Complete Hausa Novels

Ajeemal Book 2 Complete Hausa Novel

Reading file: Ajeemal_Book_2_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 17 of 24

Kamal nada shaira 6 Ammi ta sake samun cikin yan biyun ta Fadeelah da fareeda ita fareeda sunan k'anwata taci yayinda ita kuma Fadeelah ni a kayiwa mai suna, ina matukar alfahari da family na mun zama tsintsiya madaurinki daya saidai gaba daya hankalina ya koma kan Rabi da Modi da suke Nigeria especially Modi da hankalinta ya kasa kwanciya da shi g'wara ita Rabi hanun namiji take but shi Modi ahanun mace yake saboda ita ta jashi sai yanda tayi da shi wannan abu yana d'agan hankali.,

Bayan da su Reeda da Fadeelah suka kammala primary School nayanke shawaran komawa Nigeria tushe na domin hankalina ya kasa kwanciya da rarrabuwan kan ahalina saidai Kamal da babban yayansu karatunsu yayi nisa shi Kamal yana Americans shikuma Ajmal yana Dubai kowannesu da inda yake karatu dan haka koda Habu ya dawo nake sanar da shi hukunci da nayanke na komawa Nigeria tun da dalilin wanda nake aure anan din Allah ya masa rasuwa dan haka zan koma mahaifata Habu baimusa mi ni ba saidai yace mu d'an basa lokaci domin duba mana gidan da zamu zauna, aikuwa cikin satin yazo ya nuna mana amincecen gidan da ya siya mana a gida Nigeria cikin babban birnin kano gidan yayi kyau fiye da tunanin mai tunanin dan haka sai muka soma shirin komawa Nigeria , .

Koda muka dawo Nigeria muka sauka agidan da Daddy ya siya mana gidane mai kyau na alfarma babu abunda babu acikinsa komai na bukata an ta na daishi acikin gidan sai dan abunda da ba arasa ba bayan kwana biyu da zuwan mu na bukaci Daddy da ya kira Modi ya sanar dashi zuwan mu saboda ni inna kirashi baya shiga saidai shi ya kirani wani sa'i bayan lokacin watakil shi akwai yanda suke sadarwa kwana biyu da yin hakan aikuwa Modi ya turo da wata kyakykyawan mota acewarshi ad'ibomu akawomu inda suke aikuwa hakan akayi duk mukayi shiri muka shiga motar da ya aiko domin mu shi kuwa Habu motarsa na bayan mu yanabin duk inda yaga munyi har Allah yasa muka isa gidan Masha Allah gidan da modi yake rayuwa aciki yanada kyau matuka Saida kyansa zai biyo bayan wanda Daddy ya siya mana Wanda muke kokarin fara gina sabon rayuwa a ciki, balaifi anyi mana kyakykyawan tarba an gabar mana da abubuwa kala kala kama daga a bubuwan ciye ciye da na lashe lashe.

Alhamdulillah naga d'ana cikin aminci da kwanciyar hankalin da alamu shima yaji dadin ganin mu tare da jin kyakykyawan labari dawowar mu Nigeria Saida abun lura dashi tun shigowar mu Modi ke tabin Hafsatu da kallon bakinsa keson cewa wani abin ita kuwa Hafsatu ba ta shima take ba hankalinta gaba daya yana kan yarinyar da ta ke ta shiga tana fice wajan d'a wainiya da mu duk wani abunda ake da bukata ita ke samarwa cikin hanzari kaida ka ga yarinyar baka kalar y'ar aikatau ko wahala ba kyakykyawan yarinyace kuma ga hankali yarinyace karama da bata wuce sa'arsu Fadeelah 13 year's sai girman jiki da suke da shi kai ka ce yan 20 year's.

Gaba daya nima hankalina sai ya karkata yakoma kan ta nan nefa nake tambayan Modi tunda nazo banga giftawar jininsa ko guda daya ba nan yake sanar dani duk suna can ture suna karatu but nan da karshen shaikara zasuyi hutu zasu dawo insha allah daga nan zai gabatar dasu gareni amma ga k'anwarsu Nabilah Abu yafad'i yana nuna min Nabilah wacce tasunnar da kai kasa tana jiran abata umarni tayi nace dashi yanzu wannan din yar kace na tambaya da mamaki dan k'wata k'wata ba zakayi tunanin yar gidan bace duba da yanda taga Jumanah tana ta tsawata mata d'an kuskure kalilan zata hantare ta gaba daya dai yanda take mata zakayi zammani aikatau take wanda kuwa ba haka bane, nan ya fara neman da nayafe masa ataikace dai yayi aure shaikarun baya da suka wuce auran bai jimaba matar tarasu saka makon jinya da taita fama dashi wanda aka kasa gane kan lamarin har Allah ya karbi rayuwarta.

Tabbas Modi ya shayar dani ruwan mamaki ban dauka zai iya mai dani ba a bakin komai na keba a garesa da har zai iya kula wani al amarin ba tari da nasa ni ko naji labari ba ban bi takanshiba ballai nasan sauran zancen da yake natashi na nufi gurin jikata tare da janyo ta jikina wanda ya sanya yarinyar sakin wani kuka mai tsuma zuciyan mai saurare gwanin ban tausayi take parlourn ya dau shiru bawanda yake magana daddy tunda muka shigo parlourn bayan gaisawa bai iya sake cewa kala ba ya zubawa sarautar Allah ido yana ganin yanda dan uwan nasa gaba daya ya koma sususu, fareeda da Fadeelah kawai na kallah na basu umarni dasu je ciki su ta ya Nabilah hada kayanta domin kuwa tare zamu tafi zama yakare mata agidan nan, amma Jumanah ba kunya babu tsoron Allah tashiga mita mai ya sa za adauke Nabilah daga gidan bayan ansan ita ta ke mata hidman cikin gida saboda Jumanah tamkar y'ar aikin ta haka ta dauki Nabilah duk wani ayuka na gidan ita takeyi amma ban bi takan ta kan surutan ta ba su Fadeelah suka hada kayan Nabilah suka fito muka wuce har muka fice daga parlourn HAJIA Jumanah mita ta ke wa Modi mai ya sa bazai dakatar damu daga kokarin tafiya da Nabilah da mukeson yi ba shikuwa Modi ya kasa tsaida mu kuma ya ka sa jure mitar da matarsa keyi haka muka tafi muka barso,,.

Turo door din da a kayine ya sa HAJIA da ka ta wa daga labarin da take bawa Nisha suka shiga zurawa door din ido don ganin mai shigowa, ganin Ammi ne tashigo bakinta dauke da sallama yayin da hannayenta ke dauke da trary din abincin tashigo ta tsaya daga gefe tana aikawa Nisha da kallon tausayawa kafin ta ce

" Hajia ya ka mata ki je ki ki kwanta kihuta ni because kin ga ke ma ba k'oshin lapia ga re ki ba d'an numfasa wa Hajj mama tayi kafin ta gyada kai takByalli Nisha tare da shafo gefen face d'in ta tana fadi'n

"Zan tafi saida safe ki kula da kan ki" gyad'a kai Nisha tayi daga haka Hajj mama ta mike ta fi ce daga bedroom fadi'n

"To yanzu bari natafi na baki guri ki kwanta ki huta good night" Ammi tafad'i tana yi wa Nisha kyakykyawan murmushi itama Nisha murmushin yak'e ta shigayi tana g'yad'a kai daga haka Ammi tafice daga bedroom din cike da jin dadin yanda Nisha ta sake jiki, nan Nisha ta koma ta kwanta because jikin ba k'wari kuma amace duk wannan sa kewar da Nisha tayi taci abinci cikin raha da rashin damuwa kawai ta danne zuciyarta ta ne because bata son su dinga shiga damuwa ta dalilin ta but Allah kadai yasan kukan zucin da ta ke.

Washe gari da asuba Nisha yanda taga dari haka wa ye wan gari because bacci ya kasa daukar ta gefe Fadeelah da Reeda sai bacci suke cikin kwanciyar hankalin amma ita bacci ya kasa ziyartarta sam tunani duk yabi ya adda bi k'wanyarta ta kasa gaskata wannan lamarin wai ita aka daura wa aure da Ajmal papan Aheel mutum da Sam baya kaunar kasan cewar ta atare da shi in ba ya ka sance dole ba taya ma zata iya kasan cewa da shi tare da wannan ma sifaffiyan matar tashi Heelah mai bala'in kishin tsaya duk time din da taji wannan al'amarin tasan saita konata da ranta, haka Nisha ta dinga juyi saman bed ta juya nan ta juya can daga karshe taga kwanciyar ya gagara haka yasa ta sab'ulu daga saman bed tanufi bathroom because asuba tayi anata kiraye kirayen sallah ga mai niya .

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.