Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Yiwa_Kai_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 11 of 34
A É“angaren Maman Nasmah kuwa murmushi ta yi ganin cikin sauÆ™i ta fara samun nasara, za ta Æ™ara jan Hafsah a jikinta ta nuna mata ita mai Æ™aunar ta ce tsakani da Allah, tare da yi mata tarin alkhairi wanda zai saka ta Æ™ara sakin jiki da ita. A hankali a hankali tai ta bugar cikinta tana faÉ—a mata abubuwan da Anas yake so da wanda ba ya so, ta tunzura ta, ta yi masa wanda ba ya so ta hana ta yin wanda yake so. Tunda a iya wayar suka yi yau ta lura Æ™aramar Æ™waÆ™walwa ce da ita, ban da haka ta yaya don ta ce mata ta gan ta a yagule a wahalce za ta yarda? Ai ko makaho ya shafa su ita da Æ´aÆ´anta zai gane babu wahala a tattare da su, don babu yadda za a yi a ga Hafsah a ce a gidanta take rayuwa. Ana ganin ta an ga mai rayuwa cikin rufin asiri, kuma babu inda za ta shiga a raina ta, don daga gani mijinta yana da kula, ba sa tare da yunwa ko rashi na daidai Æ™arfinsu. Amma ita saboda kidahuma ce ba ta fuskanci hakan ba, don haka za ta yi amfani da son kuÉ—in da dogon burinta ta cimma nata burin........âœï¸
*Zeey Kumurya*âœï¸
[3/8, 1:38 PM] BahaushiyaðŸ‘: *YI WA KAI*
*BRIGHT PENS*
(FREE BATCH)
9.
Washegari na tashi cikin tsananin farinciki mara misaltuwa, ni kaɗai na dinga sakin murmushi ina imagining rawa da murnar da zan yi idan saƙon da Maman Nasmah ta ce za ta kawo mini ya ƙaraso. Ga ni nake kamar a mafarki, idan na tuna wai har da sarƙar gold za ta haɗo mun, sarƙa fa? Ba ma ɗan'kunne ko zobe ba. Gaskiya watan arziƙina ne ya tsaya. Na dinga kallon kaina ina hasaso ni sanye da ɗanƙareriyar sarƙa tana zuba walwali.
Ƙarfe bakwai na safe na ga ta mun text na address ɗin gidan mai gyaran jikin, ta ce na je ƙarfe tara tana jira na. Cikin zumuɗi na koma parlour inda Anas yake shirya su Sultan na zauna a kan kujera, fuskata ba yabo ba fallasa na ce. "Abban Sultan zan fara zuwa gyaran jiki yau, na ga fatata duk ta yanƙwane." Kallo na ya yi cikin mamaki sannan ya ce wa Sultan. "Ɗauki abincin naku ku je ɗakinku ku ci." Suka amsa tare ɗauka suka fice suna satar kallo na. Anas ya maido da hankalinsa gare ni tare da faɗin. "Ina jin ki, ban gane me kike nufi ba?" Kaina tsaye na ce. "Cewa na yi zan je gyaran jiki anjima, za a yi mini na sati ɗaya." Cikin rashin fahimta ya ce. "Wai wanne irin gyaran jiki? Da ma kina zuwa ne ban sani ba? Har yanzu ban fahimce ki ba Hafsah?" Cikin hasala na ce. "Da Hausa fa nake yi maka maganar nan, gyaran jiki dai wanda ake yi wa mata su yi kyau fatarsu tai ta sheƙi da fitar da ƙamshi, da kake tambaya kuma da ina yi, ba na yi, yanzu zan fara." Wani kallo da ban taɓa ganin ya yi mini irinsa ba ya wurga mini tare da faɗin. "Shi ne kuma sai a yau ɗin za ki je za ki faɗa mun? To ban shirya ba gaskiya." Tsaki na ja a cikin raina na ce. 'Sarkin tsiya aminin talauci, to ba cewa zan yi ka ba ni kuɗin ba.'
"Ba kai za ka biya ba ai, ni zan biya da kaina." Na faÉ—i haka ina huhhura hanci.
"A ina kika samu kuÉ—in?"
"Allah ne ya ba ni."
"To ba za ki je ba." Ya faɗa a fusace tare miƙewa ya bar mini parlour'n.
Da wani matsiyacin kallo na raka shi, ƙwafa na ja na miƙe kamar zan kifa na ɗauko wayata na kira Maman Nasmah, ringing biyu ta ɗaga, muryarta da alamun bacci ta ce. "Kin ga saƙona kenan?" Na ce. "Eh, ki yi haƙuri na tashe ki a bacci." Ta ce. "Ba komai, Kin tambayi mijin naki?" Na ce. "Hmm." Tare da faɗa mata duk yadda muka yi da shi. Cikin kwakwazo ta ce. "Wannan miji naki ba dai baƙar zuciya ba wallahi, ni fa tunda na gan shi yana yi miki wani murmushin gefen baki na san mugu ne, ban da haka mene na hana ki wani fita?" Kamar zan yi kuka na ce. "Kulle ne da shi da ma, ko bayani ban gama yi masa ba ya tashi ya bar ni, in dai ba tare za mu fita ba bai fiya bari na fita ba, wai shi kishi."
"Kin gani ba, muguntar kenan ai, shi yana fita yana watayawa kullum amma ke yana barin ki a gida a dunkume, saboda kar ki fita ki....." Jin motsin shi na yi saurin katse da faÉ—in. "Ina zuwa, ga shi nan." Ban jira amsar ta ba na datse kiran.
Murmushin mugunta Maman Nasmah ta yi ta ce. "Jaka, haka zan ta zura ki na kai ki na baro, miji irin naki ai abin so ne, mai kishin iyalinsa da tsare mutuncinsu, ban da mahaukaciya ce ke da ma wanne mijin arziƙi ne za ka ce masa za ka fara fita wani gyaran jiki rana tsaka ya bar ka? In sha Allahu kafin taron nan sai na yi sanadin da zai miki ko saki ɗaya ne, daga nan na fara plan B ɗina." Ta lumshe idonta tare da rungume pillown da yake ƙirjinta, wani irin son Anas sabo na fizgar ta, mutumin da ko sunansa ba ta sani ba, amma soyayyar shi ta mata mugun gamu, saboda yadda tunaninsa ya addabe ta ko lokacin yin wasu abubuwan ba ta samu yi ba a daren jiya, raba dare ta yi tana ta juyi a gado tare da hasaso irin soyayyar da take fatan su yi. Tana ganin ɗaya daga cikin mazan da take hulɗa su yana ta kiran ta amma ta ƙi ɗagawa, domin daga lokacin da ta yi tozali da Anas duk mazan duniya suka koma mata tamkar mata ƴan'uwanta, shi kaɗai take gani a Namiji. Fatanta kawai Allah ya sa mijinta ya dawo a cikin satin nan, ta rura masa wuta ya ba ta takardarta, ta yi ta yi ta gama iddarta a ɗaura mata aure da masoyinta. Komai take yi fuskarsa kawai take gani a cikin idanuwanta da murmushin da yake yi wa Hafsah. Numfashi ta sauke tare da mirginawa tana murmushi ta ce. "Ina son ka sosai mijin Hafsah Maman Sultan a yanzu, nan gaba kaɗan kuma mijin Hafsat Maman kyawawan ƴaƴan da za ta haifa maka masu kama da kai."
Ido na bi shi da shi bayan ya shigo ɗakin, cikin tsoron ko ya ji wayar da nake yi, don babu abin da ya tsana a rayuwarsa sama da wani abu ya faru a tsakaninmu na faɗa wa wani, mutum ne shi mai son sirri sosai. Shi ya sa tun da muke da shi bai taɓa kai ƙara ta gida ba da sunan na yi masa wani laifin. Yana cire jallabiyar jikinsa na ƙarasa kusa da shi fuska a murtuke na ce. "Wai don Allah Anas me ya sa kake mun irin wannan abubuwan ne? Akan me za ka hana ni zuwa gyaran jikin nan?" Ba tare da ya kalle ni ba ya ce. "Saboda na isa." Kallon sama da ƙasa na yi masa na ce. "Yanzu kai ba abin jin daɗinka ba ne zan je a gyara ni?" Ya ce. "Ba shi ne damuwata ba, inda kika samo kuɗin zuwan nake son sani." A wulaƙance na ce. "Oh, saboda ga ƴar matsiyata dangin matalauta ko? Wadda wani nawa ba zai iya ba ni kuɗi ba." Kallon takaici kawai ya mun ya juya ya fita, na bi shi da harara. Kiran Maman Nasmah na ƙara yi na faɗa mata komai. Cikin faɗa ta ce. "Wai wannan mijin naki shi ne autan maza ne da kike ta lallaɓa shi haka? Maman Sultan kar dai ki ce mini ke ma mata kika rako duniya?" Na ce. "Ban gane ba?" Ta ce. "Ai ba za ki gane ba, ni kawai ki faɗa mini idan gyaran jikin ne ba kya so na saka ta dawo mini da kuɗina." Cikin rawar baki na ce. "Wallahi ina so, kawai ban san fita ba da izninsa ba ne." Ta ce. "To sannu doluwa, idan akan maganar kuɗi ne ki ce masa ƙawarki ce kuka haɗu a social media ta ba ki, ba shikenan ba ya ji abin da yake so?" Shiru na yi, don na san hakan ma wata sabuwar fitinar ce. Fahimtar hakan ya sa Maman Nasmah ta ce. "Ko me zai yi ki faɗa masa haka, don maza ba a yi musu lako-lako, ni ban ma taɓa ganin mace mai tsoron miji irinki ba ko a labari, ko a cikin group ɗinmu ai za ki ga kowacce tana faɗa watayawarta take yi son ranta a gidanta, ke kaɗai ce fa kike cikin wannan rayuwar ƙuncin, ki zage ki ƙwatarwa kanki ƴanci, idan ba haka ba taron ma hana ki zuwa zai yi. Don haka duk abin da zai ce ki yi ficewarki, kar ki raga masa, ba a raga wa maza yanzu ko kaɗan." Cikin rashin mafita na ce "Toh shikenan." Daga haka muka yi sallama. Zama na yi ina bitar maganganun Maman Nasmah, tabbas duk abin da ta faɗa gaskiya ne, su da mazajensu ma suke hamshaƙan masu kuɗi ba sa tsoron su sai ni matar talaka. Yanda matan group ɗinmu suke watayawarsu abin ba ƙaramin burge ni yake ba, sai na ji suna cewa duk inda suke so zuwa suke. Don haka ni ma daga yanzu na ɗaura ɗamarar yin duk abin da na ga dama, na daina shayin Anas, bari ya dawo daga kai su Sultan school, zan nuna masa wargi ce ni daidai ƙugunsa. Da wannan tunanin na tashi na fara shirin tafiya gidan mai gyaran jikin. Har na sha tea ɗin da ya tafasa da bread na yi wanka bai dawo ba. Ina cikin shiryawa ya shigo, sai da kammala komai na ɗauki jakata da mayafi na nufi ƙofa fuskata a murtuke, ba tare na ce masa ƙala ba.
"Babu inda za ki je fa wallahi Hafsah." Ya faÉ—a yana tare hanya. A haÆ™iÆ™ance na ce. "Wai saboda me? Idan kuÉ—in ne dole sai ka ji wa ya ba ni to Æ™awata ce da ta zo jiya." Yana Æ™ara babbake hanya ya ce. "A ina take? Mene ne alaÆ™arki da ita?" Kaina tsaye na ce. "A group na Whatsapp muka haÉ—u." Cikin matsanancin É“acin rai ya ce. "Ban san ta ba, ban san irinta ba, ban san wace ce ita ba, ba zai yiwu haka kawai ta É—auki kuÉ—i ta ba ki ni kuma na bar ki, ki yi amfani da shi ba, don haka ki mayar mata da abinta!" A zazafe na mayar masa da raddi da faÉ—in. "Wallahi ba zan mayar ba, kai ba ka ba ni ba, ita da yake mijinta mai zuciya ne da son faranta wa iyalinsa ya ba ta har ta sammun a ciki sannan kuma ka ce na mayar saboda mutunta? Su mazansu ga kuÉ—i ga ba matsi, sai kai talaka ne za ka hana ni rawar gaban hantsi? To wallahi bari ka ji Anas, ban ga abin da zai hana ni zuwa gyaran jikin nan ba, saboda taro za mu yi a group É—inmu, kowacce mijinta ya ba ta kuÉ—i don ta fito fes sai ni ce zan tafi a duÆ™un-duÆ™un? To ba zai yiwu ba." Na Æ™arashe maganar kamar zan kai masa duka, zugar Maman Nasmah na Æ™ara tunzura ni na ci gaba da faffaÉ—a masa maganganu ya gane ba na tsoron shi a yanzu, amma na danne na Æ™yale shi haka ba don halin shi ba. Tsananin mamaki da al'ajabi su suka saka Anas sandarewa a tsaye, ya kasa Æ™waƙƙwaran motsi, hakan ya ba ni damar raÉ“awa ta gefen shi na fice. Na kai tsakiyar tsakar gida na ji muryarsa cikin matsanancin É“acin ran da ban taÉ“a jin shi a cikinsa ba, don muryarsa har rawa take yana faÉ—in. "Wallahi! Wallahi! Wallahi idan kika É—aga Æ™afa kika fita daga gidan nan a bakin aurenki!".......âœï¸
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.