Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Yiwa_Kai_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 4 of 34
*Zeey Kumurya*
[3/8, 1:34 PM] BahaushiyaðŸ‘: *YI WA KAI*
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION
*BRIGHT PENS*
(FREE BATCH)
4.
Bayan na yi wanka na fita na siyo kati, fita biyu kenan a yau ba tare da izinin mijina ba, abin da ban taɓa yi ba kenan a rayuwar aurena. Na yi sa'a ina dawowa ana kawo NEPA, da ma chajina ya yi ƙasa sosai wayar tana gaf da mutuwa. Sai da na saka ta a chaji sannan na loda katin na siya data, direct Instagram na hau na ɗora daga inda na tsaya. Nai ta ganin abubuwa kala-kala, sai da aka kira sallar la'asar sannan na tashi. Ina idarwa na koma kan wayar, amma wannan karon Whatsapp na shiga, replying messages na fara yi sannan na shiga group ɗinmu. Na tarar sun ƙara cika shi da hira kamar marasa aikin yi, haushi ne ya kama ni, don na tsani a yi hira ba na nan. Sallama na yi tare da gaishe da kowa da kowa, waɗanda suke online suka amsa mini tare da yi mini ƙorafin kwana biyu ba na leƙowa gidan, na ce abubuwa ne suka ɓoye ni. Cikin zolaya Maman Nasma ta mun voice da faɗin. "Ko dai Oga ya ɗauke ki kun tafi sabon honeymoon ne? Shi ya sa kika manta da mu saboda kina can kina ƙonewa." Yaƙe na yi na ba ta amsa da faɗin. "Ba haka ba ne." A raina kuwa na ce, 'Wannan ai sai mazajenku masu zuciyar yi.' Daga nan na yi sama na fara bitar chats ɗinsu. Na ga an yi maganar za a yi taro, tare da shawarwarin yadda taron zai kasance. Ƙarshe dai an yanke shawarar za a haɗa kuɗi a yi abinci sannan za a fitar da anko, kuma har mayafi duk iri ɗaya suke so a saka. Inda za a yi taron kuma a gidan ɗaya cikin admin ne. Majority sun yi amanna da wannan shawarar, don haka sai aka bar ta a matsaya. Aka yanke kuɗin da za a bayar 5k, sai kuma atamfa anjima za a turo wadda za a yi tare da price ɗinta ita da mayafi. Yadda kowa ya aminta da abun da murnar taron da suke na san maganar ba ta wasa ba ce. Ban da zaɓi ni ma haka na nuna amincewata tare da fatan Allah ya nuna mana lokacin.
Sai da daddare da Abban Sultan ya dawo na samu damar yin karatun Alkur'ani, da ma kusan kullum sai mun yi a tare kafin mu kwanta, da rana kuma duk Sallar da na yi ba na tashi sai na karanta ko da shafi biyar ne, amma yau ko buɗe Alkur'anin ban yi ba, saboda duk kusan wunin nawa akan waya na ƙarar da shi.
*One week later*
Zaune nake a tsakar gida na yi tagumi ina tunanin inda zan samo kuɗin atamfar ankon taron group ɗinmu, atamfar 12k ce, sai kuɗin ɗinki da na mayafi, ga takalmi da jaka duk ina son na je da sababbi masu tsada, yadda zan fito cas da ni kamar kowa don kar a raina ni. A kullum idan Anas zai fita yana ajiye mini Naira ɗari ya ce ko zan ji sha'awar wani abun na siya, ko in an kawo talla, saboda ba ya ba ni kuɗin cefane, komai shi yake siyowa, hatta kayan miya, daddawa, kuka da kanwa. To ita nake tarawa idan ina buƙatar wani abun na siya ba sai na tambaye shi ba, duk haka sai na daɗe ban siya abu da kuɗin ba, don ko unguwa zan je yana ba ni kuɗin mota, in haihuwa aka yi ko biki a dangi yana ba ni abin da zan kai na gudunmawa daidai ƙarfinsa.
Ganin ƴan group ɗinmu kowa na tura kuɗinsa ya sa a cikin kuɗin da nake da shi dubu bakwai da wani abu na je p.o.s ba tare da sanin Abban Sultan ba na ba da aka tura mini, sauran da ya rage kuma duk na ƙarar da shi a siyan data, don wuni nake a Instagram ina kalle-kalle, hakan ya sa wayata ta ƙara rakwaɓewa, rashin riƙon chajinta ya ƙaru saboda yawan caji, da ya ƙare zan jona idan akwai NEPA, idan babu kuma sai na miƙa ta gurin masu chaji. Yanke shawara na yi zan tuntuɓi Abban Sultan yau da batun, taron yana ƙara matsowa kar na je lokaci ƙure don a tsayar da date ƙarshen watan da muke ciki. Ni kuma na ƙudurce wa raina duk runtsi duk wuya sai na yi ankon na kuma je taron, saboda har wanda ba ƴan Kano ba ma za su zo, bare ni da nake cikinsa, a tsarina har waya nake son canzawa kafin lokacin, gudun kar na je da ta hannuna a raina ni.
Bayan ya dawo mun gama komai yara sun yi bacci na tunkare shi da maganar kaina tsaye na ce. "Abban Sufyan bikin ƙawar nan tawa fa Naja za a yi." Na san in na ce masa taron group ne ba zai taɓa bari na, na je ba. Da fara'a ya ce. "Masha Allah, Naja lokaci ya yi kenan? Allah ya sanya alkhairi, yaushe ne?" Na ce. "Ƙarshen watan nan ne, shi ya sa ma na ce bari na sanar maka, don an fitar da anko tuntuni, kuma mai ɗan tsada ce atamfar." Murmushi ya yi ya ce. "Ubangiji zai kawo yadda za a yi, ba za ta gagara ba in sha Allahu, ai Naja mutum ce mai zumunci kuma mai yi, don haka dole mu rama wa kura aniyarta." Na ce. "Haka ne kam." Ya ce. "Nawa ce atamfar?" Gyara zama na yi na fara yi masa lissafi.
"Atamfar 12k ce, sai kuɗin ɗinki don mai kyau nake so a mun 5k, sai mayafi da jaka da takalmi, sabbi nake son sakawa kuma masu ɗan kyau, na tambaya kowane six-six thousand ne, sai casual make up da zan yi, amma ita ban san kuɗinta ba sai na tambayo. Sannan kuma ina son ka canza mini waya kafin ranar bikin, tawa duk ta rakwaɓe ta zama jagwal."
Wani irin kallo na ga ya bi ni da shi da na kasa tantance ko na mene ne, wajen 2 minutes kafin ya numfasa ya ce. "Hafsah! Kin san lissafin da kika mun kuwa? Kusan 100k fa tunda yanzu wayoyi tsada suke yi, ko kin manta waye ni da sana'ar da nake?" Æata fuska na yi na ce. "Na sani, kuma na san ba ka rasa kuÉ—in da za ka yi mini duk abubuwan da na ce ba." Ya ce. "Haka ne, tabbas ban rasa ba, amma na rasa wadda zan É—auko na ba ki, ki yi wannan buÆ™atun, domin wadatata ba ta kai haka ba, ke ma kin sani. Na yi mamakin wannan lissafin naki matuÆ™a da gaske, domin ba ki taÉ“a zuwar mini da buÆ™ata mai girman wannan ba." Na ce. "Kamawa ta yi yanzun ma na zo maka da itan, ka san wace Naja a gurina da irin abubuwan da ta yi mini, lokacin bikinmu wacce hidima ce ba ta yi da jikinta da aljihunta ba?" Girgiza kai ya yi ya ce. "Na sani, ita ma kuma in sha Allah ba za mu Æ™i yi mata ba, amma daidai Æ™arfinmu, zan siya miki atamfa na ba ki kuÉ—in É—inki dubu uku, takalmi da jaka da mayafi kuma ki yi amfani da naki na da." Cikin takaici na dube shi na ce. "Yanzu kana da kuÉ—in amma ba za ka siya mini ba?" Ya ce. "Eh, kuÉ—ina na siyan abincin da za mu ci ne da sauran buÆ™atu, ga Sallah ta kusa, term ya zo Æ™arshe zan biya kuÉ—in makarantar su Sultan, both boko da islamiyya. Ban san ki da kafiya da naci ba, kar ki koya a yanzu please." Girgiza kai na yi na ce. "TaÉ“!" Tare da tashi na fice daga É—akin. Parlour na je na kwanta akan kujerara zuciyata cike da baÆ™inciki, kusan matan group É—inmu duka sun gama siyan komai na fitar taron, kuma kowacce cewa take mijinta ne ya siya mata, amma ni nawa mijin kamar a kansa aka Æ™are fatara da tsiya ya ce ba zai iya ba. Tsaki na ja tare da ayyana irin kalolin rashin mutuncin da zan fara shuka masa, matuÆ™ar ya dage da gaske ba zai ba ni kuÉ—aÉ—en nan ba.
A parlour na kwana, abin da ba mu taɓa yi ba kenan wato raba shimfiɗa don mun samu saɓani, na kuma san ba ya son hakan shi ya sa na yi da gayya.
Bayan Sallar Asuba ya same ni a inda na yi Sallah ya ce. "Yanzu dan na ce ba zan yi miki abin da ban da halin yi ba, shi ne kika kwana a nan? Mun samu saɓani kala-kala wanda suka fi wannan amma ba ki taɓa haka ba sai yau, me ya sa Hafsah? Me ya sa kike ɗauko wasu halaye da ban san ki da su kike yi? A Kwanakin nan gabaɗaya na daina gane kanki, duk kin canza, hatta kula da yaranki ma duk kin rage, mene matsalar ne?" Banza na yi da shi na ƙara haɗe raina kamar ban taɓa dariya ba, ina jin takaicin yadda a kodayaushe yake nuna ya damu da damuwata, amma kuma ba zai iya fitar da ni kunya ba.
"Magana fa nake miki."
"Babu komai." Na ba shi amsa ciki-ciki.
"Amma kin san ba na san magana a dunÆ™ule ko? Ina tambayar ki kina cewa babu komai, alhalin kuma da akwai." Yadda ya yi maganar na gane ya fara fusata, hakan bai sa na sakko ba, don da ma abin da nake so kenan na É“ata masa rai. Bai Æ™ara magana ba ya fice ya bar mini parlour'n. Na bi shi da harara tare da taÉ“e baki, don na san ba iya dogon fushi zai yi da ni ba, har inda nake zai zo ya same ni ya rarrashe ni......âœï¸
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.