Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Yiwa_Kai_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 29 of 34
*Zeey Kumurya*âœï¸
[3/8, 1:44 PM] BahaushiyaðŸ‘: *YI WA KAI*
MIKIYA WRITERS ASSOCIATION
*BRIGH PENS*
(FREE BATCH)
*25.*
Laure da ke laɓe a bayan labule ta yi saurin barin parlour'n ta bi bayan shi cikin tashin hankali, duk da ba ta san me yake shirin aikatawa ba amma ta san ba alkhairi ba ne. Tun lokacin da ta ga sun keɓe suna ƙusƙus shi da Laraba ta saka musu ido, hakan ya sa yanzu tana ganin Laraban za ta shiga parlour'n da ya mayar da shi kamar nasa ta bi bayanta ba tare da sun ankara da ita ba. A ruɗe ta zagaya ta ƙofar kitchen da gudu ta riga shi hawa upstairs na biyu, tana rufe ƙofa tana jiyo takun tafiyarsa yana hawowa, hakan ya sa ta ƙara ƙarfin gudun nata, da haki ta shiga bedroom ɗin da Hafsah take ta fara laluben key, a kan drawer ta hango shi, da sauri ta ɗauka har tana tuntuɓe ta kulle ƙofar ta bar shi a jiki. Dogon numfashi ta ja ta sauke tare da sakin ajiyar zuciya, idanunta akan Hafsah da ba ta da maraba da matacciya. Matar da ba ta taɓa wulaƙanta su ko yi musu wani cin mutunci ba kamar yadda wasu matan suke yi idan ana aiki a ƙarƙarshinsu, ta sakar musu komai na gidan su yi yadda suke so, ko dan wannan ba za ta taɓa bari a cutar da ita ba. Tana jin shi yana ta murɗa handle ɗin ɗakin.
Cikin mamaki Faisal yake tura ƙofar kamar zai karyata. Ganin ko motsi ba ta yi ba ya ja tsaki tare da sauka ƙasa a fusace ya fara ƙwala wa Laraba kira. A gigice ta fito tana waige-waige ta ce. "Ga ni yallaɓai." Kamar zai rufe ta da duka ya ce. "Kika ce duk kin buɗe ƙofofin? Ya aka yi kuma na je na ji ɗakin nata a rufe?" Da sauri ta ce. "Wallahi na buɗe, sai dai ko ba ɗakin da take ciki ka je ba." Tsaki ya ƙara ja ya ce. "Ba shi ne na farko ba?" Ta ce. "Shi ne." Taune lip ɗinsa ya yi tare da yamutsa fuska, kamar yay ta naushin iska haka yake ji saboda takaici, a ƙufule ya ce. "Ko dai ba ki zuba mata maganin ba ne ƙarya kika yi mini?" A tsorace ta ce. "Na zuba mata, kuma ta sha, a yadda na baro ta ma ya fara aiki a jikinta." Harara ya zabga mata ya ce. "Dalla wuce ki ba ni guri, sakarya kawai." Baki ta zunɓura ta bar masa parlour'n. Yana huci ya ɗauko wayarsa ya kira Maman Nasmah ya sanar mata halin da ake ciki. Cikin baƙinciki ta ce. "Me ya sa haka ne wai? Me ya sa nasara ta yi mini ƙaura a game da Hafsah? Ka koma ka saka ido sosai, don dole akwai abin da ya faru, ba haka kawai aka samu akasi ba." Cikin ƙunar zucin ganin samu da rashin da ya yi ya ce. "Na fi ki takaicin abun nan wallahi, don ƙofar ɗakin aka rufe da key ta ciki, kin ga babu yadda za a yi ta buɗu ta waje kenan, sai dai in ɓalla ta za a yi." Kamar za ta yi kuka ta ce. "Ba fa zan karaya ba, sai aikin nan ya yiyu ko ta halin yaya, ka samo wata hanyar da za mu cimma burin mu kafin Sallah, don maigidan za su iya dawowa a kowane lokaci, gara ka yi abin da za ka yi ka tattara ka bar gidan." Ya ce. "In sha Allah za mu yi nasara, don ba zan taɓa bari duk zaman da na yi a gidan nan ya tashi a banza ba." Ba ta ce komai ba ta kashe wayar don takaici.
Tun ina ganin dishi-dishi har na daina ganin komai, ban ƙara sanin inda kaina yake ba sai can cikin dare na farka a firgice. Salati na rafka tare da tashi zaune, hakan ya farkar da Laure da ke zaune a ƙasa tana bacci. Da mamaki na dube ta bayan na latsa wayata na ga lokaci na ce. "Laure?" Ta ce. "Na'am Hajiya." Numfashi na sauke ina jin jikina wani irin lagwab kamar an yi mini duka, ga kaina da ke sara mini. Ina rarraba ido bayan na gama tuno abin da ya faru kafin hankalina ya gushe, na ce. "Lafiya? Me kike yi a nan a wannan daren? Me ya same ni?" A raunane ta ce. "Ban sani ba Hajiya, kawai hakan da na yi shi ne kariya a gare ki, ki yi haƙuri don ban san yadda zan yi miki bayani ki gane ba."
"Kariyar me?" Na tambaya a gigice. Shiru ta yi ba ta ce komai ba, a tsawace na ce. "Ki yi mini bayanin mana, ina sauraren ki."
Kanta a ƙasa ta ce. "Wannan baƙon da ya ce shi ƙaninki ne, shi ne ya faki idonmu ya zuba miki abu a cikin kunun ayar da Laraba ta kawo miki, bai san na gan shi ba, a lokacin na rasa mafita, sai bayan da kika sha na samu na shigo, na tarar da ke cikin wani irin yanayi, duk da na ruɗe amma ban fita ba, don na fuskanci ɗakin yake son shigowa ya yi wani abun." Jijjiga kai na shiga yi cikin matuƙar mamaki, don na gane nufin Faisal a kaina. A tsorace kamar za ta yi kuka ta ce. "Amma don Allah Hajiya kar ki ce ni na faɗa miki." Cikin ƙaunar yarinya na tashi na koma kusa da ita na kama hannunta na ce. "Ko zancen ba zan yi masa ba, bare sunanki ya fito a ciki, kawai zan yi takatsantsan da shi daga yanzu, na gode sosai, na kuma ji daɗin taimako na da kika yi." Ajiyar zuciya ta sauke ta ce. "Babu komai Hajiya." Jikina fayau na tashi ina tunanin mafita, babu abin da zan yi wa Faisal face na haɗa shi da Allah kawai, shi zai yi mini maganinsa.
Tun daga ranar na koma yin duk wani abu da zan ci da kaina, ina gamawa na tattara na kai ɗaki na kulle. Saura kwana biyu sallah na kira mai kitso da ƙunshi ta yi mini, ranar sallah na shirya driver ya kai ni masallaci na yi idi. Kamar kar na baro masallacin, saboda ganin hada-hadar mutane ba ƙaramin sanyaya mini zuciya ya yi ba. Ina komawa gida aka aiko wani almajiri ya kawo mini abincin sallah ya ce ga shi daga maƙota. Na karɓa na ce an gode bayan ya yi mini kwatancen gidan. Tsabar halin da nake ciki ma na manta da ana yin wani abincin salla, don a kwanakin nan sosai tunanin su Sultan da kewar su ya addabi zuciyata, hakan ya sa na ƙara lalacewa duk na rame.
Washegari na shirya na je na gaishe da Kawu, daga nan na tafi gidan Inna Habi na yini, don ba ƙaramin ɗasawa muke yi yanzu da ita ba. Ta dinga nan-nan da ni tana cewa ciki ne da ni, ramar da na yi daga gani ta laulayi ce, ni dai na bi ta da ido kawai, a raina ina cewa. 'Ba ki san dawar garin ba ne.' Sai murna take na kusa haihuwa a gidan mai kuɗi. Sai bayan isha'i na koma gida, kamar kar na tafi, don kwana na so yi Inna Habi ta hana ni, duk da na ce mata ba ya gari ya yi tafiya.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.