Complete Hausa Novels

Ajeemal Book 2 Complete Hausa Novel

Reading file: Ajeemal_Book_2_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 15 of 24

Dan muskutawa Ammi tayi tagayara zama kafin takalli doctor fu'ad wanda ya mata zoro yana sauraron abinda zata fad'i, doctor fu'ad kai ba mutumin da za abuyewa komai bane, kamar yanda kasani shekarun baya da suka wuce Hajj mama itace silan hada auran Ajmal da Heelah , to halinda ake ciki yanzu wasu kwanaki dasuka wuce Hajia tasake hada auran Nisha da Ajmal but tayanke hukunci ne cikin bacin rai bisa rashin kunya da rashin girmamawa da Heelah da mahaifiyarta suka zo suka gabatar kwanakin baya akan wata yar hatsaniya da ya faru tsakanin Raheelah da Nisha nan Ammi tashiga korawa doctor fu'ad yanda lamarin yakasance da kuma dalilin da yasa Hajia ta zarta da wannan hukunci ba tareda tayi la akari da afkuwan wani matsalaba
dan kauda kai Ammi tayi tana murza hannayenta irin na shiga damuwa tace,"

"Duk tsawon kwanakin nan inata kokarin na fahimtar da ita cikin natsuwa bisa auran Ajmal da ke kanta amma senaji nakasa maganar tayimin nauyi because bansan da wani ido zan kalletaba kuma bansan wani irin kallo zata mana ba bisa amanarta da mukaci nadaura mata aure da da' nmu ba tareda yarda ko amikamatrta ba , sam bamu san Kamal yana da ra ayi akantaba se yanzu yasameni da batun soyayyarsu wanda yanzu shiyayi causing wannan problem din banso ta tsinci lamarin ta wannan sigarba, Ammi tafad'i tana sunnar da Kai kasa ,

wani goron numfashi doctor fu'ad ya sauke tareda jinjina kai yana mai mamakin lamarin, yama rasa tacewa but tawata fiskar yaji dadin kasan cewar hakan because tun randa yafara ganin yarinyar ya yabawa hankali da nisuwarta koma ba komai yasan zata kula dashi sosai fiye da tuna ninsa to amma yanda zai karbeta amatsayin mata yake tunanin because koda yakarbeta amatsayin mata yasan Nisha bazataji dadin zama dashi especially yanda bai gama gamsuwa da itaba, dan gyaran murya Doctor fu'ad yayi kalli Ammi yana fadi'n

"Amma senake ganin kamar bai kamata acigaba da boye batun aure tsakaninsu ba duk da ita Nisha tasani yanzu shima Ajmal yana da hakkin yasan nauyin da aka daura masa or yayi accepted or rejected dan haka boyewa bashi dawani fa'ida kamata yayi yayi azauna dasu ko duk susan matsayinsu wannan shine shawaran da zan iya bayarwa doctor fu'ad ya fad'i yana kallonsu Ammi da kamal wanda yayi zoro daga gefe yana jimami, dan gyada kai Ammi tayi alamar gamsuwa da maganar tashi batare da ta iya sake cewa komai ba,

"so nizan wuce zuwa gobe zandawo naga yanayin jikin nata duk da ba wana matsala bane kawai tsoro da firgici ne yayi causing," doctor fu'ad ya fad'i tareda mikewa nan idonsa yasauka kan su Fadeelah da Reeda wanda suke tsaye bakin door Wanda basu ankara da suba balle susan da tsayuwarsu sungama jin komai jikinsu duk asanyaye cikin sauri suka kariso ciki suna kokarin nufa bedroom din dan ganin halinda Nisha ke ciki cikin hanzari doctor fu'ad ya dakatar da su gamida fad'in,"

"Please karku dameta yanzu because tana bukatan hutu, so kudan kara hakuri"

jiki ba kwari suka nemiguri kusa da Ammi suka zauna suka sanyata tsakiya kowaccensu tajin gina head dinta jikin shouldern Ammi cikin damuwa, doctor fu'ad binsu kawai yayi ganin yanda sun wani lagwabe jikinsu duk yayi sanyi dan girgiza kai yayi daga bisani yayi sallama da Ammi yafice Kamal ya rufa masa baya jiki amace, seda Kamal yaraka doctor fu'ad harbakin motar sa kafin sukayi shaking hand doctor fu'ad ya shige motarsa yamata key mai gadi yabude masa geat yafice daga bisani Kamal shima ya juya cikin gidan direct part dinsa ya nufa inda ya iske Nabilah bisa sofa tana danna wayarta jin motsin shigowar Kamal yasa tamike cike da murmushi but lokaci daya kuma murmushin ya kawar kan face dinta ganin Kamal cikin wani yanayin wanda bata saba ganisa cikiba,

Direct bedroom taga yajufa ko inda take bai kallaba aikuwa cikin sauri itama ta tashi tabi bayanshi, koda tashiga bedroom din bakin bed taga ya yazauna yayi juguk dashi hakan yasa Nabilah karisowa inda yake tadurkusa saman carpet tadaura hand dinta saman cinyarsa tashiga tambayansa meke damunsa amma se shiru yayi bai kulataba,

" Please ya Kamal kafada min meke da munka ni matace agareka bai kamata kaboyemin matsalar data damekaba"

"ko nice nayi wani laifin ban saniba kasanar dan" ganin yanda take masa magiya duk tashiga damuwa ganinsa haka yasa yace

"Please Nabilah banason yawan tambaya ni ba abunda yake damuna so kidena damun kanki" yana fadi'n haka yamike yanufi toilet jiki ba gwari Nabilah tamike tafito daga bedroom din takoma parlour tanemigu tazauna tana tunanin meyeke damun Kamal taganshi cikin wannan halin, jim kadan taga ya fito cikin wani shirin ya fice ba tareda ya kalletaba balle yace mata wani abin, komawa tayi ta kwanta kankance me hawaye suka shiga zarya cikin idanunta sam bataji dadin kasan cewar sa cikin wannan yanayin ba to kowani laifin tayi masa bata saniba kamata yayi yasanar da ita ba yadau zafi hakaba,.

Guraren karfe 9 na dare Nisha tasaki wani dugun nufashi kafin tashiga kiciniyar bude ido seda takarewa bedroom din kallo sannan tasauke ajiyar zuciya tadauka zata bude ido ta ganta agushewarta because yanda zuciyarta wani buguwa da karfi time daya sam ba tayi tsammanin bude ido ta ganta araye ba dakin shiru yake ba kowa sai ita kadai dake kwance anrufeta da blanket, yaye blanket din tayi ta mike zaune ta najin yanda kanta yai mata nauyi tamkar an aza mata kaya maganganun Ammi ne ya shigadawo mata cikin kai yana mata yawo cikin kwakwalwarta, cusa kanta tayi tsa kan kanun kafafuwanta tashiga rera kuka har da shashsheka.

Ringin din k'aran wayarta ne yasa ta tsagaita da kukan ta shiga leka phone dinta daketa faman ruri saman bedside table but kafin ta dauki phone din I kiran ya katse jawo wayar tayi tashiga duba mai kiran 5 miss call tagani daga kawarta salma wasu sabbin hawayene suka sake kwaranyo mata ganin k'iran salma wacce ta turo mata da IV dinta tun last week auranta cikin wannan week din Nisha ba k'aramin buri ta ci ba na auran kawarta salma sai dai kafin auran salma ita andaura nata auran wani sabon k'iranne ya kuma shigowa Nisha kamar baza ta daga k'iran ba saboda yanayin da ta ke ciki bazata iya magana ba harya kusa katsewa sannan ta dauka tare da kara wa akunne ba tareda ta ce komai ba,

"Haba Nisha tun yaushe naketa kiran wayanke ba kya picking kuma baki biyoniba ni ba wannan ba yaushe za ki zo ne because ya kamata a fara komai dakefa"

" Hello wai ko ba kya ji nane kam "salma ta tambaya jin shiru ba magana sai shashshekar kuka da ta ke ji kasa kasa

"Wai mai yake faruwane Nisha naji kinyi shiru inata magana kinyi shiru qalau kike kuwa, ?" dib Nisha ta katse wayar ta sake phone d'in saman bed tashiga rera wani sabon kuka ta na cikin wannan ya nayin sai ji tayi anturo door ana kokarin shigowa wanda yayi saurin mayar da ita sense d'inta cikin hanzari tashiga goge hawayen face d'in ta ta koma ta kwanta ta rintsa ido kamar mai bacci, cikin natsuwa HAJIA ta turo door ta shigo hade tura kofar ta rufe, girgiza kai Hajj mama tayi ganin Nisha kwance yanda suka barta kamar mai bacci saka makon zuwan ta bakin door din ta jiyo sautin shashshekar kuka wanda kuma Nisha ce keyi karisowa tayi kusa da bakin bed d'in ta zauna tare da shafo kan Nisha tashiga fadi'n

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.