Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Yiwa_Kai_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 27 of 34
Tun ranar da aka kai Hafsah Maman Nasmah ta cire sim ɗinta ta ajiye, saboda ta san dole za ta neme ta a waya, ita kuma ba a wannan lokacin take son su zanta ba, ta fi son sai ta jigata tukuna, duk wani shirin aurenta ita ta shirya wa Alhaji Mansur yadda zai yi. Duk da burinta ya cika na raba ta da Anas amma ba za ta ƙyale ta haka ba, don so take ta yi wa rayuwarta babbar illar da kowa sai ya guje ta. Saboda haushin ta take ji na fara mallakar Anas da ta yi kafin ita, da kuma irin mugun son da yake yi mata. Akwai abokan mijinta da yawa waɗanda idan ta yi musu tallan Hafsah ba za su ƙi ba, amma saboda ta fuskanci bayan halin mazansu na luwaɗi Alhaji Mansur yana da wani mugun abun shi a karan kansa, ta fuskanci hakan ne ta yadda duk matan da zai aura ba sa iya zama, komai uban kuɗi da zai mallaka musu kuwa. Kuma ita ta ce ya bayyana wa Hafsah mummunan halinsa, saɓanin ita da sauran matan abokan mijin nasu da sai dai su fuskanta da kansu, ko kuma idan tafiya ta yi tafiya mazajen su bayyana musu, amma ba daga kai su ba. Ta yi hakan ne duk don kawai Hafsan ta rasa farinciki tun tana Amarya, ta kasa samun nutsuwar da ta ci kuɗin da take ta fatan samu, bare ta tara wani abun da za ta tsira da shi a gaba. Murmushi ta yi bayan ta tuno next tuggun da take haɗa wa Hafsah.
WaÉ—anda ta saka su yi mata aiki akan Anas sun sanar mata ya dawo har ma ya je gurin aiki yau. Hakan ya sa ta shirya cikin zumbulelen hijab da niÆ™ab, ta É—auki Alkur'ani na sauka mai izifi bibbiyu ta nufi gurin aikin nasu don fara aiwatar da shirinta, zuciyarta cike da fatan samun nasara.......âœï¸
*Zeey Kumurya*âœï¸
[3/8, 1:44 PM] BahaushiyaðŸ‘: *YI WA KAI*
MIKIYA WRITERS ASSOCIATION
*BRIGHT PENS*
(FREE BATCH)
*24.*
Cikin ɗoki ta shiga bayan mota, direban da zai kai ta ya ja suka fice daga gidan. Wani irin nishaɗi take ji yana mamaye dukkan zuciyarta tun kafin ta gan shi, ba ta taɓa son abu kamar yadda take son shi ba a rayuwarta, sau ɗaya ta taɓa ganin shi a zahiri, amma a kodayaushe cikin yi mata gizo yake a cikin ranta. Idan farinciki yana kisa tabbas ranar da aka ce ta zama matarsa za ta iya mutuwa. Ko da wasa ba ta taɓa tunanin za ta so wani mutum haka ba, don ba ta taɓa ma yin soyayya ba a rayuwarta, saboda tana gama secondary school babanta ya aura mata mijinta na yanzu, ba ta son shi, amma ganin irin kuɗin da yake da shi ya sa ta amince da auren nasa. A lokacin da ta gane halin shi ba ƙaramin bori ta yi akan ya sake ta ba, amma da ya toshe mata baki da uban kuɗi sai ta haƙura ta ci gaba da zama a haka. Ko da wasa ba ta bari iyayenta sun san halinsa ba har suka koma ga mahaliccinsu. Numfashi ta sauke cikin jinjina wauta da rashin rabo irin na Hafsah, na yadda idanunta suka rufe ta kasa gane qualities ɗin da Anas yake tattare da su, wanda dubban maza suka rasa a wannan zamanin. Duk da ita hakan gaba ya kai ta ita.
A daidai ƙofar shagon ogansu Anas drivern ya yi parking. Tana murmushi ta cikin niƙab ɗinta ta buɗe murfin motar ta fita. Mutanen da ta gani a bakin shagon ta nufa tare da yi musu sallama. Bayan sun amsa ta yaye niƙab ɗin ta ce. "Don Allah Malam Anas nake nema." Da sauri ɗaya daga cikinsu ya ce. "Idan aiki za a yi miki za mu iya yi mu ma, ba lallai sai shi ba." Murmushi ta yi, cikin ranta ta ce. 'Wannan aikin shi kaɗai zai iya yi mini shi duk duniyar nan.' Wani daga cikinsu ya ce. "Ƙwarai Hajiya, mu da shi ai duk ɗaya ne." Idanunta a kan shagon nasu da ba ta iya hango cikinsa sosai ta ce. "Yanzu dai yana nan ko ba ya nan? Idan aiki ne ba ku da damuwa, gabaɗaya tare za ku yi." Washe bakinsu da ya bushe raƙau saboda azumi suka yi suka ce. "Ƙarasa ciki ki tambayi Oga." Ba ta kuma magana ba ta tafi a ɗokance. Bayan sun gaisa ta tambaye shi Anas ya ce. "Ayya, Malam Anas mai mutane, duk wanda ya yi wa aiki sai ya dawo, ga shi kuma kin tari gurbi Hajiya, don ɗazun nan ya bar nan, ya zo yi mana sallama tare da sanar mana ya bar aiki." A ɗan rikice ta ce. "Subhanallah! Saboda me?" Cikin jimami ya ce. "Ban sani ba gaskiya, amma ya ce mana wani ƙwaƙƙwaran dalili ne ya saka mu yi haƙuri." Da sauri ta ce. "To yanzu don Allah a ina zan same shi?" Ya ce. "Ban sani ba wallahi, don ya ce mana zai bar garin ne gabaɗaya." A ruɗe Maman Nasmah ta ce. "Innalillahi! To ya tafi ina?" Cikin mamakin yadda ta rikice Oga ya ce. "Lafiya dai ko Hajiya? Ina fata ba kuɗin aiki kuka biya shi ba kuma ya tafi da su." Girgiza kai kawai ta yi amma ta gaza cewa komai. Ajiyar zuciya ya sauke tare da faɗin. "Yawwa, don na san Anas ba halinsa ba ne wannan, ba a taɓa kama shi da abu makamancin haka ba." Tattaro dukkanin sauran nutsuwa da dauriyar da suke ƙoƙarin tarwatse mata ta yi ta ce. "To zan iya samun nunbern wayarsa?" Ya ce. "A'a, ba ma shi da waya yanzu gaskiya, ta da kuma ba ta aiki." Ta ce. "Shikenan, na gode sosai Malam, sai anjima." Ba ta jira cewar shi ba ta juya ta fita a rikice. Oga ya bi ta da kallo, haka kawai ya ji matar ba ta yi masa ba, yana da nunbern Anas, ya ce mata babu ne saboda bai san me za ta yi da ita ba.
Tana ji mutanen bakin shagon suna cewa. "Hajiya yaushe za a yi miki aikin?" Amma ta yi banza ta wuce fuuu, ta rasa me ya sa ba ta da sa'a akan Anas, duk lokacin da take murnar abu ya zo daf sai ya koma baya, masu yi mata aiki a kansa sun ce ba ƙaramar wahala suke sha ba, da ƙyar suke samun information a kansa. Ita ba ta taɓa tunanin talaka zai yi wahalar gani haka ba, ta ɗauka available suke a kodayaushe kamar ledar pure water. Kamar tai ta zunduma ihu ko za ta ji daɗi haka take ji, ga shi ƙarin damuwarta bayan ta gama wannan fighting ɗin akwai wani a gaba, na neman yardarsa da kuma na rabuwa da mijinta.
Jiki a saɓule na ƙarasa parlourn na zauna ina ƙare wa baƙon da aka ce na yi kallo shi da yaran gabansa. Yana bi na da wani irin shu'umin kallo ya ce. "Sannu da fitowa ranki ya daɗe." Na ce. "Yawwa sannu, an ce kana nema na." Bai ba ni amsa ba sai da ya tura yaran waje sannan ya ce. "Haka ne, gurinki na zo." Gyara zama na yi na ce. "Sai dai ban gane ka ba."
"Da ma ba ki san ni ba bare ki gane ni babbar mace." Ya yi maganar yana zunkuɗowa daga kan kujerar da yake. Ban ce komai ba na bi shi da ido kawai, hakan ya sa ya ci gaba da faɗin. "Sunana Faisal, mijinki Alh. Mansur shi ya turo ni don na ɗeɓe miki kewa, na taho da yara ne saboda na ɗauke hankalin ma'aikatan gidan nan daga zargin wani abu, zan zauna a matsayin ni ɗan'uwanki na kawo miki yara ziyara su yi Sallah a nan." Cikin rashin fahimta na ce. "Ban gane me kake nufi ba, ɗebe kewa kamar ya?" Wani munafukin murmushi ya yi tare da tashi ya dawo hannun kujerar da nake, cike da duniyanci ya ce. "Haba Madam, sai na yi gwari-gwari sannan za ki gane? Mu huta mu mori junanmu a bed nake nufi." Ya ƙarashe maganar tare da ɗage mini gira gami da kashe ido. Nemar komai nawa da zan iya sarrafa kaina na yi saboda ɗimaucewa, sai bayan wasu sakanni na fara dawowa daidai, idanuna ƙyam a kansa na ce. "Idan na fahimce ka zina kake nufin mu dinga aikatawa?" Ya ce. "Yeah ƴar gari." A fusace na miƙe ina jin wani abu ya tokare mini ƙirji, nuna shi na yi cikin ƙaraji na ce. "Ni ba ƴar'iska mahaukaciya ba ce da zan aikata zina a ɗakin aurena, kuma tsabar dabbanci da hauka a cikin watan Ramadan, da azumi a bakunanmu kake furta wannan asararren zancen, to ka tattara ka bar mini gida kamar yadda ka shigo, ba da ni za a yi wannan jahilcin ba." Miƙewa ya yi ya ce. "Calm down Bab, ba yanzu za mu yi ba da ma ai, sai an sha ruwa." Cikin hargagi na ce. "Ko haɗiye shi za a yi ba sha ba sai ka bar gidan nan, get out!" Na ƙarashe maganar ina nuna masa ƙofa. Murmushi ya yi ya ce. "Abin duk ba na zafi ba ne babbar yarinya, wannan harkar mun saba yin ta da sauran matan Alhaji, tunda shi ba lafiya ce da shi ba sai ya kawo muku irinmu ku dinga rage zafi, saboda kar ya cutar da ku, kuma ko da kin samu ciki kin haihu zai yi accepting abin da kika haifa a matsayin ɗan cikinsa, zai yi masa hidima ya yi masa komai, ƙarshe idan ya mutu ma har gadonsa zai ci, babu wanda zai sani." Ban iya kuma magana ba saboda yadda zuciyata take tafarfasa na fice daga parlour'n ina haɗa hanya, ikon Allah ne ya kai ni parlona, na faɗa kan kujera da ruf da ciki, hannuna riƙe da kaina da nake jin yana mun wani irin tururi kamar zai tarwatse. Wannan wacce irin ƙazamar rayuwa ce mai cike da jagwala-jagwala, a ce mijinka na sunna shi zai turo maka gwarton da za ku dinga lalata a cikin gidansa? Har gwarton yana proud da ko ka samu ciki zai riƙe shi a matsayin ɗansa. Na rasa sunan da zan kira wannan ƙaddararren auren nawa, rayuwar jin daɗi da watayawar da nake so ga ta nan na samu, amma farinciki da walwala gabaɗaya sun ƙaurace mini kamar yadda rai yake barin gangar jiki, ba kuma na ganin alamar ko burbuɗin dawowar su, matuƙar ba sakin raina zan yi na amince da rayuwar da na saka mata sunan JIN DAƊI A DUNIYA, SHAN WUYA A LAHIRA ba.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.