Yiwa Kai Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Yiwa_Kai_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 8 of 34
*Zeey Kumurya*
[3/8, 1:37 PM] BahaushiyaðŸ‘: *YI WA KAI*
MIKIYA WRITERS ASSOCIATION
*BRIGHT PENS*
(FREE BATCH)
7.
Murmushi ta sakar mini tare da faɗin. "Na'am." Ji na yi kamar babu sauran jini a jikina saboda jirin da yake kwasa ta, dafe bango na yi tare da cize leɓena cikin rashin mafita.
'Komai zai faru kar ki nuna mata ke ce wadda kuke chat, ki dage a matsayin ke mai aikinta ce kawai, tunda ba ta taɓa ganin ki ba ko a hoto.' Zuciyata ta ba ni wannan shawarar wadda na yi na'am da ita.
'To amma sunanta da kika ambata fa?' Wata zuciyar ta tambaye ni.
Numfashi na sauke tare da ƙaƙaro murmushin yaƙe don kar ta gane da wani abu na ce. "Sannu da zuwa, mu shiga ciki ko?" Har lokacin fuskarta ɗauke da murmushi ta ce. "Toh." Sai a lokacin na lura da su Sultan da ke tsaye suna kallon mu, gabana ne ya faɗi don wanzuwar su a gidan tare da Maman Nasmah zai iya tona mini asiri, ban san lokacin da suka shigo ba, da tana ɗaki ma suka shigo maƙota zan tura su, har sai ta tafi sai na je na ɗauko su. Tsabar yadda ƙafata ta sage da ƙyar na iya ɗaga ta na bi bayansu, don har sun yi gaba ita da su Sultan. Mayar da ƙofar gidan na yi na rufe bayan na gama leƙen rantsatstsiyar motar da nake da tabbacin a cikinta ta zo, don ita ce ma wadda ta turo a group mijinta ya siya mata. Jikina a saɓule kamar zan fasa ihu na koma cikin gidan, na tarar da su tsaye a tsakar gida Sufyan yana nuna mata parlour yana cewa. "Nan ne inda Mami take kai baƙi, ki shiga." Kamar na janyo shi na rufe shi da duka haka na ji, na rasa mafita da abin yi, ga shi Maman Nasmah har yanzu ba ta ce komai da zai nuna ta gane ni ko ba ta gane ni ba. Ba don na so ba sai don ban da zaɓi na yi mata jagora zuwa cikin parlour'n. Gabaɗaya ƙamshinta mai daɗin shaƙa ya buɗaɗe gidan tun daga soro. Fuskarta a sake sosai muka gaisa, ko kaɗan ban ga alamar ƙyama ko raini a tattare da ita ba, hakan ya sa na ji zuciyata ta ɗan fara sanyi. Ga shi ta ja yarana sosai a jikinta, don Sufyan tunda ta zauna yake kan cinyarta. Ƙare mata kallo kawai nake ta ƙasan ido, fara ce tas kuma tana da ɗan jiki, maroon abaya ce a jikinta mai matuƙar kyau, ta yi rolling da mayafinta, yatsun hannunta guda ukun tsakiya kowanne sanye da zoben gold hagu da dama. Fatarta sai sheƙi take na zallar hutu da jin daɗi. Cikin lokaci ƙanƙani na tabbatar wa da kaina Maman Nasmah matar hamshaƙin mai kuɗin ce kamar yadda na daɗe ina hasashe. Ba don na gaji da kallon ta ba don ba ƙaramin kyau ta yi mini ba na miƙe na ce bari na kawo mata ruwa. Sosai ta burge ni, na ji da ma ni ce nake a matsayin da take. Kallon kaina na yi bayan na fito tsakar gida, zanin jikina duk ya yi baƙin gawayi, ga shi sai ƙaurin ledar da na hura wuta nake yi, gabaɗaya dai na yi kaca-kaca.
"Wannan wacce irin baƙar rana ce a gare ni da ta zaɓi mu haɗu da Maman Nasmah a cikinta? Ya Allah idan mafarki nake ka sa na farka, me ya sa sai da nake a wannan hargitsen za mu haɗu?" Na faɗa a fili tare da ɗora hannuna akai, hawayen baƙinciki da takaici na zuba daga idona. Ban taɓa jin kunya matsananciya irin wannan ba a rayuwata. Kitchen na yi saurin nufa jin kamar za ta fito, abinci nake son zuba mata amma ina kunyar ba ta abin da na dafa, don taliyar Hausa ce da manja da yaji, sai salad da na yanka.
"Bari na É—auko kaya a mota." Na ji muryarta ta faÉ—i haka, saurin share hawayena na yi na ce. "To."
Kafin ta dawo na shiga ɗakina na sauya kaya a gaggauce, wani lace na saka wanda Abban Sultan ya ɗinka mini sallar da ta wuce, shi ne ƙarshen ƙurewar adaka a cikin kayana. Na bulbula turare na ɗan yi ɗaurin ɗankwali mai kyau. Amma duk da haka da na fito sai na gan ni kamar almajira a kanta. Fahimtar tana jin zafi saboda babu nepa ya sa na ɗage labulen window da na ƙofa. Ta ba ni atamfar da wasu tarin kayayyaki a leda ta ce na ba wa yara, a ɗarare nake da ita, ko haɗa ido na kasa yarda mu yi. Ban taɓa sanin haka ƙarya take da kunya ba idan aka kama mutum sai a yau, duk da ita ba ta nuna mini komai ba, sai ma hira da take ta ja na, kuma ko da wasa ba ta kama sunana ba ko na su Sultan, kuma ba ta yi mini maganar group ɗinmu ba kwata-kwata balle na taron da za mu yi. Amma duk haka a ruɗe nake, Allah -Allah nake ta tafi ko na samu nutsuwa na yi tunanin mafita, tsabar rikicewa ko ruwa ban ba ta ba. Abinci da ma ba zan iya ba ta wanda na yi ba, saboda kar abin kunyar ya yi mini yawa.
Tana kokarin tafiya na ji an buɗo ƙofar gidan an shigo, wata mummunar faɗuwar gaba ce na ji ta ziyarce ni, saboda na san Anas ne kawai yake da wannan ikon, idan kuwa shi ya dawo na shiga uku na kaɗe har ganyena. Domin ba zan so Maman Nasmah ta gan shi a matsayin mijina ba, abin kunyar sai ya yi mini yawa ai.
"Ƴar aljannatah!" Na ji muryarsa da ba ta da maraba da saukar dalma a kan ƙirjina a wannan yanayin da nake ciki yana kira na." Ban amsa ba har ya yi ƙoƙarin shigowa ɗakin fuskarsa ɗauke da yalwataccen murmushi. Tun daga kansa har tafin ƙafarsa kalolin fenti ne kamar wanda ya yi birgima a cikinsu. Satar kallon Maman Nasmah na yi na ga ta ƙura masa ido. Na san a cikin ranta tana ta cewa wannan abin ne mijina? Na san ko almajirinta ya fi shi kyan gani, ga shi sana'arsa ta bayyana kanta a jikinsa, yanda ko mahaukaci ne ya shafa shi sai ya sani.
'Ni kam na ga ta kaina, yau ruwa ya ƙare wa ɗan kada.' Addu'a nake ta yi Ubangiji ya sa mafarki nake, don ganin Anas da ta yi ya fi zuwan gidan da yadda ta same ni saka ni a cikin tashin hankali. Na gama tsara ƙaryar da zan shirga mata bayan ta tafi, amma dawowar shi ta wargaza komai, domin ban ga uban abin da zan ce mata ta yarda ba kuma, tunda ta ga mijina da sana'ar yake. Duk yadda ya so control ɗin kaina kar na nuna komai amma na kasa, zuciyata cunkushe da baƙinciki na dube shi na ce. "Me ya dawo da kai?" Idanunsa a kaina yana mun wani irin kallo ya ce. "Tunaninki ne ya addabi zuciyata ya hana ta sukuni, fahimtar ba zan taɓa samun nutsuwa ba idan ban gan ki ba ya sa tilas na bar aikin na zo na gan ki na koma." Ya ƙarashe maganar tare da kashe mini ido. Wani irin ƙululun takaici ne ya ƙara cika ni, maganganunsa ko kaɗan ba su burge ni ba, kamar ya watsa mini garwashi haka na ji su. Harara kawai nake banka masa ƙasa-ƙasa lokacin da suke gaisawa da Maman Nasmah. Tsabar bayar da kai a tsakar gida ya zauna maimakon ya shiga ɗakin su Sultan ya ɓuya. Ƙwafa na yi a ciki-ciki na miƙe ina ƙaƙalo murmushi ganin Maman Nasmah ta miƙe ita ma, ƙoƙarin danne kukan da yake son kwace mini na yi na ce. "Har za ki tafi? Ki bari na gama abinci ki ci mana." Sai a lokacin na tuna ko ruwa ban kawo mata ba. Murmushi ta yi ta ce. "Babu komai wallahi, na gode ma a hakan." Ina gaba tana bi na a baya, har da rusunawarta da za ta yi wa Abban Sultan sallama. Ni kwa ko kallon shi ban yi ba, duk da ina jin shi yana mun magana. Har ƙofar gida na raka ta, na ga ashe tare da driver suke. Shi ya fito da sauri ya buɗe mata bayan motar ta shiga. A raina na ce. 'Kuɗi kenan, mai saka ai ta bauta maka ko da ba ka da sarauta.' Sai da suka bar layin na koma cikin gida bayan na saki ajiyar zuciya, ina cika ina batsewa na nufi kan Anas kamar zan fashe. Kafin na yi magana ya riga ni da faɗin. "Wace ce wannan?"
"Ban sani ba." Na faÉ—a a zafafe kamar zan kai masa duka.
Cikin mamaki ya ɗago yana kallo na baki buɗe. Kukan da yake ci na tun ɗazu na saki na ce. "Mene na dawowa yanzu bayan da ka ce sai Magriba? Kawai ka zo ka zubar mini da mutunci da ƙima a gabanta, jibi kayan jikinka da yadda kake, kowa sai ya san mijina fenti yake!" Miƙewa ya yi fuskarsa a haɗe ya ce. "Kunya kika ji don ta gan ni a haka Hafsah? Shi ne har da kuka?" Harara na zabga masa na ce. "Idan kunya ce kaɗai ma ai da sauƙi." Numfashi ya sauke ya ce. "A tunanina abin alfaharinki ne a gan ni a wajen neman halal ɗina ba haram ba, yanzu a misali a ce faɗowa gidan na yi da gudu ana bi na ana na yi mini ihun ɓarawo fa? Za ki so ta ga haka?"
"Eh wallahi! In dai a cikin kyakkyawar shiga kake da ba za ta bayyana talaucinka sosai ba, idan ya so na ce mata sharri aka yi maka." Na faɗi haka ina ƙara rushewa da kuka tare da shigewa ɗaki, duk da ba na kallon shi amma na san bi na ya yi da na mujiya.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.