Auren iyayya Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Auren_iyayya_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 28 of 33
*Bismillahir rahmanin* *Raheem*
Nanah ji tayi duk bbu daɗi duk yadda Ammih ke convincing ɗinta akan tabari sai ciko wan sojojin nan yaragu taƙi,daga ƙarshe dai Ammih tace ma Salkhan ya rakata badan ransa yaso ba hka Ammih tasa mata hijab suka fice nan suka bar Ammih da mamaki.
Koda suka je sojan dake gadi ƙofar ɗakin hana su shiga yayi,cikin sa'a da Hajja mamah tajiyo sune tafito dan Nanah taƙi barin gun shikuma,sai muzurai yake musu tasu ta sojoji.
"Hayaniyar me nakeji ne hka"? Ganin su Nanah yasata fara'ar dole,nan tace mishi yabar su sushiga.
Cikin girmama wa tagaida Hajja mamah,bbu yabo bbu fallasa Salkhan ma ya gaishe ta yana mata yame jiki,yana gama gaida ta ya juya ya fice a É—akin.
Cikin sanyi jiki take jan ƙafarta ta ƙarasa gun dayake kwance,ya kukkuje a jikinsa kallo ɗaya zaka masa kasan baccin wahala yakeyi.
Koda ta ƙarasa kawai saita fashe da kuka tana faɗin,"ban taɓa kinka ba arayuwa ta kuma ban yanke hukunci dan nasaka a damuwa ba,wlh tsoro irin cin mutun cin da matar ta mun nakeyi tun awaje knan inaga idan nashigo gidan?" "Me kake ganin zai faru ni bazan zama sanadiyar shigan ka damuwa ba wlh nayar da zan Aure ka nashirya ɗaukan duk wani abu akanka,shiru tayi kuka yaci ƙarfin ta har ranta bata ji daɗin yadda tagan sa sam.
Shoulder ɗinta Hajja mamah ta dafa,ɗagowa tayi ta kalla Hajja mamah ta sake fashewa da kuka tana faɗin,"Dan Allah Mamah kiyi hkri wlh banyi hka dan nasa shi cikin wannan halin ba,katse ta Hajja mamah tayi tana faɗin,"ko kaɗan ban zarge ki yarinya sbd tun ranar daya zo mun da lbrin kin kika shiga zuciyata kuma koda nasaki a ido,naga mutunci da kunya a tare dake to ko hkan ya faru ko karya faru,Allah ya kaddara yau sai abun nan yafaru karki saka komai aranki kinji,cikin kuka ta girgi za kai kaman wata ƙaramar yarinya halaman to.
Ta É—an jima agun kafin tace ma Hajja Mamah zata tafi,zata dawo anjima har É—aki Hajja mamah ta rakata,nan suka gaisa da Ammih take mata jejeto tare da faÉ—in zata zo ta duba sa,Anty Nusaiba ba nan ta mata yame jiki tare da faÉ—in insha Allah tare zasu zo da Ammih,sosai Hajja mamah taji daÉ—in yadda Nanah ta nuna kulawa ga Jamal tana saka rai,da insha Allah tasan yanzu É—an ta zai samu nutsuwa da Mata tagari.
Sai da sukayi sallan isha'i tym ɗin driver ɗin Anty Nusaiba yazo suka fita dukan su dan zuwa duba Jamal,koda suka je sun same sa yana Sallah basu tsaya jiran sa ba suka gaida Hajja mamah ta musu rakiya,Nanah kam kujera taja ta zauna dama raka'ar ƙarshe yakeyi har ya idar yayi addua idonta na kansa,juyo wa yayi yana kallonta eye ball to eye ball itama shi take kallo ganin bayida niyan ɗauke idonsa neya sata,hura masa isakar bakinta tana faɗin,"hey tana murmushi kunya ne ya kamasa ƙeyan sa ya sosa yana faɗin,"Ina kince baki sona? Kuma a ƙarshe kinga halin dana shiga kin zata son wasa nake miki ne ko kin zata yauda rarki zanyi,Nanah wlh kinji na rantse bazan fasa faɗa miki ba nayi bin cike sosai akanki Nanah kuma a hka nake sonki,shiru yayi yana kallonta sunkuyar da kai tayi duk saita ji bbu daɗi.
Kallonta yakeyi bbu gaggautawa,kaman daga sama ba tare da ta ɗago kai ba yaji tana faɗin,"am so sorry i didn't mean to hurt you is just that am scared of ur wife,abun da tamun was so painful shiyasa nace na hkra.
Kallon wayi with his surprised face yana faɗin, “Nanah kin zata banfi ƙarfin gidana bane? Nanah niba irin wayannan mazan bane Nanah kiyin saurin yanke hukunci ba tare da kinjira kinga wani mataki zan ɗauka ba,wlh acikin ku ba zan yarda wata ta cutar da wata ba Nanah,kinga halin dana shiga ko da girma na ko kallo ɗaya Zaki mun Nanah kisan niba yaro bane nasan me nakeyi,bazan bar ku kucutar da junanku ba hka nima nake roƙon Allah yabani ikon yi muku adalci tsakanin ku,Nanah duk saita tau saya masa taji duk bbu daɗi ɗago idonta tayi da kyar tace masa.
"Am so sorry na riga naji tsoro ne shiyasa", murmushi tayi tace masa "guest what"? Shima kallonta yakeyi kafaɗa ta ɗaga tana faɗin,"zance ma Ammih i will marry you tana faɗa tasa hannun ta ɗaya ta rufe face dinta, nan yarantar ta ƙarara ya bayyana murmushi yayi aransa yanayi ma Allah godiya, hanunsa yasa yacire hanun data rufe face dashi saide gam ta rufe idonta taƙi buɗewa,sbd kunyar dataji jin bakin sa cikin nata kawai tayi,aiko tuni ta buɗe ido ta zaro su waje tana ƙoƙarin ture sa ganin bayida niyan sakin ta yasa tafara hawaye,da sauri ya saketa yana murmushi girarsa ya ɗaga mata gira yana faɗin,"a special way to say thank you" turo baki tayi ta miƙe zata fice ji tayi ya riƙo Mata cak ta tsaya batayi gaba ba batayi baya ba, takowa yayi yazo har inda take yana faɗin, “ nayi laifi ko?tom am sorry bazan sake ba is because am excited but idan kinji haushi kira rama,ya kawo face dinsa kusa danata yana turo mata lips dinsa yanda yayi ne yasata dariya sosai har sanda kyanta ya ƙara bayyana,hanunta yakama yace "muje in raka ki karki ɓata yarinya" turo baki tayi ta fice hanunta tana faɗin,"ni wlh ba yarinya bace kuma bana so karaka ni zan tafi ni kaɗai saketa yayi yana dariya yace ,"naji muje dai"turo ƙofar Hajja Mamah ne ya sa dukan su suka kalla ƙofar kallo ɗaya zaka musu kasan basu da gsky,"Hira muka ɓige dashi nida mamanki mun sha'afa da masu jinya munata hira","yauwa mamaki tace anzo duba ki maza muje naraka ki" sunkuyar da kai Nanah tayi sum² taka ma hanyan fita,nan Jamal yace shi zai rakata Hajja Mamah ta zauna,batayi musu ba takoma ta zauna suka fita.
Koda suka isa a ƙofa ya tsaya yaƙi shiga, itama bata damu ba ƙin kallansa ma tayi ta shiga abinta,su Anty Fatima ta tarar tashiga gaishe su duk suka ansa cikin fara'a,saide Anty ce tashiga tsokanar tana faɗin,"Ashe gara daba muyi saurin sanar ma da mutane an fasa aure da munji kunya,sbd da hka Ina koma wa zan faɗa ma Sheikh mgnar sa tazama gsky tana ƙare mgnar tana dariya, sunkuyar da kai Nanah tayi batare da ta iya cewa komai ba har su Anty Fatima suka tafi tsoknar ta suke yi,Nanah dai batama iya mgna sbd kunya.
Æan garen Jamal yana komawa ya mayar da Hajja mamah cewa Nanah ta yarda zata Aure,yanda taga É—an nata na murna sosai ta tausaya masa godiya tayima Allah sosai,tabi su da fatan alkhairi da addua ranar itakan ta tasan É—anta na cikin farin ciki hkan yasa ita ma sai taji daÉ—i aranta.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.