Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Yiwa_Kai_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 32 of 34
*Zeey Kumurya*âœï¸
[3/8, 1:45 PM] BahaushiyaðŸ‘: *YI WA KAI*
MIKIYA WRITERS ASSOCIATION
*BRIGH PENS*
(FREE BATCH)
*27.*
Tuno yadda Kareema ta dinga jaddada mini sai na cire tsoro da fargaba na ari juriya da wayo sannan zan yi nasara na yi. Hakan ya sa na aro jarumta da dakiya na sunkuyar da kaina ƙasa na fara tarin ƙarya da dukkan ƙarfina. Galala ya dube ni ya ce. "Mene ne haka?" Cikin shaƙaƙƙiyar murya ina tarin kaɗan-kaɗan na ce. "Ulcerta ce ta tasar mini, da ma haka take yi time to time." Na ƙarasa maganar ina lumshe idona. Cikin takaici ya ce. "Me ya sa ba ki nemi magani ba? Ina nunbern my family doctor ɗin da na tura miki na ce idan ba ki da lafiya ki kira shi?" A wahalce kamar ciwon gaske na ce. "Bayan na baro ɗakinka bacci na yi ne, sai yanzu na tashi na yi wanka, rashin cin abinci ne." Bai ce komai ba ya samu gefen gado ya zauna. Sai da na gama sassauke numfarfashina sannan na tashi na zubo abinci, na sako spoon biyu. A gabansa na ajiye na ce. "Sakko mu ji." Fuskarsa babu fara'a ya ce. "Na ƙoshi." Karyar da murya na yi na ce. "Ka ƙara ci mana, yau ne fa farkon amarcinmu, ko ka taɓa ganin inda amarya ta ci abinci ita kaɗai ba tare da angonta ba?" Taɓe ya yi ya ce. "Ai ni ba irin sauran angwayen ba ne kin sani." Ƙara marairacewa na yi na ce. "Please, ko kaɗan ne ka ci." Tsaki ya ja ya sauko yana faɗin. "Ban taɓa auren macen da ta yi mini haka ba sai ke, anya kuwa haka kika bar ni?" Murmushi na yi na ce. "Babu abin da na yi maka, kawai ni ɗin ce ƴar baiwa." Ƙura mini jajayen idonsa ya yi, har lokacin spoon ɗin kawai ya riƙe bai kai abincin bakinsa ba, tabbacin akwai abin da yake nazari. Ban bari ko da wasa wani abu ya bayyana akan fuskata ba, ban kuma ƙara yi masa maganar ya ci abincin ba gudun kar ya yi wani tunanin daban. Sai ma ƙasa da na yi da kaina na ci gaba da cin abincina, cikin mamakin yadda har yanzu bai nemi wani abu ya suturce jikinsa ba, kuma hankalinsa kwance yake sha'aninsa, ya bar ni da aikin kau da kai. Sai day na kusa cinyewa ya yi three spoon. Hakan ya sa na tashi da sauri na zuba masa juice a glass cup, ya ɗauka ya ɗiɗɗike, na ƙara masa ya ƙara shanyewa. Ajiyar zuciya na sauke a hankali, na tattara kayan na fice da shi ba tare da na sha drink ɗin ba. Na yi kusan five minutes kafin na dawo ɗakin, ina taku bugun zuciyata yana ƙaruwa da sauri da sauri saboda fargabar abin da zan je na tarar. Har na mayar da ƙofa na rufe ban kalli inda yake ba, kaina a ƙasa na ƙarasa bakin gadon. Ina neman taimakon Ubangiji a cikin raina na ɗago na kalle shi, kallon da na ga ya yi mini ne ya saka ni jin mummunar faɗuwar gaba. Kafin na yi magana na ga ya nuna ni da hannu tare da faɗin. "Keee! Me kika ba ni ne na ji kaina yana juyawa?" Daga yadda ya yi maganar na san maganin ya fara aiki kenan. Ban ce komai ba na ja baya na ɗauki wayata tare da tsayawa ina kallon shi yadda ya riƙe kansa yana yin wasu irin abubuwa. Jikina har rawa yake saboda rashin sanin takamaiman abin da nake ji, tsoron abin da zai biyo baya ko farincikin samun nasara ne ban sani ba? Kamar mai tafiya a kan ruwa haka na ja ƙafata na koma gabansa na ce. "Mansur." Ya ce. "Uhm." Tare ware jajayen idonsa a kaina.
"Ka san ni? Idan ka san ni wace ce ni a gurinka" Na tambaye shi ina nuna kaina.
Ya ce. "Eh mana, matata ce ke." Ina sauke ajiyar zuciya na ce. "So nake ka sake ni, ka ce na sake ki Hafsah har sau uku." Baya ya yi ya kwanta ya ce. "Ba zan faɗa ba ɗin, banza kawai." Ban karaya ba na ce. "Sai ka faɗa, saboda ni bana son ka, ba na ƙaunar zama da kai." Hannunsa riƙe da kansa ya ce. "Kaina zai tarwatse, ki cire mini abin da kika sa mun a cikinsa." Sai da na ɗauko takarda da biron da already na tanade su na miƙa masa na ce. "To sai ka yarda za ka rubuta duk abin da na ce maka, in ba haka ba, ba zan cire maka ba." Da sauri ya karɓa ya ce. "Me kike so na rubuta? Zan rubuta, in dai za ki cire mini wannan abun daga cikin jikina!"
"Saki, ka rubuta ni Mansur Ibrahim Idonnera na saki matata Hafsah har saki uku." Na faɗa cikin tarar numfashi. Kamar ɗan koyo haka ya riƙe pen ɗin ya rubuta ya cillo mini." Ban ɗauka ba na danna record cikin rawar jiki, muryata ɗauke da kukan ƙarya na ce. "Me ka rubuta? Ka faɗa da bakinka na ji."
"Na sake ki! Na sake ki! Na sake ki! Tunda kashe ni kike son yi, kin zuba mini tsutsa a kaina sai yawo take mun." Ya faɗa slowly tare da lumshe idonsa gabaɗaya. Wata irin ajiyar zuciya na sauke kamar zuciyar za ta daina aiki, na yi saved ɗin recorded da tun a gurin cewa na sake ki na uku da ya yi na yi stopping ɗinsa, ban bari sauran maganar tasa ta fito a ciki ba. Hannuna kamar ana kaɗa mazari saboda rawa na ɗauki takardar na linke na miƙe. Bin sa na yi da kallo, ya yi ɗaiɗai a kwance kamar gawa, ƙirjinsa da yake ɗagwa da sautin numfashinsa shi ya tabbatar mini a raye yake. Tamkar mai tafiya a kan wuta Saboda sauri haka na bar bedroom ɗin na fice parlour, a kan tiles na zube ina mayar da numfashi kamar wadda na sha tseren gudu. Tamkar a mafarki haka nake ganin faruwar al'amarin, ji na yi kaina yana juya mini, dafe shi na yi ina maimaita Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un a fili. Na rasa me ma zan yi? Barin gidan ko kuma jiran ya farko ya dawo cikin hayyacinsa? Wani irin tsoro da ban taɓa tsintar kaina a cikin irinsa ba ne ya lulluɓe ni, na fargabar kar ya mutu ko kuma wani abun ya same shi na shiga uku. Ban san lokacin da na ɗauka zaune a gurin ba kafin na tashi na koma ɗakin, a gurguje na ɗauki jakata da na gama haɗa duk wani abu mai muhimmanci nawa na fice, har lokacin yana nan yadda na bar shi.
ÆŠakinsu Lami na je na zauna, suka bi ni da kallo amma babu halin tambaya. Ko ta kansu ban bi ba na kira Kareema a ruÉ—e na ce. "Na kammala komai fa, kuma successfully yadda muka tsara."
"Alhamdulillah! Na taya ki murna sosai wallahi, Ubangiji ya ba ki wani na gari." Ta faÉ—a cikin farinciki.
Ban amsa ba na ce. "Ni halin da na baro shi ne hankalina bai kwanta da shi ba, ina tsoron kar wani abu ya same shi." Ta ce. "Babu abin da zai faru, nan da mintuna za ki ga ya miƙe, sai da na tabbatar da ingancin ƙwayar sannan na siyo ta, wallahi Hafsah ba ƙaramin shiri na yi ba saboda kawai na taimake ki." Cikin ƴar nutsuwar da na fara samu na ce. "Shikenan, na gode sosai Allah ya saka da alkhairi." Ta ce. "Amin, ki kwantar da hankalinki fa, na ji duk a ruɗe kike, bari na je na ɗauko Maman Hanif mu shigo tare." Na ce. "Kar ya gane haɗa baki fa muka yi abin ya shafe ku?" Murmushi ta yi mai sauti ta ce. "Kar ki damu, komai cikin dabara da wayo za mu yi, ke dai kawai da ya fito ki kira ni." Na ce. "Tom shikenan." Tare da katse wayar. Runtse idona na yi na dafe ƙirjina saboda bugun da yake yi mini kamar zai bar jikina. Addu'a kawai nake a cikin raina, don ban taɓa shiga tashin hankali irin wannan ba a rayuwata. Na rasa sunan da zan kira wannan ƙaddararren auren da yin shi ya zamar mini bala'i, saki kuma yana ƙoƙarin saka mini ciwon zuciya saboda fargaba. Kamar na yi tsuntsuwa na gan ni a gidan Kawu haka nake ji.
Daf da Magriba na hango shi yana saukowa ta windown da na yaye labule saboda ganin wajen, lokaci ɗaya ajiyar zuciya da faɗuwar gaba suka yi mini rufdugu. Cikin azama na kira Kareema na sanar mata, ta ce suna bakin gate ga su nan shigowa. Ina zare ido kamar mara gaskiya na tashi na fita, bayan na ƙanƙame wayata da takardar sakin. A bakin ƙofa na tsaya a ɗarare ina kallon shi, tsaf da shi ya sha babbar riga, kamar mutumin ƙwarai. Wani mugun kallo ya jefe ni da shi ya ce. "Well-done! Ƴar matsiyata, sannun ki da ƙoƙarin ha'intata." Mannewa na yi a jikin ƙofar na fara rarraba ido ban ce komai ba. Yatsun hannunsa ya harɓa suka bayar da sautin daf-daf sannan ya ce. "Ba zan kula ki ba a nan a gaban masu aikin gidana, saboda kar mutuncina ya zube, amma za ki yi mini bayanin abin da kika saka mini da dalili anjima." Daga haka ya nufi ƙofar barin parlour'n, kafin ya ƙarasa doorbell ta fara ƙara, Laure da ke kitchen ta fito a guje ta je ta buɗe bayan ta yi mana sannu, babu wanda ya amsa mata.
Kareema ce ta fara shigowa, sai mijinta sai Maman Hanif. Kallo ɗaya na yi musu na sunkuyar da kaina ƙasa. Da fara'a ya tarɓe su kamar ba shi ya gama yi mini magana cikin hargagi da murtukewar fuska yanzu ba. Shi ya ba su gurin zama, suka gaisa cikin mutuntawa. Daga inda nake na gaishe su, Mijin Kareema yana duban shi ya ce. "Ɗazu da safe zan fita na ga shigowarka, da na dawo na tsaya na tambayi maigadi kai ne maigidan? Ya ce eh, yau ka dawo. Shi ne na ce idan na huta zan shigo mu gaisa, tunda na tare ba mu taɓa haɗuwa ba, kuma gidana ne na bayan naka." Murmushi Mansur ya yi ya ce. "Allah Sarki, ka kyauta kuwa, na gode sosai." Ya nuna Kareema ya ce. "Wannan ce mai ɗakin tawa, wannan kuma ta nan gidan jikin gidanka ce, mun fito muka haɗu da ita za ta shigo ita ma." Sheshsheƙar kukana ce ta hana shi maganar da ya buɗe baki zai yi, da sauri Maman Hanif ta ce. "Kamar kuka ko?" Kareema ta ce. "Eh, Aunty Amarya ce kuma take yi, lafiya?" Ta ƙarashe maganar idanunta a kaina. Cikin pretending ina cikin matsanancin tashin hankali na ɗora hannuna akai na ce. "Don Allah ku ba shi haƙuri, ni na ba shi ya ƙi haƙura, ku taimake ni kamar yadda Allah ya taimake ku!" Cikin mamaki Maman Hanif ta ce. "A'a, me ya faru? Ba rakiya za ki yi masa ba da ma ganin kun da muka yi?" Girgiza kai na yi na tashi a haukace na cilla mata takardar hannuna na ce. "Duba ki gani, wai ya sake ni, kuma ban da kowa, ban da wani sauran gata sai shi, don darajar Allah ku ce masa ya mayar da ni. Ya ɗauki wani matakin a kaina kowanne ne zan jure amma ban da wannan, ba zan iya ɗauka ba, ya yi mini tsauri da yawa." A firgice ta miƙe ta ce. "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Har saki uku!" Tashi ya yi shi ma ya ce. "What?" Tare da tsare ni da ido cikin wani irin yanayi. Sai a lokacin mijin Kareema ya yi magana ya ce. "Subhanallahi! Ashsha! Saki kuma? Alhaji me ya yi zafi?"
Karɓar takardar Kareema ta yi fuskarta ɗauke da tashin hankali ta ce. "Ko dai ba ki gani daidai ba ne Aunty Hafsah?"
"Zan fi kowa farinciki idan haka ne, shi ya sa na ba ku, ku duba ku gani ko idona ne yake yi mini gizo." Na faɗa ina ƙara rushewa da kuka.
Dafe kanta ta yi tana salati, Maman Hanif da sosai ruɗu ya bayyana a kan fuskarta ta ce. "I'm speechless!" Satar kallon Idonnera na yi na ga ko motsi ya kasa yi, alamun suman tsaye ya yi saboda tsananin mamaki. A hankali na sauke numfashi tare da ɗauke idona daga kansa, mijin Aunty Kareema da ya karɓi takardar ya duba ya ce. "Aikin gama ya riga da ya gama, har saki uku! Irin wanda Allah ba ya so, garin yaya haka ta faru Alhaji? Da na san abin da za mu tarar kenan da ba mu shigo ba." Dogon numfashi ya ja ya sauke, yana karɓar takardar tare da dubawa ya ce. "Ƙaddara ce kawai, ka san aure rai ne da shi, idan Ubangiji ya rubuta ya ƙare ko second ɗaya ba zai ƙara ba sai an rabu, ko ana so ko ba a so." Mijin Kareema ya ce. "Haka ne, Allah ya sa mu dace mu fi ƙarfin zuciyarmu, har an shiga sallar Magriba, mu za mu tafi Allah ya kiyaye gaba."
Zubewa na yi a ƙasa na ɗora hannu aka, ina kuka na ce. "Kar ku tafi ku bar ni ba ku saka ya mayar da ni ba don Allah." Cikin tausayawa Maman Hanif ta kama ni ta miƙar da ni tsaye, tana gyara mini hijabin jikina ta ce. "Ki yi haƙuri, ki yadda da ƙaddara, shi ne cikas imani." Ban ce komai ba na ci gaba da kukan da babu yadda za a yi mutum ya ce ba har cikin zuciyata yake ba. Sosai na hangi mamaki da ruɗu da shock a fuskar Alhaji Mansur, bi na kawai yake yi da wani irin kallo da na kasa gane ma'anarsa. Bai kuma magana ba ya juya ya fita bayan ya yar da takardar. Lallami da ban baki Maman Hanif tai ta mun kamar za ta yi kuka, sai haƙuri take ba ni, gami da yi mini nasiha. Kareema kuwa ba ta koma gida ba sai da ta tabbatar na bar unguwar, ko tsinke ban ɗauka ba daga ni sai jakata, ko kayan sakawa ban bi ta kansu ba, ni dai tunda burina ya cika ji nake kamar an tsunduma ni a cikin aljanna, sai godiya ga Allah kawai nake yi.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.