Ajeemal Book 2 Complete Hausa Novel
Reading file: Ajeemal_Book_2_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 20 of 24
"What are you thinking?"
Wani dugun numfashi doctor fu'ad yaja yana mai kallon Ajmal wanda ya tsare shi da tambaya kafin ya saki wata murmushi yana fadi'n
"Nothing" daga nan ya kai hanu shima ya dauki lallausan sandwich wanda ya ke hango shi tamkar zane
"Tun shigowa na hancina ya cikaro da kyakykyawan kamshin abincin nan nasan cewa ba gama garin delicious ake gabatar waba ashai amaryar muce ta karbi office " Doctor fu'ad ya fad'i yana kallon Ajmal ta gefen ido kafin ya danna daddad'an sandwich cikin bakinsa. shi dai Ajmal har wa yau bai kullashi ba dan yasan Doctor fu'ad inya fara zuba kamar fanfon kasuwa yake bakin ba burki kuma cikin maganarsa ya dinga sa wasa da tsokana aciki.
"Bana manta wani delicious da naci time da Raheelah ke amarya only one spoon but ranan kwana nayi ina zaryan toilet I hope HAJIA karama ta iya kayatattun delicious irin haka like Nisha ba girman parlour ta ke kamar Heelah ba "
Doctor fu'ad ya sauka layi sai barin magana yake maybe dad'in girkin Nisha ke sa shi wannan zuban, Ajmal bai san sannan da ya saki wani murmushi mai sautin ya na kallon doctor fu'ad da ke ta kada kai ya na ta faman surutu shi dai a iya sanin shi k'anwartashi ba ta da mara ba da Heelah duk ba abunda suka iya sai dai ta iya zuban surutu kamar shi
"Please kaci abincin kadaina surutun nan haka" murmushi doctor fu'ad yayi gamida da dan buga head d'insa kadan yana fad'in
Sorry fa dad'in girkin ne yasa nake ta surutu ban sani ba , honestly mutumi na yarinyar nan ta tsa moka daga k'angi ta taimake ka yanzu kayi bye bye da ordern restaurant, cikin ta kaici da maganganun Doctor fu'ad yasa Ajmal da katawa da cikin roasted chicken din da yake ya ya b'alli tissue paper ya shiga goge hannayenshi kafin ya koma ya jingina Jikinsa da kujeran yana hararo Doctor fu'ad
' wai ta tsamoshi daga k'angi ta na taimakesa, shi inbama na sihar da Ammi ta yi masa akan yarinyar da kuma nuna tana bukatan mu amalarsu tare ba da mai zaisa ma kafarta ya fara tako side din shi tun kafin zuwanta yana rayuwarsa ba cikin k'angi ko taimakon wani ba zuwanta ba zai canza komai ba kuma k'angi da taimako da yake fadi'n duk wani bauta ko hidama da take da shi biyanta zaiyi dan baya bukatar hidimar da ta ke masa a kalle shi a fiskar taimako ko fita daga k'angi,' Doctor fu'ad ganin kallon da Ajmal ke yi masa yasa shi ya saki sakin murmushin kasa kasa
"Naji kana tambayar ta ya jiki mai ya sa me ta" Ajmal ke tambayar doctor fu'ad because kasan cewarta a k'ark'ashisa zaiso sanin damuwa ko matsalarta, zame hanu Doctor fu'ad yayi shima ya shiga goge hannayenshi kafin ya gyara zama yana fad'i
"Eh to da farko dai a sumammiya naje na sa me ta Ammi da kammala suna ne suke kaiwa da kawo bisa kanta but da na duba ta bakomai bane fa ce tsorita ne da firgici duba da yanda zuciyarta ta ke bugu yana kaiwa da kawowa shiyasa mu likitoci muke da d'a wayar da kai ba kowace irin magana akeso adinga fad'awa mutum kai tsaye ba ko ya tsinci magana kamar daga sama ma'ana baiyi zato ko tsammanin jin maganar ba especially mutum mai saurin razana tsoro ko firgici ba kasan halinda zai fada ba like ita Nisha ,.
" Ammi Kamal? su sukayi coursing matsalar kakeso kace" Ajmal ya tambaya yana mai tsare doctor fu'ad da manyan idanuwansa
"Kusan haka but Ammi ta fada min dalilin faruwan hakan wanda lamarine da ya shafi tsakanin ka kai da Nisha , is very confident Ajmal ya gyara zama yana fad'in
"Ina jinka banaso kana tsayawa yayin maganar ka dunkule min zance cikin kalama daya," murmushi Doctor fu'ad yayi gamida fadi'n
"Bana tunanin zai dunkulu ta kalma daya shi yasama banso na sanar dakai yanzuba because banzo da Shirin yi maka bayani yanzu ba nayi tunanin wa re wani time da ban dan tattauna maganganun because tattaunawar is very important cikin rayuwarku kai da ita but why not na sanar dakai yanzu nasan zaka saurareni kuma zaka fahimce batuna kuma ka dau shawaran da zan baka, ".
Ajmal ya k'osa ya ji kan zance but shi kuma doctor fu'ad sai dugun ba yani yake da ma fa matsalar su kenan likitoci nan ba zasu tsaya su maka zance kai tsaye ba sundinga kwane kwane kkenan harsai mutum ya hasala
"Look idan zancen ba fa'idar na sani kabarshi kawai ina da abubuwan yii" Ajmal ya fad'i ciki takaici da bacin rai ya mike yana kokarin tafiya cikin hanzari doctor fu'ad ya kamo hanun Ajmal yana fadi'n
"I'm sorry mutumina zauna na maka bayani" because yasan halin mutumin da saurin hasala komawa Ajmal yayi ya zauna cikin hade gira ya ce
"I'm hearing you talk " cikin na tsuwa tare da kawar da wasa alamarin doctor fu'ad ya shiga zaiyyanu zantuka da labarain da ya samu da Ammi game da batun auransa da Nisha,..
______Tun bayan da Nisha ta fito da ga side din Ajmal ta nufi sashinsu a kokarin ta na shiga parlourn time d'in kamal shima ya sako kai da nufin fitowa nan suka game da juna gefensa dauke da Nabilah wacce ke biye da shi , ganin su da tayi sai da kirjinta ya d'an buga. ja ba ya Nisha ta yi ta matsa gefe kad'an tana kallonsu, Kamal fiska dauke da murmushi ya suma tambayar ta
"My sister! Ke muka shiga dubawa yanzu but ba mu tadda ke ba.
" Ya jikin naki" Kamal ya ya tambaya yana duban Nisha cike da murmushin nasa da baya yanke sai wani ikon Allah
"Da sauki Nisha ta masa cikin sanyin murya, jinjina kai kawai Kamal yayi yana fadi'n
"Masha Allah haka akeso" kafin ya juya ya kai kallonsa ga na Nabilah gamida fad'in
"Ni zan wuce sai na dawo take care of yourself" g'yada masa kai Nabilah tayi tana fadi'n
"Allah ya tsare"
Daga haka Kamal ya wuce ya nufi compound d'in gidan daidai parking space ya shiga motarsa tare da yi mata key mai gadi yabude masa geat yafice. har yabar ha raban gidan Nisha binshi da kallon ta fad'a tunani ba k'aramin mamaki Kamal ya ba ta ba kwata kwata ba wata damuwa kan face d'insa gani tayi duk tafishi shiga da muwa da kad'uwa, but shi hankalinsa akwance yake kamar ma ba shi da wani damuwa.
'kodai kwai da ma wasa yake da hankali da tunaninta ba wani sonta ya ke ba but ya cusa mata soyayyarsa da ra'ayinsa da sha'awar fara sabowar rayuwa tare da shi ' jin anruko hannayenta yasa ta dawo cikin hankalinta da tunanin da ta ta fi time din idonuwanta har sun ciko da k'walla tab.
Nisha kallon Nabilah tayi wacce ke rike da hannayenta duka biyu tana kallonta cike da murmushi tana fadi'n
"Idan ban ta kura kiba inaso mu dan tattauna wasu maganganun da ke amma fa in ban shiga time d'in ki ba, girgiza kai Nisha tayi tana fadi'n
bakomai" still Nabilah ba ta da ke hannun Nisha ba fiiiii Nabilah ta ja hanun Nisha suka nufi sashinta.
Ko bayan da suka karisa shiga parlourn Nabilah ta zaunar da Nisha bisa kujera kafin Nabilah ta koma dining area ta hadu musu coffee ta dawo ta mikewa Nisha cup d'in zazzafan coffee shekeke Nisha ke bin Nabilah da kal kafin ta karbi cup ta rike still idanuwanta ba su dainabin Nabilah da kallon mamaki ba ita kuwa Nabilah sai murmushi ta ke ta zubawa Nisha kafin itama ta nemi guri kusa da ita ta zauna tare da kai coffee d'in cup bakinta.
Sai da ta kurb'a zazzafan coffee d'in kafin ta kalli Nisha wacce ta sa ke baki ta na kallonta kamar hoto ta kasa shan coffee d'in da Nabilah ta ba ta
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.