Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Yiwa_Kai_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 28 of 34
Faisal kuwa da kallo ya bi Hafsah, bayan ta fice ya taɓe baki tare da komawa ya zauna. Wayarsa ya ɗauko daga aljihun gaban rigarsa ya fara ƙoƙarin kiran Maman Nasmah. Wadda ita ta turo shi, bayan ta gama tsara masa duk abubuwan da zai ce wa Hafsah. Amma saboda kar sunanta ya fito sai ta ce masa ya ce mai gidan ne ya turo shi, don ta san Hafsah za ta yarda da hakan tunda ta san halin mijinta, kuma babu wata hanya da za ta same shi nan kusa bare ta yi masa magana akan lamarin, kafin ya dawo garin kuma ta san ta gama samun abin da take nema. Faisal ɗaya daga cikin yaran da take hulɗa da su ne.
Tana zaune tunanin Anas ya addabe ta kiran Faisal ya shigo wayarta. Tsaki ta ja ta É—auki wayar da niyyar yin reject sai ta ga shi ne, da sauri ta É—aga ta kara a kunnenta. Kafin ta yi magana ya riga ta da faÉ—in. "Madam an samu matsala fa." Ta ce. "Matsalar me kuma?" Ya ce. "Ta Æ™i amincewa fa, kuma a yanayinta gaskiya za ta yi wuyar sha'ani." Æata fuska ta yi ta ce. "Na sani da ma, duk da wawancinta tana da tsatsttsauran ra'ayi akan addini, amma a hakan za ka shawo kanta, ina Æ™warewarka a sace zuciyar mace da yaudara suke? Ko mu kaÉ—ai kake yi wa?" Dariya ya yi ya ce. "Kin san wargi ma guri yake samu, ku da ita da banbanci ai, duk iskancin mutum sai ya samu guri yake iya baje shi." Ta ce. "Na ji, ni dai ka samu ka yi duk yadda za ka yi ko da sau É—aya ne ta amince." Da sauri ya ce. "Dole na ma ai, don na matuÆ™ar yabawa da ita." TaÉ“e baki ta yi ta ce. "Ta nan ka fi kauri da ma, saura ka je garin azarÉ“aÉ“i ka manta da abin da na saka ka." Ya ce. "Ba zan taÉ“a mantawa ba, jira nake dare ya yi na saita, da komai ya kammala kawai sai dai ki ga na tura miki."
"Good, fatan nasara."
Ya ce. "Ki saka a ranki ta tabbata, kamar an yi an gama." Ta ce. "Allah ya sa." Tare ka katse kiran. Numfashi ta sauke cikin takaici, ga rashin samun Anas ga Hafsah ma tana ƙoƙarin ba ta matsala. A yanzu burikanta biyu ne, na farko ta mallaki Anas, na biyu kuma ta ɓata Hafsah a idonsa, ya daina ganin darajarta ko kaɗan ya kuma ƙara tsanar ta, ta yadda ko da ba ta da aure a gaba ba zai yi gigin mayar da ita ba. Duk da a yadda suka yi alƙawari da Mansur duk rintsi duk wuya ba zai rabu da Hafsah ba, sai dai in mutuwa ya yi, wanda ba ta fatan hakan nan kusa.
Sai da na yi kwana uku ko ƙofar ɗakina ba na takawa, sai dai masu aiki su kawo mini komai su dawo su ɗauke. Duk da uban sintirin aiken da Faisal yake yi, ƙarshe da na gaji sai na buga wa masu aikin da yake aikowa warning, na ce kar su ƙara dawo mini da zancen shi. Ban yi yunƙurin korar shi daga gidan ba tunda maigidan ya san da zamansa, na bar shi ya gaji don karan kansa ya ƙara mai.
Yau Sallah saura kwana biyar, ina kwance a ɗaki na tasa uban tsadaddun kayan sakawana a gaba ina kallo, sarƙoƙin gold's ɗin da wata mata ta kawo jiya na ɗaga, ta ce Alhaji ne ya turo ta, ta kawo mini na yi kwalliyar Sallah da su, a gurinta yake siya wa matansa kodayaushe. Ko kaɗan kayan ba su burge ni ba, ajiye ta na yi ina girgiza kai. Duk da uban kayan lefen da ya ba ni na siya sai da ya aiko mini da kayan Sallah, tunda na jibge su ma ko kuma kallon su ban yi ba sai yau na kwaso na duba. Ajiye sarƙoƙin na yi a kan kayan na ɗauki wayata na shiga Camera, Lokacin da nake ta fata da burin zuwan shi ga shi ya zo mun, mafarkina ya cika na ganin na tara abu na bajinta irin haka na ɗauka na tura a group ɗinmu na ce ga shi ni ma mijina ya siya mini kamar yadda kowa yake yi, amma na rasa me ya sa bana farinciki kamar su, su da walwala da nishaɗi a cikin muryoyinsu a lokacin da suka videon, alamun suna cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali. Dangwarar da wayar na yi ina jin wani irin ƙunci a cikin zuciyata, so nake na fita daga gidan nan ko na awanni ne na sha iska, amma da na ce wa Kawu zan je na gaishe shi hanawa ya yi, ya ce na bari sai Sallah, ya yi wuri na fara fita yanzu. A hankali na ɗago kaina jin ana knocking, ban motsa ba na ba da umarnin shigowa. Laraba ce ta shigo bakinta ɗauke da sallama, na amsa kamar mara lafiya. Jug ɗin hannunta da ke cike da kunun aya ta ajiye a gabana tare da faɗin. "Ga shi Hajiya na kammala." Na ce. "Sannu." Tare da janyo shi a zalamance na bude, ko tsiyayawa ban yi a cup ba na fara sha, kasancewar na sha azumi sai yau na yi tsarki na ɗora ya ba ni wahala, shi ya sa na saka a haɗa mini kunun ayar mai sanyi don na sanyaya maƙoshina. Ajiyar zuciya na sauke bayan na dire jug ɗin, ina jin yadda sanyin ke ratsa ƙirjina. Bayan wasu mintuna ina son na tashi na yi Sallah amma na ji kasa, jikina ya yi mun wani iri kamar ba nawa ba, kwanciya na yi akan kayan gabana saboda yadda nake jin kamar iska za ta ɗaga ni daga zaunen da nake saboda rashin ƙwari, ko ɗanyatsana kasa motsawa na yi, ni ba mai bacci ba, ni ba matacciya ko sumammiya ba.
Fuskar Faisal É—auke da murmushin nasara ya kira Maman Nasmah, tana É—agawa ya ce. "Yes! Na ci kuÉ—ina." Cikin murna ta ce. "An yi nasara ne?" Ya ce. "Eh, yanzu mai aikin ta gama faÉ—a mini har ta sha drink É—in, maganin da na ba ta, ta zuba mata kuma sha yanzu magani yanzu ne, na san tuni ya fara aiki, nawa aikin ne kawai ya rage."
"Amma ba ya saka bacci dai ko? Don na fi son a ce idanunta biyu tar."
Ya ce. "Ba ya sakawa, kawai jikinta ne zai yi weak, ba za ta iya komai ba sai yadda aka yi da ita." Ta ce. "Yawwa, haka nake so, ka yi sauri ka je, sai na ji feedback, saura kuma garin zumuɗi ka manta da yin videon, don na ji duk ka wani gigice." Dariyar ƙeta ya yi ya ce. "Kar ki ga liafina, Beb ɗin ce ta haɗu ta ko'ina, za a amfana da ita." Tsaki ta ja cikin kishi ta ce. "Ni dai ga abin da na ce maka." Daga haka ta katse kiran.
Da murmushi a kan fuskarsa ya nufi sama inda Hafsah take, wanda already Laraba ta riga ta buÉ—e masa kowacce Æ™ofa da za ta sada shi da ciki, tutturawa kawai zai yi ya shige.......âœï¸
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.