Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Yiwa_Kai_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 14 of 34
*Zeey Kumurya*âœï¸
[3/8, 1:39 PM] BahaushiyaðŸ‘: *YI WA KAI*
MIKIYA WRITERS ASSOCIATION
*BRIGH PENS*
(FREE BATCH)
12.
Tamkar saukar aradu da ka haka na ji furucin nasa a tsakiyar kaina, wani irin abu mai zafi da zugi ya baƙunci zuciyata. Lokaci ɗaya na nemi zafin marin da ya mini na rasa, saboda wanda nake ji a cikin zuciyata sakamakon sakin da ya mun ya ninninka shi. Da ma haka sakin yake? Haka mata suke ji idan aka yi musu shi ko da su suka nema? Ji na yi duniyar tana juya mini, na daina fahimtar komai na wucen gadi. Sama-sama na ji muryar Naja ƙawata da ban san lokacin da ta shigo gidan ba tana rafka salati, tare da ƙarasowa ta kama ni a inda na ƙame kamar mutummutumi ta shigar da ni parlour ta zaunar a kan kujera. Ko da wasa ban taɓa tunanin ko me zan yi wa Anas zai iya saki na ba, na ɗauka ko da zan dinga yankar naman jikinsa ina gasawa saboda azabtarwa ba zai iya rabuwa da ni ba, saboda matsananciyar soyayyar da na san yana mini. Numfarfashi kawai nake yi. Naja da ke riƙe ni har lokacin tana sallallami ta ce. "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Hafsah me ya faru? Me ya haɗa ku da Abban Sultan? Don Allah ki ce abin da suka ziyarci kunnena lokacin da na shigo gidan nan ƙarya ne, kunnen nawa ne bai ji mini daidai ba." Girgiza kaina na yi ina hawaye na ce. "Daidai ki ji Naja'atu, kuma ni na buƙaci hakan da kaina." Ja baya ta yi a ruɗe ta ce. "Subhanallahi! Me ya yi zafi har haka ke kuwa? Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Da na san abin da zan tarar kenan da wallahi ba zan zo ba." Gimtse baki na yi tare da share hawayena na ƙwace daga riƙon da ta yi mini na dafe kaina tare da lumshe idona. A hankali a hankali na ji zafin sakin yana raguwa daga cikin raina, ina kallon Naja da ta ishe ni da tambayar sanin ba'asi na ce. "Me ya sa kika damu ne haka? Mene a ciki don na rabu da Anas?" Kallon mara hankali ta mun ta ce. "Ba don na gan ki fes kin ƙara fresh da kyau ba da sai na ce kina cikin mayen hauka ne, na zo na tarar da ku cikin tashin hankali ke da mijinki har ya sake ki sannan kuma ki ce me ya sa zan damu?" Murmushi na yi don a yanzu ba ta Anas da sakin ya yi mini nake ba, duk da ina jin ɗacin abun matuƙa a cikin raina, taron da za mu yi gobe da abin da zan saka shi ne kawai danuwata.
"Me ya sa idan na kikkira ki ba kya É—agawa? Idan na yi miki magana a Whatsapp ba kya dubawa bare ki mun reply?"
Hararar ta na yi na ce. "Saboda kin gama kunce mini zani a kasuwa mana, na yi ƙarya da ke amma kika ce wa Anas ba ki san zancen ba." Gyara zama ta yi ta ce. "Shi ne dalilin da ya sa nake ta kiran naki ai, na ji dalilin da ya sa kika aikata hakan." Baki na taɓe na ce. "Ya riga ya wuce ai." Na ƙarashe maganar ina miƙewa don fara haɗa kayana na bar wa Anas akurkin gidansa. Naja da har lokacin na lura a cikin ruɗu take ta kamo hannuna kamar za ta yi kuka ta ce. "Hafsah kin bar ni a cikin duhu fa, don girman Allah ki faɗa mini abin da yake faruwa, na ga kin ware kamar ba wadda take cikin zullumi ba." Komawa na yi na zauna don na labarta mata duk abin da yake faruwa, saboda Naja ta wuce ƙawa ko aminiya a gurina, ta zamo ƴar'uwa da ba zan iya ɓoye mata komai nawa ba. Cikin takaici na ce. "Naja Anas ba so na yake yi ba kamar yadda yake pretending, na yi da na sanin auren shi." A zabure ta ce. "Kamar ya? Ban gane ba?" Tsaki na ja na ce. "Matan da mazajensu suke son su, suke yi musu duk abin da suke so a lokacin da suke so bayan wadata su da suka yi da komai na more rayuwa suna can daban, amma ni ko kusa ba na cikinsu, ba na cikin mata masu sa'a da ake kwatance da su, ake sha'awar su, ake burin samun mazaje irin nasu." Na ƙarashe maganar kamar zan fashe da kuka. Galala ta yi tana kallo na ba ta ce komai ba. Numfashi na sauke na ce. "Ba ki gane me nake nufi ba ko? Yanzu zan ganar da ke." Ban jira amsarta ba na kwashe labarin komai na faɗa mata. A matuƙar gigice na ga ta miƙewa kamar wadda na faɗawa ranar mutuwarta, tana nuna ni da hannu ta ce. "A'uzubillah! Hafsah da ma ba ki da hankali? Ashe mahaukaciya ce ke ban sani ba?" Haɗe rai na yi na ce. "Haukan uban me na yi?" A fusace ta ce. "Ban sani ba, wallahi ba don na kai zuciyata nesa ba da sai na kikkifa miki mari, kamar na rufe ki da duka haka nake ji, I'm speechless! Na rasa me zan ce miki, innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!" Ta ƙarashe maganar tare da dafe kanta. Tsaki na ja ban ce komai ba. Komawa ta yi ta zauna tana bi na da wani irin kallo, idanunta cike da hawaye ta fara magana da faɗin. "Ko a mafarki aka ce mini za ki aikata wannan tafkeken haukan da jahilcin ba zan taɓa yarda ba, yaushe kika haukace Hafsah? Yaushe kika daina amfani da ƙwaƙwalwarki wajen yin al'amuranki? Ina iliminki na addininki yake? Kin watsar saboda son duniya da hangen dala ko?" Shiru na yi ban ce komai ba. Kamar za ta rufe ni da duka ta ce. "Kin ba ni matuƙar mamaki da kunya, akan wani banzan group kika bari salihin miji irin Anas ya yi miki har saki biyu? Saura igiya ɗaya fa a tsakaninku yanzu? Saboda wasu tsinannu Hafsah!" Ta ƙarashe maganar cikin ƙaraji. Kallon banza na yi mata na ce. "Saboda sun haska mini abin da ban sani ba na rayuwa shi ne suka zama tsinannu? Ki yi mini duk zagin da za ki mini amma ban da su, don ni sun gama yi mini komai a rayuwa."
"Sun gama kam, tunda sun cuce ki sun kashe miki aure, su kuma suna can zaune lafiya ƙalau da mazajensu." Naja ta faɗa tana jifa na da wani mugun kallo. Cikin tsagalgala na ce. "Ai su mazajensu ba talakawa ba ne, kuma da ma irin gidajensu ai ba a fatan a fita." Ta ce. "Haka ne, duk da na ga alamar kin yi nisa amma ba zan ƙi faɗa miki gaskiya ba, da tunatar da ke abin da gidahumar ƙwaƙwalwarki ta mantar da ke ba. Hafsah tun kina ƴar ƙarama a zanin goyo mahaifinki ya rasu, mahaifiyarki kuma bayan kin ɗan girma ba ki fi shekara uku ba ita ma ta bi bayan shi, daga lokacin aka dawo da ke gurin Kawu ya riƙe ki. Kawu ya yi miki riƙo na tsakani da Allah tamkar ƴar da ya haifa a cikinsa, kuma ya nuna miki soyayya saboda bai taɓa haihuwa ba, sanadiyyar hakan Gwaggo matarsa ta tsane ki, ta gana miki azaba. Ba sai na tuna miki irin uƙubar da kika sha a gurinta ba, saboda kin fi kowa sani. Yanzu idan kika bar nan kika koma gida a matsayin bazawara ya kike tunanin zamanku zai kaya ke da Gwaggo? Kina budurwa ma ba ta so ki ba balle a yanzu? Ko kin mata da wannan? Kuma idan ba gidan ba, ba ki da gurin zuwa, tunda dangin mahaifiyarki suna can Lafiya, tsakaninki da su waya ce ko chat, ba ki taɓa zuwa ba, su ma ban da lokacin bikinki ba su taɓa zuwa kun haɗu ba, can kike tunanin za ki je ki yi zawarcin a haka? Ba su saba da ke ba, ba ki taɓa zuwar musu ba, kawai sai su gan ki rana tsaka ki ce musu aurenki ne ya mutu kika koma? Ki yi aiki da hankalinki ki yi tunanin abin da zai fishshe ki, takamaiman gurin da za ki je ki zauna ma ki ji daɗi ba ki da shi idan kin bar nan ɗin, amma a haka kika kashe aurenki?" Shiru na yi don maganganunta sun fara ratsa ni, amma duk da haka ba su saka na ji zan saduda ba. Ganin haka ta ci gaba da magana da faɗin. "Abu na biyu kuma, samun mijin da yake son ka tsakani da Allah ma kamar yadda Anas yake son ki a wannan zamanin wahala yake, ya so ki tun kina ƴar ficiciyarki, ba ki san kanki ba, bare ki yi kwalliya da za a ce ita ta ja hankalinsa gare ki, kuma a lokacin ko alamar zama budurwa ba ki fara ba, bare ya ce ya ga kyanki ko jikinki ya so ki don su, hasalima a cikin rayuwar wahala da ƙuncin rayuwa ya gan ki, ya fara da jin tausayinki daga nan ya rikiɗe ya koma soyayya. Babu gatanta kin da bai yi ba tun kina gida har zuwa aurenku daidai ƙarfin ikonsa. Soyayya, kulawa, darajawa, babu wanda bai nuna miki ba. Ya taya ki aikin gida, ya kai ki unguwa da kansa, ya ɗauke miki dukkan wata ɗawainiyarki, da kika haifi ƴaƴa bai canza miki ba kamar yadda wasu mazan suke yi, ya rungume ku ke da yaranki kuka ci gaba da rayuwa cikin farinciki da annushuwa. Anas bai taɓa ragar ki da komai ba, to me kike nema a gurin miji da ya fi wannan? Me kike da buƙata? Ke ba matsalar kishiya, ba ta uwar miji, ba ta ƙannensa ko yayye ba, miji ba ya dukanki, ba ya cin mutuncinki bare zagi. Amma saboda hauka ki dinga hangen na wasu can da ba ki san irin taskun rayuwar da suke ciki ba, wallahi Maman Sultan daɗi ne ya yi miki yawa, da kuma kin samu Anas ɗin mai haƙuri. Da ma an ce samu mai saka hauka." Baki na zunɓura na ce. "Hmm, duk waɗannan bayanan naki kin san dai na fi ki sanin da su ko?" Ta ce. "Eh, amma ba kya duba su ai." Na ce. "Eh, saboda ni yanzu ba su ne a gabana ba." Naja da take jin kamar ta rufe ni da duka ta ce. "Ƙaton gida da hawa manyan motoci su ne a gabanki ko? Ki faɗa mini matar da kika sani da always mijinta ne yake saka mata data da katin da za ta yi waya, idan za ta je unguwa ko'ina ne ya ba ta transport, na tabbata da za ki cikiya kafin ki samu ɗaya sai kin samu 50 da ba a yi musu. Ke fa tsabar daɗi ko sana'a ba ki taɓa gwadawa ba, saboda ba ki da buƙatar komai, yi miki ake kina daga kwance ƴar gata. Kuma ko ma ba wannan ba, kwanciyar hankali ya fi komai a rayuwar nan, ka ci ka sha, ka yi ibada ba wani tension ka yi baccinka, me ya fi wannan daɗi? Anas shi ne gatanki, shi ne suturarki, shi ne rufin asirinki, ko kaffara ba zan yi ba idan kika rabu da Anas ba za ki taɓa samun miji kamar shi ba, don irinsu a yanzu ba su da yawa, sun yi ƙaranci." Da sauri na ce. "Zan samu wanda ya fi shi mana, sosai ma." Murmushin takaici ta yi ta ce. "Ban san lokacin da kika koma mayyar kuɗi ba, idan kuɗi kike nufin za ki samu wanda ya fi Anas za ki samu sosai ma, amma samun mai nagartar shi ne zai yi miki wahala. Ana cewa mazan aure sun yi ƙaranci, ba ƙaranci suka yi ba, samun nagari nagartacce ne ya yi wahala. Kin gan ni nan, ban rasa mijin aure wanda zai aure ni ba, amma na rasa nagartacce wanda nake da yaƙiyin zai riƙe ni saboda Allah ya kyautata mini, wanda ya san ma mene ne auren, don matsalar da take damun mu yanzu majority ana auren ne kawai ba don an san mene ne shi ba, ba don an ɗauke shi ibada ba, ana yin shi ne don wata buƙata, ko a bi kyau, ko kuɗi, ko neman ɗaukaka, ko dan a ce mutum ya yi auren shi ma, gabaɗaya ba ga matan ba, ba ga mazan ba, duk an daina aure saboda Allah da bauta masa, ƙalilan ne masu yi don haka. Wasu kuma ilimin zaman auren ma da yadda za su tafiyar da junansu a zamantakewar auren ne ba su da shi. Rimi-rimi za ki ga mutum ya zo mini da gaske da niyyar aure, amma daga mun yi dogon zama zan gane ba za mu zauna inuwa ɗaya ba, masu kuɗin da masu kyan da talakawan duk suna zuwa, amma samun nagartaccen a ciki ya yi wahala, saboda Juma'ar da za ta yi kyawu tun daga Laraba ake gane ta. Maza na gari sun yi wahala Hafsah, ki riƙe mijinki gagam wallahi, idan ba haka ba za ki yi da na sani mara amfani, za ki yi nadama a lokacin da time ya ƙure miki, za ki yi saki na dafe. Yanzu da za ki yi shela ki fadi halin Abban Sultan ki ce idan da mai son shi za ki bari ta aure shi sai kin ga mata dubu sun zo, kuma da kike ta cewa talauci ai shi ba talaka ba ne, yana da rufin asirinsa, bai taɓa gazawa ba tunda kuka yi aure. Na ga gidan hayar da kuka fara zama kafin Allah ya hore masa ku yi naku, abokan hayar taku sha'awar ku suka dinga yi, yadda yake kula da ke da tattalin ki, ya ba ki lokacinsa. Mama kullum cikin sam barka take yi miki, kullum aka tashi zance aka ce maza sun zama ƴan kansu yanzu sai ta bayar da misali da ku, ta ce ƙawar Naja kuwa ta yi dace da mijin marainiya, Allah ka ba wa ƴaƴanmu irinsa." Baki na taɓe don ni gabaɗaya hankalina yana kan yadda za a yi na fito fes a taronmu na ce. "Sai faɗar alkhairinsa kike amma ban ji kin faɗi aibunsa ko ɗaya ba, mutumin da yake zuba mun uban kulle, kamar wata kayan kadara." Numfashi ta sauke ta ce. "Alkhairin nasa ne ya fi aibun yawa, kulle kuma tabbas na san yana da shi, kuma da ma ai ɗan Adam tara yake bai cika goma ba, amma duk da haka ai ba ya hana ki zuwa biki ko sunan dangi da na maƙota, duk abin da ya faru na jaje yana barin ki, ki je, fita ce haka barkatai babu dalili yake hanawa, ko so kike ya bar ki kina wuni a maƙota da gantali a unguwa?" Hararar ta na yi na ce. "Ban sani ba, tunda ba ke ake turkewa a gidan kamar akuya ba ai dole ki ce haka. Nan gidan Maman Sadik ga baki ga hanci, jikin gidana amma sai na yi watanni ban je mata ba, tun suna shigowa su har sun gaji sun daina saboda ba na zuwa."
"To me za ki je ki yi musu? Na ga Asma'u cousin É—ita da suka zuna a bayan layin nan yabon ki ta dinga yi, lokacin da aka yi wani faÉ—a har da zuwa police station, a saboda irin yawon gulmace-gulmacen nan da ake yi na bin gidan maÆ™ota kullum, ta ce kin huta abinki, ko me za a yi na tashin hankali babu ke a ciki, asirinki a rufe. Amma ke kin raina hakan ko?" Na ce. "Ai shi saboda kar na fita na ga halin da duniya da take ciki ne ya sa yake kullen, kar kuma na ga yadda maza suke bauta wa matansu tunda shi ba ya yi." Naja ta ce. "Ko? To kar ki nutsu ki san inda yake yi miki ciwo, duk da zan yi miki uzurin rashin sanin halin da duniya take ciki, na rayuwar Æ™arya da packaging da mutane suka É—aura wa kansu, shi ya sa kike ganin kamar su waÉ—ancan matan komai gaskiya suke faÉ—a. Tunda babbar wayar ma ba ki daÉ—e da fara riÆ™e ta ba." Cikin Æ™osawa da jawabanta na ce. "Su fa ba maÆ™aryata ba ne, saboda sun sassan gidajen juna suna zumunci, idan Æ™arya suke ai ba za su bari a je inda suke ba." Jinjina kai ta yi ta ce. "Ni fa ban ce ba masu kuÉ—i ba ne, amma ba zai yiwu a ce duka group É—in ke kaÉ—ai ce talaka kamar yadda kike faÉ—a ba, kuma masu kuÉ—i wanda suka tashi a cikinsa ba za su yi irin wannan banzar rayuwar ba, ta komai naka sai ka tura a group an gani, ka yi son a sani, sai dai ko Æ´an taka haye ne Æ´aÆ´an Malam Shehu suka auri masu kuÉ—i, shi ne ba a saba da rayuwar ba ake nuna wa duniya, ko kuma duk packaging ne kashe kai ake a yi abin Æ™aryar. Kuma ko da ma masu kuÉ—in ne kina da tabbacin kowacce tana zaune lafiya cikin kwanciyar hankali kamar ki? Wata Æ™ila mijinta mai duka ne, wani É—an shaye-shaye, wani mai bin mata ko maza, wani ma kuÉ—in ba na halak ba ne, ba ki san ta yadda suke samun su ba." ÆŠaga mata hannu na yi na ce. "Kar ki yi musu mugun fata kuma." Murmushi ta sake yi ta ce. "Misali kawai nake ba ki, ba wai ina nufin hakan ba ne, kawai dai ina faÉ—a miki ne don na san ba za a rasa ba. And lastly yanzu Æ™warya ta bi Æ™warya ake yi, idan kina tunanin za ki kashe aurenki ki fita ki auri mai kuÉ—i to kin yaudari kanki, don kowa É—an'uwansa yake aure, talaka sai talaka mai kuÉ—i sai mai kuÉ—i, sai dai ikon Allah da tsananin rabo ne yake saka mai kuÉ—i ya auri talaka." MiÆ™ewa na yi a fusace na ce. "Ya ishe ki haka wannan cin fuskar da kike mun!" Ita ma miÆ™ewar ta yi ta ce. "Idan na ci miki fuska ai kaina na ciwa Hafsah, gaskiya nake faÉ—a miki, kuma da ma an ce É—aci gare ta, ki zauna, ki nutsu, ki yi nazari da kyau don Allah, ko don Æ´aÆ´anki da ke kanki. Zan kira Anas mu yi magana da shi idan na koma gida, zan ce masa ni na hana ki tafiya, na san ba zai Æ™i mayar da ke É—akinki ba in sha Allah. Duk da na ga ransa a matuÆ™ar É“ace ya bar gidan nan lokacin da na shigo, don ba na jin ma ya lura da ni. Please Æ™awata ki watsar da mutanen can, ki manta da su, ki bar group É—in ki goge numbers É—insu, ke ki canza sim ma gabaÉ—aya yadda ko sun kira ba su same ki ba, idan ba haka ba wallahi za su kai ki su baro." Na ce. "Na ji na gode." Bi na kawai ta tsaya tana yi da kallo na wasu sakanni. A sanyaye ta ce. "Idan kika bar Anas ba shi kaÉ—ai kika butulcewa ba, har da ubangijin da ya tsamo ki daga cikin jarrabawar rayuwa, ke kuma kike Æ™oÆ™arin siyen ta da kuÉ—inki. Kina da iliminki na addini daidai gwargwado, kin san arziÆ™i da talauci duk na Allah ne, a kullum Ubangiji cikin raba arziÆ™i yake da Æ™wace shi, babu wanda aka haifa da dukiya, kowa da kika gani a nan gidan duniya ya samu kuma a nan zai bar shi. Don haka wannan kaÉ—ai ya ishe ki darasi a rayuwa. ƳaÆ´a da miji na gari da lafiya su ne babban arziÆ™i a duniyar nan, kuma duk Ubangiji ya ba ki su, maimakon ki gode masa sai ki raina?" Shiru na yi don zuwa yanzu maganganunta sun fara ratsa ni sosai, ganin haka ta dafa kafaÉ—ata ta ce. "Zan tafi, ina fatan za ki yi amfani da dukkan shawarwarin da na ba ki, sannan kuma don girman Allah kar ki Æ™ara kwatanta haukan zagin Anas, bare ki taÉ“o iyayensa, ina jiye miki siyen ticket É—in wutar jahannama da hannunki, tunda kin san hukuncin mai aikata abubuwan da kike yi a musulunci. Don haka idan kunne ya ji jiki ya tsira!" Daga haka ta É—auki jakarta ta juya ta fice. Kasa kataÉ“us na yi na bi bayanta da kallo kawai cikin mutuwar jiki, gabaÉ—aya ta gama É—aure ni da jijiyoyin jikina. Na shafe kusan mintuna biyar kafin na ja Æ™afata na shiga É—aki. Ringing na tarar wayata tana yi, na Æ™arasa na lalubo ta na duba na ga har kiran ya katse, missed call sama da 10 na tarar na Maman Nasmah. Ban yi yunÆ™urin bin ta ba don na san ban da ishashshen katin da za mu yi doguwar magana. Wani kiran nata ne ya Æ™ara shigowa, tsayawa kawai na yi na Æ™ura wa wayar ido, zuciyata na kokwanton na É—aga ko kar na É—aga? Na bi shawarar Naja na fita daga group É—in na manta da su na ci gaba da rayuwata kamar da, ko kuma na ci gaba da zama a cikinsu da burin kasancewa kamar su ko ta halin yaya?........âœï¸
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.