Auren iyayya Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Auren_iyayya_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 26 of 33
Zaune take hankalin ta kwace ice-cream ne a hannunta tana kallon wani Nigerian film,tym to tym take shan ice-cream din harya fara melting,bbu zato bbu tsamma ni taji an karɓa ice-cream din dake hanunta anyi jifa dashi cikin tsiwa ta ɗago idonta tana kallon yadda ransa yake a ɓace tayi ƙasa da kai, "meya haɗa ki da Nanah?!!! Tsawan daya mata sanda ta razana shiru tayi bata ce komaiba,sake daka mata tsawa yayi yana tambayan ta still shiru tayi masa sanda taga yafara cire belt kafin ta miƙe cikin ƙarfin hali da tsiwa tana faɗin, "ce maka akayi nayi mata wani abun?tsaya niko kalarta ma nasa nine lalle inada aiki tun kafin ta shigo ashe sun gama dakai,lalle nida wani abu waishi bita zai² .
Kafin ta ankara tuni ya wanke ta damari masu zafi guda biyu,har sanda ta zauna ga fitsari data sake jin azaban marin dayayi mata,kuka ta fashe dashi tana faɗin, "lalle ni ka mara akan wannan karuwar mazina ciya wacce da aurenta take zina har zaka iya ɗaukan hanu akanta ka mareni,lalle biri yayi kama da mutum kace kaima kashi ga sahun kwarta yen nata kome kayi dai² kafin ta ƙarasa yakuma kai mata wasu Marin zafafa biyu,ga ba ɗaya daina gani tayi sai duhu bbu abinda take gani saiji tayi yana faɗin, "kije gida na sake ki saki ɗaya nagaji da baƙa ƙen halinki wlh sbd damuwa irin taki zan zan ƙara aure ko zan dace,kuma karuwa dakike faɗa natiga ki sanin wannan hka nagani kuma nake son kayana sbd hka nabaki 1hour ki haɗa jayanki kiyi gaba.
Baiko saurare ta ba yayi fice wansa cikin ɓacin rai.
Æangaren Nabila kam kuka sosai tayi me tsuma zuciya,wai har ita za'a kora akan wata banza karuwa tare da Habiba suka haÉ—a kayan su dan dama agunta take haka ta tattara kan Æ´aÆ´an ta suka fice daga gidan.
Yana fita gidan mahaifiyar sa ya wuce,bai ɓoye mata tunda kiran da Nanah ta masa har hukuncin da yayenke ma Nabilah,sosai hankalin hajja mamah ya tashi jin abunda ya faru cewa tayi yakai asibitin bbu musu suka kama hanya,Ammih da Anty Nusaiba suka tarar nan Hajja mamah tayita ba Ammih baki,kafin kace kwabo asibiti yacika duk ƙannan mahaifin Nanah sun cika asibitin, sai magrib kafin suka watse sai tym ɗin Salkhan yazo ganin halin da Nanah ke ciki sosai yatada masa da hankali kasa zaune da tsaye yayi, Jamal ne yashigo da kayan tea da abinci dasu bargo tare da te makon wasu sojoji dake biye dashi,sake gaida Ammih yasake bata baki nan suka gaisa da Salkhan da sai ƙanshi yakeyi,ya ɗan jima kafin ya cire bunch din one thousand ya ajiye Ammih,yana faɗin ko za'a nemi wani abu Ammih badan taso ba ta ƙin karɓa tayi tace yayi hidima dayawa amma daya tashi sai ya jiye gefenta ya fice.
Koda yakoma gida bbu kowa baiyi mmki ba dan yasan zata rina wanka yayi,ya sake figan motan sa zuwa gidan su Nabilah,ransa a mugun ɓace yashiga gdn suka gaisa da iyayenta koda ta hangi motansa ya shigo kallon Habiba tayi tana faɗin, "aina gaya miki bazaiyi iya ba kuma wlh bazan koma ba saiya sha wahala ni zai wulaƙan ta akan wata karuwa.
Cikin mutunta juna Jamal bai ɓoye musu komai ba duk abunda yasani ya mayar musu,kuma yaƙara da faɗin wlh abunda yasa bai faɗa mata ba gudun irin hkane kuma sai gashi abunda yake gudun ya faru,sosai ran mahaifin ya ɓaci kira yashi ƙwalla mata a gigice tafito tare da Junior ƙaramin ɗan su daya ƙi bacci wai shi yana jiran babansa,gu tanema gefe ta zauna ta sunkuyar dakai dan tasan babanta yana da zafi, "abunda kikayi yanzu kina ganin kin kyauta knan kiyima kanki adalci,mahaifiyar ki ita kaɗai ce aguna dazaki ce ke kinada yancin da zaki kalla namiji lafiyayye kaman Muhammadu kice bazai ƙara aure ba,Allah ya hallataasa ke kice bazaiyi ba tom yanzu dawa kike yaƙi dashi ko da Allah daya halalta masa,cikin zafin ran bataso mahaifinta ya goyi bayan Jamal ba tace, "Abbah fa karuwa ce wacce zai aura wlh duk bin ciken danayi hka nake ji ance abinda yaraba ta da mijinta na fari kuma ɗan uwanta ne tsabar karuwan cine.
"Ubanki nace Nabila auren karuwan haramun ne kuma dakike faɗin hkan kina da shaida akan hkan kin taɓa kama ta da idonki kin gani,da yawan mutane fa harshen su shi zaikai su wuta baki san ranar gobe kiyama zaki tashi sheda bane,na kwaɓe ki dajin Kalman karuwar nan kowa datasa ƙaddarar kika sani akansa ta shiryu baki san akan hakan sai yayi sanadiyar shigan sa aljannah ba,ki kiyaye wlh nasake jin abu makaman cin hka wlh ranki sai yayi mummu nan ɓaci,Zainab kodai kekika ɗaure mata gindi ne take iskancin nan? "Haba Alhaji wlh ko kaɗan kana kallon yadda kulun cikin nasiha nake da Nabila ni duk jikina ne wlh yayi sanyi narama rasa me zance ne.
"Dan Allah dan Annabi Muhammad S. A.W Alh Jamal kayi hkri mun san kanayi ka kuma kaci gaba dayi nan suka basa hkri,har yace ya maida ta koda kuwa kalmar karuwa datake kiran Nanah dashi ba ƙaramin zafi yayi masa ya daiyi hkrine kawai sbd albarkacin iyayenta.
Cikin faÉ—a mahaifinta yace ta É—ako gyale su tafi amma ga mamakin su sai cewa yayi dare yayi gobe ta dawo ta É—auki Junior suka tafi,koda takoma É—aki tayi kuka kaman ranta zai fita kafin tayi bacci.
Washe gari da sassfe ya shirya zuwa asibiti nan Hajja mamah takira sa tace yazo ya tafi musu da abinci,hakan ko akayi lafiyyan chips da doya da miyan ƙwai tayi musu da tea dayaji kayan ƙamshi, yakama hanyan asibiti ana yabar junior ma.
Koda ya isa asibitin ancire ma Nanah oxygen din,Ammih tace masa ta farka da asuba har sun ɗanyi hira takoma,yaji daɗin hkan sosai nan Ammih tayi serving dinsa duk da yace mata ya ƙoshi amma koda ta zuba tabasa tsab yacinye kaɗan ya rage,bai bar asibitin ba sai wajen azzahar su Anty Nusaiba da dasu Anty Fatima duk sun soma cika shiyasa yayi musu sallama ya tafi,gun Dr yanufa suka gaisa nan yake tambayar sa ya jikin nata yace insha Allah bbu komai zata samu lfy,da haka ya wuce office ɗinsa.
Yau kwanan Nanah huɗu Alhamdulillah jiki da sauƙi harta na ɗan zama kuma takanyi hira da mutane,Dr ne ma yake cewa bayan san tadinga yawan mgna,Nanah wannan kwanciyan nata a asibiti taga gata gun dangin maifinta, dangin mahaifiyarta da gun su Hajja mamah,ɓan garen Jamal kam ransa aɓace yake kullun yazo da mutane yana so ya keɓe da ita sam bbu hali.
Æangaren Nabila koda ta dawo kayan ta duk tayi parking daga É—akin sa takoma nata É—akin bbu wani abu dayake shiga tsakanin su,yasan shi mabuÆ™a cine sosai saide sanin halin matarsa yasa dole yakoma kansa hkri tare da shan magani dan azzauna lfy shikuma ba ma'aboci bin mata bane sam cikin ikon Allah bayayi.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.