Complete Hausa Novels

Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Yiwa_Kai_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 16 of 34

Sai da Naja ta koma gida ta huta sannan ta kira Anas, duk da halin tashin hankalin da yake ciki da zazzaɓin da ya rufe shi lokaci ɗaya amma da sauri ya ɗaga yana fatan Allah ya sa zancen Hafsah za ta yi masa, saboda duk da abin da ta yi masa ko kaɗan son ta bai ragu a cikin zuciyarsa ba. Bayan Naja ta yi sallama ya amsa ta ce. "Abban Sultan idan babu damuwa ina son don Allah mu yi wata magana ne da kai, idan kana free yanzu, in kuma kana abu idan ka gama sai ka kira ni." Ya ce. "A'a babu abin da nake yi, ina sauraren ki." Ta ce. "To Masha Allah, ɗazu na zo gidanka na riski wani mummunan al'amari da bai mun daɗi ba ko kaɗan wallahi, ya kuma saka ni a cikin tashin hankali mara misaltuwa, kana nan ma na zo, amma saboda yanayin da kake ciki na san da ƙyar idan ka gan ni. Hafsah ta faɗa mini komai da yake faruwa, na yi mata faɗa sosai tare da ba ta shawarwari, kuma na ga alamar ta ɗauka daga yanayin yadda jikinta ya yi sanyi. Shi ya sa na kira na roƙi alfarmarka, akan don Allah ka yi haƙuri ba don halinta ba, ka mayar da ita ɗakinta, saboda tana gidan ma a can na baro ta, na hana ta tafiya." Numfashi ya sauke ya ce. "Anya kuwa Hafsah za ta risina? Don abubuwanta sun daina ba ni mamaki yanzu sai dai tsoro. Don da farko ma na yi tunanin ba ta cikin hayyacinta ne, sai daga baya na gane tsantsar iskanci ne da burin shirme da ruɗin shaiɗan." Naja ta ce. "In sha Allahu ba za ta sake ba, ka yi haƙuri, ta faɗa mini komai babu abin da ta ɓoye mun, amma ni na yi mata uzuri, saboda rashin mai ba ta shawara da ƙarancin wayewa sun taka muhimmiyar rawa a wajen habbaƙa al'amarin nan, amma komai ya zo ƙarshe in sha Allahu, zan kawo Mama da kaina har gidan ta ƙara yi mata faɗa, ba na son Kawu ya ji zancen nan, don kansa duk son da yake yi mata sai ya kusa balla ta." Ya ce. "Tom shikenan Naja, na gode sosai Allah ya saka da alkhairi, amma da na so na bar ta, ta je gida ta huta, idan ta gaji da zaman gidan ne." Naja ta ce. "A'a fa, da yardar mai duka komai ya zo ƙarshe, kuma kai ma da ka sani ka ƙwace wayar tata ka karya sim ɗin da ka fuskanci inda matsalar take. Da may be abun bai yi tsamari haka ba."  Ya ce. "To ai ba ta bari mun yi magana ma ta fahimta ba bare na gane inda matsalar take, sai dai kawai ɗan abun da na fahimta daga maganganunta na baya da gugar zanan da ta dinga mun, da zuwan wata ƙawarta gidan." Cikin takaici Naja ta ce. "Allah ya kyauta ya ƙara ganar da ita, Da iliminta amma na rasa inda ta ajiye shi ta ɗauki kishiyarsa." Ya ce. "Ni ma mamakin da nake yi kenan, don ban taɓa zaton za ta iya ambaton sunan mahaifana ƙarara ta haɗa kuma da cin mutunci ba."
"Ka yi haƙuri, na san ta yi hauka da wauta, kuma ta ɓata maka rai matuƙa, amma ka taimaka ka mayar da ita, ba na son na ga kun rabu wallahi, ba na son ta yi asarar miji irinka."
Runtse idonsa ya yi don har lokacin muryar Hafsah ba ta daina yi masa kuwwa a kunne ba, a sanyaye ya ce. "Shikenan na mayar da ita, Allah ya sa ta yi nadamar abubuwan da ta aikata har cikin zuciyarta." Ajiyar zuciya Naja ta sauke ta ce. "Amin ya rabb, na gode sosai da ka fahimci ni da kuma wannan alfarmar da ka mun, Ubangiji ya ƙara muku zaman lafiya da kwanciyar hankali, Allah ya kaɗe fitina a tsakaninku da sharrin shaiɗan, ya sa makamancin hakan ba za ta kuma faruwa ba." Ya ce. "Amin ya hayyu ya ƙayyum, ke ma Allah ya ba ki miji na gari." Murmushi ta yi ta yi masa sallama ta katse wayar. Shiru ya yi yana tunanin rayuwarsu ta da shi da Hafsah, ya so rabuwa da ita na har abada ko don ya nuna mata daraja da ƙimar da iyayensa suke da shi a wajensa, amma darajar su Sultan da kyautatawar da ta yi masa a da su saka sanya ya amince ya mayar da ita. Amma ba zai koma gidan ba a yau, su Sultan ma ba zai mayar da su ba, don da ma da ya ɗauko su ɗazu daga tahfiz gidan wani abokinsa ya kai su, ya ce musu Hafsan ta je unguwa ne. Ya san Naja za ta kira ta, ta faɗa mata duk yadda suka yi, zai gani idan za ta neme shi, inda da gaske ta yi nadamar abubuwan da ta yi masan.

Bayan Magriba na ce wa Maman Nasmah zan koma gida, don na san zuwa yanzu Naja sun yi magana da Anas kamar yadda ta alƙawarta, kuma na san ba zai ƙi mayar da ni ba, duk da ba ni da tabbas, don ban taɓa yi masa irin ko da makamancin irin wannan laifin ba na taɓa mahaifansa. Ga shi wayata ta ɗauke ta ƙi kunnuwa gabaɗaya, bare na kira ta ko ita ta kira ni. Hana ni tafiya Maman Nasmah ta yi, ta dinga yi mini faɗa kamar za ta ari baki, wai shi bai neme ni ba, bai mayar da ni ba amma zan komar da kaina saboda zubar da aji da rashin sanin ciwon kai, ta takura sai na kwana a gidanta, gobe inda an gama komai sai na tafi. Don dole ba don son raina ba na amince. A daren muka je saloon aka yi mana wankin kai da na ƙafa, aka kuma kawo mini kayana da sabuwar waya kamar yadda ta faɗa, har da kuɗin liƙi sabbin ƴan ɗari biyar-biyar. Farinciki, murna da ɗoki suka saka na manta da Anas da babinsa, na ci gaba da shirin taronmu da za mu cashe mu raƙashe a gobe.
Kallon Hafsah kawai Maman Nasmah take tana yi mata murmushin mugunta a zuciyarta, saboda ita kaɗai ta san me ta shirya mata a wannan kwanan da za ta yi a gidanta.......✍️

*Zeey Kumurya*✍️
[3/8, 1:40 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI*

MIKIYA WRITERS ASSOCIATION

*BRIGHT PENS*
(FREE BATCH)

*14.*

Har sha biyu na dare ta wuce ban yi bacci ba, ina zaune a tsakiyar makeken gadon da nake na tasa kayana a gaba ina aikin kallon su, sai jujjuya dalleliyar wayar nake a hannuna ina sakin murmushi.
"Allah ka cika mini burina, ka nuna mini ranar da ni ma zan yi kyauta ga wani ninkin ba ninkin ɗin wannan." Na yi maganar ina bin bedroom ɗin da ya kusa rabin gidana gabaɗaya a girma da kallo. Gado, wardrobe, mudubi duk suna gefe ko rabin ɗakin ba su ci ba. Ƙuntataccen ɗakina na tuna, wanda space ɗinsa da ya rage bai fi ya ci ƙaramar tabarma biyu ba. Tsaki na ja na tattara kayan ba don na gaji da ganin su ba na kwanta. Sai na ji kuma na kasa baccin, duk da juyin da nake yi a gadon ina bararrajewa son raina. Tashi na yi na rage hasken ko shi ya hana baccin ɗauka ta. Amma still ya ƙi zuwa, tunanin Anas da su Sultan na ji ya cika zuciyata, wata irin kewar su da ban taɓa zaton yin ta ba ta ziyarce ni. Duk yadda na so na yakice su amma abu ya ci tura. Taune leɓena na yi ina ayyana da dare bai yi sosai ba sai na koma gidana a yau, don na gane ba zan taɓa iya rayuwa babu mijina da ƴaƴana ba, ko kuɗin da nake so da shi nake son mu yi ba wai mu rabu ma, amma shi ya ƙi gane hakan bare ya ba ni haɗin kai. Da ƙyar na samu bacci ya ɗauke ni lokacin da dare ya kusa rabawa.
Washegari bayan na yi sallar asuba na koma bacci, sai bayan 10 na tashi muka fara shirin tafiya taronmu. Mai kwalliya ta musamman ce ta zo ta yi mana har gida ni da Maman Nasmah. Zuwa bayan azhar mun gama shiryawa cikin ankonmu. Na daɗe ina kallon kaina a mudubi saboda ba ƙaramin kyau na yi ba ni kaina na sani. Maman Nasmah ta dinga yi mini hoto a wayarta, don tawa har yanzu ba a kunna ta ba, ni ban iya using iphone ba ita kuma ta ce sai mun nutsu za ta saita mini komai. A wata luntsumemiyar mota mai numfashi muka tafi gidan Aunty Billy, muna baya driver yana gaba shi kaɗai. Sosai harabar gidan da aka yi wa decoration ya yi kyau, mun tarar da sama da mutum 20 a gidan sun zo. Da gudu wasu suka taho suka rungume Maman Nasmah, ta nuna musu ni, suka ce ko da ba ta faɗa ba sun san ni ce, saboda sun san duk inda suka gan ta za su gan ni a gurin, tunda kowa ya san ita ce babbar ƙawata a group ɗin. Zagewa na yi aka shiga hada-hada da ni, ina jin kaina kamar kowa tunda na saka gold da sauran kayan kwalliya masu tsada.
Sama da mutane 60 ne suka halarci taron, kuma duk ƴan group ɗin namu ne, kowacce kuma ta saka anko, ta yi ɗinki mai tsada da sarƙar gold ɗin da aka ce. Sosai muka yi kyau kamar yadda muke fata. An ci an sha, an yi rawa an cashe an tattauna, abin gwanin ban burgewa. Hakan sai ya ƙara mini son group ɗin sosai, na ji ko me za a yi ba zan fita daga cikinsa ba. Mun sha hotuna da video kamar ba gobe. Sai da aka kusa tashi Maman Nasmah ta saka mini sim ɗina a cikin sabuwar wayar, ta nuna mini yadda zan yi kira da wasu ƴan abubuwan, sauran kuma ta ce sai mun koma gida za ta nuna mini. Kaf matan da suka zo taron babu wadda ta kai ni duhu, saboda kowacce sai na gan ta fara ƙal, waɗanda ba fararen sosai ba kuma duk sun fi ni haske, duk da gyaran jikin da aka mun, alaƙanta hakan na yi da don su matan masu kuɗi ne ni kuma matar talaka ce.
Messages na gani da numbern Naja, na farko ta ce tana ta kira na a kashe, na biyu kuma ta ce ina ina? Ta zo gidan ba na nan, alamun tun jiya ta yi su kenan. Sai yau da ta ƙara cewa ta je da safe ba na nan, sai na ƙarshe kuma wanda da alama ba ta daɗe da yin shi ba, ta ce duk inda nake na koma gidana don Anas ya mayar da ni tun jiya, idan ba haka ba za ta je ta faɗa wa Kawu duk abin da yake faruwa. A tsorace na bar filin rawar da muke na ja Maman Nasmah gefe na ce. "Ni fa tafiya gida zan yi yanzu, na ga Magriba ta kusa." Kallon sama da ƙasa ta yi mini ta ce. "Saboda me? Ya kira ni ne? Ba gidana za ki koma ba da ma?" Girgiza kaina na yi cikin fargaba na ce. "Bai kira ni ba, amma ƙawata ta yi mini text ta ce ya mayar da ni." Tsaki ta ja ta ce. "Ita ƙawar taki ya aka yi ta sani?" In brief na ba ta labarin tattaunawar da muka yi da Naja. Tafa hannuwa ta yi ta ce. "Shi ne kike wannan rawar jikin komawar? Bai kira ki da kansa ba tun jiya amma daga an yi miki text an ce ya mayar da ke duk kika gigice haka? Hafsah wai wacce iriya ce ke ne? Akan namiji? Namjin ma talaka." Kamar zan yi kuka na ce. "Ba haka ba ne, ina tsoron ƙawar tawa ta faɗa wa Babana ne." Taɓe baki ta yi ta ce. "To bari ki ji, ita ƙawar taki ita ce babbar munafuka kuma maƙiyiyarki, saboda ba ta son ki da arziƙi, da tana son ki da arziƙi ba za ta ce ki rabu da mu ba, bayan kin faɗa mata yadda muke da irin kyautar da na yi miki, amma saboda tana baƙincikin ki yi mu'almala da masu kuɗin da ita ba ta yi shi ya sa ta ba ki wannan gurguwar shawarar, za ta ce kar ki fara gayu ki bar ta a baya." Girgiza kai na yi na ce. "Naja ƙawata ce ta haƙiƙa tun muna yara, tana so na da son ci gabana sosai, ba za ta taɓa yi mini abu don hassada ba gaskiya, kawai dai tana faɗa mini tata fahimtar ne." A sheƙe kamar kashi ta saki baki tana kallo na, kafin ta jijjiga kai ta ce. "Taɓɗijan! Amma gaskiya ba ki san halin da duniya take ciki ba, to ki je ki tambaya ki ce kaf yanzu a rayuwa wa ya fi rashin amana da nuna hassada, za a faɗa miki a ce aminiya ce. Tun yaushe aka daina ƙawancen tsakani da Allah, kowa zuciya da tsatsa burinsa ya ga ya fi ɗan'uwansa ci gaba. Idan kuma kina tantama akan maganata ki je ki ce mata ta auri miji talaka kamar naki, za ki ji abin da za ta ce, wanda zai nuna ba ta so, amma ke tana danƙwarar da ke akan ki zauna." Jinjina kai na yi, zan yi magana Aunty Billy da ta ƙaraso inda nake ta riga ni da faɗin. "Ku ce aminai kuna nan kuna zantawa?" Murmushi muka yi duk da nawa na yaƙe ne. Ta ce. "Ku zo mu je ku gaisa da Ogana, ya dawo yanzun nan, ya gaisa da kowa ban da ku." Maman Nasmah ta ce. "Shi ya sa na ga bakinki ya ƙi rufuwa, ashe rabin ran kika gani." Ta ce. "Bari ke dai, har ya ƙara mini da kuɗin liƙi." Faɗaɗa fara'a Maman Nasmah ta yi ta ce. "Ai na sani da ma, ni da na san dawar garin, duk dawowa da ma kin ce da kyauta yake yi miki sallama, kamar nawa mai gidan, shi ma yana dawowa zai ce ungo." Dariya suka kwashe da ita tare da tafawa suka yi gaba. Na bi su abaya kamar saniyar ware, a raina ina faɗin. 'Wato su mazajen nasu da kuɗi suke tarɓar su kullum? Gaskiya matan masu kuɗi suna shanawa da yawa, ga ƙaton gida, ga abinci lafiyayye, ga sutura mai tsada, ga hawa mota da sauran abubuwan more rayuwa."
Wani part ɗin muka shiga daban ba inda ta kai mu da za mu yi Sallah ba, ba ƙaramin dauriya na yi ba gurin ɓoye ƙauyancina, saboda haɗuwa da tsaruwar shi. Na kasa gane tsakanin gidan Maman Nasmah da na Aunty Billy wanne ya fi kyau da girma, saboda kowanne ya kai duk inda ake son gida ya kai a tsaruwa. Cikin fara'a kamar ya san mu muka gaisa da mijin nata, ta ƙasan ido na ƙare masa kallo. Irin alhazawan nan ne da kuɗi da hutu suka zauna a jikinsu, ga shi ɗan dumurmuri ya sha babbar riga cikin kaya na alfarma. Irin dai mijin da mace ba za ta ji kunyar nuna shi ba ko a ina ne. Anas ne ya faɗo mini a rai, na ja tsaki ƙasa-ƙasa, tare da addu'ar kar Allah ya kawo ranar da wata a group ɗinmu za ta ƙara ganin shi a matsayin mijina bayan Maman Nasmah. Don abin kunya ne a gare ni.
Bayan mun fito Maman Nasmah ta ce mini. "Wai tafiyar za ki yi da gaske na ga kina abu kamar a ce ƙyet! Ki gudu?" Ɗaga mata kai na yi ban ce komai ba. Aunty Billy ta ce. "Saboda me? Ki bari a tashi mana, ba wani ɗadewa za a kuma yi ba fa, ana yin Magriba DJ zai tafi." Kafin na yi magana Maman Nasmah ta yi karaf ta ce. "Mijinta ne ya kira ta yaron ta babu lafiya, shi ya sa." Ajiyar zuciya na sauke ina ƙara jin son ta a raina, saboda duk yadda za ta yi kar asirina ya tonu sai ta yi. Aunty Billy ta ce. "Ayya, Allah ya ba shi lafiya, bari na zo to ina zuwa." Bayan ta bar gurin Maman Nasmah ta ce. "Ki yi tafiyar ki kar ki yi wa kowa sallama tunda kin nace, saboda su Maman Suhail tun jiya suke ce mini ina ne gidanki za su je, yanzu idan suka ji za ki tafi bin ki za su yi. Gobe idan Allah ya kai mu da safe sai ki zo gidana, zan saka wani a cikin my driver's ya kai ki ɗaya daga cikin guest house ɗinmu, ki zauna a can a matsayin nan ne gidanki, sai su zo nan su same ki, idan za ku tafi zan haɗa miki da wadataccen abincin da zai isa a ci da drinks. Zan ba su address ɗin yanzu idan sun tambaye ni ina ne gidanki. Bana son su je ainihin gidanki su raina ki ne, shi ya sa na yi wannan dabarar." Ban san lokacin da na rungume ta ba tsabar farinciki na ce. "Ya Allah! Na rasa da bakin ma da zan gode miki wallahi, duk abin da za ki yi ki kankaro mini mutunci kin san shi." Tana murmushi bayan ta raba ni da jikinta ta ce. "Ƙauna ce ta kawo hakan, ke dai duk abin da na ce ki yi kawai ki bi, don ba zan taɓa cutar da ke ba." Cikin zumuɗi na ce. "Na tabbatar da hakan takwara, Allah ya bar mu tare." Ta ce. "Amin."
Kayan ciye-ciye da abinci da lemuka Aunty Billy ta haɗo ta ba ni, na yi musu sallama na tafi cikin sauri, don na ga Naja ta fara doka mini kira. Allah ya taimake ni ina fita titi na samu mai napep, ya ce zai kai ni har gida a 2k. Ban tsaya ja'inja ba na shiga, saboda ina da ishashshen kuɗi a hannuna ragowar na liƙin da Maman Nasmah ta ba ni.
Mun fara tafiya mai napep É—in ya ce. "Hajiya ga wata mota tana bin mu a baya, ko kin san su ne?" Girgiza kai na yi na ce. "A'a." Ya ce. "To dai wannan mu take bi, amma bari na shiga ta layuka don na tabbatar, idan mu yake bi zai shigo shi ma." Na ce. "To." Don ni hankalina gabaÉ—aya ya yi gida, burina kawai na gan ni a cikinsa, don ba na son maganar abin da yake faruwa ta je kunnen Kawu, na san na lahira sai ya fi ni jin daÉ—i a gurinsa. Da gudu motar da take bin bayanmu ta zo ta wuce mu ta tsaya a gabanmu. Cikin faÉ—uwar gaba na ce. "Innalillahi! Su waye wannan? Me suke nema a gurinmu?"
"Sai Allah." Mai napep ya faɗa a tsorace bayan ya tsayar da babur ɗin. Fita ya yi ya je suka yi magana, ina ta leƙen su a tsorace na ga ya dawo ya ce. "Hajiya ke suka biyo, da ma daga layin da kika fito na ga su ma sun fito." Dafe ƙirji na yi a firgice na ce. "Na shiga uku! Me zan yi musu to?" Yana murmushi ya ce. "Ki je ki ji, amma na tabbatar ba cutar da ke za su yi ba." A tsorace na kalle shi na ce. "Ko dai bakinku ɗaya da su?" Ya ce. "Wallahi ban ma taɓa ganin su ba sai yau, ki daure ki je, sun ce ba jimawa za ki yi ba." Girgiza kai na hau yi na ce. "Ka shigo ka ja mu kawai mu tafi, ni sauri nake babu inda zan je."
"Ko mun juya sai sun kuma bin mu, ki je kawai ki ji me za su ce ki dawo, don Allah!" Ya yi maganar cikin roƙo.
Ina kallon layin da babu kowa sai mu kaɗai na ce. "Wai maza ne ma ko mata?" Ya ce. "Mata ne." Ajiyar zuciya na sauke na fita ina waige-waige a tsorace, sai a lokacin na lura da sababbin kuɗin da suke hannunsa, tabbacin cin hanci suka ba shi, shi ya sa ya dage sai na je. Kamar kar na ƙarasa, saboda haka kawai na ji zuciyata tana bugawa. Tsayawa na yi cak a gaba da napep ɗin amma ban ƙarasa inda motar take ba. A hankali na ga an buɗe front seat an fito, damm! Ƙirjina ya buga da ƙarfi bayan na yi tozali da mai fitowar........✍️

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.