Complete Hausa Novels

Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Yiwa_Kai_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 23 of 34

*Zeey Kumurya*✍️
[3/8, 1:42 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI*

MIKIYA WRITERS ASSOCIATION

*BRIGHT PENS*
FREE BATCH

*20.*

Ƙura wa hoton farko da na buɗe ido na yi, ina bin kowacce gaba ta jikinsa da kallo ɗaya bayan ɗaya. Baƙi ne amma mai haske ba mai duhu ba, kuma yana da ƙiba, sannan ba matashi ba ne kamar yadda na yi tunani don ya fara manyanta, amma a muryarsa da yadda yake magana na ɗauka bai fi matashi ɗan 35 years ba. Hannunsa da ya fi fuskarsa haske sosai tabbacin hutu na kalla ina murmushi. Daga yanayin suturar jikinsa da gurin da aka yi masa hoton kaɗai ma ya gamsar da ni. Ci gaba da kallon sauran na yi, wasu ma duk a ƙasashen waje ya ɗauka. Reply na yi mata da thanks kawai na fita daga chat ɗin. Wani irin fayau nake jin zuciyata kamar an wanke mini ita da tsintar wannan dami a kalan da na yi.
Da yamma na je gurin masu siyar da kati na yi musu transfer ɗin na 15k suka ba ni kuɗin, daga nan shagon masu siyar da mayuka na je na siya mai ɗan kyau da sabulu da turare, dan so nake na fara gyara jikina kafin ya zo mu haɗu. Ina son na je gidan Maman Nasmah saboda mu fi tattauanawa yadda yakamata amma ina tsoron Kawu, don ɗan nan da can idan na ce za ni da ƙyar yake bari na.
Tun wayar da muka yi da Mansur ba mu kuma waya ba har sai washegari da safe, ya kira ni ya ce ayyuka ne suka yi masa waya, muna gama wayar shi ma kamar jiya ya turo mini da credit na 20k. Da ma jiya da muka yi chat da Maman Nasmah na faɗa mata ta ce ai shi bai mayar da 20k kuɗi ba, indai Idonnera ne yanzu na fara ganin ɓarin kuɗi.
Ranar Monday na yi wa Kawu ƙaryar zan koma asibiti, ciwon kai da na ƙirji sun ƙara dawo mini, ya dinga yi mini faɗa da nasiha akan na cire damuwa a cikin raina, na zama mai tawakkali, don shi duk a zaton shi damuwar sakin ce take sanya mini ciwon. Na ce masa in sha Allah zan rage, sannan ya bar ni na tafi. Banki na je aka buɗe mini account, ina zuwa ban wani tsaya bin layi ba, saboda wanda Mansur ya haɗa ni da shi, shi ya zo ya shigar da ni ya yi mini komai. Bayan an gama na kira shi, bai ɗaga ba kamar yadda na yi zato ya katse ya kira da kansa.
"Ranki ya daɗe." Ya faɗa cikin sanyin muryarsa. Murmushi na yi na ce. "Tare da naka, an kammala komai shi ne na kira na sanar maka." Ya ce. "Ma sha Allah, yanzu na ji ni daidai, amma da Madam babu account babu hanyar da zan tura mata kuɗin da za ta siya kayan kwalliya ta mun ai ba kanta." Dariya na yi na ce. "To dole kai sai ka tura mini kuɗi?" Ya ce. "Mene amfaninsu idan ban ba ki ba? Kin ga kwana ukun a takure na yi su saboda ban tura miki kuɗi ba, don haka yanzu turo mini account number ɗin kawai na fara tura miki kuɗin powder kafin na zo." Cikin farinciki na ce. "An gama." Tare da katse kiran na tura masa. Tabbas sai yanzu na samu namiji irin wanda ya dace da ni, mai buɗaɗɗen hannu ba irin Anas matsolo ba, tsabar so da tarin dukiya har matsuwa ya yi ma ya tura mini kuɗi. Ƙarar shigowar message ya saka ni saurin duba wayata, yawan kuɗin da na gani ya saka ni zaro ido ina ƙara bitar zirukan, idan ba idona ne yake yi mini gizo ba one million na gani. Ban gama tantacewa kiransa ya shigo. Cikin azarɓaɓi na ɗaga, na ce. "Na ga alert, Ranka ya daɗe ai kuɗin sun yi yawa." Cikin dariya ya ce. "One million ɗin? Ai ni kira na yi na ji idan ba za ta isa ba na ƙaro." Na ce. "A'a, ta yi yawa ma na go...."
"Babu godiya a tsakaninmu, don haka daga yau kar ki kuma, million kuma ki shirya tarɓar ta, don kin kusa fara kyautar ta nan kusa ba ma a ba ki ba, don haka ki daina cewa ta yi yawa." Ya katse ni da faɗin haka.
Ƙara dashare bakina na yi don tun ɗazu ya ƙi rufuwa na ce. "Tom shikenan my dear, Allah ya ƙara arziƙi da wadata." Ya ce. "Amin, ki jira a nan bank ɗin yanzu zan turo ɗaya daga cikin yarana ya kai ki shopping Mall ki zaɓi duk abin da kike so, kafin na dawo mu je tare." Danne ruɗun da nake ciki na yi na ce. "To." Daga haka muka yi sallama.
Ni kaÉ—ai na dinga murmushi, na manta a cikin mutane nake, don gabaÉ—aya na kasa control É—in gigicewar da kuÉ—in suka saka na yi.
Har yaron nasa ya zo muka tafi ban daina kallon alert ɗin ina murmushi ba. Ƙara ruɗewa na yi bayan na shiga cikin motar da ya zo da ita, don ba ƙaramar haɗuwa ta yi ba. Wani haɗaɗɗen guri ya kai ni, ya ce na ɗauki duk abin da nake so, Oga ya bayar da maƙudan kuɗaɗe. Na yi dariya kawai ban ce masa komai ba. Zagewa na yi ban yi wa kaina ƙauro ba na jibgi kaya, ina ganin na loda da yawa amma yaron ya ce sun yi kaɗan ya ƙara ɗibar mini wasu. Da muka je gurin biyan kuɗi na ji kuɗin kayan ba ƙaramin girgiza na yi ba, amma shi ko a jikinsa ya zaro ATM ya ba da aka zara muka taho. Rashin sanin ta yadda zan shiga gida da uban kayan ya sa na ce ya kai ni bayan layinmu, na kai su ajiya gidan wata mata da muke mutunci da ita.
Bayan mun ƙarasa na shiga na yi mata bayani ta ce. "Inyee, su Hafsah har an fara zaurawan ne?" Murmushi na yi tare da ƙirƙirar abin da zan faɗa mata, don ba zan nuna ina son shi ba a ce da ma muna tare tun da, ko kuma a gane plan ɗina. Cikin ɓata rai alamar ba na so na ce. "Wallahi kuwa Maman Sabir, daga na je asibiti wani mutumi yay ta bi na da naci da magiyar na ba shi lambata, bayan na ba shi kuma ya ƙi ƙyale ni wai sai ya kawo ni gida, shi ne ya tsaya a wani guri ya yi mini siyayya, na ce ba zan karɓa ba amma ya nace, har ƙaryar ni matar aure ce fa na yi masa amma ya ƙi yarda." Ta ce. "To ai abin farinciki ne wannan, sai ayi ta addu'a Ubangiji ya sa da shi za a yi idan da alkhairi." Na ce. "Gaskiya ni ban shirya aure yanzu ba, ko zan ƙara aure ba yanzu ba." Ta ce. "A'a kar ki yi wannan gangancin, domin kuwa dama ce Allah ya ba ki, ai haka abin yake da ma, mace tana yin idda za ki ga maza sun fara tururuwar zuwa mata, kamar waɗanda ake sanarwa." Na ce. "To Allah ya kyauta, bari na je na dawo." Cikin tsokana ta ce. "To ki gaishe shi ki ce in ji surukarsa." Na yi dariya kawai ban ce komai ba.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.