Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Yiwa_Kai_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 5 of 34
*Zeey Kumurya*
[3/8, 1:36 PM] BahaushiyaðŸ‘: *YI WA KAI*
MIKIYA WRITERS ASSOCIATION
*BRIGHT PENS*
(FREE BATCH)
5.
*BRIGHT PENS...* _suna mara ba da masu buƙatar a tallata musu kasuwancinsu, masu siyar da turarruka, kayan sawa, magani komai da komai, cikin sauƙi za a tallata musu a cikin duka littafan guda uku🤙🼠*CUTARWA, MUNAFUKIN MIJI, YI WA KAI*_
Tsari👯ðŸ»â€â™€ï¸
Duk page É—aya 200
Duka littafin kuma 600
Shafi biyar a littafi É—aya 1000
A littafai uku kuma 3000
Domin Æ™arfin bayani sai a yi wa wannan number magana 08164069385🤙ðŸ¼ðŸ‘¯ðŸ»â€â™€ï¸ðŸ«¶ðŸ«¶ðŸ¼
Shi ya tafasa ruwan zafi suka sha tea da bread, ko tsinke ban ɗauke ba har ya dawo daga kai su Sultan school ya karya ya ɗauraye cups ɗin da suka ɓata ya gyara gurin. 300 ya ajiye mini ya ce idan mai kifi ya kawo na siya na saka a miya, ga kayan miya can ya taho da shi ya ajiye a kitchen. Motsi ban yi ba balle na tanka masa har ya fice daga gidan.
Ranar haka muka ƙara kwana kowa zuciyarsa babu daɗi, don da ya dawo ko sannu da zuwa ban yi masa ba, na dai yi girki saboda cikina da ƴaƴana.
A haka kwanaki uku suka shuɗe babu wata jituwa a tsakaninmu, duk yadda ya so mu sulhunta ni kuma na ƙi, magana dubu in zai yi ba zan tanka ba, yara ma idan yana nan ba na sakar musu fuska, idan suka ishe ni da magana na daka musu tsawa na hantare su. Hakan ba ƙaramin ɓata masa rai yake yi ba, kuma ina yi ne duk dan na takale shi amma ba ya kula ni. Makwanci kuma tuni na raba mana da ma, tun ranar a parlour nake kwana ko a ɗakin su Sultan.
Yau ya siyo mana kayan abinci da sabulun wanka da na wanki, ya haɗo da wani turare da ya san ina so, ya kawo mini har gabana ya ajiye, amma na ƙi ko ɗaga kai na kalle shi bare na ce na gode. Kasancewar Friday ce su Sultan suna gida, shi kuma da ma idan ya dawo daga masallaci ba ya kuma fita, zai zauna mu yi karatu ko hira ko mu fita unguwa tare.
Ina ɗakin su Sultan a kwance ina kallon haɗaɗɗun girke-girken da aka turo a group ɗinmu, da yake Juma'a ce majority abinciccikan gargajiya suka yi, ban da haɗiyar yawu babu abin da nake yi, saboda kusan kowanne da zuƙu-zuƙun nama a kansa.
"Garin daɗi na nesa." Na faɗa kamar zan fashe da kuka, dafadukar da na yi yau ce ta faɗo mini a rai, wadda ba ta da maraba da ta gidan bikin ƙauye a gurina. Tsaki na ja na tashi zaune tare da ajiye wayar hannuna. Duk wani abun gayu da abinci da ake turawa ni ban taɓa turawa ba, ina tsoron kar hakan ya sa su gane talaka nake aure su raina ni. Kowa yana taɓuka abun arziƙi a group ɗin amma ban da ni, komai ni ce koma baya. Ga shi an san ni sosai, ina daga cikin mutum biyar da suka fi kowa magana a gidan, shi ya sa ko daɗewa na yi ban hau online ba sai su yi ta cikiya ta, a yanzu ma sai da Maman Nasma da Aunty Billy mai group ɗin suka yi tagging ɗina, suka ce ni rowar abincin nake musu ne da ban turo nawa ba? Ƙaryar na je unguwa na yi musu. Tagumi na yi na fara tunanin ko tashi zan yi na yi dambu ne na tura musu? Tunda ina da gyaɗa da zogalen da ya siyo ɗazu, saboda yana son miyar zogale shi ya sa duk lokacin da zai siyo kayan abinci sai ya haɗo da shi. Murmushi na yi na miƙe ina faɗin. "Haka za a yi." Duk da ba a nan gizo yake saƙar ba, tunda ban da wayar da zan ɗauki hoton dambun ya fito ya yi tar kamar nasu, da haɗaɗɗun food flak's ɗin da zan zuba irin nasu, kuma su akan dinning suke jerawa su ɗauki hoto su turo, ni kuwa gidana ko tiles babu sai ledar tsakar ɗaki. Gwauron numfashi na ja na koma na zauna saboda tunawa da na yi shinkafar da zan yi amfani da ita ma ita kanta sai na yi zaman tsincewa, ba kamar su da sai dai kawai su saka abu su kamfata a cikin buhu su wanke su dafa ba. Takaici goma ashirin da hamsin duk suka cika mini zuciya. Tsabar tunanin ranar da mafarkina zai zama gaskiya ban san Sultan ya shigo ɗakin yana ta sallama ba sai da ya taɓa ni. A fusace na doka masa tsawa tare da faɗin. "Mene ne?" A firgice ya ɗan ja baya idanunsa cike da ƙwalla ya ce. "Abba ne ya ce ki shirya mu je gidan Kawu." Tsaki na ja na ce. "Ka ce masa bana jin daɗi." Yadda yaron ya yi sororo yana kallo na cikin hawaye sai jikina na fara yin sanyi, na ji kamar na zubar da makaman yaƙina na haƙura da batun zuwa taron gabaɗaya, na rungumi ƴaƴana da mijina kawai mu koma rayuwarmu kamar da.
Janyo shi na yi jikina cikin sanyin murya na ce. "Kar ka yi kuka yaron kirki, I'm sorry na yi maka tsawa." Cikin kuka ya ce. "Mamy kin daina son mu yanzu, kullum sai dai ki yi ta yi mana faɗa da tsawa." Kansa na shafa na ce. "Ai uwa ba ta taɓa daina son ɗanta har abada my son." Bai kuma magana ba har na share masa hawayen fuskarsa, ajiyar zuciya ya sauke ya ce. "Kin daina yi mana faɗa ko?" Ɗaga masa kai na yi ina murmushin da suka kwana biyu ba su gan shi a fuskata ba. Ta window na hango Abban Sultan tsaye yana kallon mu, ɗauke kai na yi tare da ture Sultan daga jikina. Fita yaron ya yi shi kuma ya shigo, muryarsa da alamun maɗaukakin ɓacin rai ya ce. "Duk abin da za ki yi ya tsaya iya kaina Hafsah, amma ban da ƴaƴana, ba za ki tusa musu damuwa a cikin zuciya tun suna ƙanana ba." Haɗe rai na yi sosai na ce. "Ai ni ba ƴa ba ce da kai kake cusa mini damuwar."
"Me nake miki? Me na rage ki da shi a zamanmu?" Ya tambaya a kaushashe.
Ɗage kafaɗa na yi tare da taɓe baki ban ce komai ba.
"Tambayar ki nake yi fa."
Numfashi na sauke na ce. "Babu komai." A fusace ya buÉ—e baki zai yi magana sai kuma ya fasa ya juya ya fita, na raka shi da harara.
Wayata na janyo na kunna data na ɗora daga inda na tsaya, hirar taron da za mu yi kawai ake yi a group ɗinmu, hakan ya ƙara dugunzuma hankalina, domin ranakun taron da suka rage ba su fi goma ba, ga shi abubuwan da nake yi ya sa ba mu ƙara zancen ƙaryar bikin Naja da na cewa Abban Sultan za a yi ba, bare ya ba ni ko iya kuɗin da ya alƙawarta ne, har yanzu bayan 5k ɗin taron da na tura ban ƙara wani shiri akai ba, saboda ba ni da ko sisi. Na ja tsaki ya fi cikin kwando na rashin mafita.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.