Complete Hausa Novels

Ajeemal Book 2 Complete Hausa Novel

Reading file: Ajeemal_Book_2_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 2 of 24

Alhamdulillah abaiyane wanda yasa tayi hanzarin mikewa dasauri tabar gurin tanufi bedroom da gudu , nan fa su Nisha da Reeda suka rufa mata baya , daga nan fa dukansu suka shigayin hamdallah lallai yayansu yayiwa k'anwarsu zabi nagari sede fatan dacewa , "

Masha allah komai yayi kyau yanda akeso , duk da tafiya tasameni cikin week dinan ammade zanje muzauna da dan uwana (abu)muga abunda yadace se musamu mutsaida bikin ko nan da 1 month tunda bawani abunda zamu tsaya jiraba, sede muyi fatan Allah ya aramana tsawon rai da lokaci, nan su ammi suka shiga amsawa da

"Ameen ,

yau kowa farinciki fal zuciyarshi , Fadeelah kamar tazuba ruwa akasa tasha saboda tsan tsan murna da farinciki , haka suka wuni suka kwana cikin nishadi , washe gari da safe karfe 8 Nisha tayi wanka tafito takimtsa jikinta tashirya tsaf cikin duguwar gown tareda yafa mayafi bisa kanta tanufi fita side din Ajmal ,

kamar yanda ya fada baya bukatan wani abu daga bangaransu , tana isa part dinshi kamar kullum seda suka gaisa da securityn dake wajan sanan tasamu daman shigewa ciki, koda Nisha tashiga ciki hamdallah tayi ganin bakowa cikin parlourn

sidi sidi , tashiga kitchen, seda tafara g'yara kitchen din takimtsa komai daga bisani tashiga duba kayayyakin da zatayi amfani dasu bada wani bata lokaciba tashiga hada masa dadda dan delicious data saba , cikin dan kankanin lokaci ta kammala komai tafito tajerashi komai slowly takenyinshi gudun kar wanan masifaffiyar matar tajiyuta, nan tasuma kokarin komawa kitchen din but kankace kwabo heelah tabaiyana a parlourn kaikace kamar jiratake, "

Mayya dama nasan kece mai mini buruntu a kitchen, tundaga sama nakejin motsi akasa mai kikazo dauka? heelah ta tambaya yayinda take kokarin karisawa ga nisha wacce tayi tsayowar soja batare da tawaiwayoba , "

tambayarki nake kibani amsa kinyi ajiya a kitchen dinne da kikazo dauka , Heelah takuma tambaya tareda juyo da nisha suna fuskantar juna, "

Uhm breakfast nazo na hadawa papan aheel, Nisha tace tana zare ido,"

Uhm yayi kyau dakinbar wannan muzuran dakikeyi ba koranki zanyiba , because ke yar aikin mijinane Mai mana hidima , Bakomai kicigaba da aikinki , sede warning dina dake shine banason wadanan kazamun kafafuwan naki yasake taka bedroom din mijina da sunan g'yara , wannan nikeda hurumi da hakki akanshi inafatan kin gane,? but babu laifi kig'yaramin nawa bedroom din , dan matsawa Heelah tayi dining table area tashiga duba girkin da Nisha tashiryawa ajmal, dan tabe baki tayi sannan tace,"

Inada bukatan abinda zanci yanzu wadannan abubuwan DA kika shirya banida ra ayinsu, ko zaki iya shiga kitchen kigirkamin abinda nakeda bukata ,"

kiyi hakuri aunty niba yar aiki bane bazan iya sake girkawani abin yanzuba because inada abunyi yanzu, nisha tafadi tana mai kokarin barin parlourn ,"

ke tsaya Heelah tafad'i gami da janyota baya, mekike nufi dake ba yarki bane bayan aikatau kekawoki side dina kuma akarkashin mijina kike , dole kikasance akarkashin matar shi, dan haka kiwuce kije kiyi abunda nasaki , cike da takaici Nisha tadubi Heelah tana fadin"

Eh akarkashin mijinki nake but kekuma ban kasance akarkashinki kiba because ni yar hidiman mijinkinkine bakeba , dan uwa kuma yayana nadauki mijinki ba uban gida ba,, incede kima macece kamarni , zaifi kyau kishiga kitchen kiyiwa kanki abunda zakici , ni inada abunyi nisha tana fadin haka tajuya zatafice , aiko cikin takaici da bakin ciki heelah batayi wata wataba tasha gaban nisha tadauketa dawani gigitaccen mari wanda yasa nisha zubewa kasa ta tallafe gefen face dinta tasaki kuka wuiwui kamar karamar baby , "

tas Nisha taji andauke heelah damari itama wanda yasa nisha mikewa daga durkuson datayi tana kallonsu, Ajmal ne tsaye jikinsa sanye da white jallabiya wanda yake tsaya tundazo daga sama yana hango rikicinda Heelah keyi, ganin marinda Heelah tayiwa Nisha yasa yayi saurin sakkowa cikin bacin rai yadauki Heelah DA mari seda taga wasu taurari, "

nikamara? heelah ta tambaya tana kallon ajmal wanda shima Itan yake kallo cikeda takaici,"

saboda namari wannan mara kunyar yarinyar shine kasa ahanu afiskana da sunan mari , abunda bantaba fiskanta daga garekaba wlh azim yau kajawo mata kwanan kabari Heelah tafadi akidime tayi wajan dining tazari wata yar karamar wuka zatayi kan Nisha dashi,

Nisha kamar wacce aka dasa agurin gaba daya tatsorata takasa yin gaba ko baya , ganin abunda Heelah ke kokarin aikatawa yasa Ajmal yashiga gaban Nisha yatare Heelah daga abunda takeson aiwatarwa rike hand din Heelah yayi tareda fisge dan karamin wukar dake hanunta yacillashi gefe , daganan yasa hanu ya sunkuci Heelah saman shoulder dinsa ya haura da ita sama, direct bedroom dinta ya nufa da ita , seda yakata harsaman bed ya wullar da ita daga bisani cikin hanzari yabar dakin tareda baida kofar yarufeta tabaya da key, Heelah kamar wanda hauka yasuma taba kwakwalwarta haka take dukan kofar da karfi tana fadin Ajmal yazu ya bude yau seta kashe nisha,

ajmal ko ajikinsa haka yanufi downstairs cikin sauri , amma kafin isowarshi , Nisha najin motsin sakkowanshi ahanzarce tasamu daman watsawa dagu tayi waje, Ajmal naganin fitarta yasa yakoma yazauna kan sofa , yadau mintuna yana zaune agurin daga bisani yamike yahaura sama yanufi bedroom din Aheel, koda yashiga yasamu dan nasa se bacci yake tasha hankali kwance , hakan yasa Ajmal ya fice daga bedroom din Aheel yanufi nashi dakin ,

yana shigowa yadauki phone dinsa domin duba time karfe 9 dawasu yan mintuna gakuma miss call dayasamu cikin wayarsa jikin screen din wayar anrubuta "

My blood , phone din ya ajiye yanufi toilet yayi wanka yafito yashirya cikin shiri maikyau daga bisani yanufi kasa, kotakan breakfast din biyeba yawuce yafita abunsa ,

Aban garan Nisha kuwa tana barin side din Ajmal tanufi part dinsu direct bedroom dinsu tawuce tasamu su reeda se bacci suke basuda niyan farkawa yanzu, itama kwanciyar tayi tana share hawayenta tareda maida ajitar zuciya , bakaramin takaici tajiba da marin da Heelah tayimata, amma ko bakomai taji radadin da takeji yarago tunda agabanta Ajmal yasa hanu yawanke matansa da mari saboda ita , bakaramin jindadin hakan tayiba ,

ko bakomai da lamamun tana da dan mutunci aidonsa tunda ya iya marin matarsa akanta abunda baitabayiba kuma yanuna baccin ransa sosai afili, to kuwa itama yanzu takejin takudiri damaran farantawa mijinta tareda yimasa hidima yanda yakamata tunda ita tagaza

daha bacci mai nauyi yadauketa because dama tagaji gashi jiya batayiwani bacci sosaiba saboda kwana tayi tana karantu exam dazatayi na jam gobe gashi dasafe ta tashi dawani aikin kuma,

Misalin karfe 11pm nisha bacci mai nauyi take , cikin baccin taji anataba mata tafin yan kafafuwanta, but takasa bude idanunta because baccine sosai acikinsu haka cikin muryan bacci Nisha kefadin ,"

Uhm uhm Banaso!

cankuma sejitayi ankoma anakokarin jan pillown data kwanta Kai ahankali, jin head dinta nakokarin barin saman pillow yasa tabude ido ahankali , tar tabude idonta gamida tashitsaye tsakiyar gadon tana zazzare idanu , farkon bude idonta ganitayi kamar Ajmal tagani yana tsaye kanta, daga bisani kuma data murza idon dakyau Kamal tagani tsaye yana washe mata baki yana fadin,"

Surprise!

da mamaki take binshi da kallo sekuma tamaida kallonta ga dakin ita kadai su fadeelah basanan sekuma takalli kamal wanda keta zubamata murmushi kamar gonar auduga, "

Ya kamal! Kaine? nisha tafad'i ahankali, dariya yakwashe dashi kafin yace,"

Year I'm nacanza mikine? yafadi yana mata kayataccen murmushi, sakkowa nisha tayi daga bedroom din tana fadin, "

saukan yaushe? Ina aunty nabilah? dan matsowa yayi kusa da ita yana fad'in "

Nayi surprising din kune because
duk gidan nan bawanda yasan da zan dawo ya ajmal ne kaide yasani in fact ma shiya daukomu daga airport, kallonshi kawai Nisha keyi tana murmushi,"

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.