Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Yiwa_Kai_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 26 of 34
Yau idan an kai azumi huÉ—u, da rana ina zaune a É—akina ina karatun Alkur'ani da na manta rabon na yi, hawaye ne yana zuba a kan kuncina, wani irin abu mai É—aci da maÆ™aÆ™i ne ya tsaya mini a Æ™irji, ga kewar su Sultan da ta cika mini zuciya a kwanakin nan. Rufe kur'anin na yi na rushe da kuka. Wacce irin amarya ce ni mara daraja da har an yi sati guda amma ango bai zo ya gan ni ba? Na tambayi kaina cikin takaici. Abin da yake Æ™ara baÆ™anta mini rai kullum sai na tambayi gateman ya tabbatar mini da Mansur yana nan Æ™alau cikin Æ™oshin lafiya. Bayan na yi kukan mai isata na tashi na haye kan gado, saboda jin maganin baccin da na sha da asuba ya fara aiki, rashin bacci ya sa na ba da aka siyo mini da yawa, kullum idan aka sha ruwa sai na sha nake iya bacci, haka ma bayan sahur. Cikin baccin na ji ana lalubata, a firgice na farka jin ana Æ™oÆ™arin haÉ—e mini ruwan ciki da katifar gadon, Allah ya ba ni sa'a na wancakalar da ko ma waye tare da tashi zaune ina Æ™oÆ™arin kurma ihu. Wanda na yi tozali da shi ya sa na fasa, Æ™ura masa ido na yi cikin wata irin mummunar faÉ—uwar gaba. Muryata na rawa na ce. "Mansur!" Bai amsa ba sai Æ™ara kusanto ni da ya yi, daga shi sai gajeren wando. A ruÉ—e na ja baya na mannu da fuskar gado fahimtar abin da yake nufi. Jikina na rawa na ce. "Na shiga uku! Mansur azumi fa ake yi, ko ka manta ne?" Cakuma ta ya yi cikin wata Æ™atuwar murya ya ce. "Ke kika san azumin." Tare da fara raba ni da kayan jikina. Duk yadda na so Æ™wace kaina amma na kasa, don Æ™arfi ya gwada gurin matse ni. Ba yadda ya bi da ni kamar dabba babu wasan komai ne abin damuwata ba, azumin da ke bakinmu da yadda yake Æ™oÆ™arin amfani da ni ta baya shi ne babban tashin hankalina. Yana daf da cimma burinsa Allah ya ba ni sa'a na Æ™ara hankaÉ—e shi a karo na biyu cikin zafin nama. Kamar an yi cilli da ni na yi tsalle na bar kan gadon na koma gefe, jikina na kyarma cikin razani na ce. "Mene haka? Me kake shirin aikatawa? Laifi biyu? Ga azumi ga kuma ta gurin da ubangiji ya haramta." Na Æ™arashe maganar cikin kuka. Tsaki ya ja ya ce. "Duk ke kika san wannan, ni kawai abin da na sani buÆ™atata ta biya." Ido na Æ™ura masa cikin kokawa da numfashina cikin dokawar zuci, tabbas wannan shi ne wanda Maman Nasmah ta tura mini pictures É—insa, shi ne ya zo gidanmu zance har sau biyu, shi ne kuma aka É—aura mana aure da shi, ya zo ranar É—aurin aure aka yi mana hotuna. Amma ba wannan muryar tasa ce muke waya da ita ba, waccan mai daÉ—in sauraro da magana cikin taushi ce, wannan kuma Æ™atotuwa ce mai hawa kai a maimakon ta kwantar da zuciya. To me hakan yake nufi? Muryar ce ta canza ko kuma me? Na tambayi kaina cikin tsananin ruÉ—ewar rashin sanin wanne iri miji na aura da yake Æ™oÆ™arin aikata manyan laifuka ga Allah da ni matarsa ta sunna a cikin wannan wata mai girma da tarin falala? Wanda kowa burin shi ya nemi rabauta da samun dacewa a gurin mahaliccinsa.........âœï¸
*Zeey Kumurya*âœï¸
[3/8, 1:44 PM] BahaushiyaðŸ‘: *YI WA KAI*
MIKIYA WRITERS ASSOCIATION
*BRIGH PENS*
(FREE BATCH)
*23.*
Miƙewa tsaye ya yi ya ɗora ƙafarsa ɗaya a kan gadon tare da gwiwar hannunsa a kanta, yana murmushin mugunta ya ce. "Na manta fa, ashe ban yi miki bayanin wane ni ba." Ban ce komai ba na ci gaba da ja baya a tsorace, ƙirjina na dokawa da ƙarfin gaske. Taku ya yi ya ya fuskanto ni, fuskarsa a haɗe kamar ba shi ya gama murmushi ba ya ce. "Kamar yadda aka ce miki sunana Mansur Ibrahim Idonnera, don ba zan na ce miki ba, saboda ba da ni kike yin duk chat ɗin da kika yi da waya ba." Waro ido na yi a firgice na ce. "Ban gane ba, waye kai ɗin? Me ka shirya mini da ka shigo cikin rayuwata?" Kamar ba zai yi magana ba sai daga can ya ce. "Ban da lokacin kaina ma bare wanda zan ba wa wani, hakan ya sa na yi nesa da dangina, sakamakon yawan ƙorafin da nake sha daga gurinsu. Na yi aure aure sun fi goma amma matan ba sa iya zama, duk da sai an kai ruwa rana nake iya sakin su. Lokacin da Hafsat matar abokina ta zo mini da maganarki ba ƙaramin farinciki na yi ba, domin ke ce daidai irin macen da ko ta ƙarfin tuwo dole ta zauna a matsayin matata, ta kare mini mutuncina tare da ɗauke hankalin mutane daga zargin wasu abubuwan." Cikin rashin fahimta na ce. "Saboda me dole sai irina? To ni ma wallahi ba zan zauna ka dinga wannan rayuwar dabbobin da ni ba, dole ka sake ni!" Dariya ya fashe da ita ya ce. "Ai har abada ni da ke mutu ka raba, za ki zauna a nan gidan ki ci gaba da yi mini gadin shi, idan ma wannan ɗin ya yi miki kaɗan zan iya canza miki wani, kuɗi kuma ba ki da matsalar shi, amma samun lokacina da yin wata mu'amala ta aure a tsakaninmu babu. Idan za ki tuna duk lokacin da zan zo mu haɗu muryata a dashe take, ina yi miki ƙaryar ina mura, to babu murar da nake yi, kawai bana son ki gane ba da ni kike waya da chat ba ne, da wani yarona na haɗa ku yadda za ki fi aminta da ni, don ni ban da lokacin wata soyayya. Iyayen da na yi amfani da su a gurin auren ki ba na gaskiya ba ne, wasu daban na samu na hayo, sannan kuma ranar da kika ce babanki yana son gani na, ba ni na je ba, Abdurrahman ne wanda kuke soyayya da shi a matsayin ni, da fatan kin fahimta?" Girgiza kaina na shiga yi ina fatan a ce mafarki nake, wani irin jiri ne yake ɗiɓa ta, kwata-kwata ban gane me yake nufi ba, na kasa gane inda maganganunsa suka dosa. Durƙushewa na yi tare da fashewa da kuka. Yana murmushin mugunta ya ce. "Akwai kuɗi! Ga ƙaton gida da motoci kala-kala, ki kwantar da hankalinki ki kwashi arziƙi kawai, ki mora ki fantama, ko da ma ba abin da kike so ba kenan?" Kallon shi kawai na ɗago ina yi amma na kasa cewa komai. Kafaɗa ya ɗage tare da faɗin. "And kuma idan amfanin da zan dinga yi da ke ta baya ba zai gamsar da ke ba, kina da right ɗin hulɗa da duk namijin da kike so, idan ma ke za ki dinga biyansa zan ɗauki nauyin hakan, don ba zan tauye ki ba." Ya ƙarashe maganar tare da nufo inda nake. Duk da halin ruɗun da ya fara taɓa mini ƙwaƙwalwa da na shiga, amma haka na miƙe fahimtar mugun nufinsa again na shige toilet na sakawa ƙofa key tare da jingina a jikinta ina sauke wahalallen numfashi. Har lokacin gabaɗaya maganganunsa suna amsa kuwwa a cikin kaina, ina jin shi yana ta ƙoƙarin buɗe ƙofar amma Allah bai ba shi sa'a ba har ya gaji ya tafi. Ajiyar zuciya na sauke na yi zaman ƴan bori a tsakar toilet ɗin. Tambayar kaina na dinga yi tsakanin Maman Nasmah da Mansur wa ya yaudare ni? Shi ya ɓoye mata gaskiyar halinsa ko kuma ita ma ta sani ta munafurce ni? A fili na ba wa kaina amsa da faɗin. "Ba ta sani ba, soyayyar da take yi mini na yi amanna ba za ta taɓa cutar da ni ba, ta haɗa ni da shi don na samu ingantacciyar rayuwa ashe gurɓatacciya zan samu. Tabbas da ta san yana yin wannan mummunan abun da ba za ta taɓa bari ya aure ni ba." Babu abin da ya fi ɗaga mini hankali sama da cewar ya yi ina da right ɗin hulɗa da wasu mazan, kuma da aurensa a kaina, hakan na nufin ba ya kishi na, ya aure ni ne kawai saboda na zama kariya a gare shi kamar yadda ya faɗa.
A toilet ɗin na ƙarasa sauran wunin ranar, damuwa da tsananta wa kaina tunani suka taro suka haifar mini da wani irin matsanancin ciwon kai da jiri. Sai da aka kira Magriba na samu na lallaɓa na fita, ruwa kawai na ɗauka a fridge na sha na faɗa gado na kwanta tare da runtse idona. Tunanin Anas da tarin soyayya da kulawar da ya nuna mini a lokacin amarcinmu na fara tunawa, lokaci mai daɗi da sanya nishaɗi a zuƙata gami da wuyar mantawa. Wasu irin zafafan hawaye ne suka shiga zarya a kan kuncina. Ina ji ana ta buga mini ƙofa amma na kasa tashi na buɗe, duk da na san ba zai wuce masu aiki ba ne. Har aka yi isha'i ina kwance a cikin wani irin yanayi. Tunawar da na yi ban yi sallolin wunin nan gabaɗaya ba ya sa na tashi cikin sauri na je na yi alwala na fara ramawa a zaune, don ba zan iya tsayuwa ba. Bayan na idar na lallaɓa na fita parlour, na tarar an shirya mini lafiyayyun kayan buɗa baki, an jera su a kan center table, baki na taɓe bayan na gama bubbuɗewa. Duk haɗuwar lafiyayyun abincin ko kaɗan ba su burge ni ba, sai ma wani ɗaci da na ji ya ƙara cika mini zuciya. Zama na yi a kan carpet ina ƙarewa falon kallo, so nake na tursasa zuciyata ta yi accepting wannan sabuwar rayuwar da na tsinci kaina a ciki amma ta ƙi, da na tuno Mansur ɗan luwaɗi ne sai na ji komai ya kwance mini. Zuciyata a ƙuntace na tashi na koma ɗaki na ɗauki wayata na ƙara trying nunbern Maman Nasmah, amma har yanzu a kashe take. Data na kunna na hau Whatsapp, nan ma ba ta hau ba. Kamar na tambaya a group ɗin ko da mai wata nunbern tata sai kuma na fasa. So nake na yi sharing wannan damuwar tawa da wani ko zan ji sanyi a raina, musamman ma ita, sai dai tunda na yi auren nan da Kawu kawai nake waya, shi kuma ko karen hauka ne ya cize ni ba zan yi masa wannan zancen ba, shi da takaimaiman wanda na aura ma bai sani ba, ta ina zan fara yi masa bayanin mun ɓoye masa mai kuɗi na aura ni da Inna Habi bare har mu zo kan wannan gaɓar? Naja ce ta faɗo mini a rai, na manta har numbernta na goge sai da na duba na ga babu. Cikin takaici na cillar da wayar tare da fashewa da kukan rashin sanin abin yi, har baccin wahala ya kwashe ni ban sani ba.
Wajen Asuba na farka, a firgice na tashi zaune saboda tozali da na yi da Mansur yana waya. Zuba masa ido na yi ina sauraren abin da yake cewa fuskarsa É—auke da farinciki.
"Eh yanzu na sallame shi, yaron ya yi sosai ai, irin wanda na ce kuma aka samo, na ji daɗin shi ba kaɗan ba Alhaji Labaran, ga shi ɗan shawalwali bai san komai ba, ni na fara sha'anin da shi." Ya yi shiru alamar yana saurare, daga baya ya kwashe da dariya tare da faɗin. "Kar ka damu, idan zan dawo zan taho da shi kai ma ka ɗana, don nawa ne shi kaɗai ba yarda zan yi mu dinga sharing ba." Da sauri na toshe kunnena fahimtar inda zancen nasu ya dosa, ina maimaita Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un a cikin raina, abin da nake jin labarin shi, nake ganin kamar ba ya faruwa saboda munin shi, amma yau ni nake rayuwa da wanda yake aikata shi. Ganin ya gama wayar na dube shi na ce. "Tir da halinka wallahi, ga ka kamar wani kamilalle ashe ba na Allah ba ne, kana da damar auren duk kalar matan da kake so har huɗu, amma gara ka dinga saɓon Allah ka....."
"Ke!" Ya daka mini razananniyar ƙara.
Hakan ya tilasta mini yin shiru ba tare da na shirya ba. Yana nuna ni da hannunsa ya ce. "Ki tsaya iya matsayinki, babu ruwanki da rayuwata da abin da nake aikatawa, kuɗi kika gani kika aure ni, to idan ma ba ki sani ba ki sani wannan abun shi ne silar duk wani arziƙina, kuma yanzu na fara kamar yadda ban da ranar dainawa. Sai kuma abu na ƙarshe da nake son sanar miki, kuskuren da za ki yi a rayuwarki shi ne ki yi gigin sanar da wani wannan sirrin nawa. Ina son ki sani idan za ki shekara kina faɗa babu wanda zai yarda da ke, kuma hakan daidai yake da siya wa kanki tikitin uƙubar rayuwa. Mafita a gare ki kawai ita ce ki zauna ki ci arziƙi, ki rufe mini sirrina ki bi ni da ido kawai." Ya ƙarashe maganar tare da janyo locker jikin mudubi, kuɗi ne cike a cikinta maƙil, nuna mini ya yi ya ce. "Ga shi nan naki ne, sannan duk wata za ki dinga ganin alert, kuma kar ki ga yau na ƙyale ki, ba wani na haƙura da ke ba ne, idan nan dawowa gare ki." Ban iya ba shi amsa ba saboda tsantsar rashin imani da tausayin da nake gani a kan fuskarsa. Bai damu da rashin maganata ba ya ci gaba da faɗin. "Ba ki da kowa ba ki da wani gata, danginku duka matsiyata ne, don haka ki taimaki talaucinku ki iya bakinki, ina fatan idan kunne ya ji jiki ya tsira." Tamkar mutum-mutumi haka na zama, na dinga bin shi da ido kawai a tsorace. Kayan jikinsa ya cire tas ya saka jallabiya kawai, kunnensa kare da waya yana faɗin. "Ka ƙaraso? To gani nan." Ya fita. Girgiza kai na yi don ko bai faɗa ba na san wani abokin shashancin nasa ne ya zo ya tafi gurin shi. Wani irin tsoron shi na ji yana mamaye ni. Ban yi sahur ba na zarce da azumi, don ko ruwa bana marmarin sha saboda ɗacin da bakina yake mun. Gari na fara haske Idonnera ya bar gidan ba tare ya yi mini sallama ba, sai bayan tafiyarsa na ji a bakin gateman da ya zo tambaya ta idan da akwai abin da ya ƙare a cikin kayan abinci za a siyo.
Bayan kwana uku ina tsaye a gaban mudubi ina kallon uwar ramar da na yi, a hankali na yi ƙasa da idona na sauke su akan himulin kuɗin da Mansur ya bar mini. Na rasa me ya sa zuciyata ta kasa yin farinciki da mallakar su, so nake na cire damuwar komai a cikin raina amma abu ya gagara. Idan na tuna furucin shi da ya tabbatar mini da duk kuɗin nan nasa ba ta halattacciyar hanya ya same su ba sai na ji ko ruwan gidan na kasa sha, musamman idan na tuna da hukuncin jikin da aka ciyar, aka shayar, aka tufatar da haramun da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama da ya ce mana, sai na ji komai na gidan ya ƙara fice mini daga rai. Ga rashin cin abinci da ya haifar mini da wani irin ciwon ciki da na ƙirji. A cikin kwanakin da ba su yi ashirin ba na gane ba kowane kuɗi ne farinciki da jin daɗin duniya ba kamar yadda Naja ta sha faɗa mini. Ga ni dai a gidan kuɗi da ya ji komai na more rayuwa, ga kuɗin kuma a gabana mallakina ina da damar yin yadda na so da su amma na kasa samun farinciki da sukunin zuciya tunda na shige shi. Girgiza kaina na yi na fice daga ɗakin, don ba ƙaramin gajiya na yi da wannan rayuwar kaɗaicin ba, ko da masu aikina ne gara na je na yi hira ko zan ji sanyi a raina. A parlour'n tsakiya muka ci karo da Laraba, ta rusina ta gaishe ni tare da faɗin. "Hajiya kin yi baƙo a ƙasa." Cikin mamaki na ce. "Baƙo! Waye?" Ta ce. "Ban sani ba, amma dai namiji ne tare da yara maza guda biyu a hannunsa."
"Kuma ya ce gurina ya zo?"
Ta ce. "Eh, Maman Sultan ya ce ma, wai idan na ce miki haka za ki fi gane ke yake nufi." Haka kawai na ji gabana ya faɗi tun kafin na ga ko waye, ban ce komai ba na nufi ƙofa na fita, na manta ko mayafi babu a jikina.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.