Ajeemal Book 2 Complete Hausa Novel
Reading file: Ajeemal_Book_2_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 11 of 24
karfe 9 na dare familyn an hadu cikin kata faren parlourn bayan kammala dinner suka shiga gudanar da fira a tsakaninsu gwanin sha'awa, Ammi Hajia Goggo rabi, tareda yan matan Ammi, gefe ga Kamal tareda muhaiseen Wanda Kamal ya daukoshi daga airport dazu ba Wanda yasan da zuwanshi hatta mom dinsa Goggo rabi batasan da zuwansa ba se ganin shi tayi shima Kamal din muhaiseen kirashin kawai yayi yace gashi ya sauka Kamal yaje ya daukoshi , Aheel dake zaune cinyar Ammi ya nata zuba hamma da alamar bacci cikin idanunsa because duk ya gama yin laushi,
" da alamufa yaron nan bacci yakeji naga se g'yan'gya dawa yake gaba kidaya bacci ya kama idonsa" Goggo rabi tafad'i tana kallon Aheel da idonsa sukayi ciki sun kankance, Ammi s hafo gefen face din Aheel tayi tana kallon shi daga bisani takalli Nisha wacce itama hankalinta yake kan Aheel
" ya kamata akai little ya kwanta because dare yayi sosai " aiko kafin Ammi tarufe baki Aheel yatashi sukuf dashi yanufi Nisha yasuma kokarin kama hanuta sutafi, bamusu Nisha tabishi suka fice daga parlourn su hajia se murmushi suke tareda cigaba da hiransu , Jim kadan Kamal da muhaiseen suka tashi sukafice daga parlourn suna dan k'usk'us atsakanin su
"kije ki gyara bedroom din da yayanku yasauka a shimfuda bedsheets , komai yazama clean" Ammi tafad'i cikin yayi na bada umurni tana kallon Reeda, ba bata lokaci Reeda tashiga fadi'n
"to"
daga haka tamike tafice , bajimawa suma suka shiga watsewa because sundau tsawon lokaci suna firan, koda Reeda ta isa bedroom din da ya muhaiseen yasauka baya ciki da alamar bai kariso bedroom din ba suna tareda Kamal, bedroom din a tsaftace yake komai fine because dama ba abarin ko ina da datti agidan ko dayaushe anasharewa a tsabtace shi agoge ko ina bedsheet dine kadai ba ashin fidawa se time din da bako ya ziyarci dakin ,
karisawa Reeda tayi ta bude wardrobe tadauko wani kyakykyawan bedsheet mai taushi tareda blanket tashiga shinfida bedsheet din saman bed daga bisani tadaura blanket saman bedsheet din , tana tsaka da gyaran muhaiseen ya turo door yashigo idonsa yasauka kan Reeda dake kimtsa masa bed nan yashiga sakar mata murmushi tareda karisowa ciki, itama Reeda murmushi tamayar masa tareda maida hankalinta ga abinda take but bata ankaraba seji tayi muhaiseen bisa bayanta yarungumu waist dinta gafi da sakalo face dinsa ta gefen wuyarta yana fadi'n,"
I miss you very much my pretty gaskiya nayi kewarki dayawa na kagu adaura auramu na daukeki natafi dake , nifa banki gobe ashafa mana fatiha nawuce dakeba , but Daddy yakaimu har 2 month wanda hakqn yamin nisa gaskiya ya muhaiseen yafad'i yayinda yake sake rungumar Reeda a jikinsa yanajin yanda sonta da kaunarta yake sake zama sabo fil cikin zuciyar shi, jin yanda ya muhaiseen ya rungumuta tamakar zai maidata jikinsa yasa gaba daya setaji wani irin yanayin da tunda take arayuwa bata taba jinsaba ga kamshin turarensa mai masifar dadi dayasa takasa janye jikinsa daga nata bata ki sutabbata hakaba har tsawon rayuwa ,
ba karamin kewarsa takeba itama ganinsa yayiwa idonta tsada se adau tsawon lokaci basuga junaba sede suyiwaya ko video call nan ma se inyana free because kullum cikin busy yake bugu dakari gari ba daya kuma baicika zama kasarba, jin shiru batayi maganaba ta tsaya kamar sak'aguwa yasa yajanye jikinsa tareda juyo da ita but seyaga ta lumshe ido murmushi ya muhaiseen yayi yana fadi'n
"Yadai " tareda shafo gefen face dinta, bude ido Reeda tayi dasaure gaba daya tafada duniyar tunani ta mance ida take nan tasuma yar kame kame
"Uhm am ba abunda kakeda bukata? Zan iya tafiya ?"
" That's means ke bakiyi missing dina ba" muhaiseen ya fadi'n tareda yin baya ya zauna bisa sofa dakin yana kallonta, girgiza Kai Reeda tayi tana fadin
"Aa ya muhaiseen meyasa zakace haka?"
"gashi kuwa kina fadi'n zaki tafi kibarni cikin kewarki maimakon kizauna kitayani fira har wayewar gari , fito da ido waje Reeda tayi tana fadi'n,"
" wayewar gari fa kace ?
"Eh mana bawani matsala ai Dan munraya dare kina min firan soyayya mai dadi" muhaiseen ya amsa yana mata k'ayataccen murmushi, dariya kawai Reeda tayi gamida tabe baki tana fadi'n
" Muk'wana lapia " tana fadi'n haka tajuya zata fice ,
"ba ki jiba " jin muryan muhaiseen na magana yasa Reeda dakatawa daga fitan da take kokarin yi tajiyo tana kallon shi Wanda ya mike yanufi inda take , kallon kallo sukashiga yiwa juna kafin muhaiseen yadan numfasa ya Kai hanu ya janyo hand din reeda sannan ya sanya dayan hand dinshi bisa pocket dinshi ya zaro wani box dan karami gwani sha'awa wanda ke dauke da kyakykyawan rings na gold mai haske da kyalkyali zoben ya zaro daga box din yasaita yatsar Reeda natsakiya ya sanya mata akwai ya zauna mata damas gwani kyau rings din ba karamin sake fito da kyakykyawan hand dinta tayiba,
"I'm sorry pretty wannan karamin kyautace daga gareni but zoben nan yayiwa hand dinki kyau ko mace hand din ki yayiwa rings din kyau, muhaiseen yafad'i gamida murmushi yana kallon Reeda wacce tasake baki ta zaro ido waje yayinda take kallon hand dinta tana juyashi gamida karewa zoben kallon,
" wow ! wow!! Ya mu muhaiseen gaskiya rings din nan ya yayi kyau sosai ya burgeni matuka thanks you so much gami da sunbatan zuben tana murmushi farin ciki,
" but wannan kyakykyawan sumbatar niyakama ta ayiwa ba zoben ba , dagowa Reeda tayi takalli muhaiseen wanda ya miko mata face dinsa gamida rintsa ido yana mata alamar nuni da yatsansa ta sunbaci kumatunsa aikuwa ba tsammani yaji saukan k'ayataccen kiss bisa kuncinsa saide kafin yabude ido tuni tajuya baya tabude door tafice da saurin, lumshe ido yayi tareda shafa kumatunsa inda ta sumbace shi sauke ajiyar zuciya yayi kafin ya tattaro nitsuwarsa ya shiga cire kayan jikinsa ya sanya towel yanufi toilet wanka yayi sosai daga bisani ya fito ya sanya white jallabiyar sa yanemi saman bed ya kwanata yadau lokaci yana dan tunane tunane face dinsa yana kallon sama sannu ahankali bacci b'arawo ya saceshi,
itama Reeda koda takarisa bedroom dinsu tasamu Fadeelah tayi d'aid'ai tana bacci da alamar baccin ta yayi nisa sosai ga wayarta dake gefe saman bedside table yanata kawo hasske alamar Kira but phone din ta sanyashi silent shiyasa baza aji karantaba dan leka phone din reeda tayi domin ganin mai uzurawa da wannan Kiran ganin boyayyiyar number ne wato ( private number) yasa ta share tashiga neman Nisha cikin bedroom din but ba ita ba alamarta ,.
'bade tunda takai Aheel side din su bata dawo ba' Reeda ta tambayi kanta ganin cewa bata da amsa tambayar ta yasa ta d'an tabe baki daga bisani tashiga yin Shirin bacci kafin ta kwanta tareda rungumu hand dinta tana kallon d'an ya tsanta wanda ke sanye da kyakykyawan zoben gold da hubbynta ya yasanya mata yaude da mutukar murna gamida annashuwa cike da tunanin gwarzon masoyin nata bacci yayi awungaba da ita,..........
'haba Nisha ashe duniya zata iya rudanki ki mance da mahaifinki ? asha akwai rayuwa cikin daula da jin dadi zai iya mantar dake tushenki , Nisha Ina alkhari da kikayimin akan kasance wa da mahaifinki atare dake? ashe zakiya mancewa da abbanki cikin sauki haka? shin kinsan wani irin hali yake ayanzu ?
"wakeup! wakeup !!mana yanzu dan fitowar nan da mukayi daga gida harkin kiyi bacci, Fadeelah ke magana yayinda take tashin Nisha daga d'an gajeren baccin da tayi, nan Nisha tashiga zazzare idanu tana kallonsu se zuba ke tsatstsafo mata idonta yayi jawur dashi yayinda zuciyar ta kuma keta maimaita sunan umma because mafarkin datayi da ita yanzu bisa tuhumar da take mata akan abbanta na nauyin da ta daura mata ,
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.