Complete Hausa Novels

Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Yiwa_Kai_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 19 of 34

A ɓangaren Maman Nasmah kuwa tsalle ta doka cikin farincikin murnar samun wani chance ɗin a sauƙaƙe na raba Hafsah da Anas. Za ta yi amfani da hakan tai ta ƙara cusa mata son rayuwar gidan kuɗi har ta yi nasarar raba sun. A cikin mazan da take hulɗa da su za ta haɗa ta da guda ɗaya su dinga waya da chatting a matsayin shi ne mijin Aunty Billy. Don ba ƙaramin daɗi ta ji ba da Hafsah ta ce mata ba ta karɓi card ɗinsa ba, bare ta kira shi ya ci gaba da yi mata maganar banza asirinta ya tonu na ƙaryar da ta zabga mata. Ita kanta ba ƙaramin kaɗuwa ta yi da ta ji mijin Aunty Billy ya bi Hafsan, kuma tsabar ƙwanƙwararre ne shi ya bayyana mata manufarsa ba tare da tsoron komai ba. Murmushi ta yi a fili ta ce. "Ashe ba namu mazajen ne kaɗai bunsuraye ba." Za ta ci gaba da nuna wa Hafsah son ta take yi tsakani da Allah da kuma burin taimakon ta, yadda duk abin da ta ce mata ta aikata za ta yi ba tare da jinkiri ba.

Wuni na yi ina abu ɗaya wato tunanin mafita, a ƙarshe na yanke shawarar amincewa da abin da Maman Nasmah ta faɗa, na rabuwa da Anas na fita na auri mai kuɗi irin mijin da nake fata da burin samu. Idona ya rufe gabaɗaya, ƙaton gida da rawuwar jin daɗi kawai nake hangowa, na manta da ƙalubalen da za su biyo bayan faruwar hakan. Da kaina na kira ta na sanar mata na amince, ta nuna mini ta ji daɗi sosai, don mutumin mai suna Alhaji Kyauta ya ƙara kiran ta a kaina, ta ce masa wasa take yi masa ba ni da aure za ta haɗa mu. Na nuna mata ba zan iya mu'almala da shi da aure na ba, ta san abin da za ta faɗa masa kafin na rabu da Anas sai mu fara magana a lokacin. Ta ce tom shikenan babu damuwa, amma na yi komai cikin sauri kar a ja lokaci, na ce mata in sha Allah.
Tun daga ranar na fara sauke wa Abban Sultan tsibiri-tsibirin kwandon rashin mutunci da tijara, wulaƙancin yau daban na gobe daban. Duk abin da na san ba ya so shi nake yi, wanda yake so kuma na daina yi. Ci gaba da maganganun abubuwan kuɗi da turo su a group ɗinmu shi yake ƙara tunzura ni, don na sha alwashin ba zan bari wani taron da za mu kuma yi ya zo ina cikin wannan akurkin gidan ba. Saboda an tsayar da cewar duk bayan wata shida za mu dinga yin taron, amma ba za a sake yi a gida ba sai dai a kama guri..........✍️

*Zeey Kumurya✍️*
[3/8, 1:41 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI*

MIKIYA WRITERS ASSOCIATION

*BRIGH PENS*
(FREE BATCH)

*17.*

Yau ta kama Laraba, wanda ya yi daidai da watanni uku da fara takun saƙar mu da Anas. Ina zaune a ɗaki da hantsi ina chatting tare da kallon su Sultan da suke ball a tsakar gida, da yake ana cikin hutu ne babu school.
Ƙara kishingiɗewa na yi cikin jin daɗin hirar da muke yi a group ɗinmu. Don yanzu ban da matsalar data, Maman Nasmah tana saka mini ishashshiya tare da kati, chaji ma ban da matsalar shi saboda ta aiko mini da sabuwar power bank. Wani video Aunty Billy ta turo, da sauri na yi loading na buɗe, don yanzu duk wani motsinta akan idona yake. Wani haɗaɗɗen gida ne da ya gaji da tsaruwa gurin gini da kayan alatun da suka ƙara ƙawata shi. Gidan mai hawa uku ne, bedrooms da parlourn cikinsa kuwa kasa ƙirga su na yi, kuma kowanne da kaya a cikinsa. Na maimaita kalla ya yi sau biyar sannan na haƙura ba don na gaji da kalla ba. Abin da na ga ta rubuta ne ya saka ni tashi zaune a zabure ba tare da na shirya ba. Sake watching video ɗin na yi cikin zazzaro ido kamar zan saka su a cikin wayar. Ina nuna gidan da ɗan'yatsana na ce. "Kan uba! Da gaske ko da wasa?" Ban kai ga samun amsa ba kiran Maman Nasmah ya shigo, cikin rawar jiki na ɗaga. Ba tare da mun gaisa ba ta ce. "Kin ga abin da Aunty Billy ta turo?" Da rawar murya na ce. "Gidan da ta turo ta ce za su koma a Abuja ita da mijinta?" Ta ce. "Eh, kin ga abin da nake faɗa miki ko? Kina nan zaune sai ta gama tatike shi, wannan uban gidan ko ni mijina ba shi da kamar shi, ki yi ki yi ki bar gidan talakan nan amma abu ya gagara, na tabbata da tuni yanzu ke za ki shiga gidan, don yana ta damu na akan maganarki, ko ɗazu da safe ma ya kira ni, kuma ya ce da an yi auren naku Abujan zai kai ki." Wani yawu na haɗiye mai ɗaci cikin takaici na ce. "To ya zan yi? Anas ya ƙi saki na, na yi masa tijarar, na yi bala'in amma ya ƙi, ba fa na yin komai a gidan shi yake yi, sai ya kai shabiyun dare bai yi bacci ba yana ta kujiba-kujiba da aikin gida." Maman Nasmah ta ce. "Taɓ! Amma wannan mijin naki wanne Iri ne shi? Kamar ba zuciya a ƙirjinsa?" Na ce. "Bala'in haƙuri ne da shi, kuma idan bai ga damar yin abu ba babu wanda ya isa ya saka shi, kuma yana so na sosai, da ma na san da wahala ya iya rabuwa da ni." A zafafe ta ce. "Ba wani so, da yana son ki ai da ya yi miki duk abin da kike so, kawai dai ya san idan kuka rabu ba zai samu wadda zai dinga cuta ya dunkume a gida kamar ki ba ne, shi ya sa. Ni dai abin da na kira na faɗa miki ki yi sauri ki dage ku rabu a cikin satin nan, ki san duk yadda za ki yi ku rabu a wuce gurin. Saboda na gaji da yi wa Alhaji Kyauta ƙarya, kullum ta yau daban ta gobe daban, don ya ce mini shi aure yake da buƙata cikin gaggawa, idan abin nan ba zai yiyu ba ya haƙura kawai ya nemi wata." Da sauri na ce. "A'a, ba ni iya yau zuwa gobe kacal, na san me zan yi." Ta ce. "Ya fi miki dai."
Bayan mun gama wayar na ci gaba da kallon gidan ina hasaso kaina a ciki, da tuni ni ce zan wataya a cikinsa amma Anas ya yi mini buƙulu, ƙwafa na yi ina ayyana abin da zan yi masa yau idan ya dawo, wanda na san duk nacin shi dole ya rabu da ni.
Ina nan zaune na ji an buga gida, Sultan ya je ya buɗe suka dawo tare da mai bugun, Naja ce, kuma da alama daga gurin aiki take, don sanye take cikin fararen kaya na nurses. Ba yabo ba fallasa na amsa mata sallamar da ta yi. Bayan ta shigo ta yi wa kanta mazauni ta ce. "Hajiya Hafsah, ana ta sana'ar ne? Don na ga yanzu U are always online, ko garin ma ba kya ji." Fari na yi da ido tare da faɗin. "Na kusa zama Hajiyar dai in sha Allah." Ta ce. "To Ubangiji ya tabbatar ya nuna mana lokacin, da fatan kin gama fushin da kike yi da ni?" Yamutsa fuska na yi na ce. "Fushi kuma? Akan me?" Ta ce. "Eh mana, tun daga ranar da na zo ɗin nan shikenan ba kira, ba magana a chat bare ki zo gida kuma." Taɓe fuska na yi na ce. "Au babu komai to, Allah ne kawai bai nufa ba." Ba ta ba ni amsa ba sai wayar hannuna da na ɗaga ta ƙura wa ido, kamar wadda ta ga abin tsoro haka ta nuna wayar ta ce. "Hafsah! A ina kika samu wannan Iphone 14 ɗin?" Jujjuya wayar na yi na ce. "Tsohon zance, tun yaushe na yi ta, wata ƙawata ce da take auren hamshaƙin mai kuɗi ce ta siya mini, ta ce idan mijinta ya dawo ma za ta saka ya siya mini 15." Kamar Naja za ta yi kuka ta ce. "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Hafsah kina da hankali kuwa? Da kika karɓi wannan wayar mai tsada kin tabbatar saboda Allah ba da wata manufar ta baki ba? Kin ma ce wanda ta ba ki da farko an sace, ganin kayan kika yi ko kuma wasu ta ƙara siya miki?" A gadarance na ce. "Wasu ta sake siya." Shiru ta yi na wasu sakanni sannan ta ce. "Anya ba da wata manufar ta yi miki wannan kyautar ba? Hafsah ki dinga tunani da ƙwaƙwalwarki fa, kar son duniya da ruɗun shaiɗan su kai ki su baro." Tsaki na ja na ce. "Babu wata manufa sai ta alkhairi, kuɗi ne kawai da su, wannan ai ba wani abu ba ne a gurinsu." Ban jira cewar ta ba na buɗe wayata na koma kusa da ita na fara nunnuna mata abubuwan da suke turowa a group ɗin, tare da ba ta labarin gidajen waɗanda na je na gano. Tana kallon gidan da Aunty Billy ta turo ta ce. "Don Allah na tambaye ki mana?" Na ce. "Ina jin ki?"
"Wa ya saka ki a group É—in nan? Yaya aka yi kika tsinci kanki a cikinsa?"
Murmushi na yi na ce. "Ke ma ya burge ki ko? Ai group ɗin nan yana da shiga rai, duk wanda ya zauna a cikinsa ba ya iya fita, ga shi mutanen ciki duk ƴan gayu ne masu haɗin ka..." A ƙufule ta katse ni da faɗin. "Ni ba wannan na tambaye ki ba, yadda aka yi kika kasance a group ɗin nake son ji." Tashi na yi na koma inda nake da farko sannan na ce. "Wata ƙawata ce da muka yi islamiyya tare, ta turo link ɗin a group ɗinmu na ƴan'ajinmu, a nan na gani na shiga." Naja ta ce. "To ita ƙawar taki har yanzu tana cikin group ɗin?" Na ce. "A'a, kamar a ranar da na shiga ma ta fita, da muka haɗu kwanaki ta ce mini wayarta ce ta lalace, duk wanda muka shiga tare ma sun fice, sun ce ba za su iya da uban suturun da ake yi a group ɗin ba."
"Sai ke da rabon wahala yake jan ki shi ya sa kika zauna ko?" Ta faɗa cikin faɗa da ɗaga murya. A fusace na ce. "Ke Naja! Haifa ta kika yi ne da za ki dinga yi mini magana cikin faɗa da tsawa? Na gaji da abubuwan da kike mini, ki ƙyale ni, babu ruwanki da rayuwata, ki fita daga sabgata, ki tsaya iya matsayinki." Jinjina kai ta yi ta ce. "Na ji, amma ko da wannan ne karo na ƙarshe da zan faɗa miki gaskiya sai na faɗa miki."
"To ba na so." Na faɗa cikin ƙaraji.
Miƙewa ta yi tare da cillo mini wayata, a sanyaye ta ce. "Idan har kina cikin group ɗin nan ba za ki taɓa ganin duk wata gwanintar da Anas zai yi miki ba, saboda abubuwan da suke turowa na mahaukatan kudi, wanda duk da ban sani ba, rabi da ƙwata duk ƙarya ne. Amma irinki masu ƙaramar ƙwaƙwalwa ba za su gane hakan ba. Ko za ki ƙi ji, ko za ki ƙi amfani da shawarata ba zan fasa faɗa miki gaskiya ba. Anas namiji ne ɗaya tamkar da dubu, idan kika yi gangancin rabuwa da shi za ki yi danasani mara amfani, a lokacin da time ya ƙure miki." Tsaki na ja na ce. "To ko Anas ɗin za ki aura ne Naja? Tunda na ga kullum cikin yabon shi kike." Murmushi ta yi mai ciwo ta ce. "Tabbas da zan samu miji mai nagarta kamar Anas babu abin da zai hana ni auren shi, ko da kuwa ni zan dinga cikon kuɗin cefane, in dai ba shi da hali ne ba mugunta ba ce. Amma Anas babu aure a tsakanina da shi har abada, saboda kin riga da kin yi mana katangar ƙarfe da hakan. Ki saka a ranki har abada ni Naja ko da kin mutu ba zan taɓa auren mijinki ba. Gaskiya ce kawai nake faɗa miki." Taɓe baki na yi na ce. "Ba wani nan, kawai don dai talaka ne shi ya sa ba za ki aure shi ba, amma da mai kuɗi ne sanda za ki auren shi ma wa ya sani?" Cikin takaici ta ce. "Ke ce kuɗi yake gabanki, abin da ba ki sani ba ma ni zuwa na yi na faɗa miki an kawo kuɗina tun last month, an saka biki nan da 3 months." A sheƙe na ce. "Allah ya sanya alkhairi." Ta ce. "Amin na gode, duk da a wulaƙance kika amsa, saboda ina ɗora ki a turbar gaskiya, ki je ki ci gaba, ai ta ɗora ki a kan keken ɓera, KANKI ZA KI YI WA ba wani ba, don ba zan fasa maimaita miki ba ki da wani gata a duniyar nan bayan Ubangijin da ya halicce ki sama da Anas ba." Cikin ƙosasa da surutunta na ce. "Shi gatan ne da shi? Yanda ba ni da kowa shi ma hakan yake." Tana gyara zaman jakarta a kafaɗarta ta ce. "Shi namiji ne, ba shi da matsalar neman matallafi a rayuwa kamar ke, zai iya yin rayuwarsa shi kaɗai ma a cikin gidansa, amma ke kuwa a matsayinki na mace dole sai kina ƙarƙashin wani!" Tsaki na kuma ja ban tanka mata ba. Ta ce. "Hmm, Hafsah kenan, yau ni kike wa haka akan wasu can haɗuwar jiya-jiya?" Na ce. "Na yi ɗin, hurumin da ba naki ba da kika shiga shi ya janyo miki." Ta ce. "Haka ne, kowa rai ya yi wa daɗi babu kamar mai shi, in sha Allah daga yau ba zan ƙara yi miki magana akan wannan rayuwar da kika ɗaukar wa kanki ba." Cikin kora da hali na ce. "Ya fi miki alkhairi, ki sakar mini mara ki bar ni na yi rayuwata yadda na ga dama." Sallama ta mun ta tafi bayan ta ƙara yi mini bitar maganganunta da kwata-kwata ba su da mazauni a gurina, don tamkar amahin shata haka na ɗauke su. Ban da ƙona mini rai ma babu abin da suke yi. Na fara yarda da maganar Maman Nasmah da ta ce hassada da baƙincikin mu'amalata da ƴan gayu take yi.
Wunin yau cikin tufka da warwara na yi shi, don ko girkin rana ban yi ba, na jiƙa wa su Sufyan garin kwaki suka sha suka wuce islamiyya. Da suka dawo kuma na ba su ragowar abincin da suka ci da safe, na ce musu idan uban nasu ya dawo ya nemo musu abin da za su ci da daddare ko ya dafa musu. Ni kuma na ci biscuit ɗin da na siya da yawa na ajiye saboda da irin haka, na kora da ruwa. Daf da Magriba na ɗauko bola na wargatsa a tsakar gida da soro, na ɗebi ruwa na kwara a kai. Da kaina na fita ƙofar gida na ɗebo ƙasa na tila akai. Na yi hakan ne saboda Anas, don na san ba ƙaramin ɓaci ransa zai yi ba idan ya zo ya tarar da gidan a haka, saboda ba ya son ƙazanta ko kaɗan a rayuwarsa, ga shi da ƙyanƙyami, kuma kafin ya fita sai da ya share gidan tas. Toilet kuwa da Sufyan ya yi bayangida hana shi flushing na yi, na ƙara damalmala bakin masan na bar shi a haka, duk saboda ya gani ransa ya ɓaci. Da ƙyar Sultan ya iya yin alwala, sai kakkame jikinsa yake ya na ɓata fuska cikin ƙyanƙyami. Sufyan kuma ya na fitowa daga ɗaki ya kama bakinsa ya ce. "Mami wa ya yi mana wannan ƙazantar a gida?" Na ce. "Ban sani ba don ubanka." Jijjiga kai ya yi yana keɓe baki ya ce. "Taɓ, idan Abba ya dawo zai yi faɗa, ki yi sauri ki gyara kar ya zo ya gani." Ban kuma tanka masa har ya ƙaraci surutunsa ya yi shiru, Sultan kuwa da ya san ni na yi bai ce komai ba. Bayan ya idar da alwalar ya ɗauko tsintsiya zai fara shara na ƙwace na kora shi waje.
Tare da suka dawo da Baban nasu, ina daga É—akin su Sultan na ji yana cewa. "Mene wannan kuma a gidan kamar kwata ?"
Daga nan ban san ya aka yi ba sai ji na yi ya faɗi tim a cikin cakwalin. Da sauri na fito na haske shi, ganin shi na yi kwance male-male, ƙoƙarin tashi ya yi cikin hanzari, ban san lokacin da wata irin dariya ta ƙwace mini ba, saboda tozalin da na yi da fuskarsa ta yi dagaje-dagaje da ruwa da ƙasa da bolar da na zubar.........✍️

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.