Complete Hausa Novels

Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Yiwa_Kai_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 12 of 34

*Zeey Kumurya*✍️
[3/8, 1:38 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI*

*BRIGH PENS*
(FREE BATCH)

10.

Cak na tsaya kamar an kafe ni, don furucin a bakin aurenki da ya yi ba ƙaramin dukan zuciyata ya yi ba. Kamar na koma na fasa fitar, amma sai na ji ba zan iya ba, hakan ya sa kawai na ci gaba da tafiyata ba tare da na waiga ba, duk da na ji motsin fitowarsa tsakar gidan. Idan akwai abin da nake da tabbaci cikakke a kansa to shi ne son da Anas yake mini, na san ba zai taɓa iya rabuwa da ni ba, wannan maganar tasa ma ya yi ta ne kawai a matsayin hargagi, amma na san ba har cikin zuciyarsa take ba. Idan ma har cikin ran nasa ne matsalar shi ce ba tawa ba, don kamar yadda Maman Nasmah ta faɗa idan ina nuna ba na tsoron shi sai ya fi shayi na.
Na shafe kusan mintuna talatin kafin na ƙarasa gidan mai gyaran jikin saboda akwai nisa daga unguwarmu, ina zuwa babu ɓata lokaci ta fara gudanar da aikinta, ta na yi tana ba ni labarin kuɗin Maman Nasmah da na mijinta, don akan wannan gyaran jikin nawa ma sai da ta ninka mata kuɗin sau uku akan yadda take yi. Sai na ji ina ma ni ce ake labarin kuɗina da na mijina, na dinga addu'ar Allah ya nuna mini ranar ni ma zan zama irin haka, a dinga labarina da kwatance da ni. Sai yamma lis na baro gidan, matar tana ta yabon kyan fatata, ni kuwa gani nake murnar kuɗin da aka ba ta ne kawai ya sa take ta koɗa ni, babu wani kyan fata da nake da shi kamar yadda Maman Nasmah ta faɗa.

Yau Anas ko fita bai yi ba, takaici da mamakin Hafsah sun saka ya zauna yay ta tunane-tunane, hakan ya haifar masa da ciwon kai. Bai taɓa zaton zai ce wa Hafsah idan ta yi abu a bakin aurenta za ta aikata ba. Shi ya dafa musu abincin rana ya yi sauran aikace-aikacen gidan.
Sai bayan Magriba na koma gida, na tarar ba ya nan sai su Sultan kaɗai a parlour suna homework. Da gudu suka taso suka rungume ni, Sufyan ya ce. "Mami ina kika je? Muna ta neman ki, kin tafi kin bar mu." Kayan hannuna wanda Maman Nasmah ta aiko mini da shi na ajiye a kan kujera na ce. "Unguwa na je, ku ƙarasa aikin naku na ba ku kayan daɗi." Da murna ya koma ya ci gaba. Sultan ya ce. "Mami na zubo miki abinci? Abba ya dafa mana macaroni." Na ce. "To bari na shiga na ajiye kayan nan na fito." Sufyan ya ce. "Za ki biya mana karatu yau ko Mami? Idan mun iya ki yi mana tatsuniya irin na ranar nan." Na ce. "To." Kawai.
Sai da na yi Sallah sannan na baje kayan na dudduba, duk abin da ta lissafa za ta ba ni babu wanda ta manta ba ta sako ba, har da kuɗi 30k wai na transport zuwa gidan gyaran jiki, kuma ta ce gobe na tafi da atamfata za ta aiko a karɓa akai mini ɗinki. Ina ɗaga sarƙar gold ɗin da na shafe mintuna ina lailaya ta na ce. "Allah ka saka wa wannan mata da alkhairi, ka ba ni ikon faranta mata kamar yadda ta faranta mini a yau." Kamar zan zauce haka nake ji tsabar farinciki, na ƙara tabbatarwa Maman Nasmah masoyiyata ce ta haƙiƙa, don ta gama yi mini komai, tunda ta fitar da ni kunyar zuwa taron nan. Sai da na gama tsallena da rawar murnar daɗi na kira ta don na yi mata godiya, har lokacin kuma Anas bai dawo ba. Bayan mun gaisa ta ce. "Ya aka yi ya bar ki kika je kuma?" Ina murmushi na ce. "Shawararki na bi ai, na nuna masa bai isa ba, shi ne har da cewa idan na fita a bakin aure na." Maman Nasmah ta ce. "Gara da kika yi masa haka, ki ci gaba da ƙwatar wa kanki ƴanci, kar ki bari takaicin Namiji ya kar ki, namijin ma wani banza talaka da ko ɗawainiyarki bai gama iya ɗaukewa." Shiru na yi don ba na jin daɗin yadda take yawan zagin Anas da aibata shi, duk da wani lokacin idan na yi nazari gaskiya ta faɗa, amma mijina ne duk lalacewar shi, kuma ina son shi a haka.
"To da kika dawo me ya ce kuma?" Ta katse shirun nawa da faÉ—ar haka.
Na ce. "Ba ya nan na dawo, har yanzu kuma bai dawo ba." Ta ce. "To kar dai ki raga masa, ni shawara nake ba ki wadda za ta fishshe ki, don so nake na ga kina rayuwa mai inganci, idan ya faɗa miki ɗaya ki mayar masa da goma zafafa, kar ki ƙara yarda ki kuma irin rayuwar bayan da kuka yi da shi, wani ladabi da biyayya duk ki zubar da su a gefe, ki daina wannan aikin wahalar da na zo na tarar da ke kina yi kin yi ciɗin-ciɗin kamar wadda aka haƙo daga rami, yadda kika ga na zo gidanki haka nake zama kodayaushe a gidana, ina daga kwance masu aiki ne suke yi mini komai. To akan me zan kashe kaina? Haka kawai na yi baƙi watarana su gan ni a ƙazance, ai abin kunya ne." Na ce. "Haka ne, na gode sosai, zan yi duk yadda kika ce." Daga haka muka yi sallama na katse wayar. Kayan ciye-ciyen da ta kawo jiya shi muka ci ni da su Sultan, na yi musu wanka na kwantar da su, sai murna suke yau na ja su a jiki kamar yadda muka saba a da. Har wajen sha ɗaya Anas bai dawo ba, har na kwanta na ji na kasa bacci, don ba ya taɓa kaiwa haka a waje, bare kuma ya fita ba na nan ya bar yara kaɗai a gidan. Ina ƙoƙarin kiran shi a waya ya shigo. Kamar babu abin da ya faru na ɓacin rai a tsakaninmu kafin na fita haka ya mun magana, ya sanar mini jiran shagon dare ya yi wa mai gidansu tunda bai samu ya yi na rana ba. Ganin haka na nuna masa kayan da Maman Nasmah ta ba ni, amma ban da sarƙar gold ɗin, saboda kar ya yi magana. Bai nuna ɓacin ransa ba ya ce Allah ya sanya alkhairi. Na yi mamakin shi sosai, don na ɗauka zai yi mini bala'i ne.
Washegari da na ce masa zan koma gidan gyaran jikin bai hana ni ba, ya dai roƙe ni akan kar na yi dare irin na jiya, na ce masa in sha Allah. Sai da na yi abincin rana na kai maƙota da uniform ɗin islamiyyar su Sultan sannan na tafi. Tun ƙarfe bakwai na ga Maman Nasmah tana ta kira na, amma saboda aiki ban samu sukunin kiran ta ba, sai da na hau napep. Ta na ɗagawa ta ce. "Ya kuka yi da faƙirin mijin naki? Shi nake ta kiran ki na ji amma ba ki ɗauka ba." Cikin mamakin yadda yanzu kullum muka yi waya ko chat sai ta ji me yake wakana tsakani na da Anas na ce. "Me ya sa kika damu ne?" Ta ce. "Saboda ina son na ji halin da kike ciki mana na ba ki shawarar da za ta fishshe ki, ni fa tamkar ƙanwata da muke ciki ɗaya haka na ɗauke ki, kullum da ke kwana nake tashi, wannan mulkin mallakar da yake yi miki ji nake kamar ni ake wa wallahi." Cikin jin daɗi da ƙara yarda da soyayyar ta a gare ni na ce. "Allah Sarki ƙawata, to ki kwantar da hankalinki, don komai ya wuce a tsakaninmu ni da shi, ba ki ga yadda ya mun jiya ba, faran-faran, yau ma tare muka fito, bai hana ni ba." Kamar wadda ta firgita haka na ji ta yi magana da faɗin. "Ban gane ba! Bai ce miki komai akan daɗewar da kika yi ba?" Na ce. "Bai ce ba, kawai dai ya ce kar na daɗe yau."
"Kuma kin nuna masa kayan da na ba ki?"
Na ce. "Eh." Shiru na ji ta yi na wasu sakanni, daga baya ta ce. "Kin ga shawarar da nake ba ki ta yi aiki ko? Da kin ci gaba da yi masa lako-lakon nan da tuni jiya ya ƙare miki tijara, amma abin da nake so da ke kar hakan ya sa ki koma masa kamar da fa, idan ba haka ba zai ci gaba da juya ki kamar waina ne, yanzu kin saka masa tsoron ki a cikin zuciya, ya gane ko babu shi za ki iya rayuwa, tunda har ya yi miki barazana da saki kuma kika shallake, to haka ake yi wa maza a zauna lafiya da su, idan kuma kika ce za ki raga musu sai su mayar da ke baiwa, dabba ma ta fi ki daraja a gurinsu." Cikin gamsuwa da maganganunta na ce. "Tabbas haka ne, don da a da ne Anas ya hana ni abu na yi sai ya saɓa mini sosai, amma jiya har da haƙuri ya ba ni, ai na faɗa miki yana tsananin so na, ba zai taɓa iya rabuwa da ni ba."
"Yawwa, to ki yi amfani da wannan son ki gara shi kamar taya, ke ma ki shigo samun mu manyan mata isassu a gidajensu, za ki ga yadda zai na rawar jiki a kanki da yi miki biyayya."
Bayan mun gama wayar na yi shiru ina nazartar maganganun ta, tabbas duk abin da ta faɗa gaskiya ne, na yi kuma amanna da su, duk da na yi niyyar mu koma kamar yadda muke a da ni da Anas, don da ma dalilin da ya saka nake yi masa duk wani rashin mutunci saboda ba zai fitar da ni kunya ba ne, amma tunda na samu duk wani abu da nake buƙata na fitar taronmu ban da wata sauran damuwa.
Kasa zaune ko tsaye Maman Nasmah ta yi bayan sun gama wayar, ko kaɗan ba haka ta so ji ba, ta so a ce Anas ya na dawowa ya yi wa Hafsah fata-fata ya kore ta a daren, hakan ya ƙara tabbatar mata ba ƙaramin so yake yi wa Hafsan ba kamar yadda ta faɗa. Dole ne ta ƙara ƙaimi da dagewa gurin ziga Hafsah da nuna mata mijinta ba kowa ba ne face talaka mara daraja, za ta yi amfani da son rayuwar kuɗin da Hafsah take da shi ta cimma burinta. Wani murmushi ta saki lokacin da wata idea ta to mata cikin kwanyarta kamar an zira mata ita. A fili ta ce. "Duk rintsi duk wahala dole na mallaki mijinki Maman Sultan!"
Da daddare da muka kuma waya da Maman Nasmah ta ce na takura wa Anas ya siya mini sabuwar waya kafin ranar taro, kowa yana turo abin da mijinsa ya yi masa a group amma ban da ni, saboda nawa mijin ya fi kowa fatara sai ya kasa tsinana mini komai. Ya na dawowa ko bari ban yi ya zauna ba na ce. "Abban Sultan taron da na ce maka za mu yi fa saura kwana biyar, kuma gaskiya ni ina buƙatar sabuwar waya kafin ranar." Ya ce. "Ba mun gama wannan maganar ba Hafsah?" A harzuƙe na ce. "Ba wani mun gama, ni kawai ka siya mini." Ya ce. "Zancen kike so."
Masifa na shiga surfa masa kamar wata uwarsa, ta inda nake shiga ba ta nan nake fita ba. Na dinga jifan shi da kausasan kalamai. Bai ce mini ƙala ba har na gaji don kaina na yi shiru ina huci. Ina hawa online a lokacin na ga an ci gaba da turo abubuwa, kowacce ta na cewa mijinta ya siya mata kaza, ya ba ta kaza, ya kawo mata kaza. Hakan ya ƙara tunzura ni, na dinga Allah wadai da auren Anas, don da na san haka masu kuɗi suke bauta wa matansu da ko sama da ƙasa za su haɗe ba zan auri talaka ba. Ga shi ana ta tagged ɗina ana cewa ni ina nawa abubuwan? Rashin abin cewa ya sa ba na yi musu reply.
Duk wata tijara da rashin mutunci babu wadda ban yi wa Abban Sultan ba akan ƙin siyo mini wayar da ya yi, na daina aikin komai a gidan, tsakani na da su Sufyan sai hantara da zagi, musamman idan yana gidan, amma duk da haka ko ɗaga kai bai taɓa yi ya kalle ni ba bare ya tanka, duk da ina ganin tsantsar ɓacin rai a kan fuskarsa.
Yau ya kama saura kwana biyu taronmu, da daddare bayan na dawo daga gidan gyaran jiki ina zaune a gefen gado ina kallon fatata yadda ta yi wani irin kyau da sheƙi abun gwanin burgewa. Kallon yadda jikina ya koma kaɗai ya na saka ni a cikin matuƙar nishaɗi. Kiran Maman Nasmah ne ya shigo wayata, da murmushi na ɗaga tare da yin sallama, bayan ta amsa na ce. "Ya shirye-shirye?" Ta ce. "Shirye-shirye Alhamdulillah, ai mu mun gama komai, rana kawai muke jira." Na ce. "Masha Allah, Allah ya nuna mana wannan rana dai da rai da lafiya, mu sha shagali mu mori bidirin tanadin da aka yi mata." Ta ce. "Amin, amma dai ya kawo miki wayar?" Na ce. "Hmm, ina fa! Ai da ƙyar ya siya mini, ko tanka ni ba ya yi fa." Ta ce. "Taɓ, kowa kuwa da sabuwar waya zai je gurin nan, daga mai ta million sai mai ta sama da haka, ke kaɗai ce za ki tashi da jagwal." Cikin yaƙe na ce. "In sha Allah ni ma da sabuwa zan zo, bari ya dawo gidan." Ta ce. "Allah ya sa, ki san dai duk yadda za ki yi ya siya miki atou." Na ce. "In sha Allah." Daga haka muka yi sallama ta kashe wayar. Miƙewa na yi na fara zarya a ɗakin, ina tunanin hanyar da zan bi na samu waya mai tsada irinta ƴan group ɗinmu, na ƙulla na ƙunce amma ban da wata hanya sai Anas ɗin dai. Citson yatsa na yi na ce. "Oh Allah, ni Hafsah wacce ƙaddara ce ta kai ni auren mara zuciyar da ba zai iya nemo kuɗin da zai wadata ni da shi ba? Ya mayar da ni zarra a cikin mata ni ma kamar su Maman Nasmah." Tsaki na ja na koma na zauna tare da rafka tagumi. A haka ya dawo ya same ni, na tarɓe shi da kallon banza tare da jan dogon tsaki. Bayan ya rage kayan jikinsa ya na ƙoƙarin barin ɗakin na yi tsalle na sha gabansa, ina bin shi da wulaƙantaccen kallo na ce. "Anas don Allah wai kai wanne irin mutum ne? Ko babu zuciya a ƙirjinka ne da za ka yi amfani da ita ka nemo kuɗi a duk inda suke ka yi mini abin da nake da muraɗi?" Numfashi ya sauke tare da ƙoƙarin raɓawa ta gefena ya fita amma na ƙara tare hanyar, ina hawaye na ce. "Wai mahaukaciya ka mayar da ni a gidan nan ne da sai nai ta maka magana ka ƙi Kula Ni?"
"To ai ba ki da maraba da ita." Ya faɗa fuskarsa ba yabo ba fallasa. Bai jira amsata ba ya ci gaba da magana da faɗin. "Duk abin da za ki yi da cin mutuncin da za ki mun na yi wa kaina alƙawarin ba zan kula ki ba, bare na biye miki, har ki yi ki gama." Ƙugu na riƙe a harzuƙe na ce. "Ai ban da ranar ganawa idan har ba za ka yi mini abin da nake so ba, na gaji da zama sai dai na ga a yi wa wasu abubuwa ni ba a min, alhalin su ma mazajen nasu mutane ne kamar kai, ba fin ka suka yi da komai ba, abin da suke yi suke samun kuɗi kai ma za ka iya." Girgiza kai ya yi cikin tsantsar takaici ya ce."Allah ya ganar da ke Hafsah, amma ba zan gajiya da yi miki wannan addu'ar ba." Ina ƙoƙarin ƙara yin wata maganar ya hankaɗe ni ya fice, ƙwafa na yi na koma na zauna ina jijjiga jiki. Sabbin wayoyi da motocin da ƴan group ɗinmu suka tutturo mazajensu sun siya musu sai gizo suke mun a cikin kaina, babban abin da ya fi ɗaga mini hankali yadda duk wadda ta turo abu wani sashi na gidanta ya fito sai na gan shi haɗaɗɗe ginin zamani, wani parking space ma kaɗai sai a saka gidana a ciki ya zauna har da ragowa. Gabaɗaya Anas da duk wata kyautatawa, kulawa da soyayyar da yake min sun fice mini a rai, rayuwar gidan kuɗi da jin daɗi kawai nake hange. Na tabbata yadda nake kwana da wuni da tunanin ranar da mafarkina zai zama gaske idan aka auna jinina ba ƙaramin hawa za a ga ya yi ba.
Duk yadda na so mu yi fitina da Anas a daren nan amma ya ƙi biye mini, ƙarshe ma ficewa ya yi ya bar mini ɗakin ya koma nasu Sultan. Da Asuba ina tashi na ɗora daga inda na tsaya, na dinga watsi da kayan ɗakina ina jifan shi da shi, tare da gasa masa duk maganar da ta fito daga bakina. Don hankalina a matuƙar tashe yake na ganin har ana i gobe taronmu amma ban mallaki sabuwar waya ba, kuma kamar yadda Maman Nasmah ta faɗa duk kyawun da zan yi a gurin, da tsadar kayan da zan saka a banza za su tashi idan ban da rantsatstsiyar waya, saboda akwai video da za a yi mana wanda kowa zai ɗaga wayarsa a ciki, so ake mu tashi kan media a taron nan namu, ai ta yawo da videos da pictures ɗinmu, mu zama topic of discussion a ranar, shi ya sa aka ce kowacce ta sako gold. Don haka duk rintsi duk wahala ba zan bari na zamo takashin baya ba, dole duk abin da za a yi ya zamto ina gaba-gaba.
Yau idan na je gidan gyaran jiki shi ne za a mun lalle, amma saboda zullumin rashin waya ya sa har 8 ta wuce ban fara shirin tafiya ba. Ina kwance ina aikin kallon hotunan wayoyin da fiye da rabin ƴan group ɗin suka turo a tsakanin shekaran jiya da jiya Abban Sultan ya shigo ɗakin. Kamar an tsikare ni na tashi zaune na dirga daga kan gadon a haukace na je gabansa na haska masa rakwaɓaɓɓen screen ɗin wayata na ce. "Kalli yadda ake abin arziƙi, kalli irin wayoyin da mazajen wasu suka sissiya musu, ni kam Anas anya ka na so na kuwa? Gobe ne abin nan amma ka fitar da ni kunya abu ya gagara." Tankwaɓar da wayar ya yi ya ce. "Ban taɓa sanin ba ki da hankali ba Hafsah sai yanzu, kin taɓa ganin mutum ba shi da gashin wance ya ce sai ya yi irin kitsonta? Kin san kuɗin da mazajen nasu suke da shi ne?" Ina huci na ce. "Ai ba da kuɗin suka zo duniya ba, nema suka yi, kai ma sai ka fita ka nemo a duk inda suke." Murmushin takaici ya yi ya ce. "Kin yi nisa my love, ba za ki taɓa jin kira ba, abu ɗaya nake fata shi ne Allah ya sa ki je ki ga mazajen nasu ba su da wani abu da suke nema ido rufe, wanda ni kuma ina da shi, na san daga nan za ki dawo cikin hayyacinki." Wulaƙantaccen kallo na bi shi da shi, ina keɓe fuska kamar na ga kashi na ce. "Har akwai wani abu da talaka yake da shi da mai arziƙi zai rasa? Ai kuɗi babu abin da ba sa samar wa mutum a duniya." Girgiza kai ya yi ya ce.
"Kamar yadda Ubangiji yake raba arziƙi ga wanda ya so haka yake raba lafiya da sauran baiwa ga bayinsa, don ka na da kuɗi bai zama lallai ka na da lafiya ko kuma wani abu mai muhimmanci a rayuwarka ba, na san ba za ki taɓa gane duk wani abu da zan faɗa miki ba a yanzu, balle ki yarda da ni, saboda nausawar da kika yi a cikin wani tunani na banza da wofi. Shi ya sa na tattara ki na watsar na zuba miki ido ki yi duk abin da za ki yi ki gama, zan dai ci gaba da yi miki addu'ar Ubangiji ya ganar da ke cikin gaggawa." Wawan tsaki na ja tare da galla masa harara, ina jin kamar na kikkifa masa mari. Bai ko kalle ni ba ya ɗauki abin da zai ɗauka ya fice. Rashin sanin abin yi ya sa na tafi inda na ajiye kayan da Maman Nasmah ta ba ni don na ɗauka na tasa su a gaba na kalla kamar yadda nake yi kullum ko zan ji sanyi a raina. Sai dai me? Neman duniya babu wanda ban yi ba amma babu su babu alamar su, gabaɗaya na ƙara hargitsa ɗakin, na yi wa komai filla-filla, amma ko alamar abu mai kama da su ban gani ba. A haukace na fita parlour ina sharce zufa na duba amma nan ma babu, kitchen, toilet, ɗakin su Sultan, soro babu inda ban duba ba amma ban gan su ba, har bokitin da nake zuba shara sai da na zazzage a ƙasa na duba. Amma kaya suka ce ɗauke mu inda kika ajiye....✍️

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.