Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Yiwa_Kai_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 10 of 34
Duk yadda na so yau ba zan kunna wayata gabaɗaya ba amma na kasa, wajen tara da mintuna na ɗauko na kunna cikin dokawar zuci. Bayan na kunna data direct Whatsapp na shiga na duba group ɗinmu. Duk yawan messages ɗin da na tarar sai da na bi ɗaya bayan ɗaya na ga babu inda aka yi maganata, kuma da Maman Nasmah aka sha duk hirar da aka yi. Ƙaƙƙafar ajiyar zuciya na sauke, don ni duk a tunanina za ta faɗa musu ta zo gidana ta ga ni matar talaka ce. Fita na yi ba tare da na ce ƙala ba, duk da na gagga an yi cikiyata.
Ta private na ga Maman Nasmah ta mini saƙo har uku, cikin faɗuwar gaba na buɗe. Na ga ta ce. Ta kikkira ni a kashe, da fatan lafiya. Na ce mata lafiya ƙalau. Ina mamakin yadda kodayaushe tana online, ko dan su ƴan gata ne komai sai dai a yi musu? Ba kamar mu da muke wuni cikin wahalar ayyukan gida ba. Ta mun reply da. 'Masha Allah.' Danne zuciyata na yi na ce mata da fatan ta je gida lafiya? Ba ta ba ni amsa ba, sai ta kira ni. Na ɗaga cikin mutuwar jiki, ji na nake kamar wadda ta yi wa Sarki ƙarya aka kama ta. Sallama ta mun na amsa Idanuna cike da hawaye.
"Allah ya sa ba kya tare da baban Sultan na kira ki da daddare."
Na ce. "Eh ba ma tare." Ta ce. "Har Salamatu ta faɗa miki na kai mata atamfar kenan? Don ni tun kafin na ƙarasa gidan nata nake kiran wayarki a kashe, ko tana da wani layin naki ne?" Maimakon na yi murna Maman Nasmah ba ta gane ni ce ba sai na ji saɓanin haka, wato tsabar a mawuyacin halin da ta gan ni da mai aiki na yi mata kama? Cikin danne kukan da ya taho mini na ce. "Ai ni kika tarar ba Salamatu ba." Ban san me ya sa na ji na zaɓi kawai na faɗa mata gaskiya ba. Kamar za ta fasa mini dodon kunne saboda ƙaraji na ji ta ce. "What? Ke kuma Namecy? Ke ce wannan matar duk a yagule a wahale?" Hawaye na zuba daga idona na ce. "Ni ce."
"Taɓ! Amma gaskiya jin ki ya fi ganin ki, muryarki mai daɗi da sanyi babu wanda zai yi tunanin a wannan gidan kike rayuwa gaskiya, I'm sorry idan kin ji babu daɗi, mamaki ne ya kusa kashe ni."
"Babu komai, shi ya sa na kasa bayyana muku wace ce ni saboda kar a raina ni." Na faÉ—i haka cikin son wanke kaina.
Ta ce. "Kin yi farar dabara kam, don aka gane haka kike ba ƙaramar wulaƙantacciya za a mayar da ke ba, Allah ya taimake ki mun haɗu kafin ranar taro." Na ce. "Taimakon me? Ai yadda kika gan ni su ma haka za su gan ni ranar." Ta ce. "Haba, never kina da ni ki je a haka, zan aiko miki mayukan shafawa masu tsada wanda za su gyara miki fata kafin ranar, da turaruka da sabulan wanka, da jaka da mayafi da takalmin da za ki saka ranar, ke har da sarƙa da ɗan'kunne gold da kuɗin da za ki yi liƙi a gurin. Kina da ni ai ba za ki taɓa kunyata ba ƙawata." Wani tsalle na doka daga zaunen da nake ina jin kamar an yaye mini duka damuwata na ce. "Gold fa kika ce?" Ta ce. "To mene ne a ciki? Me aka yi aka yi wani gold? Ke dai kawai ki kwantar da hankalinki tawan, har gurin makeup zan kai ki a yi miki." A rikice na ce. "Wayyo daɗi, kamar kuwa kin san tunda aka fara maganar taron nan tunanin yadda zan yi na fito fes kawai nake yi, na god..."
"Babu godiya a tsakaninmu ai Namesy, kin fi ƙarfin komai a gurina, da kin faɗa mini ma tun da ai da ba wannan zancen ake ba, wani tunani ne ma ya faɗo mini yanzu a rai, kawai zan haɗa ki da mai mun gyaran jiki ta yi miki na amare na sati ɗaya, yadda za ki fi yin kyau da sheƙi ranar taron, har ƙunshi ma za ta yi miki." Ƙasa jurewa na yi na tashi da wayar ƙare a kunnena na fara taka rawar murna, da na san haka Maman Nasmah take da kirki kuma take so na da tuni ba na faɗa mata gaskiya ba. Tsabar farinciki rasa abin cewa na yi. Sai da ta ce ko ba na jin ta sannan cikin dariya na ce. "Farinciki ne ya hana ni magana." Ta ce. "To za ki je gyaran jikin na kira ta yanzu na sanar mata?" Na ce. "Me zai hana? Ubangiji ya so ni da rahama na butulce." Ta ce. "Okay, amma tun safe sai dare za ki koma gida fa." Da sauri na ce. "Kai! Duka satin kuma?" Ta ce. "Eh, mene a ciki?" Na ce. "Baban Sultan ne da ƙyar ya yarda gaskiya." Ta ce. "Saboda ba ya son ci gabanki? Bai ba ki kuɗi kin yi ba kuma za ki yi ya hana ki? Idan kika yi kyan ai shi ma zai ji daɗi, ki ce masa gyaran jiki ne ba wani abu ba." Na ce. "Duk da haka, da ƙyar ya bari, na san halin shi, zai ce ga yara ga kula da gida ba zan fita na wuni a waje ba." Ta ce. "Caɓdijan! Gaskiya matan talakawa kuna ƙoƙari, ko da yake da ma an ce talaka akwai baƙar zuciya da mugunta. Ni mijina duk inda na ce masa zan je ba ya hana ni, kuma ya ba ni kuɗin da zan yi amfani da shi ko nawa ne. Sorry sis, amma kuna ƙoƙari fa, ga talauci ga mulkin mallaka." Numfashi na sauke kamar zan yi kuka na ce. "Hmmm, to ya za mu yi?" Ta ce. "Ai ni ba zan iya ba, kuma ku ma har da laifinku, ku kuke nuna musu lako-lako tun farko, miji ba wata uwar yake muku ba, amma ku yi ta yi musu biyayya, yanzun dai duk yadda za ki yi ki samu ki je gyaran jikin nan gaskiya, idan ba haka ba ranar taro ki tashi kamar almajira a cikinmu, idan kuma ki ka ƙi zuwa kowa zai gano ki, saboda da ma ana ta complain kwana biyu kin ja baya a group, ni kankaro miki mutunci nake son yi. Da safe zan faɗa miki yadda muka yi da mai gyaran jikin na tura miki address ɗinta." Daga haka muka yi sallama ta katse wayar.
Tagumi na rafka ina bitar maganganun Maman Nasmah, musamman na ƙarshe. Wato mu matan talakawa mu ne a wahale? Mu mazaje suke takurawa, su kuwa komai suke so barin su ake yi su yi, ga kuma rayuwar ƴanci da wadata. Na san Anas da bala'in kulle, abu in ba na dole ko na dangi ba bai fiya bari na zuwa ba, ya fi son duk inda za ni mu je tare saboda kishin tsiya, shi ya sa nake ta tunanin ta yadda zan faɗa masa zuwa wannan taron namu, ga kuma gyaran jiki da ya kunno kai, amma dai zan fara tambayar shi na ji abin da zai ce, idan ya hana ni na yi ficewa ta, don gaskiya Maman Nasmah ta faɗa, mu muke yi musu lako-lako, shi ya sa suke mana yadda suka so.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.