Complete Hausa Novels

Auren iyayya Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Auren_iyayya_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 30 of 33

Suna isa bbu ɓata lokaci suka shiga zaɓen kaya,wani yace shiya ke so ta ɗauka wani kuma batama sanin yasa cikin kayan su sunayi suna hira suna wasa da dariya,nan ma pics din suka sakeyi kafin sukaje gun biya card dinsa yabayar yabiya niƙi² aka fitan musu da kayan tana tsaye gefensa aka gama lodawa bayan motan,suna juyawa ya zagayo ya buɗe mota zata shiga kenan kaman daga sama sukaji,“ashe ke mayau dari yace ina alƙawarin Auren wlh ba soja ba ko buratai ne saina yaƙe sa kuma nayi duk yadda zanyi na Aure ki,Nanah mugama watsewar ni dake kice zaki juya mun baya bayan kin ɗanɗa nar dani wannan daɗin kina nufin zan bari ya kubuce mun lalle,wlh sai kinyi dana sanin wulaƙantani,tunda yafara mgna Nanah ke hawaye dga ƙarshe ma shige wa mota tayi ta cigaba da rera kukanta,Jamal ma ganin tashiga ne yasa shima yashiga yaja motar da gudu suka bar gun.

Tunda suka kamo hanya take kuka rarrshin duniya taƙi shiru parking yayi,cikin ɓacin rai yace,"tunda bazakiyi shiru ba bani number sa wayanta ta lalubo taciro num dinsa ta miƙa masa ya ɗauka ya miƙa mata wayan,janyo ta jikinsa yayi yana shafa bayan ta halamun rarashi sun jima a hkan kafin tayi ajiyan zuciya,tayi shiru cikin sanyin murya yace, " karki damu komai yazo ƙarshe bashi mahau kaciba zaiyi hankali,inaso ki kwantar da hankalinki kinji bbu abinda zai faru sai khairan insha Allah kai daga masa alamun to, lips dinta yayi sucking for like 5mins kafin ya saketa suka kama hanya guda.

Kwance yake shame² a 3seater kallo ɗaya zaka masa kasan yana cikin damuwa, cikin sanyi murya tashigo tace masa,"ana sallama dakai waje cigaba wa yayi da karka ɗa ƙafarsa kaman baiji ba,sake nanata masa tayi tsawa ya mata wanda idan da sabo ta saba yamike ya kinkimi jallabiya sa yasa yafice,da ido tabisa yana fita ta zauna agun tafara rera kukanta daya zame mata jiki,dukan cikinta take tana faɗin wannan abu dayaƙi fita yajaza mun bala'i wlh Yaya Maina dole narabu dakai bazan dauwa ma a baƙin cikiba.

Yana fita yaga Hilux din sojoji bbu mgna har yajuya zai gudu ɗaya daga cikin su ya,"kana daga kafa sai gawarka aiko cak ya tsaya suka ƙara so sanda suka zane sa da bulala agun yayi liss kafin suka sa shi cikin mota zuwa Barack ɗinsu.

Ranar wuni yayi yana tsallan kwaÉ—o idan kuma ya tsaya zana,kwanan sa uku yana dakuwa duk yafice hayyacinsa ya jeme.

Ɓangaren matar sa kuma a titi taji lbrin abunda yafaru dashi,mai makon taji haushi sai murna takeyi yau kwananta uku tana abun da takeso bbu mai Mata tsawa bare takura.

Cikin wani ɗaki yake aka ciro sa aiko ganin Jamal yasa tuni ya zube a ƙasa yana faɗin,"ranka shi daɗe na tuba wlh Allah natuba yafeni dan Allah da darajar iyayen ka kasake ni hka,tunda yafara mgna Jamal kallonsa yakeyi sanda ya gama kafin yace , "baka sansu ba daka sansu daba bazaka ci zarafin mutane ba, ciro wayan sa yayi ya nuna masa hoton Nanah "yace kasan wannan? "Wlh ranka shidaɗe ban santa ba banma taɓa ganin ta, murmushi Jamal yayi yana faɗin,"ka kalla fa da kyau anya baka santa ba ya ƙare mgnar cikin zolaya, "ranka shidaɗe nifa ban ma taba ganinta ba a ina ma zan santa,sam ko mai kama da ita ban taɓa gani ba bare nasanta.

Murmushi Jamal yayi yace masa,"riƙe kunenka a gigice ya riƙo su,"Daga yau naraba ka da Nanah kasa aranka baka ma taba ganinta ba bare kasanta,bbu kai bbu ita Idan kuma kaƙi ji to idan kakuma shiga nan gawarka ce zata fita kajini!!

"Wlh najika garinma saina barshi"

"Wannan ya rage naka kuma inaso ka goge duk wani abu dakasan natane awayan ka kaji ko bakaji ba,kai barshi ma É—aya daga cikin sojojin ya haÉ—a su tare suka je aka suka taho da wayar koda sukaje matar ganin sa datayi taga yadda yakoma sanda ta tausaya masa duk magiyan datama sojojin na subarsa abanza ne kuma still bai fasa hararta ba ganin hkane yasata komawa gefe suka fice, Koda suka isa agun aka fomating wayan aka basa abunsa aka sallame sa.

Da kyar yake tafiya dan yaji jiki sosai ya daku napep ya tara ya roƙa ya kaisa gida yashiga ya ɗakko kuɗi ya basa, koda yashiga gida duk ta rude tana tambayan sa banza yayi da ita yana faɗin,"bansan muna furci da yawan tambayan ina ruwanki jeki ɗaura mun ruwan wanka ki kawo mun abinci,sum² ta miƙe tana kunshe dariya tafice. Daga ƙarshe dai ita ta gasa ta haɗa harda mugunta tayi masa ranar ko bacci baiyi ba sbd ciwon jiki yadda yaga dare hka yaga rana.

Akwana a tashi bbu wuya ana jibi É—aurin Aure komai ya kamalla na kayan Aure,akwati 8 yamata yayi ma Nabilah biyar saide ko daya kawo mata nata agun tabar masa tace bata so,shima agun ya bari yace yafita hakkinta.

Akwati sunji kaya Masha Allah ankshe kuÉ—i sosai akan akwatinan ,side din da bbu kowa ne yasha gyara yaso rabasu Hajja mamah tace ya haÉ—a hka ya haÉ—asu badan yaso ba.

Ɓangaren Ammih kam Nanah tasha gyara kaman bbu anjima,saide tunda biki ya matso ta sa ƴarta a arai ko abincin arziƙi bata ci duk ta rame tayi fayau,daga ta kalla Noor sai hawaye,Salkhan kam shima duk abun duniya ya damesa ganin zai shiga damuwa kawai sai yafara azumi yana kaima Allah kukan sa kuma Alhamdulillah sosai yaji sauƙin abun.

Yau yaka juma'ah bayan an idar da Sallah ne misallin, ƙarfe 2:15 aka ɗaura Auren Hadiza da mijin ta Muhammad Jamal,ɗaurin auren da manyan mutane da dama suka hallara kuma suka shaida, mijin Anty Fatima shiya bada Auren Nanah su Salkhan ansha shadda milk colour dataji zubi,ɓangaren Anga ba'a mgna ansha shadda Skye blue sosai yayi kyau bakin nan yaƙi rufuwa,sai gaisawa yakeyi da jama'a.

Nabilah kam tunda ta tabbatar yau za'a É—aura Auren,tun safe take kuka har kanta na sarawa shikam tare da yaran sa da sukayi ankon shadda yafice.

Ɓangaren Nanah kam tunda Salkhan ya zo musu da lbrin an ɗaura Aure,duk jikinta yayi sanyi tunda ta zauna gu ɗaya takasa mgna,cikin wani tsadden lace take maroon colour tayi kyau sosai,maimuna ce data zo bikin mussan take ta faman zolayan ta saide sam takasa sukuni,Noor ce tashi go cikin doguwar rigar lace anko sukayi da Nanah tayi kyau sosai da juice a hanunta tana miƙama Nanah,ɗago tayi tana kallon ta cikin sanyin murya tace,"ban san irin son danake miki ba ƴata amma insha Allah zanzo na ɗauke ki koda ga bayane,ita dai Noor bata san me take faɗi ba kallon mamanta kawai take tana rikin saita sha juice din da take bata,kurba tayi tana faɗin,"uwar yan daru nasha dariya tayi kuma tafara rikin ta sauke ta bbu musu tamata peck a kumatu ta sauke ta harta fita a ɗakin ita take kallo,sai kuma ta ɓige da tunani maimuna ce ta clapping hanunan ta tana faɗin,"Wai meyasa Nanah kike yawan tunani baki tunanin a age ɗinki zai affecting ɗin,kisani fa komai ya faru da bawa ƙaddara sa ce babe am advising you ki manta komai kici gaba da rayuwarki, murmushi ta mai kyau tayi tace ma maimuna,"babe wlh bazaki gane bane ina tunanin rabuwa da wannan princess ɗin tawane ta ƙare mgnar cikin damuwa.
Kusa da ita maimuna ta dawo hanunta ta riƙe cikin nata tace,"karki damu idan dai Noor tana da gata kuma am sure mijinki bazai hanaki riƙe Noor ba,saide problem din gun babanta zai taso kin san ba yarda zaiyi ya rabu da ƴar saba,uwa uba yana raye ƴarsa tayi agola i don't think zai yarda but ki gwada kiga.
"Ajiyan zuciya Nanah tayi tace,"kuma mgnar ki hkane nasan halin Yaya Salkhan sai wani ikon Allah zai bari,dan duk son danake ma Noor gani nake yafini tana kaiwa nan ta share hawayen ta,"kinga problem dina dake knan yawan kuka wlh bari nabar mgnan hka tunda kin fara maimuna ta ƙare mganan cikin damuwa,ta mike ta miƙo mata tissue paper tana faɗin ki goge face dinki na miki make-up din kinga tym is going,yanzu zakiji ana a fito mutafi,jikinta bbu ƙwari ta miƙe ta nufi hanyar toilet.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.