Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Yiwa_Kai_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 13 of 34
*Zeey Kumurya*âœï¸
[3/8, 1:39 PM] BahaushiyaðŸ‘: *YI WA KAI*
*BRIGHT PENS*
(FREE BATCH)
*11.*
Cikin matuƙar gigita da ɗimauta na koma ɗaki kamar wadda ta rasa duk danginta, na ƙara duba ko'ina har inda kayan ba za su shiga ba amma still ba ta sauya zani ba. Tamkar ledar da ke narkewa a wuta haka na zube a tsakar ɗakina na baje a kwance ina sakin numfashin wahala.
"Na shiga uku! Su kuwa kayan ina suka shige? Idan har ta tabbata ɓata suka yi na gama kaɗewa har ganyena!" Na faɗi haka a fili ina ɗora hannuna akai daga kwancen da nake. Kamar ɓeran da ya hangi kyanwa haka na miƙe zumbur na fara laluben inda na cilla wayata, da ƙyar na gano ta a cikin kayan sawarmu da na yi musu ɗaiɗai a tsakar ɗakin kamar na rabon gado. Wani farfar na ga tana yi, a hakan na lalubo numbern Anas na yi Dialing. Sai da ta kusa katsewa ya ɗaga bakinsa ɗauke da sallama. Ban bari ya ƙarasa ba bare na amsa na ce. "Anas ka ɗaukar mini kayan nan da matar nan ta ba ni ka sauya musu gurin ajiya ne?" Ajiyar zuciya na ji ya sauke bai ce komai ma. A harzuƙe na ce. "Magana fa nake yi maka." Yana sauke numfashi ya ce. "Relief nake samu, don yadda kika yi magana cikin tashin hankali na ɗauka mutuwa za ki faɗa mini an yi." Cikin ƙufula na ce. "To ba gara mutuwar da wannan rasa kayan da na yi ba, kayana fa Anas wanda zan yi fitar kunya da su gobe? Don girman Allah da darajar su Inna idan ka gan su ko kai ɓoye ka dawo ka ba ni! Don Allah ba don ni ba, wallahi idan ta tabbata kayan nan sun ɓata zuciyata za ta iya bugawa." Na ƙarashe maganar tare da fashewa da kuka. Cikin lallami da son kwantar mini da hankali ya ce. "Ki nutsu dai ki duba su da kyau Hafsah, don ni tun ranar da kika nuna mini su ko ƙyallin ledar da suke ciki ban ƙara gani ba, don haka suna gidan, tunda babu mai shigowa bare ya ɗauka." A ruɗe na ce. "Ba sa nan, wallahi na duba ko'ina har toilet da cikin bola ban gan su ba, ba sa nan fa Abban Sultan, don Allah ka taimake ni ka zo ka taya ni dubawa, ko idona ne ya makance daga ganin su." Ya ce. "Tom shikenan gani nan." Na ce. "Yawwa, ka yi sauri." Daga haka na kashe wayar.
Duk da gajiyar da na yi sai da na ci gaba da bincike kafin ya ƙaraso. Ina cikin yi tunanin kiran Maman Nasmah na sanar mata halin da ake ciki ya faɗo mini, da sauri na ɗauki wayar na kira ta, kamar mai dakon kiran ta ɗaga da sauri, don ni ko ringing ban ji ta yi ba. Ina share hawayen da ya yi male-male a kan fuskata na ce. "Takwara ina cikin tashin hankali, ban ga kayan da kika ba ni ba gabaɗayansu." Cikin mamaki ta ce. "Kamar ya ba ki gan su ba? Wanne kaya ma tukunna?" Na ce. "Wanda zan saka gobe mana? Komai da komai ɗin da kika aiko mun da shi fa, har sarƙar gold ɗin!" Numfashi ta sauke ta ce. "To ai ni ban ga abun damuwa ba a nan tunda kin san wa zai ɗauka?" Da sauri na ce. "Sai dai in aljanu ne, amma ko Abban Sultan bai san inda na ajiye su ba, saboda ɓoyo nake yi musu kamar na ganin mutuwa." Ta ce. "To ko na ganin ƙiyama ne ga shi nan mijinki ya gani ya sace."
"Sata kuma?"
"Eh mana, to idan ba shi ba wa zai ɗauka? Su Sultan ƴaƴanki ƙanana ko kuma kin yi wani baƙon ne a gidan ban sani ba?"
Cikin ɗaurewar kai na ce. "Babu wanda ya shigo gidan ma tunda kika kawo kayan bare baƙon zama, daga ni sai mijina da ƴaƴana a gidan, kuma na kira shi tun ɗazu na tambaye shi ya ce ko ganin su bai yi ba, balle ya ɗauka, Abban Sultan ba ya ƙarya, da ya ɗauka zai faɗa mini wallahi, ko da wasa yake mini yadda ya ji hankalina ya yi mugun tashi zai ce shi ya ɗauka." Dariya na ji ta sheƙe da ita kamar sabon kamu, tana dariyar ta ce. "Lallai Namecy har yanzu da sauran ki a karatun ɗa namiji, to bari ki ji, ko rantsuwa na yi ba zan yi kaffara ba shi ya sace kayan zai je ya siyar, ƙila ma ya daɗe da cin kasuwarsu, ke kina nan kina cewa ba zai ɗauka ba." Girgiza kaina na fara yi cikin tantamar abin da ta ce, don ko kusa ban kawo Anas zai ɗauki kayan nan da niyyar sata ba, saboda shi mutum ne da kayan wani bai dame shi ba kwata-kwata, tun farkon aurenmu idan zan samu duniya ba ta gabansa, kuma ba ma ni ba, naturally ɗinsa kayan wani ba ya gabansa, ban taɓa jin ya mun zancen abin wani yana burge shi ba, bare ya roƙa, mutum ne shi mai wadatar zuci, abinsa na karan kansa kawai ya sani, da shi yake amfani. Zan shaide shi a wannan fannin. A sanyaye na ce. "Anas ba zai mun sata ba Maman Nasmah." A zafafe ta ce. "Ke kika sace abinki kenan ko kuma kayan su suka ɗauke kansu? Wai ke wacce iriya ce ne? Ina ganin ki kamar mace mai wayo ashe ba haka ba ne? Ki nemi abu ki rasa a gida kuma daga ke sai shi amma ki dinga cewa ba shi ya ɗauka ba, ki yi tunani da ƙwaƙwalwarki mana, kin ce babu wanda ya shigo gidan ma tunda na ba ki kayan bare a ce ko shi ya ɗauka. Ina nuna miki Annabi kina runtse ido, ga abu a fili amma shegen son miji ya sa kin baɗa wa idonki toka kin ƙi gani. To ki karkaɗe kunnanki ki saurare ni da kyau, mijinki shi ya ɗauke kayan nan ya siyar babu ko tantama, ko ki yarda ko kar ki yarda. An faɗa miki ana yarda da maza ne yanzu, idan da akwai abin da ya fi komai rashin tabbas l a duniyar nan to namiji ne. Kin faɗa mini inda kike ɓoye kayan can bayan wardrobe ɗinku ne, idan ba wanda ya san da gurin a ɗakin ba ta yaya za a ɗauki kayan? Aiko ɓarawo ne ma duk ƙwarewar shi a sata ba zai yi tunanin da abu a gurin ba, sannan kuma a yadda kika faɗa mini mijin naki ya ƙyale ki kina yin abin da kike so ya isa ya sa ki gane wata gadar zaren yake shirya miki, ya yi miki lumbu-lumbu ya kwashe kayan. Kin san tsadar kuɗin sarƙar nan kuwa? Ya na ganin shi bai mallaki kuɗinta ba ke kin mallaka ai ko don baƙinciki da hassada ya ɗauke. Na san halin mazaje irin naki talakawa da yawa, kullum matansu cikin kawo mana complain suke idan sun zo neman taimako, talaka akwai baƙar zuciya da mugun hali, ba sa so su ga matansu sun fi su cigaba, don haka tun wuri gara ki farka daga mummunan bacci da kike ki san abin yi." Shiru na yi ina nazarin maganganunta, wani ɓarin na zuciyata ya yarda da ita, wani kuma ya na jaddada mini ko duniya da abin da yake cikinta na mallaka Anas ba zai taɓa ɗaukar mini ko tsinke ba, idan ban ba shi ba. Cikin rashin sanin wanne ɓangare na zuciyar tawa zan bi na ce. "Bai taɓa ɗaukar mini abu ba fa, gaskiya ba shi ya ɗauka ba, sai dai in....."
"To waye?" Maman Nasmah ta katse ni cikin kufula. Ban ba ta amsa ba ta ci gaba da faɗin. "Da kike cewa bai taɓa ɗaukar miki abu ba kin taɓa mallakar abun miliyoyi ne? Million ai ba dubu ba ce, da zan faɗa miki price ɗin sarƙar nan sai kin riƙe baki, mantawa na yi ma ban haɗo miki da receipt ɗinta ba. Ni gaskiya nake faɗa miki, saboda na ga so ya rufe miki ido, mutum ba ya son cigabanki ya ga kin samu abin duniya ya sace amma kina yabon shi, just common waya ya siya miki ya kasa saboda maƙo amma kike tunanin ba zai ɗauki abin miliyoyi ba, wa ya sani ma ko ya daɗe da yin cinikinta sai yau ya fake ki ya ɗauka ya kai aka ba shi kuɗin, ina nuna miki haske kina ƙara luluƙa kanki cikin duhu. Amma tunda kin ƙi ganewa bari na ƙyale ki, gaba idan ya kuma tafka miki wata babbar satar kya yarda don dole a lokacin da dare ya yi miki, tunda na nusar da ke tun farko don ki yi wa tufkar hanci amma kin ƙi fahimta." A razane na miƙe tsaye daga zaunen da nake, don zuwa yanzu na fuskanci gaskiya Maman Nasmah take faɗa mini, idan na yi la'akari da yadda yau Anas bai dawo gida ba daga kai su Sultan tahfiz, alhalin ko karyawa da wanka bai yi ba, kuma hakan ba ɗabi'ar shi ba ce, tabbacin ya tafi siyar da kayan kenan. Jijjiga kai na yi ina jin kamar zuciyata za ta fashe na ce. "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Me ya sa Anas zai mun haka? Sai ana i gobe taronmu zai mun wannan tozarcin?"
"Baƙin halin talaka kenan, ke kuwa kya fita a gan ki fess sanye da ɗanƙareriyar sarƙar gold shi kuma yana fama da kaya duk fenti?"
"To wallahi bai isa ba! Bari ya dawo gidan sai ya fito mini da kayana."
Maman Nasmah ta ce. "Atou, ki zage ki zabga masa rashin mutunci da tijara ya fito miki da kayanki, kar ki sake ki raga masa ko na sisi, wannan miji naki ai jaraba ne, ga tsiya ga sata, ban da ƙaddara ai kin wuce ajinsa, yadda kike Black beauty ɗin nan ai da manyan alhazawa kika dace, kwata-kwata ba ki yi dace da miji ba." Rasa abin cewa na yi saboda tsabar baƙinciki da takaici, cikin kuka na ce. "Na gode sosai Maman Nasmah, zuwanki cikin rayuwata alkhairi ne, tunda ga shi kina fayyace mini abubuwan da ban taɓa tunanin za su faru ba, na gode da nusar da ni ɗin nan kika yi." Ta ce. "Haba, mene na godiya, ai na faɗa miki tamkar ƴar'uwata ta jini haka na ɗauke ki, don haka babu godiya a tsakaninmu, abin da nake so da ke kawai duk wani abu da ya shige miki duhu ki faɗa mini zan ba ki shawara in sha Allah." Na ce. "Na gode, zan kira ki anjima na faɗa miki duk yadda muka yi da shi." Ta ce. "Allah ya kai mu, ina ƙara jaddada miki dai kar ki raga masa fa, ki buɗe masa wuta ya fito miki da kayanki." Na ce. "In sha Allahu." Tare da kashe wayar na yi cilli da ita cikin ƙunar zuci kamar ita ce Anas ɗin. Wani irin tafarfasa da turirin bala'i ne kawai yake kai kawo a cikinta. Maganganun Maman Nasmah sun yi zaman kafaffen rodi a cikin zuciyata, na yi amanna da yarda da su ɗari bisa ɗari, don a yanzu ko tantama ba na yi Abban Sultan ne ya sace mini kayana.
Rasa inda zan saka kaina na ji daÉ—i na yi, na dinga safa da marwa daga tsakar gida zuwa É—aki kamar zautacciya, filin zuciyata cike da tanadin tulin buhunhunan tijara da rashin mutuncin da zan zazzage a kan Anas.
Ina bakin ƙofar soro na haɗa kaina da bango na ji an buɗe ƙofar gidan an shigo, kamar wadda ta ga abin tsoro haka na ɗago kaina da sauri na bi shi da mugun kallo, ban amsa sallamar da ya yi ba na fara magana cikin ɗaga murya. "Ina kayana? Kar ka ce mini komai kawai ka fito mun da kayana." Sororo ya yi yana kallo na cikin rashin fahimta, fuskarsa ɗauke da maɗaukakin mamaki ya ce. "Rashin kayan ne ya zautar da ke haka kike sunbatu marasa kan gado?" A fusace na ce. "Idan akwai abin da ya fi mahaukaciya ka kira ni da shi ma Anas bai dame ni ba, abin da na sani kawai wallahi sai ka dawo mun da abuna, ka je duk inda ka kai ma ko ka siyar da ka sata ka karɓo k...."
"Sata kuma? Ni kike alaƙantawa da sata yau? Me zan yi miki da kayanki? Me za su ƙare ni da shi?" Ya yi maganar yana nuna kansa cikin ɓacin rai. Ɗage kafaɗa na yi na ce. "Oho maka, ka na tsammanin ba zan gane kai ba ne ka sata? Daga ni sai kai a gidan idan ba kai ba wa zai ɗauka?" Girgiza kai ya yi cikin takaici ya ce. "Wallahi Hafsah inda kika ajiye kayanki ma ban sani ba bare na ɗauka, rantsuwa ba ɗabi'ata ba ce kin sani, amma na rantse miki da zatin Allah ba ni na ɗaukar miki kayanki ba, ki dai tuna ko kin cilla su wani gurin kin manta, ban da haka wa zai ɗaukar miki? Wa ma ya shigo gidan?"
"Kai mana!" Na faÉ—a ina zabga masa harara.
Numfashi ya sauke ya ce. "Da farko na É—auka da wasa kike da kika nuna kike zargi, amma yanzu ban ga alamar hakan a tattare da ke ba, ban taÉ“a tunanin akwai ranar da za ta zo a rayuwarmu ki alaÆ™anta ni da sata ba, kin fi kowa sani na da abin da zan aikata da wanda ba zan yi ba, ban san me na yi miki ba Hafsah kika zaÉ“i ki ta É“ata mini rai, kar ki kai ni bango na yanke hukuncin da duk ba zai mana daÉ—i ba." Baki na taÉ“e na ce. "An yi walÆ™iya na ga duk wasu mugayen halinka da a da son ka ya rufe mini ido ba na gani, don haka ko me za ka yi ka daÉ—e ba ka yi ba, Æ™arÆ™ari ka ce za ka sake ni ko? To idan ba ka sani ba ma ka sani shi na fi buÆ™ata a yanzu, don in na rabu da kai wanda ya fi ka komai da komai zan aura." Taune leÉ“ensa ya yi yana hucin É“acin rai ya ce. "HuÉ—ubar da suke yi miki kenan?" Na ce. "Oho maka, ni dai yanzu ba dogon surutu na nema ba, kawai ka fito mini da kayana, don ba ka siya mini ba, ba ka isa ka É—auke wanda aka ba ni ba wallahi." Ya ce. "Sai ki yi ta yi, Allah ne shaidata kuma shi zai bayyana gaskiya." Cikin zaÆ™alÆ™ala na riÆ™e Æ™ugu na ce. "Aikin banza, gayyar tsiya kawai da rashin zuciyata, ban da mugun hali babu abin da mutum ya iya, ko da yake an ce gado ba karambani ba ai, tunda ba ka tashi ka ga ana yi a gidanku ba ai kai ma ba ka yi a gidanka ba." Cak ya tsaya daga Æ™oÆ™arin shiga É—akin da yake, ya juyo ya zuba mini idanunsa da suka yi jajir É—in bacin rai, muryarsa na rawa ya ce. "Hafsah! Me kike nufi?" Ba tare da tsoro ko dogon nazarin sakamakon da maganata za ta janyo ba na ce. "Abin da yake akwai shi nake nufi, wanda ya kasa riÆ™e É—ansa ya turo shi almajiranci ta yaya zai iya kula da matarsa har ya yi mata duk abin da take so? Ka ga kenan ba a Æ™asa ka É—auka ba." Jikinsa har tsuma yake saboda tsananin fushi da É“acin rai, don da farko na É—auka duka ne zai yi idan ya Æ™araso inda nake, amma sai na ga ya kama hannayena ya damÆ™e a cikin nasa, muryarsa kamar mai shirin fashewa da kuka ya ce. "Cin mutuncin har da iyayena da suke Æ™asa Hafsah? Kar ki fara don Allah! Kar ki fara abin da zuciyata ba za ta É—auka ba wato sako iyayena a cikin sabgar mu, don ba zan jure ba, zuciyata za ta iya tunzura ni na aikata abin da ban yi niyya ba, kar ki bari mu yi asarar juna saboda wasu can da ba ki san su ba, ba ki san da alkhairi suke nufin ki ko da sharri ba. Please na roÆ™e ki ko dan su Sultan, ina son ki, ban shirya rabuwa da ke. Kuma kar ki manta yanzu igiyar aurenmu saura biyu, furucin da na yi a baya na idan kika fita a bakin aurenki ya riga ya tabbata saboda kin fitan, na shiga tashin hankali a sanadin hakan, amma ke na ga ko a jikinki, to don girman Allah kar ki bari saura biyun ma su tsinke mana." Dogon tsaki na ja tare da fizge hannuna, ko kaÉ—an ban ji tausayinsa ko kuma na ji kalamansa sun ratsa ni ba, sai ma wani irin haushin shi da ya Æ™ara rufe ni, musamman da na tuno gobe ne taronmu, kuma shi nake zargi da sace abubuwan da za su saka na zama tauraruwa a taron, da kuma baÆ™incikin Æ™in siyo mini wayar da ya yi, alhalin matan group É—inmu komai suke so mazajensu suna yi musu cikin gaggawa. Ga uwa uba huÉ—ubar Maman Nasmah, da ta dinga jaddada mini na tabbatar na matuÆ™ar É“ata masa rai, ya ji babu daÉ—i shi ma kamar yadda na ji. Cikin son Æ™ara Æ™ona masa rai na ce. "Ai da ma wanzami ba ya son jarfa, to tunda ba ka so in dinga taÉ“a maka Iyaye, ka sake ni na je na auri wanda zai so ni, ya gatanta ni, ya yi mini duk abin da nake so a duniya, mai kuÉ—i ba faÆ™iri irinka ba." Bai ce komai ba ya juya kamar zai tashi sama alamun ba ya son ci gaba da jin maganganun da nake yi. Jikinsa sai kyarmar tsantsar É“acin rai yake. Da sauri na bi bayansa na riÆ™o rigarsa, cikin fitsara na ce. "Na gaji! Na gaji da wannan takaicin naka! Ka sawwaÆ™e mini idan ka cika É—an halak a cikin Binta da Musa!" Ban san lokacin da ya juyo ba sai ji kawai na yi ya É—auke ni da wani wawan mari da ya saka ni kifawa. Da sauri na dafe kuncina tare da É—aga kaina na kalle shi ina hawaye. Sai na ga shi ma nasa idanun da suka kaÉ—a suka yi jajir cike suke da Æ™walla, muryarsa a dashe saboda tsananin tashin hankali da É“acin rai ya ce. "Ki je na sake ki Hafsah!".......âœï¸
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.