Complete Hausa Novels

Ajeemal Book 2 Complete Hausa Novel

Reading file: Ajeemal_Book_2_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 7 of 24

am dama coffee na hadu maka kokanada bukata Nisha tafadi muryarta harsakewa yake harta suma kokarin kasa kasa da hannuta ganin bai karba cikin sauri doctor fu'ad ya amsa yana fadi'n,"

sannu da kokari sister kamar kinda abunda yake da bukata kenan doctor fu'ad yafad'i yana mata kataccen murmushi, itama dan murmushin tayi jiki asanyaye takalli ajmal wanda yasuma lumlumshi ido allura yasuma ratsashi daga bisani tamaida kallonta ga doctor fu'ad wanda keta zuba murmushi kamar gonar auduga kafin tajuya tafice tabasu gari , doctor fu'ad naganin fitanta yajiyu yakalli ajmal wanda ya lumshe ido bacci ya fara cinye idonshi doctor fu'ad cup din coffee ya mayar ya ajiye bisa table ya kai hanu yadauki akwatin agajinsa daga nan yasuma kokarin ficewa ganin mutumin nasa yasamu bacci seda yarage masa hasken dakin kafin doctor fu'ad yasamu daman ficewa daga bedroom din yajanyo masa door din yarufe , yana fitowa daga side ajmal yashiga motarshi mai gadi yabude masa geat yafice yaso yashiga sugaisa dasu hajia but saurin dayake bazai bari yakarisa cikin gidan ba yabari sewani lokacin da ya ware na musamman,

yaumade kamar kullum bayan sun kammala dinner dinsu suka koma parlour akashiga taba hira kamar yanda kasaba gabaki daya family da kakalli fiskokinso zaka fahimci suna cikin nishadi da jin dadi , daya yasanar dasu gobe Daddy zaiyi tafiya kamar yanda yafad'i musu abaya , kuma sanar dasu cewa sun zauna da dan uwansa sun tattauna tsakaninsu yakuma sheda musu yanda sukayi sun tsayar da bikinsu fareeda da fadeelah zuwa 2 month masu zuwa inshallah, su hajia ba karamin dadi sukajiba da wannan kyakykyawan labarin ,"

Masha Allah to allah de yakaimu yasa albarka cikin lamarin , hajia tafadi cikin murna da farin ciki goggo rabi Daddy da ammi sukashiga fadi'n,"

Amin Banda su reeda da suka shiga kallon junasu suna muzurai farin ciki ba amma magana Nanda dan wasu lokaci suma zasu zama matan aure gurin mazajensu , sede ita hajia karama( fadeelah) ta dan damu because gashide ana maganan tsaida ranar bikinsu but ko saudaya basu zauna da mutumin nata sun tattauna tsakaninsu balle kowannensu yabada labarin yanda yake feeling dan uwansa to amma de tazubawa sarauta Allah ido taga yanda lamarin zai kasance, "

Alakullihalin tunda alamaru suntafi yanda yakamata nimade zuwa jibi jirgina zai daga zan koma gida nima, "

Au wai tafiyar zakiyi baza kitsaya ayi bikin da keba seki koma gaba daya naga month din bayawa Daddy yafad'i cikin zolaya yana kallon goggo rabi wacce tafiddo ido waje ,"

wani ! rufamin asiri gida yayi kewata nafa jima anan tun bikin kamal yau kusan wata daya kenan gashi har ansamu rabo inanan ina zaune ai gwara natafi daga baya nakuma dawowa ga baki daya family dariya sukashigayi jin batun goggo rabi sunsa ba karamin miss dinta zasuyiba zayi miss barkwancinta , sun raba dare suna hira har guraren 10 daga bisani sukashiga yiwa juna sallama kowa yanufi makwancinsa ,

gari yayi shiru gida yayi tsit su nisha duk sunyi shirin bacci sun kwanta , reedane kawai take zaune bisa sofa tana waya da habibinta Wanda take sanar da ita zaizo seda suka kammala wayan tadawo bed takwanta zuciyar ta fari tas farin ciki da annashiwa ba a magana , aka har bacci ya dauketa , Nisha kuwa lumshe ido kawai tayi but bacci yakasa daukanta ta juyanan ta juya can bacci yaki , nan tunanin ta yashiga tuna mata yanayin da suka kasance dazu da ajmal, yanda tayiyo zafin jikin ajmal bisa jikinta time din dasuka fad'i bed dakuma time dinda yarungumota Wanda yasanya tsikar jikinta tashi , mikewa tayi zaune tazauna ,"

oh Allah koya jikin nasa yanzu ?

Phone din ta tadauka ta sakko daga bed din tanufi parlour shiru parlourn ba kowa harta doshi hanyar fita se kuma taja ta tsaya ganin dare yayi sosai gashi tasan wannan uwar tsiwar Heelah tanan batasan ya zasu kareba but tamatsu taga ya yanayin jikin nasa yanzu, haka tanemi guri tazauna tana ta sakawa da kuncewa mafita dayane yazo mata Kiran line din Ajmal kamar yanda yace zata iya kiranshi taji koyanada wani bukatan duk da ba kowani lokaci yake daga kiranba balle yanzu dayake cikin halin rashin lapia, ba wani tsayawa bata time tashiga kiranshi kamar yanda tunanin ta ya bata,

Ajmal wanda tashinsa kenan tun bayan da Doctor fu'ad ya masa allura bai farkaba se yanzu 11 cikin yanayin kasala da rashin karfin jiki Ajmal ya yaye blanket din jikinsa saboda zufanda yasuma tsatstsafo masa alamar cewa zazzabin ya sauka adafe yanufi toilet wanka yayi sosai tareda alwala ya fito, sam bai lura da Heelah wacce take kwance saman sofa tamike bacci yayi awungaba da ita se yanzu daya fito idonsa yasauka kanta, kauda kanshi yayi yashiga zaro wata jallabiyar yasanya sannan yashin fida sallayan yashiga jera sallolinda suka biyoshi,
seda yamika sallonshi duka sannan ya sallame ya ninke sallayan yadawo saman sofa ya zauna abincin da Nisha takawo masa dazu yashiga budewa because yunwa ya tashi dashi acikinsa, Heelah jin buruntun bude food flakes yasata motsawa tabude ido tana kallonshi,"

Dear wani irin bacci kayine yau din nan? Heelah tashiga tambayan Ajmal cikin muryan bacci shiru yayi mata yana kallon try din abincin da Heelah tajera a table din Heelah mikewa tayi ta taso tamatsu gareshi tana fadi'n,"

bari nayi serving dinka nan tashiga kokarin serving dinshi ya tsaya kawai baice mata komaiba gaba daya jiyayi ransa yadagule masa ganin ba abincin da Nisha tashigo masa dashi dazubane wani sabon girkin heelah tayi daban, kallon abincin yashigayi time din da take serving dinshi pepper soup din kazace da soyayyiyar doya da kwai girkin ko kamshi mai dadi baya bayarwa balle kasa ran zaimaka dadi abaki komawa yayi yajin gina da jikin sofa haryaji yunwar da yakejima tatafi, sam bai ji dadin canza masa girki data yiba kusa dashi Heelah tasamu tazauna tadaura hand dinta saman cinyarshi tasuma fadi'n,"

kayi shiru Dear meya samekane yau? tun bayanda muka dawo nadauko Aheel daga school mukazu muka taddaka kana bacci still har dare yayi sosai haka Aheel da mararin son farkawanka yayi bacci baka bude idoba nima naita yawo akanka shiru baka bude idoba ni harna tsoritama nace ko mutuwa kayi amma sena fahimci kana numfashi meyasameka kaketa wannan baccin haka kalau kake kuwa?"

I'm fine yabata amsa a takaice,

Alright kasamu kaci abincin ga gashashshiyar cheese burger with sausage pizza danayi mana order time din da muke dawowa nasan kanaso Heelah tafadi tana mai kai hanu tadauki plate din burger da pizza tamika masa ba musu ya gyara yamasa jin order tayi dan haka seya Kai hanu yadauki lallausan cheese burger yakai baki yasuma ci, barina hadu maka coffee daga haka Heelah tamike tafice bajimawa ta dawo dauke da cup din coffee tamika masa ya amsa ba tareda da wani jinkiriba ,
ataikace burger da pizza kadai ajmal ya iya ci papper soup din baiwuce tabi daya yayiba ya kauda plate din gefe ya Kai hanu yadauki phone din shi, 4 miss call yagani ankirashi koda yaduba yaga 2 miss call from staff and another miss call from Doctor fu'ad phone din nashi a silent take shiyasa ko karanta baijiba idonsa yarintsa ya kuma budewa time yakai idonsa ya duba 12 dan haka seya ajiye wayar baikira kodaya daga cikin suba because dare yayi sosai, mikewa yayi yanufi bed dinshi ya kwanta ya rintsa ido Heelah naganin haka itama tabishi tahaye saman bed din nashi takwanta ajmal yanajin motsinta agefenshi amma yaki bude idon shi harseda yaji takai hanu saman k'irjinsa ta rungimushi tashige jikinsa kamar mai komawa ciki yasa yabude manya manyan idonsa yana kallonta wacce itama shidin take kallo tana masa murmushi,

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.