Complete Hausa Novels

Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Yiwa_Kai_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 1 of 34

[3/8, 12:45 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI*

*BRIGHT PENS*
(FREE BATCH)

MIKIYA WRITERS ASSOCIATION

1

Iskar hadarin dake kaɗawa ba ta saka na yi yunƙurin tashi don kwashe abubuwan dake tsakar gidana ba, saboda gudun kar ruwa ya sauko. Ina nan zaune kamar an dasa bishiya ban ko motsa ba, ina ta kuncewa da saƙa yadda za a yi ni ma na zamo ɗaya daga cikin fitattun mata na wani group ɗin WhatsApp da nake ciki. Ganin wankin hula yana ƙoƙarin kai ni dare ya sa na sauke wani wahalallen numfashi tare da miƙewa na fara kintse-kintse. Ina yi ina tunanin da wani hamshaƙin mai kuɗin nake aure ko gida mai tsakar gida ba zan yi rayuwa a cikinsa ba, bare na yi fargabar kar ruwa ya taɓa mini abubuwan amfani.
Bayan na gama na shiga ƙaramin falona na zauna na kishingiɗa akan kujerar zaman mutum biyu. Kallon ko ina nake yi a ɗakin ina bitar kayan cikinsa kamar ba nawa da na saba gani kullum ba. Kujeru ne kawai saiti da labulaye, sai ƙaramar TV ta ƙasa. Ban san lokacin da na ja wani dogon tsaki ba lokacin da hoton wata Hajiya da ta turo ɗazu ya faɗo mini a rai, wanda aka ɗauke ta a gaban tamtsamemiyar TV'n bango dake cikin wani rantsatstsen falo. A karo na barkatai cikina ya murɗa saboda yunwar dake ƙwaƙular hanjina, tsabar karanta wasiƙar jakin da na tsaya ina yi ko abincin rana ban ci ba, ga shi Magriba ta kawo kai. Ba don son raina ba sai don ban da zaɓi na miƙe na zubo shinkafa da waken da na girka na zuba mata mai ishashshe, ga salad da tumatir a gefe da yajina da ya ji magi. Cikin takaici na fara cakuɗa ta ina keɓe fuska kamar na ga kashi.
"Ko ɗan kifi babu akai balle ƙwai." Na faɗa a fili ina tuno haɗaɗɗun girkunan da matan group ɗin nan suke turowa, wanda yake wadatuwa da lafiyayyen nama. A maimakon kidahumar ƙwaƙwalwata ta tuno mini waɗanda ba su da shi, waɗanda da za su gan ni za su ce dama ni ce su, waɗanda kullum suke kwana su tashi da fargabar abin da za su ci.
Haka na tuttura abincin na tashi na je na kwanko hannuna, ina ƙoƙarin komawa ɗaki yarana maza guda biyu Sultan da Safyan suka shigo da gudu bakinsu ɗauke da sallama. Bin su na yi da kallo ganin yadda uniform ɗinsu ya yi datti, komai dare ko gobe da safe sai na wanke musu kafin su kuma sakawa. Hasasowa na yi da matar mai kuɗi ce ni kamar matan cikin group ɗin nan da sai dai masu wanki su wanke musu. Cikin rige-rige suka zo suka rungume ni kowa na ƙoƙarin karanta mini abin da aka koya musu a islamiyya.
Zare su na yi daga jikina, cikin tsawa da zare ido na ce. "Mene haka? Ba ku da hankali ne?" Bi na kawai suka yi da ido don hakan baƙon al'amari ne a gare su. Ni kuwa gare ni haushin mahaifinsu da nake ji ne ya shafe su, na baƙincikin bai zo a mai kuɗi ba.
Ina shiga ɗaki suka biyo ni jikinsu duk a sanyaye. Kamar yadda mahaifinsu ya horar da su idan sun yi mini laifi su ba ni haƙuri haka Sultan ya dube ni ya ce. "Mami mun yi miki laifi ne? Ko gudun da kika hana mu muka yi ne ya ɓata miki rai?" Kallon shi na yi kafin na yi magana Safyan ya riga ni da faɗin. "Ni ban yi ba Mami, Yaya ne ko?" Numfashi na sauke tare da janyo su jikina na ce. "Kuna yi wa Abba addu'ar Allah ya ba shi kuɗi mu koma ƙaton gida kuwa?" Bi na da ido kawai Sultan ya yi, Safyan ne ya ce. "Irin gidansu Zuhura?" Da sauri na ce. "Eh, ko ba kwa so?" Sufyan ya ce. "Muna so." Shafa kansa na yi ina murmushi na ce. "Yawwa yaron kirki, mu ma mu zama ƴan gayu yanda mutane za su dinga sha'awar mu, mu dinga cin abinci kullum da nama da kaji." Cikin tsallen murna ya ce. "Eh Mami." A hankali Sultan ya ce. "Mami amma da ba kya cewa mu yi wannan addu'ar, haka kawai kike cewa mu ce Allah ya buɗa wa Abba." Na ce. "To yanzu ku fara, don in ma bai yi kuɗin ba barin shi za mu yi mu je mu samu wanda zai kai mu ƙaton gidan, don ba zan ci gaba da rayuwa a wannan akurkin ba." Bi na kawai suka yi da kallo don ba su gane abin da nake nufi ba.
Bayan na cire musu uniform na zuba musu abinci suka fara ci na fita na É—auro alwala na dawo parlour'n don tayar da Sallah. Ina tsaki na kunna torchlight Æ´ar madaidaiciya wadda ake yi mata chaji saboda babu Nepa. Cikin raina ina tunano yadda matan cikin group É—in nan suke labarin kodayaushe suna samun Nepa a unguwanninsu, saboda ta masu hannu da shuni ce, idan ma an É—auke za a tayar da inji ko kuma a kunna solar.
Idar da Sallahta ya yi daidai da shigowar kira cikin wayata. Sultan ne ya miƙo mini na karɓa na duba mai kiran, ɗaya daga cikin members ɗin group ɗinmu ce ta kira ni, wadda muka fi mutunci da ita saboda sunanmu ɗaya. Ɗagawa na yi tare da yin sallama. Ba ta amsa ba saboda maganar da take yi, daga yadda na ji tana bayar da umarnin a kwashe kajin da mijinta ya zo da su a saka a fridge na san da mai aikinta take. Wani yawu na haɗiye tare da tambayar kaina yaushe ni ma zan gan ni a wannan level ɗin?
"Namesake." Na ji muryar Maman Nasma ta faÉ—a.
Cikin fara'a kamar tana gabana na ce. "Na'am, kin gama maganar ne?" Ta ce. "Eh, ya gida? Ya sa Sultan da Dad ɗinsu?" Na ce. "Duk suna lafiya, ya su Nasma da Abul?" Ta ce. "Alhamdulillah, yanzu ma suka hau sama gurin Dadinsu, ya dawo sun tafi karɓar chocolate." Na ce. "Ayya." Kawai. Ta ce. "Ban gan ki online ba ne, na ga kuma an ci gaba da gabatar da kai a group kowa yana turo pic ɗinsa da na yara, shi ne na ce bari na taɓo ki na ce ki zo ki ba mu naki, na san yadda muryar nan taki take da zaƙi zankaɗeɗiyar mace za mu gani." Yaƙe na yi na ce. "Toh shikenan, bari na hau yanzu na tura, su Safyan ne suka dawo daga islamiyya na tsaya sallamar su, da na gama na yi Sallah, shi ya sa ban hau ba." Daga haka muka yi sallama na katse wayar. Shiru na yi ina jujjuya ƴar akwalar wayata a hannuna, wadda kuɗinta ko dubu ashirin ba zai yi ba. Uzurin da na ba wa Maman Nasma ba shi ya hana ni hawa online ba, chaji ne ishashshe ban da shi, kuma ba tabbas ɗin kawo Nepa, ga fitilarmu idan chaji ya ƙare sai dai na koma haskawa da ta wayata. Dogon tsaki na ja cikin takaici na kunna data, direct WhatsApp na shiga cikin group ɗin *Zumuncinmu* na fara kallon hotunan da aka tutturo, hannuna har rawa yake gurin bubbuɗewa. Zuƙa-zuƙan mata kawai nake gani a haɗaɗɗun background, na wannan yana wane na wannan. Na ga yadda ake ta wow wow tare comments. Fita na yi na shiga gallery na fara duba nawa hotunan da na yarana wanda duk aka yi su da wayar hannuna, sai na gan mu wasu dususu kamar almajirai. Jinjina kai na yi na ce. "Taɓɗijan! Yanzu ta yaya zan tura wannan hotunan? Ai ko karen hauka ne ya cize ni ba zan soma ba." Ficewa na yi na koma WhatsApp na shiga group ɗin, tagging ɗina na ga an yiyyi akan na tura nawa, don sun gan ni online. Cikin tsinkewar zuci da sanyin gwiwa na ce zan tura musu yanzu, bayan na bibbi pictures ɗin da aka turo da. 'Masha Allah.'
Direct ta group ɗin na shiga gallery na fara bin pics ɗin cikin wayata ɗaya bayan ɗaya, akan na wata ƙawata da muka yi secondary school tare da take auren mai kuɗi na tsayar da idona. Tana sanye cikin abaya mai kyau a gaban ka'aba, a ƙasa mai tsarki aka yi mata hoton, last zuwan da suka yi Umrah da mai gidanta ne ta turo mini hoton. A take zuciyata ta ba ni umarnin na tura musu shi kawai na ce ni ce, ba tare da nazari ko tsoron abin da zai je ya dawo ba na danna shi ya cika screen ɗin wayar.
"To ni ma ga ni, ina yi wa kowa fatan Alkhairi." Na rubuta caption da haka tare da turawa.......✍️

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.