ba idan banga comments* *yadda yakamata ba zan ajiye book din nagode🥰🥰* **son* *so fisabillah nanah khadii nayi ku over much love dearies* 😘🥰

*Bismillahi Rahmanir* *Raheem*

Sai wajen 2 Ammih tadawo hayyacinta sosai miƙewa tayi ta zare drip ɗin hanunta takama hanyan fita, buɗe ƙofan da'akayi ne yasa salkhan ɗaga idonsa, da sauri ya ƙaraso ya riƙe Ammih dai² da ƙaraso war wata nurse,ƙoƙarin maida ɗakin suka farayi saide sam taƙi ganin abu yafi yaƙarfin su yasa nurse kiran Dr cikin sauri ya fito zuwa gun.

Yana zuwa ya kama hannunta zuwa É—akin bbu um bbu umum tabisa duk tare suka shiga da nurse din da Salkhan,bakin gado ya kaita ta zauna cikin sanyi murya tafara mgna "Dr dan Allah ina neman alfarma kubani gawar Æ´ata muje gida na kwana ina mata addua,badan yaso ba haka ya bata magun guna ya yayi sallama suka kama hanyan gida.

Jikin Salkhan jikinsa sosai yayi sanya driving ɗin ma da kyar yakeyi ambulance na biye dasu a parlor aka ajije gawar,nan Ammih ta buɗe face din Nanah tana kallo kukane mai cin zuciya cike da nadama ya kuɓuce mata.

"Kiyafe mun yar nan son zuciyata da son abun duniya ta yasa na biye wa son zuciyata da sharrin haɗai daya huren kunne na cuceki kuma nacuci kaina haƙiƙa nima Allah bazai barni ba sbd nayi anfani da darajar da Allah yamun na tauye hakkin ki gashi narasa ki forever and ever nikam nashiga uku narasa ƴata ɗaya tilo,Allah ya yaye miki yasa Aljannah ce makomar ki nayafe miki Allah ya yafemu gaba ɗaya,kuka sosai Ammih keyi kaman ranta zaifi cikin ƙarfin hali Salkhan yazo ya ɗaga Ammih yana faɗin,Ammih yanzu nanah bata buƙatar kuka adduan ki kawai take buƙata kuka sosai Ammih keyi takasa controlling kanta.

Jan hannunta Salkhan yayi zuwa sama yace ta huta shi zai kwana da gawan yana Addua ,to kawai tace masa takoma ta zauna shikuma ya gangara don tema konsa ɗaya Dr yabashi kaftan yasa toilet din ƙasa yashiga yayi alalo saide still agun yaga Ammih dur ƙushe tana kuka,dafa kansa yayi dan shima kansa ciwo yake masa kaman zai faɗo ya ƙarasa gun, "Ammih kije kiyi alola kizo muyi karatun tare,bbu musu kaman wata yarinya ta mike tahau sama da Qur'ani da hijab har ƙasa ta sakko sa turare kala² ta fesa nan suka dukkufa karatun Alqur'an mai girma.....

Sai da kayi kiran sallan farko suka tafi sallah,Ammih na idar da sallah duk da daurewa kawai takeyi zuciyanta ba ƙaramin ciwo yake mata haka tafara kiran yan uwa da abokan arziƙi tana sanar musu,cikin ikon Allah kafin a iddar da sallan asuba duk yan uwanta dake kusa sun iso,ganin su ya sake sata wani sabon kuka Anty nusaiber kam kukanta take sosai duk abunda ya faru ranar auren ke dawo mata haƙiƙa sun shiga hakkin yarinyar nan zamanin nan ba'a auren dole bare na ƙiyayya tunda sun tabbata dukansu basu son juna suka dage sanda akayi abunnan.

Kafin kace wani abu gida yacika da jama'a ciki harda tsirarin dangin mahaifinta tass aka wanke ta aka shiryata cikin likkafinta ana aka É—aga ta zuwa gidanta na gsky......

_Kuyi hkri da wannan wlh naso yi dawa kitchen nashiga fatan zaku fahimmceni nagode sai kunjini wani page_ _É—in_

*Daga alƙalamin✍🏽* 📝

*Nanah khadii💅🏽* 🛍️

*08069224458*
[8/28, 1:11 PM] Nana Khadiiii: 🕯️🕯️ *AUREN ƘIYAYYAH* 🔥🔥

*ELEGANT ONLINE WRITER'S* 📚

*A short story* 💋

*Na Nanahkhadii* 💅🏽🛍️

*Marubuciyar👇🏽*

*Cousins ne*

*Aruwan sama* *kaddara tasame*

*Almajiri ko attajiri*

*Hamdan paid book* *and now typing....* ✍🏽

*Auren kiyayya*

🅿️2️⃣0️⃣🔁 2️⃣1️⃣

*This book is dedicated to my dearies my* *Dost and my behty can't heart you less you guys mean* *a lot to me* 💝💖

*Bismillahir rahmanin* *Raheem*

Ammih tunda daga tabbacin an É—aga gawan Nanah anfita dashi take kuka mai cin zuciya tabita da addua har akayi sallah,saide Salkhan amotar gawar shima yake.

Can gefe kuwa Maina na hango idonsa sunyi jawur dan kukan dayayi har yafita hayyacinsa,haka aka sallace ta aka kama hanya da ita.

Tafiya tayi nisa kaman dai² Nanah tafarka jitayi an ɗadɗaure ta kanta tasoma juyawa bbu wanda ya lura,kaman daga sama tayi wani atishawa daya dawo da hankali su baki ɗaya aiko kafin kace kwabo masu dira na dira masu ihu nayi,ganin haka yasa mabiyan su ma duk suka tsaya kaman za'ayi hatsari saide kuma dayake Allah da iko yake bbu wanda yaji ciwo saide masu dira dasuka gurgurɗe,ɓan garen driver kam shima parking yayi ganin yadda duk titi ya rikice ya fita da gudu.

Ƙoƙarin yaye ɗaurin da akayi mata take cikin ikon Allah ko tsab ta yaye shi, Salkhan da shima ya dura yake gefe ganin fa fa gske tadawo a tsorace ya ƙara so gun ya warware ta,ya tayata ta zauna da ido tabisa da kallo duk da bata cikin hayyacinta da alaman mamaki take kallonsa,ga mutane data gani sai guje² akeyi ana kallonta.

Cikin ƙarfin hali ya cire jallabiyan sa ya saka mata yajata zuwa cikin motar gawan direct asibiti ya wuce da ita,ɓangaren su Ammih kam anata koke koke gida duk ya ruɗe anata kuka.

Koda suka isa asibiti Dr kansa sanda ya tsorata ganinta ita dai duk abinda sukeyi da ido take kallonsu bata iya ko mgna saide yadda mutane keyi yake bata matuƙar mmki,cikin sauri Dr yafara aikinsa gwaje² yayi sosai kafin yayi mata allurar bacci,office yakira Salkhan yayi masa bayanin dagon suma tayi me tafi da nunfashin mutum saka makon mugun bugawar da zuciyarta tayi ta tsorata ne shine ya haifar mata wannan abun amma bbu komai insha Allah zamuyita mata alluran bacci har tadawo hayyacinta.

Da gudu ya faɗo cikin gidan har matan dasuka zo ta'aziya sanda suka tsorata ganin yaddah yashigo a firgice,Anty Nusaiba ce tamiƙe cikin zafin rai tafara Magana "baka da hankali ne zaka shigo gida haka daga gadi lalle kasamu guri,haki yakeyi sosai ga zufa ya wanke shi kaman anjikasa da ruwa guri yane ma ya zauna yanata hakkinsa,da kyar yayi controlling kansa ya kalla Ammih yace "gawar ta tashi wlh fatalwu wa ta miƙe wlh fatal wace yau nagani da idona,cikin ɓacin rai Anty Nusaiba ta daka masa tsawa tana faɗin ashe mahaukaci ne kai bamu sani ba tashi kabar nan dan kana buƙatar addua naga mutuwar kaman tamafi taɓaka fiye da kowa,duk harga gin da take masa baiko kulata ba dan shi yasan abunda yagani, masu ta'aziya kam sai tausayin sa akayi daga gani sun shaƙu ne kowa sanda ya tausaya masa agun.

Still motan kai gawan Salkhan yashiga zuwa gida daga shi sai boxers da vest kasa shiga yayi saboda mata ne acikin gidan,da kyar ya tura ƙofa kansa a ƙasa ya kutsa zuwa Parlour inda Ammih ke zauna ya tsuguna saide yakasa cewa komai duk matan dake gun da mamaki suka zuba masa ido duk sai yaji bai sake ba,cikin ƙarfin hali yace yana son ganin Ammih da kyar ta iya miƙewa sbd yadda zuciyarta ke ciwon dan yadda Dr yabata mgani bata ma ko tuna dashi ba bare tasha, gefe suka koma sunkuyar da kansa yayi ƙasa,da kallo Ammih tabisa saide bata ce komai ba,ɗagowa yayi ya kalleta yace "Ammih Nanah fa bata rasu ba tafarka tana asibiti Dr yace dogon suma tayi,zaro ido Ammih tayi tana faɗin "ban gane ba kana nufin Nanah na bata rasu, kodai mafarki nakeyi kokuma kaima dai ka tabune, kallonta yayi yace Ammih yanzu haka daga asibiti nake muje kigani da idon ki,wani tsalle tayi ta rungume Salkhan tana faɗin "Alhamdulillah ashe Nanah na bata tafi tabarni ba muje ka kaini na ganta,kafin yayi wani mgna tuni tafita Parlour tana ihu tana faɗin "jama'a Nanah na bata rasu ba wlh tana asibiti,da ido duk suka bita nan mai gadi ya miƙe yana faɗin "kunji ko ba ƙarya nayi ba ai na faɗa muku kikace bani da hankali,kafin kace wani abu garin kano ya gauraye da lbrin gawa ta tashi haka gidan rasuwa tuni ya rikice,masu kukan farin ciki nayi masu murna nayi.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.