Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Yiwa_Kai_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 18 of 34
Ina shiga cikin gida ana ɗauke NEPA, wani irin ƙunci da takaici ne suka cika ni, na tuno tunda na je gidan Maman Nasmah ko motsi wutarsu ba ta yi ba, haka ma gidan Aunty Billy. Tsaki na yi na zaro sabuwar wayata na kunna fitila na haska gidan. Kayan hannuna na fara kaiwa kitchen sannan na shiga toilet na yi alwala na yi Sallah. Bayan na idar na zauna bitar abubuwan more rayuwar da na gano, babban abin da ya fi burge ni yadda idan mutum zai shiga unguwar su Maman Nasmah sai an tsayar da shi a bakin gate ɗin ginin da ya zagaye unguwar, an tambaye shi gidan wanda zai je ya kira shi sun yi magana da security ɗin. Sabga cikin mutunci da arziƙi dai. A cikin gidanta kuwa babu wani abu mara kyau da ƙayatarwa, toilet kaɗai ya isa ɗauke wa mutum dukkanin damuwarsa saboda tsananin kyansa, ga fanfon ruwan sanyi daban na ruwan zafi daban. Gabaɗaya yanzu da na gan ni a gidana sai na ji duk na ƙuntata, kamar ba na samun wadataccen nunfashi ma tsabar ƙanƙantar gidan.
Sai wajen goma ya shigo gidan shi da su Sultan, bai kula ni ba, ni ma ko kallon shi ban yi ba. Na É—auki abincin da na taho da shi muka ci tare da Æ´aÆ´ana, muna ci suna labarin gidan da suka je, bayan na gama shan uwar tambayar ina na je na tafi na bar su.
Ni kaɗai na kwanta a ɗakina don Anas ko parlour'n bai shigo ba, na gane nufin shi, so yake na je na ba shi haƙuri, ni kuma abin da bai isa ba kenan a yanzu, don ba zan iya fama da talauci da faɗin rai ba.
Kusan raba dare muka yi muna hira da Maman Nasmah, ta ba ni labarin abubuwan da aka tattauna bayan na taho, ni kuma na faɗa mata yadda muka kasance da Abban Sultan. Ta ce ko za mu shekara a haka kar na sake na ba shi haƙuri, don ita mijinta tunda suke ba ta taɓa ba shi haƙuri don ta yi masa laifi ba, ko ita ce mara gaskiya shi yake bin ta yana lallaɓa ta. Ina ta son na ba ta labarin biyo nin da mijin Aunty Billy ya yi amma har ta sauka daga online ban faɗa mata ba. Yau ma sai na ji na kasa bacci, saboda yadda gadona tun na aure yake ta ƙarar tsufa, ga katifar duk ta lotse, ta wani gurin har layi-layin katakon karagar gadon ana jiyowa. Luntsumemen gadon da na kwana a kai jiya kawai nake tunowa, na san da shi ne da tuni bacci ya ɗauke ni yadda na kwaso gajiyar nan. Tashi zaune na yi ina firfita saboda zafin da ya addabe ni da sauron da yake ta mun kuwwa a kunne duk da na ɗaura net. Na san in dai ba nepa aka kawo ba, ba zan taɓa iya bacci a cikin wannan izayar ba. Jiya na kasa bacci saboda kewar ƴaƴana da mijina duk da ina cikin ɗakin da babu wani abu na wahala zai hana ka bacci, yau kuma ga ni a tare da iyalin nawa, amma azabar sauro da zafi sun hana ni bacci. Kenan da a irin gidansu Maman Nasmah nake tare da ƴaƴana da mijina babu abin da zai dame ni bare ya hana ni bacci? Jinjina kaina na yi ina ayyanawa a raina ko ta halin ƙaƙa sai mun bar gidan nan mun koma wani ƙato wanda ya haɗa komai na rayuwa nan kusa, don na gane kamar yadda ba zan iya rayuwa ba su Sultan ba haka ba zan iya ci gaba da zama a cikin talauci da ƙuncin rayuwa ba. Tilas ko ni ko Anas mu nemo kuɗi ko a ina ne mu yalwata rayuwarmu.
'To amma ni a ina zan samo?' Zuciyata ta yi mini wannan tambayar.
Mijin Aunty Billy da one million É—in da ya ce zai ba ni don kawai na saka kati ne ya faÉ—o mini a rai, tamkar shi ne amsar tambayar da zuciyata ta yi mini........âœï¸
*Zeey Kumurya*
[3/8, 1:41 PM] BahaushiyaðŸ‘: *YI WA KAI*
MIKIYA WRITERS ASSOCIATION
*BRIGH PENS*
(FREE BATCH)
*16.*
Saurin girgiza kaina na yi. A fili na ce. "Ba zan iya yin abin da yake buƙata ba, ina kuma roƙon Ubangiji ya tsare ni da aikata hakan har abada. Zan nemi wata hanyar dai daban." Ci gaba na yi saƙawa da kwancewa har bacci ya ɗauke ni.
Washegari bayan sallar asuba na janyo wayata na hau online, har su Sultan suka tafi school ban sauka ba bare na yi yunƙurin yin aikin gida. Shi ya shirya su ya yi musu komai, tsakani na da su gaishe nin kawai da suka zo suka yi na amsa ne. Kafin ya dawo daga kai su na fita na ɗauko ragowar abincin jiya don na fara jin yunwa na ci na yi wanka na shirya. Ina zaune a bakin gado Anas ya shigo ɗakin ya buɗe wardrobe, kamar na share shi kamar yadda ya yi mini sai na fasa na ce. "Ina kwana?" Ba tare da ya juyo ya kalle ni ba ya ce. "Lafiya ƙalau." Ban san me ya hau kaina ba na tsinci kalmar haƙuri ta subce daga bakina zuwa gare shi, don ganin da na yi masa yanzu sai na ji wata irin kewa da son kasancewa da shi sun baibaye ni. Duk yadda na so ɗaurewa amma na kasa, sai da na bayyana masa abin da yake nuƙurƙusa ta. Bai ƙi ba ya biye mini ba tare da ya nuna mini wani abu na ɓacin rai ko kaɗan ba. Sosai ya nuna mini soyayyar da na yi wa kaina buƙulun samun ta na tsawon kwanaki, ni kaina na san samun namjin da ya iya soyayya da taraiyar mace kamar Anas zai yi wahala.
Wajen ƙarfe sha daya ya shirya ya fita a gaggauce saboda makarar da ya yi. Ya na ficewa na bi bayansa zuwa gidan Maman Nasmah saboda uban kiran da take doka mini. Ina zuwa gidan nata ko zama ban yi ba ta dube ni cikin faɗa ta ce. "Wai me kika tsaya yi a gidan ne? Ina ta kiran ki kika ƙi ɗauka, kin san kuma dalilin kiran." A ladabce na ce mata. "Ki yi haƙuri, bari na yi sai ya fita, don yanzu ma ko tambayar shi ban yi ba na fito." Baki ta taɓe ta ce. "Aikin kenan, tsoron miji kamar wani mala'ika, sai ki je ku tafi, don su Maman Suhail suna ta kira na wai za su taho, ke ma sun kikkira ki ba ki ɗauka ba." Na ce. "Eh, duk na ga missed call ɗin da ina hanya."
Sai da ta ba ni wata abaya mai kyau sabuwa na saka sannan muka tafi, don cewa ta yi kayan jikina ba su yi ba, marasa tsada ne, duk da ƙurewar adakar da nake ganin na yi.
Madaidaicin gida ne mai kyau guest house É—in nasu, sama da Æ™asa ne, ga shi ya sha kayan furnitures masu kyau da tsada. Sai na ji da ma zai zama gidan nawa a gaske, don ko iya shi na samu burina ya gama cika. Kusan su goma ne suka zo, muka sha hira da hotuna. Na dinga kai wa da komowa ina jin kaina na kumbura. Akwai komai na amfani a gidan, kuma fes muka tarar da shi kamar mutane suna rayuwa kullum da kullum a cikinsa. Abinci da drinks É—in da Maman Nasmah ta aiko sun wadata sosai, don har ragowa suka yi. Sai yamma lis suka tafi, ni kuma sai bayan Magriba na bar gidan ba don na so ba na koma gidan Maman Nasmah. A gaggauce na yi mata sallama na wuce gida, bayan ta nace sai na kwana ni kuma na Æ™i. Don na ga Abban Sultan yana ta kira na. A gidan na tarar da shi ya cika ya yi fam, na yi sallama ya amsa ciki-ciki. Sai da su Sufyan suka koma É—akinsu na dube shi na ce. "Ka yi haÆ™uri don Allah, wani babban uzuri ne ya fitar da ni." Jinjina kai ya yi ya ce. "Shi ne kuma ya sa kika Æ™i neman iznina? Kika je kika kai har dare? Kin san yaran nan za su dawo daga school amma ba ki damu da halin da za su shiga ba idan sun dawo ba kya nan? Ba ruwanki sabgar gabanki ce kawai ta dame ki." Æata fuska na yi na ce. "Yanzu fisabilillahi daga dawowata sai ka tarÉ“e ni da faÉ—a? Ko hutawa ai ka bari na yi, kuma ba ka san lafiya nake ba ko ba lafiya ba." Cikin takaici ya ce. "Na san Æ™alau kike Hafsah, a zatona maganganun da muka yi É—azu komai ya wuce, za ki yar da sabbin halayen da kika tsiro ki zo mu koma rayuwarmu kamar da, amma tunda har yanzu da saura ki ci gaba, sai dai ina so ki sani ba zan É—auki wannan gantalin yawon da kika tsiro da shi ba." Daga haka ya miÆ™e ya fice daga É—akin. Raka shi na yi da harara tare da jan dogon tsaki, don ni ta gidan da na baro mai AC da wutar nepa kodayaushe nake ba ta shi ba. Bayan na yi Sallah na kira Maman Nasmah muka sha hira, na dinga kwarara mata godiyar fitar da ni kunyar da ta yi, har za mu yi sallama na tsayar da ita na ba ta labarin duk yadda muka yi da mijin Aunty Billy. Shiru ta yi har na yi tunanin ko kiran ya katse ne sannan ta ce. "Hmmm, ai shiru kawai na yi miki na ji ko za ki mun zancen da kanki, don bayan an tashi daga taron ya bi ni har gida ni ma. Har na tsorata ya ce ya kwantar da hankalina, wadda ya gan mu tare ya gani yake na so, kuma da aure yake son ki shi da gaske yake, saboda bai taÉ“a tunanin matar aure ce ke ba, shi ne ya ce bari ya gwada ki da farko ya ga irinki, don tun kafin magana ta yi nisa gara ya san irin matar da zai aura." Ajiyar zuciya na sauke na ce. "Haba, ni fa na yi mamaki sosai, na ce ga shi kamar kamilalle ashe ba haka ba ne." Da sauri ta ce. "TaÉ“, ai mutumin kirki ne sosai, don ko a unguwarsu ba ki ga yadda ake yabon shi ba, ga shi da kyauta da sadaka, kawai ya yi hakan ne don ya gwada ki, ai ya faÉ—a mini komai bai É“oye mini ba." Na ce. "Allah Sarki, har ina munana masa zato." Dariya ta yi ta ce. "Ai kuwa kin É—auki haƙƙin shi, don son tsakani da Allah yake yi miki, so na gaskiya. Saboda a maganganunsa na fahimci ba Æ™aramin so yake yi miki ba, ga dukkan alamu ya kamu da yawa." Na ce. "Uhm, shi ya sa abin da yake ta damu na, ni kaÉ—ai na dinga cewa ya san ina tare da matarsa ya yi mini maganar banza, ko tsoron na faÉ—a mata bai ji ba." Da sauri ta ce. "To kin gani? Wannan ma kaÉ—ai ya ishe ki gane ba halinsa ba ne, don ba haka Æ´an iskan mazan suke ba, daga ganin ki ya fara yi miki magana wadda ba ta kamata ba, ba tare da ya san wace ce ke ba, kuma a sanadiyyar matarsa ya san ki. Ai Æ´an iskan sai sun ja mutum a jiki sannan suke bayyana musu buÆ™atarsu." Na ce. "Haka ne kuma." Ta ce. "To yanzu dabara ta rage wa mai shiga rijiya, ke ce wuÆ™a da nama suke hannunki, don wannan wata gwaggwaÉ“ar dama ce da kika samu ta cikar burinki cikin sauÆ™i." Cikin rashin fahimta na ce. "Ban gane ba, kamar yaya?"
"Ya kamata ki gane kuwa, saboda abin a zahiri yake, ki rabu da wannan faƙirin mijin naki ki zo ki auri mijin Aunty Billy, ki zama matar mai kuɗi ke ma kamar yadda kike fata."
Dafe ƙirji na yi cikin zaro ido waje na ce. "Na kashe aurena kenan?" Ta ce. "Eh mana, mene a ciki to?" Na ce. "Gaskiya da akwai damuwa, ina son mijina kuma ban san rabuwa da shi da ƴaƴana, sannan kuma na rasa wa zan aura sai mijin Aunty Billy? Duk yadda muke da ita?" Tsaki ta yi ta ce. "Daɗina da ke ƙwaƙwalwarki ba kodayaushe take ja ba, ai idan kun rabun da ƴaƴanki za ki tafi ba barin su za ki yi ba, wannan mijin naki kuma mene abin damuwa a rabuwa da shi? Kin samu dama amma kina ƙoƙarin yin wasa da ita. Idan kin auri mutumin nan ba ƙaramin hutawa za ki yi ba, ki wataya son ranki, ƙasashen waje kuwa duk wadda kike so ita za ki je ki shana a lokacin da kike so. Aunty Billy kuma duk yadda muke da ita ai bai kai yadda muke da ke ba, ina son ganin kin ci gaba ke ma a rayuwa kin zamto kamar mu, don haka akan wata can Billy ba zan ƙi taimakonki ba. Ki tsaya ki yi tunani da kyau kar ki yi wa kanki sagegeduwa, mutumin yana da bala'in kuɗi, kuma a zuwan da ya yi muka zanta ba ƙaramin son ki na fuskanci yana yi ba, da na ce masa kina da aure ba ki ga yadda ya ruɗe ba." Numfashi na sauke ina hasaso kaina a ƙaton gida matsayin mallakina, ina hawa mota driver yana ja na, ga suturu na alfarma da zan dinga sakawa. Na tuno tarin masu aikin Aunty Billy, na san ni ma idan na aure shi haka zai ɗibar mini su, su dinga mun komai ina daga kwance. Jin na yi shiru ya sa ta ce. "Bari na bar ki, ki yi tunani, amma ni da za ki ɗauki shawarata da kin amince kawai, sai ki bar komai a hannuna, na san me zan tsara na faɗa masa. Ƙarin abun daɗin kuma bai taɓa haihuwa ba, matsalar kuma daga Aunty Billyn ne ba daga shi ba, don mun taɓa maganar da ita. Kin ga da kin je kin fara haihuwa zai ɗauki son duniya ya ɗora miki ke da ƴaƴan, da ma ga shi ke uwar maza ce, sai ki ta haifa masa su, dukiyarsa da komai nasa su zama mallakinsu." Cikin ɗaurewar kai na ce. "Yanzu ni na rasa ta cewa ma, amma ki ba ni zuwa dare, zan yanke shawara." Ta ce. "Tom shikenan Allah ya kai mu."
Bayan mun gama wayar na miƙe na fara safa da marwa ina saƙawa da kuncewa. Tabbas Maman Nasmah gaskiya ta faɗa mini, wannan wata dama ce da na samu, amma inda matsalar take Kawu nake ji da hukuncin da zai ɗauka a kaina idan ya san ni na kashe aure na, sai kuma kallon da ƴan group ɗinmu za su yi mini idan suka ji labarin na auri mijin Aunty Billy, da ita kanta ma. Amma duk wannan bai kai son rayuwar kuɗin da nake yi tasiri a cikin raina ba, don sosai nake ji a jikina na kusa kaiwa matakin da nake so na zama matar hamshaƙi. Hango mutumin kawai nake da cikar kamalarsa da yadda kuɗi ya bayyana ko ta ina a jikinsa, alamun ya jiƙu a cikinsa.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.