Complete Hausa Novels

Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Yiwa_Kai_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 30 of 34

Rayuwa ta ci gaba da juyin wainar ƴar koyo da ni a gidan Alhaji Mansur Idonnera, na ja watanni huɗu amma babu shi babu dalilin shi, ba waya ba chat, sai dai aiken kuɗi kawai. Ban san haka nake da buƙatar namiji da kulawar shi ba sai a wannan lokacin, ga shi babu wanda nake da shi da zan faɗa masa damuwata ya ba ni shawara, Maman Nasmah har sau biyu ina zuwa unguwarsu ina bulayi amma ban yi dacen samun gidanta ba. Har a group ɗinmu na yi cikiyarta, su ma suka ce neman ta suke yi.

Ranar wata Lahadi ina zaune na tasa TV a gaba da sunan kallo, amma babu abin da nake fahimta wanda ake yi a ciki. Knocking aka yi na bayar da umarnin shigowa, Laura ce. Cikin ladabi ta ce. "Hajiya kin yi baƙuwa." Da mamaki na ce. "Baƙuwa kuma?" Don tunda na zo gidan babu wanda ya taɓa zuwa, ko nawa ko nasa. Cikin fatan ya kasance Maman Nasmah ce na ce. "Je ki shigo da ita." Tare suka dawo da matar, na bi ta da kallo don ban san ta ba. Fuskarta ɗauke da fara'a ta ce. "Sannu da hutawa." Murmushi na yi na ce. "Yawwa, Bismillah ki zauna mana." Tare da ba wa Laure umarnin ta kawo mata abin taɓi. Bayan mun gaisa ta ce. "Kin ga baƙuwar fuska ko? Maƙociyarki ce, tun lokacin da aka kawo ki nake ta zuba idon ganin amarya za ta shigo a gaisa na ji shiru, yau dai na cewa maigidan bari na shigo mu gaisa, haƙƙin maƙota ba a rayu ba a san juna ba." Na ce. "Allah Sarki, kin kuwa kyauta, na gode sosai Allah ya saka da alkhairi, ina ta son na shishshiga ɗin kuma Allah ne bai nufa ba." Ta ce. "Babu komai, ni gani ai na zo." Murmushi na yi na ce. "Kin samu ladan, Allah ya bar zumunci." Ta ce. "Amin." Da na tambaye ta ina ne gidan nata, ta yi mini kwatance sai na ga ashe ita ta aiko mini da abincin Sallah kwanaki. Mun taɓa hira da ita, hakan ya sa na ji daɗi kamar an rage mini damuwar da take damu na. Washegari sai ta ƙara dawowa tare da yaranta masu kyau mace da namiji, har ta bar su suka ɗan jima a gurina. Yara masu da hankali da shiga rai. Bayan kwana biyu ta ƙara zuwa muka gaisa, ta ce amma tunda na ƙi zuwa ba za ta ƙara zuwa ba ita ma. Hakan ya sa ni ma na fara shigar mata. A hankali a hankali muka fara sabawa da ita, tana da kirki sosai, ga ta da addini da sanin darajar ɗan'adam. 
Yau ta zo muna cikin hira ta dube ni ta ce. "Aunty Amarya ni kuwa ina so na yi miki wata tambaya, Allah ya sa ba zan yi miki shishshigi ba." Tattara hankalina na yi duka a kanta na ce. "Ina sauraren ki Maman Hanif, ki yi mini duk tambayar da kike so, babu wani shishshigi da za ki yi, ai ni da ke mun zama ɗaya." Numfashi ta sauke ta ce. "Tun ranar da na fara ganin ki na lura kamar akwai wani abu da yake damun ki, daga ranar har zuwa yau kuma kullum a haka nake ganin ki, ba wai ina son jin sirrinki ba ne, ina so na ji ne kawai ko zan iya ba ki shawarar da za ta zamo miki mafita, saboda ni ba na ƙaunar na ga mutum a cikin damuwa ko kaɗan, musamman wanda nake tare da shi." Numfashi na sauke jin ta sosa mini inda yake yi mun ƙaiƙaiyi, a raunane na ce. "Tabbas akwai abin da yake damu na, wanda ya girmi ƙwaƙwalwata na kasa samun mafita." Ido kawai ta zuba mini alamun ni take saurare. Gyara zama na yi na ce. "Matsalar gidan aure ce, mijina ne matsalata!" Waro ido ta yi ta ce. "A yadda kike a cikin wannan gidan idan za ki kwana kina cewa kina cikin damuwa wani ba zai taɓa yarda ba, saboda babu abin da babu na more rayuwa, duk da duniya cike take da ƙalubale, kuma mai ɗaki shi kaɗai ya san inda yake yi masa yoyo." Jijjiga kai na yi tare da gimtse baki na ce. "Tabbas haka ne, don ni ma kafin na shigo gidan abin da zuciyata take faɗa mini kenan, sai daga baya na gane ashe hangen dala ba shiga birni ba ne, ashe kuɗi ba shi ne farincikin da jin daɗin rayuwa ba." Girgiza kai ta yi ta ce. "Ba zan ce abin da kika faɗa ba daidai ba ne, amma akwai masu kuɗin da Alhamdulillah ga dukiyar ga kuma kwanciyar hankali." Da sauri na ce. "Kuma kuɗin na halal ne ba haram." Murmushi ta yi ta ce. "Sosai ma, yadda a talakawa akwai na gari da na banza haka ma a masu kuɗin akwai. Kamar yadda akwai wanda Ubangiji ya ba su duniya da lahira. Bari na ba ki misali da ni karan kaina, kin je gidana kin ga yadda nake, Alhamdullillah mijina yana da rufin asiri daidai gwargwado, don duk shekara Hajj da Umrah ba sa wuce shi, kuma tsaftatacciyar sana'a yake yi, ɗan kasuwa ne, kuma mutum ne mai tarin ilimin addini da na zamani." "Kuma yana ba ki kulawa yadda ya kamata?"
Ta jinjina kai ta ce. "Sosai ma, yana taya ni ayyukan gida, yana ba ni lokaci mu yi hira, har lokacin koya mini karatun addini ni da yara ya ware mana, kuma duk wasu buƙatunmu na rayuwa yana yi mana daidai ƙarfinsa, a zamanmu ba ya muzguna mini, ba ya cutar da ni, rayuwa muke yi mai cike da annashuwa, Alhamdullillah shi ne kawai abin da nake cewa game da mijin da Allah ya ba ni." Cike da sha'awar irin rayuwarta na ce. "Ma sha Allah, da ma ba duka aka taru a ka zama ɗaya ba, amma da har na saka a raina rayuwar kuɗi babu jin daɗi a cikinta, ko kuma idan da jin daɗin kuɗin ba na halak ba ne." Ta ce. "To cire ma tun wuri, ai shi arziƙi yalwa ce daga Ubangiji yake yalwata bayinsa da shi, ba zai yiyu ba kuma a ce duk wanda ya ba wa ba ta hanyar halak ya nufa ya samu ba ko kuma ya hana shi jin daɗin rayuwa ba, kawai dai ya danganta da rayuwa ta zo wa kowane bawa daga ubangijins." Shiru na yi cikin gamsuwa da bayaninta, wato ni ce ban yi dace ba kenan? Yadda ta siffanta mijinta exactly irin Anas, banbancin su kawai shi takala ne, mijinta kuma mai kuɗi ne. Babu mamaki ƴan group ɗinmu ma duk sun yi dacen, shi ya suke yin rayuwarsu normal cikin farinciki, hakan na nufin da zan rabu da Mansur ni ma zan iya yin dace da miji mai kuɗi kuma nagartacce a gaba . Katse mini tunani ta yi da faɗin. "Mun shiga wata hirar daban, ba ki faɗa mini matsalar taki ba." Numfashi na sauke kamar zan yi kuka na ce. "Rashin kulawar miji shi ne babbar matsala! Ya wadata ni da komai na more rayuwa, amma kwata-kwata ba shi da lokacina, tunda muka yi aure sau ɗaya ya taɓa zuwa ya kwana ɗaya tak ya tafi." Na ƙarashe maganar ina jin kamar an yaye mini wani abu da ya tokare mini ƙirji, saboda yau na samu chance na faɗa wa wani damuwata.
"Tafiye-tafiye yake yi kenan?"
Gyaɗa mata kai na yi. Ta ce. "To me ya sa ba za ki dinga bin shi ba tunda kina takura?" Idona cike da ƙwalla na ce. "Ya ƙi yarda ai." Cikin jimantawa ta ce. "To ki yi haƙuri ki karɓi ƙaddarar ki kawai, ki ta addu'a da shawo kansa har ya haƙura ya dinga tafiya da ke." Girgiza kai na yi a raina na ce. 'Ba za ki gane ba ne.' A fili kuwa sai na ce. "Ba zai taɓa yarda ba wallahi, kuma ni idan a haka za a ci gaba tafi ba zan taɓa farinciki ba har abada." Cikin tausayawa ta ce. "Subhanallahi! Kar ki ce haka, ki ci gaba da addu'a, in sha Allah komai zai warware, addu'a tana saurin canza abubuwa." Ta ba ni shawarwari sosai tare da alƙawarin za ta kawo mini wasu addu'oi na dinga yi, in sha Allah za su daidai mini al'amurana.
Ta dalilin Maman Muhsin na san wasu maƙotan namu, a ciki na haɗu da wata da jinina ya haɗu da nata sosai mai suna Karima, duk da unguwar ba irin wanda muka taso ba ne, nan kowa rayuwarsa yake yi, sai abu ya faru ake ɗan leƙa mutum, amma duk da haka ina shiri da su biyun nan sosai.
Duk da na samu waɗanda suke ɗebe mini kewa amma damuwa ta kasa bari na, wata shida da aurenmu amma har yanzu Mansur bai ƙara zuwa ba, ni kaɗai sai na zauna nai ta tunanin ina yake tafiya ya daɗe haka? Anya kuwa zan iya ci gaba da rayuwa a wannan yanayin? Duk yadda na so tursasa zuciyata ta haƙura amma ta ƙi aminta, kulawa da tattali kawai take buƙata. Gabaɗaya na ƙara bushewa kamar mai cutar ƙanjamau. Na yi nisa a cikin tunanin da ya aure ni na ji an dafa kafaɗata. A zabure na ɗago, ajiyar zuciya na sauke ganin Karima ce. Bayan ta zauna a kusa da ni ta ce. "Ki yi haƙuri na tsorata ki." Yaƙe na yi na ce. "Ah..babu komai."
"Tunanin me kike yi?" Ta tambaye ni tana bi na da kallo.
Ƙasa na yi da kaina don ji nake kamar na saka kuka ko zan ji sassauci a cikin zuciyata. Ba ta damu da shirun da na yi ba ta ce. "Me zai dame ki har ki yi nisa a cikin tunani haka, na shigo ina ta sallama amma duk ba ki ji ba?" Maimakon na ba ta amsa sai na fara hawaye, ban saba da damuwa ba a rayuwata, don ko takurar Gwaggo ba ta kai wannan tsanani ba a gurina, hakan ya sa na kasa jure mata, raunina yake bayyana ga duk wanda zai tambayi abin da yake damu na." Gyara zama ta yi tana fuskanta ta, ta ce. "Na san abin da yake damun ki Hafsah, saboda matar da mijinki ya saka last kafin ya aure ki cousin ɗita ce." Da sauri na kalle ta kamar ban fahimci me ta ce ba. Gyaɗa kai ta yi ta ce. "Kin yi mamaki ko?" Na ce. "Eh." Muskutawa ta yi ta ce. "Ban jima da tarewa a unguwar nan ba, don kin riga ni ma zuwa, tunda muka zo na ga gidan nan aka ce da mace a ciki na fara tausaya mata tun kafin na gan ta, don na san duk wata ƙazanta da halin maigidan. Cousin ɗin tawa ita ta fara zama a gidan nan, yana sabon shi, ba ki ga yadda aka dinga yi mata murna ba lokacin aurensu, na dace da irin mijin da ta yi. Sai dai ko shekara ba ta yi ba ya sake ta, familynmu aka dinga zuzutun ita kuwa me ya fitar da ita daga wannan gidan hutun? Sai dai kawai ta ce kwanan auren ne ya ƙare, da haka ta rufe bakin mutane, amma ni ta faɗa mini komai ba ta ɓoye mini ba da yake muna shiri sosai." Tana rufe baki ta latsa wayarta ta nemo hotunansu tare ta nuna mini, jikina na rawa na karɓa na gani. Tabbas Alhaji Mansur Idonnera ne da wata, ya washe baki kamar mijin arziƙi, sai hotun ita da amaryar ne da shi duk a ranar. Tana karɓar wayar bayan na gama gani ta ce. "Ba zan tambaye ki abin da ya kai ki auren shi ba, don na san ƙaddara ce, saboda in dai ba sani ka yi ba, babu yadda za a yi ka ce ba mutumin ƙwarai ba ne." Da sauri na ce. "Wallahi haka ne, siffar mutanen kirki gare shi." Halayen shi ta fara lissafa mini wanda na sani da wanda ban sani ba, hakan ya tabbatar mini da gaske take ta shan shi ciki da bai. Ina kuka na ce. "Don Allah ki faɗa mini yadda cousin ɗin taki ta yi ta rabu da shi, wallahi na gaji da auren nan, so nake ya sauwaƙe mini kawai, na gaji! Ba zan iya ba!" Miƙewa tsaye ta yi ta ce. "Ba ta faɗa mini wannan ba, amma akwai shawarar da zan ba ki, wadda matuƙar kika bi ta babu makawa sai mijinki ya sake ki cikin ruwan sanyi ba tare da kun kai ruwa rana ba." Maganata har harɗewa take gurin azarɓaɓin cewa. "Don Allah ki taimake ni ki faɗa mini."
"Yanzu kuwa." Ta faɗi haka tare da komawa ta zauna ta fuskance ni da kyau...........✍️

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.