Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Yiwa_Kai_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 3 of 34
*Zeey Kumurya âœï¸*
[3/8, 1:34 PM] BahaushiyaðŸ‘: *YI WA KAI*
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION
*BRIGHT PENS*
(FREE BATCH)
3.
Washegari bayan na yi sallar asuba na koma na kwanta duk da ba bacci nake ji ba, don ban saba yin shi a irin wannan lokacin ba. Kuma na san su Sultan za su tafi school, amma rashin data ya sa duk takaici da ɓacin rai ya cika mini zuciya. Bayan Anas ya gama karatun Alkur'ani da azkar ya dube ni ya ce. "Wai har yanzu wannan yanayin bai bar ki ba? Ba mun gama magana jiya ba?" Fuska babu walwala na ce. "Na ce maka akwai wata matsalar ne?" Ya ce. "A'a, alamu dai kawai na gani." Siririn tsaki na ja na juya masa baya. Bai ce komai ba ya tashi ya fita, ina jiyo shi suna buruntu shi da ƴaƴansa. Har bakwai na safe ta wuce ina inda nake ban ko motsa ba, na ɗora da daga inda na tsaya a tunanin da ya aure ni. A lokacin su Sultan suka shigo ɗakin bakinsu ɗauke da sallama, juyowa na yi na kalle su tare da amsa musu, ganin jikinsu da ruwa alamun wanka ya yi musu ya sa tilas na tashi na fara shafa musu mai. Bayan sun gaishe ni Sultan ya ce. "Mami ba ki da lafiya ne yau ba ki fita kin yi mana girki ba?" Gyaɗa masa kai kawai na yi. Cikin marairacewa Safyan ya taɓa goshina ya ce. "Sannu Mamina, kin sha magani?" Shafa kansa na yi na ce. "Ai ban da maganin ciwona a yanzu, amma idan kuna addu'ar da na ce shi ne maganin zai samu." Sultan yana saka wandonsa ya ce. "To mene yake miki ciwo?"
'Talauci.' Na faÉ—a a cikin raina. A fili kuwa ban ce komai ba.
Tare muka fita parlour, na tarar har Anas ya dama mana kunu ya siyo ƙosai, yana kallo na ya ce. "Zuba musu su ci mu tafi, sun kusa latti, bari na yi wanka kafin su gama." Kamar wadda ya faɗawa mutuwa haka na ɗaga masa kai fuskata a cuskune. Duk da ba na kallon fuskarsa amma na san tsayawa ya yi yana kallo na, kamar ban san yana yi ba na tsugunna na fara tsiyaya kunun a ƙananan cup. Ina jin shi ya ja dogon numfashi sannan ya fita, raka bayan shi na yi da harara.
Na Kunna wayata ina dube-dube ya dawo ya shige ɗaki, ya ƙara fitowa kamar mai neman wani abu ya koma. Na san me ya sa ya yi hakan, a tunaninsa ko ban gan shi ba ne ko kuma tuni yake yi mini, saboda ya saba kullum ni nake shirya shi tsaf. Bayan ya gama ya fito ya kama hannun su Sultan ya tafi kai su school. Ina tunanin ranar da mafarkina na ganin lokacin da drivers za su dinga kai su Sultan school a haɗaɗɗiyar mota na fita tsakar gida, na gan shi fes har shara ya yi, da ma kuma kusan kullum shi yake yi, don tun ina amarya indai yana gida tare muke yin aiki, yanzu kuma da hidimar su Safyan ta ƙaro sai muke raba aikin, shi ya yi shara da wankin toilet ni kuma na yi wanke-wanke da abun kari da gyaran ɗaki. Idan kuma ba zai fita da wuri ba har wanke-wanken yake yi da dama kunu ko tafasa ruwan tea, ni kuma na shirya su Sultan.
Cups ɗin da yaran suka ɓata na wanke na koma ɗaki na fara gyarawa. A haka ya dawo ya same ni, yana duba time ya ce. "Mu je mu karya kar ƙosan ya ƙara yin sanyi." Ɗan yamutsa fuska na yi na ce. "Ba na jin yunwa, ka je ka ci kawai." Fuskarsa da maɗaukakin mamaki ya ce. "Hafsah! Wai kina cikin hayyacinki kuwa? Ni ne fa Anas mijinki amma kike yi mini irin wannan abubuwan, me yake damun ki ne?" Ban ce komai ba na ci gaba da aikina, duk da na san hakan ba ƙaramin ƙular da shi zai yi ba, don ya tsani yana yi wa mutum magana yay masa shiru. Ganin ya ƙi fita na juya na kalle shi na ce. "Ka yi haƙuri, mu je mu ci abincin." Girgiza kai kawai ya yi ya fice daga ɗakin.
Ina son mijina da ƴaƴana, kuma ba na son ɓacin ransa, amma burina na son zama hamshaƙiyar mace matar mai kuɗi ya canza mini komai a cikin raina, don a yanzu ban da wani fata sama da haka. Kuma gabaɗaya a da ban san ana irin wannan rayuwar kuɗin ba, saboda a cikin talakawa na tashi a nan na rayu, ina dai jin labarin masu kuɗi, amma ban taɓa tunanin jin daɗin rayuwarsu ya kai haka ba sai a SANADIN WAYA. Zuciyata ta kwaɗaitu matuƙa da irin wannan rayuwar.
Duk wani rarrashi da nasiha sai da Anas ya mini kafin ya fita, hakan ya sa na É—an saki raina, muka rabu lafiya kamar yadda muka saba kullum.
Fitar shi babu jimawa message ɗin kati ya shigo wayata, da ma na faɗa masa ban da data ne, ya ce yana fita zai tura mini. Da rawar jiki na loda katin na siya data, har wani zuƙo jikina yake yi mini saboda zumuɗin shiga group ɗinmu na ga abin da aka yi da ba na nan.
Hirarraki burjik na tarar an yi, a hankali na fara bi tun daga farkon inda na yi offline. Rabin hirar ta yabon hotunan juna ce, daga nan aka fara zancen kaya, lace ɗin jikin wata ne ɗaya daga cikin admin ta ce sun yi ankon shi a wani biki, kuɗinsa dubu ɗari biyu da wani abu. Zaro ido na yi na koma kan pic ɗin matar na yi zooming na ƙara kallon kayan da kyau, a anko kawai an yi na sama da 200k? Ina kuma ga normal kayan sakawa na gida ko na Sallah?
Ci gaba da bin hirar na yi, na ga wadda ta saka kayan tana faɗar kuɗin ɗinkin da aka yi mata 30k. Haka dai nai ta bi ina kallon hirar tare da haɗiyar yawu, jin yadda suke zancen maƙudan kuɗaɗe a kayan sakawa kawai da takalmi da jaka. Abin da ya fi komai ɗaukar hankalina videon bikin da wadda ta ce sun yi ankon lace ɗin ta turo. Wani haɗaɗɗen hall ne da ban taɓa jin labarin irinsa ba a rayuwata balle na gani. Ga hamshaƙan mata sun kame a kan kujeru, wuya da kunnuwansu duk gwala-gwalai ne. Na maimaita kallon videon babu adadi, kamar na yi tsalle na faɗa cikin wayar saboda yadda abun ya yi mugun ƙayatar da ni. Wasu mahaukatan kuɗaɗe ake liƙawa kamar ana watsa duwatsu.
Ba don na gaji da kallon videon ba na haƙura na koma na ci gaba da bin chat ɗin nasu, don tsabar kallo sai da na haddace duk wani abu da ake yi a cikin videon da maganganun mc. A cikin hirar na ji wata ta ce ta ga bikin a Instagram, daga nan aka fara zancen ƙayatattun bukukuwan da ake ɗorawa a manhajar ire-iren waɗannan da ma wanda suka fi su. A take na ji ina son na shiga Instagram ɗin ni ma na gani. Da wannan zumuɗin na fita daga Whatsapp na koma play store na ɗauko app ɗin, bayan ya gama installing na yi ƙoƙarin buɗewa amma ya ƙi saboda ban da email account, ga shi ban san ta yadda zan buɗe shi ba. Na koma group ɗin da nufin na tambaye su ko sun sani amma sai na ga kamar ajina zai zube, hakan ya sa na fasa na miƙe na zari hijabina na rufe gida na fita. Wani gida a layinmu dake da wadatuwar samari na je suka buɗe mini a nan take, na yi musu godiya cikin tsananin farinciki sannan na dawo gida. Zaman dirshan na yi a tsakar ɗaki ina kallon video's a Instagram baki buɗe, ashe ko rabin tsaruwa da haɗuwar bukukuwan ba su fasalta ba a group ɗin. Ban ajiye wayata ba har sai da na ga sun daina buɗewa, alamun datata ta ƙare. Ni da take yi mini kwana shida amma yau a cikin awanni ta ƙare, ashe shiga kowane apps a social media ɗin ma sai masu kuɗi, kullum ina ji suna ta zancen apps kala-kala, ashe ba ƙaramin data suke jibgawa a wayoyinsu ba. Wannan tunanin ya ƙara girmamar burina a cikin raina, na ji a yanzu babu abin da nake so sama da na ga na je irin waɗannan bukukuwan, ko kuma ya kasance an yi akan wani nawa ko wanda na sani da za a gayyace ni, duk da zan fi so a ce a bikina shagalin ya kasance. Tunanin ƴar walimar da aka yi lokacin aurena ya sa ni jan dogon tsaki tare da cizon yatsa.
Sai sha biyu na rana saura na iya tashi na ɗaura girki, ina aikin ina imagining ranar da zan gan ni a cikin irin manyan haɗaɗɗun halls ɗin bikin da na gani, ni ma na tura a group ɗinmu aita mun fatan alkhairi da yaba bikin. Don yadda aka yiwa wadda ta turo sun yi bikin Allah ya sanya alkhairi abun ya burge ni matuƙa, don na san da irin namu gajari-gajari ta turo ba ballai a kula ba, amma wannan kowa sai rububin yi mata fatan alkhairi yake yi.
Lokacin da su Sultan suka dawo ban kammala girki ba, kuma ba na jin na taÉ“a yin hakan in dai ba cuta nake ba, kafin su dawo na gama komai, amma yau sai da suka makara a islamiyya. Na dinga mita ni kaÉ—ai ina cewa. "Da matar mai kuÉ—i ce ni ina za a samu wannan matsalar? Ina daga kwance kamar matan cikin group É—inmu ina latsa waya masu aiki za su yi komai su gama, throughout suna online saboda ba sa aiki a gidajensu, amma ni hura gawayi ma kaÉ—ai ya ishe ni, Allah ka kawo mini karshen wannan wahala da jarabar, don sai a yanzu na fuskanci auren talaka ba Æ™aramin jidali ba ne." Na Æ™arashe maganar kamar wadda take cikin wani mugun tsananin taskun rayuwar.......âœï¸
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.