Complete Hausa Novels

Auren iyayya Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Auren_iyayya_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 20 of 33

Kallon Noor kawai takeyi sbd tausayin yarta takeji yanzu, ringing din wayan tane ya dawo da ita daga tunanin datakeyi,hannunta tasa ta ɗakko ganin sunnan Jamal yasata tayi picking,. "Hlo my heart beat shine baza ki kira kiji kona isa gida lfy ba anya kin damu dani kaman yadda nadamu dake kuwa? Ya ƙare mgnan cikin zolaya,ajiyan zuciya ta sauke tare da faɗin "Afuwan yanzu nake son aika maka massage ma naga saƙo thank you,but saurin katse ta yayi yana faɗin "but me basuyi kyauba ko sorry kisan zabin namiji sai a slow,dariya ce ta kwace mata tana faɗin "aibaka ma ji mezan ce ba kuma ka tsateni ƙoƙarin cire Noor tayi zata ajiye ta,aiko kuka ta fashe dashi ɗan tsaki tayi ta sake juya ta kafin tace
"Hlo kanaji? "Yes inajin ki madam babyn mu ke kuka ko? "ajida ita we will talk later bye love you bai ko saurare ta ya kashe wayan,ji tayi zuciyarta ta buga a ina yasan kuma inada baby nidai ban faÉ—a masa ba duk gabaki É—aya kuma sai taji duk tunaninta ya canza.

"Tunani tashigayi kala² daga ƙarshe tace "Allah gatana ajiye Noor tayi ta shiga toilet saide kafin tafito Noor kam tama fara yaga paper bag din dake gun,da sauri ta ƙaraso tana faɗin "Wlh daɗina dake wani zubin ɓarna kaɓa tayi tafara ciro wani ɗan box ƙara mu anyi rapping dinsa nan ta shiga buɗewa,. "Wow"! Abinda tace knan ganin wani haɗeɗɗen wrist Watch sai shining yake yi duk jikinsa stones ne, "gsky agogon nan yayi kyau Masha Allah" abunda tace knan wayan ta ɗakko ta tura massage,

" _Thank you for the gift yayi kyau_ __sosai_ _thank you"_ ta aika masa.

Murmushi yayi bayan ya gama karanta massage din yana faÉ—in "da kaÉ—an da kaÉ—an dai"

Yau kwana uku Kenan hankalinta kwance bata da wata damuwa, ɓangaren Jamal kam suna waya bbu laifi,Maina kuma tunda ga ranar bai sake ko nemanta ba hankali ta kwance, yau takama Friday kuma yau za'a yaye Noor tunda ta tashi tausayin yarta takeyi,daga ta kalleta saitaji hawaye har Ammih sanda ta kula da hkan tin safe bata shaba gashi har kusan la'asar sai cika dasukayi, Noor kam daga tayi rikici sai Ammih tabata Kunu ko tea ko tuwo, duk da hkan bata fasa rikici ba kusan 5,pm suna zaune Parlour Salkhan yashigo da leda huɗu niƙi ñiƙi a hannun sa,Nanah ce ta ƙarbe sa tana gaida sa bbu yabo bbu fallasa ya ansata,gun Ammih suka ƙarasa da kayan suka ajiye ya gaida ta,Noor ke kuka tana miƙewa Nanah hannu saide Salkhan yasa hannu ya karɓe ta suka fita.

Suna shiga mota ganin titi tayi shiru yawo yayi da ita sosai harda su kayan sawa ya sayo mata su turare,su takalma sosai yayi mata siyayya kafin su dawo tayi bacci.

Ga magrib Ammih ya tarar zata haura masa ya miƙa mata Noor yafice sallah, Sai wajen 8 kafin ya shigo suna zaune a dining table da kayan da bai samu ya shigo dasu ba ɗazu.

"Salkhan lfyn ka kuwa?, Ɗazu ka siyo su uban kayan tea su custard da sauran su yanzu ma kasake zuwa kayi wani siyayyan wannan yazama ɓarna me yarinyar nan tarasa? "Kuma ni da kunun garga jiya zan yayeta su friso din da ka sayo saide kaida uwarta kushanye.

Murmushi kawai yayi ya wuce da kayan sama É—akin Nanah ya ajiye kayan ya dawo dining yayi serving kansa,saide kaman daga sama yaji Nanah na faÉ—in. " Mun gode Yaya Salkhan,da kallon mmki yabita saide baice komai ba yaciga ba da cin abinsa sa, Ammih na lura da Nanah da baifi spoon uku ci abinci ba sai jujjuya wa kawai takeyi.

"Waime yake damun ki ne kisa abinci a gaba kinata ja gwalgwala wa kinsa cinyewa, yamu tsa face tayi tana faɗin "Ammih wlh zazzaɓi nakeji banajin daɗine.

"Ai wannan dolene dama daurewa zakiyi kici kisha mgnani,. "Sorry Nanah kozamu je asibiti ne É—ago ido tayi suka kalli juna da sauri ta sauke nata tana faÉ—in "aa zan sha magani yanzu thank you". "Ok tom akwai mgnaninne konaje na sayo?

"Akwai yanzu zan sha"tana faÉ—in hka ta mike zuwa sama duk kuma sai yaji bbu daÉ—i shima hka yakai nasa abincin kitchen bai gama ciba,tebe baki Ammih tayi taci nata abincin kafin ta haura sama.

"Wanka tayi tasha magani ta kashe wayanta ta kwanta dan yau Noor gun Ammih zata kwana,saide kaman wasa har wajen ƙarfe 2:am na dare batayi ba kuma tanajin kukan Noor daga ɗakin Ammih,sai wajen 3:am Ammih tashigo ɗakin Nanah yi tayi kaman tana bacci sanda Ammih ta tashe ta,ta miƙe tana sosai idonta kallon ta kawai Ammih tayi tana murmushi,. "Kiji ja'irar yarinyar nan ashe ta iya kiran sunanki wai Nanah tana nuna mun ƙofa,. "Shine nace bari nakawo ta taci uwar da zata ci,hanu Nanah tasa ta karɓa Noor atare sukayi ajiyan zuciya kwanciya tayi jikin Nanah kuma saitayi shiru,fara rikici tayi tana ɗaga rigar Nanah tana kuka sosai,Ammih nazaune gefe tana kallonsu Nanah duk ta rikice tama rasa meza tayi,kawai saita fara hawaye miƙewa tayi ta ɗauki zani tasata a baya tafara kewaye ɗakin,sun ɗan jima ahaka kafin bacci sai tym din dukan su suka samu suka kwanta.

Washe gari da asuba Salkhan yashigo duba su duk suna bacci,haka ya koma saida yagama shirin fita office ya shigo Ammih ce kaÉ—ai a Parlour ya gaishe ta yana mata yasu ka kwana, "Kasan halin mutuniyar dukan mu bbu wanda yayi bacci saida uku na dare ya wuce suna sama.

Haurawa yayi yafara knocking har zai juya yaji tace. "Come in" a hankali yatura ƙofar yashiga atampace doguwar riga a jikinta tayi kyau sosai saide kallo ɗaya zaka mata kasan batajin daɗi,. "Ina kwana Yayah Salkhan? "Lfy klau Alhamdulillah ya jikinki ya kuka kwana?
"Rau rau tayi da ido kaman zatayi kuka tace "nikam zazzaɓi na damuna Noor dinma naji jikinta da zafi sosai, "subhanallahi takawa yayi har inda Noor ke kwance tana bacci yasa hanunsa a wuyanta yaji zafin jikinta sun gumarta yayi yana faɗin, "Saka hijab dinki nakaiku asibiti.

"Bbu musu ta sako hijab din dan gsky tanajin zazzaɓi sosai koda suka cewa Ammih zasu asibiti cewa tayi sai sun dawo.

Suna zuwa asibiti Dr yabasu mgnani dukan su biyu,tunda suka shigo mota Noor ke kuka Nanah tayi rarrashin harta gaji ji tayi idonta sun cicciko,guri yanema yayi parking yana faɗin kawota ko zatayi shiru miƙa masa Noor tayi ya karɓe ta yafita a motan,yashiga supermarket din dake gun parked din sweet ya saya mata,tun kafin su fito ya buɗe ya bata taɗan yi shiru saide ga mamakin sa bbu Nanah bbu dalilinta fara kalle kalle yayi can ya hangota Maina ya riƙe hanunta tana ƙoƙarin kwace wa ganinsa datayi ne yasata ihu tana faɗin "Yayah Salkhan kate nakeni da sauri ya ƙaraso gun ya ajiye Noor yakaima Maina naushi sosai suka soma dakuwa,Nanah datara sa abinyi kawai saita fashe da kuka mai cin zuciya bata san tym ɗin data shiga tsakiya takaima Maina Mari har guda biyu ba tana faɗin, "Wai so kake kashe nine duk cikin kuncin daka sani baka ganine kanka kawai kasani, why!!why!! Mainah na roƙe ka pls stay away from my life i hate you, Salkhan kam Noor dake kuka agefe yasa hanu ya ɗauka yaja hannun Nanah suka soma barin gun,saide kaman daga sama sukaji yana faɗin,. "Wlh Nanah saikin aureni koda auren ƙiyayya ne sai mun kasance mata da miji ni dake wannan zumar dana ɗan ɗana sai nakawo ta gidan nacigaba da lasarta aduk sanda naso!!!

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.