Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Yiwa_Kai_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 33 of 34
Kawu da ke riƙe da takardar sakin bayan na yi masa bayani ya ja gwauron numfashi ya ce. "Na rasa abin cewa saboda tsabar kiɗima, abin da zan ce kawai Ubangiji ya ba mu ikon cinye wannan jarrabar gabaɗayanmu, Allah ya sa haka shi ya fi alkhairi, ya tsayar iya haka." Na ce. "Amin, Kawu har yanzu ba a kawo su Sultan ba ko?" Ya ce. "Hmm, sai haƙuri, jarrabawa ce, ki ta addu'a kawai kar ki gaza, fatanmu kawai Allah ya sa suna cikin kulawa da ƙoshin lafiya." Cike da kewa da ƙaunar ƴaƴana na ce. "Amin."
Sosai nake cikin farincikin yar da ƙwallon mangwaron da na yi na huta da ƙuda, ina jin Gwaggo tana ta ya da habaici amma ban bi ta kanta ba. Juyi na yi a kan tabarmar da nake kai ina ji na sakayau, gabaɗaya damuwar da ke danƙare a cikin raina ta tafi. Ɗanmitsitsin ɗakin da nake ciki a yanzu mai ɗauke da tarkace ya fi mini tangamemen da na baro mai cike da kayan alatu.
Ban san da bakin da zan gode wa Kareema ba, na wannan farar dabarar da ta samar mini. Ban taɓa zaton kuma abun zai zo da sauƙi haka ba, duk da na san addu'ar da na dage da ita ba dare ba rana ce ta sanya Ubangiji ya taimake ni ya ba ni nasara.
Wajen ƙarfe goma Kareema ta kira ni, bayan mun gaisa ta ce. "Ya kike je gida?" Na ce. "Lafiya ƙalau Alhamdulillah, na gode na gode, na rasa ma abin da zan ce miki saboda farinciki." Dariya ta yi ta ce. "Babu komai ai,kar ki damu, ni kaina nan murna nake yi miki ba kaɗan ba, barkanki, kin tsallake rijiya da baya, wai yaushe ma ya dawo ne?" Na ce. "Yau fa, ga shi cikin ikon Allah an yi komai an gama, gaskiya kina da basira sosai, ni ina zan yi tunanin yin haka? Kuma abin da ya ba ni mamaki yadda bai musa ba, ko record ɗin ma ban saka ba ya amince ya yi sakin." Ta ce. "Ai ya san dalili, ya riga ya gane ke kika haɗa komai, shi ya sa ba zai ce ƙala ba." A raunane na ce. "Allah ya sa kar ya ce zai yi mini wani abun da zai cutar da ni a matsayin ɗaukar fansa."
"In sha Allah babu abin da zai iya, ai kuma an riga an gama, wata mai tsautsayin kawai zai nema ya ƙara aura, ba ni labarin yadda lamarin yakasance, ya aka yi ya sha drink ɗin ne?"
Kwashe labarin komai na yi na ba ta.
Cikin dariya ta ce. "Amma ke ma fa kina da wayo, kin yi ƙoƙari sosai, ga kukan da kika yi kamar gaske, gaskiya za ki iya acting, kamar a Film fa." Dariya na yi na ce. "Mene ma ba zan ba, yadda nake gudun mutuwata haka nake gudun gidan nan, ba ki ji yadda nake ji na ba yanzu, farinciki mara misaltuwa." Ta ce. "Ma sha Allah, Maman Hanif ta ɗauka ƙin sakin kike da gaske, ta damu sosai." Na ce. "Allah Sarki baiwar Allah, mijinki fa? Ya san komai?" Ta ce. "Eh, na ɗan tsakura masa, shi ne ya ce mu je ba matsala, ya san me zai masa da ba zai kawo komai a ransa ba, ban san ya aka yi ya san yau ya dawo ba, amma na fi tunanin maigadi ya tambaya kamar yadda ya faɗa." Na ce. "To an gode, kun yi jihadi Allah ya ba da lada." Ta ce. "Amin ya hayyu ya ƙayyum, wannan miji naku ai ba na zama ba ne, Allah ya raba mu da zuri'armu da irinsu." Na ce. "Amin." Daga haka muka yi sallama ta ce da safe ma yi waya.
Daren wannan ranar shi ma ban runtsa ba, na dinga tunanin Anas da kulawar shi a gare ni, duk yadda na so kawar da tunanin amma na kasa. Na dinga tambayar kaina me kuma zai faru da ni a gaba? Wacce irin rayuwa zan shiga kuma? Zawarci ko kuma wani auren zan yi? Na yi auren kuɗin amma gara gidan talatan da na guda sau dubu a kansa, amma duk da haka har yanzu ina nan da burina, musamman idan na tuna maganganun Maman Hanif da ta ce masu kuɗin na gari suna nan da yawa, ko dan kar a ce na ci baya ba zan auri talaka ba a gaba, sai mai hali amma sai na zaɓa na darje da na ƙwarai. Kamar mafarki na yi na farka haka nake ganin aurena da Idonnera, na saka a raina ko a cikin masu kuɗin shi ne ba na gari ba, wataƙila a gaba na yi dace. Har Faisal da ban san lokacin da ya bar gidan ba sai da na tuno. Addu'ar fatan shiriya na yi musu na watsar da lamarinsu.
Washegari da safe Gwaggo Habi ta zo ta dinga yi mini faɗa kamar za ta dake ni, da kaicon barin da na yi mai kuɗi kamar Idonnera ya sake ni, ban ji nauyinta ba na ce ba shi da lafiya ne, don ko idda ma ban da ita a kaina. Da ta ji haka ne ta sauko, amma duk da haka sai ta ce ban da jaraba irin ta yaran zamani da na zauna a hakan ai, tunda ga kuɗi ba sai na yi haƙuri ba. Na ce shi ya sauwaƙe mini da kansa saboda kar ya dinga cutar da ni.
Wajen azhar sai ga direba da kayan sakawata niƙi-niƙi, wai Alhaji ne ya aiko shi da su. Hakan ya ƙara kwantar mini da hankali, na tabbatar ya haƙura kenan, na yi nasara.
Da daddare ina zaune na yi tagumi ina tunanin rayuwa da yadda ta zo mini kira ya shigo cikin wayata. Ko kallon ta ban yi bare na É—auka, Æ™ishirwar son ganin Æ´aÆ´ana ita ta fi komai damu na a yanzu, na yi mamaki sosai da har yanzu Anas bai kawo su ba, ji nake kamar na tafi Æ™auyen nasu na je na gano su. Gefe guda kuma ina tunanin inda Maman Nasmah ta shiga da ta yi wannan É“atan dabon, ba Æ™aramin son mu haÉ—u na ba ta labarin abubuwan da suke faruwa nake yi ba. Ganin an Æ™i daina kiran ya sa na janyo wayar na duba, baÆ™uwar number ce, hakan ya sa na É—an yi jim kafin na É—aga bakina É—auke da sallama. Muryar Alhaji Mansur na ji ba tare da ya amsa ba yana faÉ—in. "Sannu Æ´ar matsiyata, kin yi Æ™oÆ™ari fa sosai da tarkon da kika haÉ—a mini, ga shi kin yi nasara ya kama ni. Na daÉ—e ina mamakin yadda aka yi kika iya Æ™irÆ™irar wannan dabarar, to abin da na kira faÉ—a miki shi ne, har yanzu a tafin hannuna kike, kuma tanadin uÆ™ubar rayuwar da na tanadar miki da Æ™uncin da zan saka ki a ciki sai kin ji gara zaman gidan nawa da kike gudu sau miliyan da shi, don haka ki shirya, sai kin yi nadama da danasanin rainin hankalin da kika yi mini. Sai na wulaÆ™anta rayuwarki na É—aiÉ—aita ta, nan ba da jimawa za ki yi bankwana da farinciki na har abada. Ba ki da kowa ba ki da komai, bare ki samu mai tsaya miki, za ki gane kin tsokano tsuliyar dodo. Kuma ki sani duk inda za ki shiga a faÉ—in duniyar nan ba za ki taÉ“a tsere mini ba, ko'ina sai na saka an Æ™waÆ™ulo mini ke. Bayan na gama illata ki na saka a bazar da ke, kin fi kowa sanin ba ki da wanda zai iya ja da ni a kaf danginku da mutanen da kika sani, bare ki yi tunanin kai ni Æ™ara." Ya ja tsaki cikin tsananin É“acin rai sannan ya ci gaba da faÉ—in. "Ba a taÉ“a raina mini hankali irin wannan ba, amma kanki kika yi wa ba ni ba, don ba zan taÉ“a bari ki Æ™ara wani jin dadi ba a rayuwarki har abada!" Daga haka ya kashe wayar........âœï¸
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.